Sashe 37
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba karamin mamaki yayi ba da yaga ta soma hawaye da gaske tana buga kafa. Baka ga yadda na dade ina yin kwalliyar nan ba shine zaka ce banyi kyau ba. Hankalinsa ya tashi ganin tana kuka yace wasa fa nake miki. Hannunta ya ja ya zaunar da ita a kan cinyarsa a kujerar yace haba Cutie ke kin fiye rigima. Meye abin kuka don na dan tsokaneki. Zuhra ta wani shige jikinsa duk ta kunyar da take ji...to ni ba yau saboda kai nayi kwalliyar ba amma baka ce nayi kyau ba. Hannu ya kai yana shafa gashinta da yake ta sheki...da gaske ni kika yiwa kwalliya? Me yasa?
Fuskarta ta dago tare da ware idanunta hawaye na fita ta gefe amma murmushi take yi. So nake na nuna maka nagode da ka zama yayana kake kulawa dani yanzu. Ya Hamza bazan taba mantawa da kirkinka ba a rayuwata. Allah ne Ya hadamu don ka zama yayana ka canja min rayuwa. Sai kuma ta dan harare shi...amma kaga nan, ta nuna lips dinta. Bazasu manta da yadda suka sha dalli a wurinka ba. Kai Ya Hamza ka iya cin zali ko sannu baka taba yi min ba. Komai Zuhra tayi burgeshi take yi, yayi dariya yanzu yanzu kike yabo na kin koma korafi. Turo lips din ta kara yi.... gasu ka basu hakuri sai na janye korafin. Yace naki, lokacin ba tsiwa kike min ba. Wani hawayen yaga ta soma yace oh Cutie baki san wasa bane..to rufe idonki na baki hakuri.
Ba musu Zuhra ta rufe ido tana murmushin jindadi zai bata hakuri. Abinda bata taba tsammani ba yayi mata. Da farko ji tayi kamar ya dan shafasu da dan yatsansa har tsigar jikinta ta tashi sai dai kafin ta gudu ya hade bakinsu wuri daya. Kissing dinta yake sosai ta kasa koda kwakkwaran motsi saboda yanayin da ta tsinci kanta. Hamza bai barta ba sai da suka kusa minti biyar a haka yana bin har wuyanta da duk fuskarta yana kissing. Kiran sallar Magriba ne yasa ya kyaleta ba don yaso ba. Kasa kallonsa tayi harda rufe fuska da hannuwanta. Ya Hamza duk kasa ni jin kunya, ni daga yau ko kallonka bazan iya ba. Murmushi yayi mai nuni da tsantsar jindadi da kaunarsa gareta sannan ya sauke mata hannun da ta rufe fuska. Gira ya daga mata kinga kujerar nan ya kamata ki bata mahimmanci a rayuwarki. Kanta a sunkuye tace meyasa? Idanunsa a kanta yace saboda a kanta Ya Hamza ya fara kissing din Cutie kuma yasan taji dadi.
Tsananin kunyar da taji yasa ta tashi da gudu ta bar falon. Dariya yayi shima ya tashi yaje yayi alwala ya tafi masallaci.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 57
Batul Mamman(Mrs)
Tare ta hada musu abinci bayan isha ta kai falonsa. Dariya yayi yace har kin gaji da wasan buyan ne? To karaso sai ki bani a baki. Dan harararsa tayi Allah Ya Hamza zan tashi. Haka kawai ina zaman zamana kasa duk minti daya sai nayi tunaninka sai naji kamar na tona kasa na shige. Hannunta Hamza ya kama yana mata wani kallo kasa kasa, Cutie da gaske kina tunani na? Tell me, me kika fi tunawa. Sunkuyar da kanta tayi kasa tana wasa da yatsun hannunta. Yace nifa bana son gulma, yarinya taji dadi kina so kina kaiwa kasuwa. Bari muci abinci ni yunwa nake ji sai mu koma kujerar tamu ko. Naga kamar karatun yayi miki dadi.
Karshen kunya dai Zuhra ta gama ji ko kanta ta kasa dagawa. Shi kuwa Hamza yana sane yake ta tsokanarta, dariya ma yake mata. Kasa cin abincin tayi ta tashi zata fita. Yace ina kuma zaki? dawo kinji, na dena tsokanarki. A kunyace tace kayana zan kwashe daga dakinka tunda gobe su Khalifa zasu dawo. Damuwa karara ya gani a fuskarta, yasan ba dawowar su Khalifa kawai take son cewa ba. Har inda take tsaye yaje ya riko hannunta suka dawo suka zauna. Cutie kina tunanin idan Izzy ta dawo zan tashi daga Ya Hamzanki? Daga kan da zata yi kawai sai kuka ya kwace mata. Dama ga ciwon mara da ya fara matsa mata sannan ga shagwaba. Kuka take sosai Hamza yana ta aikin rarrashi. Da kyar ya samu tayi shiru ya dan ja hancinta. Cutie baki da dama, daga magana sai kuka. Tace to irin yadda kake yi min da zaka cigaba idan ta dawo? Hamza yayi murmushi ganin cewa Zuhra ta damu dashi. Kada kisa komai a ranki na damuwa. Idan ta dawo zan raba muku kwana saboda bamu gama lessons dinmu ba, ya fada yana murmushi. Ranar girkinki zaki yi abinci dani kuma zaki kwana a dakina. Ya danyi dariya nasan kwanciya kusa dani ne bakya son denawa shine harda kuka. Yarinya ta soma sabawa da jin dumin maigida a kusa da ita. Ji tayi kamar ta nutse a kasa don kunya kawai sai ta soma salati, ni kada kayi min sharri bayan kaine da ka ganni sai ka rinka wayon taba ni. Yace karewar tabaki yau da kaina zanyi miki wanka. Jin haka yasa ta tashi da gudu ta barshi shi kadai.
Wurin su Hamida ta koma suna ta hira suna bata labarin samarinsu Haidar da Yasir. Zuhra tace kuce mun kusa shan biki. Haka suka cigaba da hira cikin nishadi hankalin Zuhra a kwance Izzatu bazata dawo da wuri ba. Saboda yadda take fargabar dawowar Izzatun har mafarki tayi wai ta dawo Hamza ya koma yadda yake da.
Mararta ce ta soma murdawa sosai hirar ta soma gagararta. Adabiyya ce ta kula da yadda take rike ciki tace Anti Zuhra tun dazu na kula kamar baki da lafiya. Tace marata ce take ciwo bari naje na kwanta. Bayan ta hau sama Hamida tace ikon Allah naji ance da anyi aure ake dena ciwon nan kinga har yanzu bata dena ba. Adabiyya ta kai mata duka to uwar tsurku. Amma seriously naji wasu sunce idan mace bata dena bayan aure ba tana haihuwar fari take denawa.
Wanka Zuhra tayi da ruwa mai zafi sosai sannan ta fito ta shirya cikin kayan bacci riga da dogon wando na cotton. Yanzu dai bata sake da kamshi bare kuma ana period dole duk mace ta kula sosai da kanta. Gado ta hau tana juyi saboda ciwon ya fara yawa. Duk wata a gida haka take fama ranar su Umma basa samun baccin kirki.
Har shabiyu saura Hamza na aiki Adabiyya ta leka tace masa sai da safe saboda an dauke wuta. Yace yau anyi abin kai baku jira nazo na tasheku ba. Ina Antin taku? Hamida ce ta bashi amsa, Yaya ta tafi daki tun dazu bata da lafiya. Kashe laptop din yayi ya taso meyasa babu wanda ya fada min a cikinku. Suna soma hawa sama maigadi ya tayar da inji. Hamza ya rufe ko'ina ya wuce dakinsa.
A kan gadon ya hangota ta nade wuri guda yayi zaton bacci take yi ya je yayi wanka. Yana cikin saka kaya yaga sai juye juye take tsakanin bangaren hagu da dama tana rike da ciki. Rigar ya fasa sakawa ya zo ya dafa bayanta. Cutie me ya sameki? Baki da lafiya kuma shine baki fada min ba. Cikinta ta nuna masa tana kokarin tashi zaune. Shi kuma ya taimaka mata ta tashi yace murdawa cikin yake yi? Ko toilet zaki je bari na taimaka miki. Baza'a rasa flagyl ko imodium ba a cikin first aid box. Takaici ya kama Zuhra me yake nufi da cewa cikinta ya murda, wato a tunaninsa...... kai amma ya cuceta da zaiyi wannan tunanin. Yana kokarin dagata muje na kaiki toilet ta dage ta doke hannunsa harda zumbura baki tace ni ba ciwon shiga toilet nake yi ba. Hamza yace oh kina fama da ciwo kina tsiwa. To me ya same ki? A hankali tace marata ce take ciwo. Yace sai kice min period pain ne, ko muje asibiti? A'a zuwa safiya zai dena ta amsa da 'yar kunya. Gyara mata kwanciya yayi sannan shima ya kwanta a kusa da ita yana mata sannu. Kusan minti shabiyar ciwon ya lafa daga baya ya dawo sosai. Hamza ya rasa me zaiyi mata taji dadi hawaye take yi kawai abin tausayi. Ko kula da cewa babu riga a jikinsa ma bata yi ba ciwo ya isheta kuma tace ita babu maganin da take sha har ya dena.
Ruwa ta bukaci sha ya tafi ya debo mata a dispencer din falonsa. Tana gama sha tace Ya Hamza...yes Cutie me kike so? Tace zaka shafa min bayana. Tausayinta ne ya kamashi ta kwanta ruf da ciki ya rinka shafa mata bayan a hankali. Kamar zata yi bacci amma kwanciyar taki dadi ta sake juyawa. Ya Hamza...dan kwanciya yayi ya rankwafo kusa da ita. Yace ina jinki Cutie na, me kike so? A dan kunyace tace zaka shafa min cikina? Umma tana yi min a gida ina jin dadi. Ji yake kamar ciwon ya dawo jikinsa ta dena hawayen da take yi. Hannunsa ya dora akan cikin ya soma shafa mata a hankali. Da ta gaji sake kwanciya tayi ta tura pillow kasan cikinta. Shi dai Hamza duk abinda tace haka yake mata. Daga baya ya dage sai sun je asibiti tace a'a zata warke zuwa safiya. Ba su suka yi bacci ba sai wurin hudu. Ta riga shi yi ma ya gyara mata kwanciya a jikinsa shima yayi.
Ana asuba ya farka ya tafi masallaci. Da ya dawo ya kwankwasawa su Adabiyya kofa ya sanar dasu su hada breakfast harda maigadi Zuhra bata jindadi. Doguwar rigarsa kawai ya cire ya dawo ya kwanta. Cikin 'yan mintuna bacci mai nauyi ya dauke shi. Ba su farka ba sai shabiyu saura. Zuhra ce ta fara tashi ta ganta kwance a jikinsa kamar wata mage. [10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 58