← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 67

Sashe 36

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wani daki ake yin lallen Zuhra tabi bayan Sa'adatu ta shiga. Ai kuwa mutum daya suka tarar ana tsara mata ado sosai. Sa'adatu tace ni dai kada kiga ina ta kallonki wallahi kamar na taba ganinki a wani gida. Zuhra tace kila mun hadu, a wace unguwa ne? Sa'adatu ta soma bata labarin wasu da suka tare a unguwarsu ana walima aka yiwa wata April fool. Wallahi sai kuke dan yimin kama da yarinyar duk da ba kare mata kallo nayi ba. Murmushi Zuhra tayi sannan tace nice yarinyar. Sa'adatu ta bude baki don Allah da gaske? Ana ta rade radin mijin matar ya auri yarinyar. Don Allah ke ce? Zuhra tayi ajiyar zuciya. Nice, har an kusa wata biyu da auren. Sa'adatu tace lallai Zuhra rayuwarki ishara ce ga wawayen mata. Duk yawancin matan unguwar nan da Izzatun nan ta gayyata walimar tarewarsu sai da suka zageta ranar da abin ya faru. Yadda kika san kanwata aka yiwa wulakancin nan, har maigidana na bawa labarin abinda ya faru. Mai lallen ce ta fita karo leda Sa'adatu ta matso kusa da Zuhra. Ko baki fada ba nasan aurenku da mijin Izzatu bazai zama na jindadi kamar na kowa ba duba da irin abinda ya faru da farko. Amma zan baki shawara ki rike mijinki sosai yadda har abada idan Izzatu ko mai hali irin nata tayi niyyar daukan al'adun wasu zata sake tunani. Kinga yau muka fara haduwa amma haka kawai naji ina sonki da alkhairi. Zuhra dai sai murmushi take yi. Auren da yake da lokacin karewa wane rike miji zata yi?... Sa'adatu tace kina son mijin naki? Kanta ta sunkuyar kasa kawai tana murmushi. Ai an gama wannan murmushin naki ya isheni amsa. To kalleni da kyau bari na koya miki karatun saye zuciyar mijin matar da bata san inda ke mata ciwo ba. Ina ma da Ummu Sudais muka zo wurin nan. Don baki ga yadda tafi kowa jin haushi ba ranar. Kada kiga kamar cin fuska amma ko ba'a fada ba wayewarki da ta Izzatu ba daya ba. A irin haka tayi miki wayo har hakan ta faru. Abu na farko da nake so dake shine daga yau mijinki ya ga kin canza masa gabadaya. Canji irin wanda zaisa ko fita yayi yana tunanin Zuhra a gida. Ki rike TSAFTA sosai domin ita ce abu na farko da kowane miji yake nema daga matarsa. Duk kyaunki da iya kwalliya idan baki da tsafta ko jiki na wari miji bazai so kusantarki ba. A hankali kuma zaki fice masa a rai ya fara neman wata. Na biyu ki iya KWALLIYA irin ta zamani amma fa ba mai yawa da za'a kasa ganeki ba saboda tsabar fuska tasha fenti. Na uku SHAGWABA,Zuhra ba sai na bata lokaci ba a nan. Duk mijin da zaki mayar da kanki yarinya a gabansa dole ya soki. TATTALI DA ADANI yana da kyau ga dukkan matar aure. Babu namijin da zai so ya auri matar da take da almubazzaranci. GIRMAMA IYAYE da son 'yan uwan miji shima yana karawa mace daraja a idon mijinta. IYA ABINCI wannan kowa yasan shine jigon dorewar zaman lafiya a gidan aure. KULAWA, maza nason mace ta kula dasu tamkar yara kamar yadda muma muke son hakan. Ki rage kunya domin ba'a son don kinyi aure ki ajiyeta gabadaya, ki nunawa mijinki so da kauna ta sigar da zai manta da yadda ya auroki ya rike ki da zuciya daya. Ke kike aurensa saboda haka kinsan bukatunsa, idan baki sani ba kisa ido sosai ki nemi soyayyar mijinki da gaskiya. Abu na karshe kuma mafi mahimmanci shine ki rike ALLAH SWT DA MANZONSA SAW, idan kika yi haka to in sha Allahu komai zai zo miki da sauki. Mu 'yan unguwar nan duk 'yan bayanki ne wallahi. Abinda duk ya shige miki duhu zan baki numberta sai mu rinka zumunci.

Zuhra tsaf ta nade shawarwarin Sa'adatu tayi mata godiya sosai. A ranta ta kudurce in Allah Ya yarda zata yi iya kokarinta taga cewa Hamza bai saketa ba domin tsakani da Allah tasan tana sonsa. Karshe ma sai kafin a fara lallen tace ita gyaran jiki zata fara yi tunda suna yi. Bayan an gama aka yi mata lalle da retouching. Idan kaga Zuhra sai ka zata ba ita bace jiki sai sheki yake don ma na rana daya tayi. Hamza sai waya yake Adabiyya na dauka tace ba'a gama ba har sai da ransa ya baci yace wane irin abu suke yi a wurin. Sai karfe biyar Zuhra ta kira shi lokacin ya dade da komawa gida. Yaso yi mata mita sai dai tana zuwa gaban motar ta daga masa hannuwanta tana dariya.. Ya Hamza lallena yayi kyau? Fasa fadan yayi saboda yayi kyau din. Baki da ja aka yi mata tamkar wata amarya. Hamza na son mace tayi lalle amma Izzatu tace kauyanci ne shiyasa bata sake yi ba tun na aure.

Wai ya labarin Izzatu a Kaduna???
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 56

Batul Mamman(Mrs)

Izzatu na tsaye akan Tala ta gama hada kayan su Khalifa suna ta shiri washegari zasu koma Kano. Tuno babban dalilin da zai kaita Abuja tayi tace kinga Tala ki hada harda kayan Nana ku tafi tare. Ga wannan wayar zan rinka kiranki akai-akai kina sanar dani abinda ke faruwa a gidan. Nasan babyna bazai kula wannan yarinyar ba amma dai ki sa ido kafin na dawo. Ki rinka yi masa girki saboda nasan ya wahala a siyan abinci kwanakin da bana nan. Tala tace to Maman Khalifa. Izzatu tace ba to ba aiki zaki min. Idan kika ga zata shige masa ki hanata ni na baki wannan damar sannan ki kular min da yara bana son suna cin kazantar da take kira abinci. Sosai ta karantawa Tala dukkan abinda take so tayi mata idan ta koma. Daga nan suka shirya aka tafi kai amarya. Sai da suka kaita akayi sallar magariba suka shirya aka tafi dinner wadda ango ya shirya.

Ko wanka Zuhra bata yi ba da suka koma gida sai da tayi sauce din hanta wanda yaji albasa da kayan lambu sannan ta dafa farar shinkafa. Harkar girki duk aikin Anti Faiza ne shiyasa take son yi mata siyayya mai kyau idan zata je gidanta. Hamida da Adabiyya sun tayata suka hada komai sannan aka fara layin wanka. Zuhra kayanta ta dauka ta fita ta tafi dakin Hamza. Yana falonsa yana aiki shiyasa ta shiga kai tsaye.

Bata dade da shiga toilet din ba ta fito zuciyarta babu dadi. Tasan yau da kyar zata sami bacci tunda abin yazo. Matsanancin ciwon mara yake saka mata. Dama kwana biyu kenan tana jin alama. Dakinta ta koma ta dauko pad sannan ta dawo ta shiga wanka. Lallenta ya kara yin fes dashi. Harda humra ta dauko a dakinta tabi duk jikinta ta shafa musamman cinyoyinta. Sannan ta fesa turaren jiki kala daban daban. Dogon skirt ta saka baki mara fadi don ya kama mata jiki sannan tasa wata jar top itama ta kamata sannan hannunta dan iya kafada kawai ya rufe. Sake fesa turare tayi sannan tabi gashin nan da yasha gyara tayi styling dinsa. Ta taje shi baya ta zubo da wani ya rufe mata rabin fuska. Juyi ta rinka yi gaban madubi tana yiwa kanta dariyar yadda zata je gaban Hamza a haka. Kwalliyarta ta dan gyara wadda tayi alkawarin mayar da hankali ta kara koya sannan ta fito daga dakin.

Kamar abin kirki har ta fara saukowa ta koma daki neman mayafi. Ai da kunya taje gaban Ya Hamza a haka. Tana shiga dakin su Adabiyya suka fara yaba kyan da tayi. Karfafa zuciyarta tayi ta bi bayansu suka sauka.

Sai da ta dan tsaya a kofar falon tana tunanin da tadda zata shiga a haka. Daga baya dai ta tuna yanzu dama ce ta samu da zata yi kokarin samun soyayyar Hamza idan ba haka ba nan da 'yan watanni sunanta bazawara. Muryarta a can kasa tayi sallama sannan ta shiga ciki. Hamza na zaune a kan wata kujera irin mai juyawar nan a gaban wani table daga karshen falon yana aiki a computer. Bayansa take iya gani shima ba tare da ya juyo ba yace ni yau munyi fada Cutie. Duk sai shareni kike yi tunda muka dawo sai yanzu zaki zo. A hankali take tafiya tana gwada yadda taga mata masu ji da gayu suna tafiya. Ta hadu dasu kala kala a salon yau. Cikin nutsuwa ta karasa kusa da shi kamshinta mai dadi ya sanar masa da isowarta. A daidai bayan kujerar ta tsaya tace Ya Hamza bazaka juyo kaga kwalliyata ba? Murmushi yayi amma yaki juyowa. Ni lessons din da na koya miki bamu zo kan jan aji ba amma har kin koya. To nima nawa zanyi miki bazan juyo ba. Turo baki tayi ta soma shagwaba....Allah sai ka gani. Ji yayi tasa iya karfinta tana kokarin juyo kujerar. Ko da ta juyo dashi da kyar sai taga ya runtse ido. Duk kiyi ki gama bazan kalleki ba yau. Murmushi tayi sannan ta matso da fuskarta kusa da tashi har yana jin numfashinta. Ya Hamza don Allah ka bude idonka ka gani. Irin kwalliyar da zanyi ce idan na sake aure. Bukatarta ta biya domin tana rufe baki ya bude idanunsa suka sauka a kanta. Ya tsani ta rinka zancen idan sun rabu balle kuma idan tana cewa ga abinda zata a gidan sabon mijinta. Mikewa tayi ta soma juya jikinta a gabansa. So da kaunar Zuhra ke kara karfi a zuciyarsa. Kallonta yake kamar ba ita ya aura ba saboda yadda tayi masa kyau. Da ya kula tana jindadin kallon nasa amsa take jira sai ya dan tabe baki....to,kin so kiyi kyau amma dai da saura. Muryarta kamar zata yi kuka tace da saura fa kace? Hamza yayi murmushi eh mana. Da akan wannan 'yar kwalliyar kika zo zaki dameni.
Chapter 36 · 0% Book details