← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 67

Sashe 26

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari meeting din gaggawa ya kira da dukkan maaikatansa. A nan yake sanar dasu abinda Mr Oscar yayi. Inuwa sakatare yace shi yayi mamaki da ya ganshi a banki amma tunda manaja yace da yardar Hamza aka saki kudin shiyasa bai tayar da zancen ba. Maaikatan suka tambayi Hamza garin yaya haka ta faru yace matsalace ta taso daga gida a lokacin. Yana kujerar tsakaya a conference room din yadda kowa zai iya ganinshi a katon zagayayyen table dinsu yace kada ku damu in sha Allah bazan bari kwazonku ya tashi a banza ba. Sauran cheques din ya nuna musu Allah Yasa na rarraba da guda daya ne Oscar ya dauka ba karamar matsala zamu shiga ba. In Allah Ya yarda zan san yadda nayi na fito da wata miliyan goman da zamu hada musu. Next zuwan Mr Peter kasar nan zamu hada musu kudinsu. Ayyukan gabanmu kuma kunga manyan projects ne. Ina rokon kuwa dage ayi ingantaccen aiki. Sannan ina neman afuwarku na kasancewata shugaba mai sakaci da aiki. Muryoyi ne suka rinka tashi suna fada masa babu komai. Wani yace yallabai irin haka shine yake sa bawa ya kara jajicewa da imani. Ba karamin dadi yaji ba da yadda suka yi masa uzuri. Bayan sun gama tattaunawa addua suka yi aka rufe taron. Shima sai ya sake samun kwarin gwiwa tare da yiwa kansa alkawarin bazai sake basu kunya ba.

Kafin ya koma Izzatu ta gama hada duk kayan da zata bukata na tafiyar. Idan ta tafi sai lahadi ta sama zata dawo. Sannan ta sanar da Zuhra zatayi tafiya. Tala ma ta hada nata kayan dana yara.

Suna zaune a falo daga Zuhra sai Izzatu tace idan mun tafi basai kinyi girki da Sweetyna ba. Zai rinka siyan abincinsa, da zaki yarda ma kawai ki tafi gidanku ki kwana biyu kafin na dawo. Zuhra tace a ranta lallai Izzatun nan ma, daga aure sai tafiya gida a kwana? Wannan ai sai mutane su gane lallai auren babu lafiya. Izzatu tace kinyi shiru ko ba kya son zuwa gida. Nasan dole zaki fi jindadi da sakewa a nan to amma....Zuhra taji haushin maganar tace ba haka bane, su Baba zasu yi tunanin ko akwai matsala. Kinga idan akayi sakin laifinsa zasu gani. Izzatu tayi dan tunani eh haka ne fa. To ki zauna amma ko da wasa kada ki shiga harkarsa nasan shima bazai shiga taki ba don ba sonki yake ba. Murmushi Zuhra tayi tana jin yadda Izzatu ke fada mata bakaken maganganu.

Dubu dari Hamza ya bawa Izzatu kafin su kwanta. Tayi murna amma fuskarta ta nuna ba haka taso ba. Yana daga kwance yace ya akayi ne? Juya kudin take yi a hannu babu komai, nayi tunanin zaka karamin ne saboda yara. Ga Tala zan tafi da ita don ta kula dasu. Tashi yayi zaune ba shiri, da Tala zaki tafi amma baki fada min ba? Tunaninsa bai wuce zaman da zaiyi da Zuhra shi kadai ba na kwana takwas. Izzatu tace da bakinka kace ko unguwa zani na dade na rinka tafiya da ita. To zan sami karin kudin? No, yace tare da sake kwanciya. Bani dasu. Idan kin dawo akwai maganar da nake so muyi. Ta tashi ta saka kudin a jaka. Indai ba Zuhra ka fara so ba ko meye babu damuwa. Hamza ya girgiza kansa kawai ya kwanta, halin Izzatu sai ita. Wato gara duk abinda zai faru ya faru akan ta zauna da kishiya.

Washegari da wuri suka shirya kafin goma duk kayansu suna mota. Suna gama breakfast dreban da yake kai su Khalifa makaranta ya iso. Tare zasu tafi ya dawo a motar haya ya barwa Izzatu motar. Idan sun tashi dawowa ya koma ya dauko su. Har bakin mota Zuhra ta rako su. Hamza ya rungume 'ya'yansa sannan suka wani manne da juna shi da Izzatu ana kiss a gaban mutane. Kunya duk ta ishe Zuhra. Ita kuwa Tala dama ta saba gani. Nan suka tsaya har motar ta fita maigadi ya rufe gate.

Ajiyar zuciya Zuhra tayi tana tausayawa kanta yadda zata zauna ita kadai a gidan. Kasancewar Hamza ba tafiya zaiyi ba bai dameta ba tunda ba harkar juna suke shiga ba. Ciki ta koma zata tafi dakinta Hamza ya shigo yace ki shirya bayan azahar zamu fita. A sanyaye ta dan juyo gida zaka mayar dani? Na fada mata zan zauna a nan saboda kada a zargi wani abu a gida. Hamza yace Izzatu tace ki koma gida ne? Wai ita zai nunawa bai sani ba. Tace eh jiya ta fada min. Dan guntun tsaki yayi. Izzy ta fiye rigima itama. Ki shirya zamu je ki gaisa dasu Baba sannan muje gidanmu. Wani tsalle tayi da yasa ya matsa gefe kada ta bige shi. Alhamdulillah ta fada ta haye sama cike da murna. Wani lokacin sai ya ganta kamar mai hankali, idan abin ya motsa kuma ba kanta. Daga murya yayi yace idan na dawo daga masallaci baki shirya ba an fasa. A hankali tace zaka sha mamaki.

Ai kuwa yasha mamakin domin yana dawowa daga masallacin ya ganta zaune kwam a falo ta gama shirinta. Tuna masa tayi da ranar da ya fara ganinta har ya kusa bigeta da mota. Duk zafin da ake a gari fuskarta sai kyallin foundation take. Tabi girarta da pink din jagira ta gyarata, da yake kayan jikinta akwai green sosai har mayafin haka ta saka green din eyeshadow. Sai yan labbanta da ta zanawa bakin lining sannan ta saka jan janbaki da ya fito sosai. Abin bai bashi dariya ba ma, wannan wace irin kwalliya ce. Mtswwww

Da taji yayi tsaki ga wani kallo da yake binta dashi sai jikinta yayi sanyi. Shi dama bai ma gama shiri ba don jallabiyace a jikinsa. Muje yace da ita yana shirin hawa bene. A tsorace tace ina???? Sama ya nuna mata da hannu. Kawai gani yayi ta durkusa gwiwoyi a kasa idanunta sun ciko da hawaye don Allah kada mu fasa zuwa. Don Allah ka kaini naga Ummana da Babana. Yayi yar dariya au gorin iyaye zaki min? Girgiza kai tayi da sauri a'a Ummanmu da Babanmu nake nufi. Yace to naji tashi muje yana murmushi. Da gaske sama taga zai hau sai ta dan ja baya. Hannunta kawai ya kama ya ja ta suka hau saman tana ta tirjewa. Wani abu yaji ya soki zuciyarsa da ya kama mata hannu.
[9/25, 3:55 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 43

Batul Mamman(Mrs)

Har suka isa gidan babu wanda yayi magana a motar. Ficewarsa ma yayi daga motar ya shiga gidan ya barta. Kwafa tayi sannan ta fito da ledarta a hannu. Hanyar da yabi itama ta bi. Sai ta ganshi a bakin kofa yana tsaye...kinji yadda naji dazu da kika fita baki jirani ba. Bude baki tayi....lahhh wai haushi kaji. Sai kuma yaji haushin kansa meye zai biye mata harda ramawa. Gyaran murya yayu shi a dole a bawa. Shige muje ya nuna mata hanya.

Dakin Mama suka fara zuwa bata ciki. A hanyarsu ta zuwa dakin Hajiya suka hadu da Adabiyya. Wani ihu ta saki tare da kankame Zuhra. Oyoyo Anti Zuhra....Hamida naji ita ma ta fito daga dakinsu suna ta ihun murna Zuhra na murmushi. Hamza yace lallai yaran nan. Kirikiri kun nuna min bakwa son uwar 'ya'yana. Hamida tace to Yaya ai itama ba sonmu take ba. Tana fada ta shige daki da gudu don tasan muguntar dallin bakin da yake mata. Adabiyya ta gaishe shi sannan taja hannun Zuhra suka tafi kitchen.

Hajiya na dora ruwan tuwo suna hira da Mama. Adabiyya na shiga Hajiya tace wato don kada kuyi aiki kunce zakuyi karatun jarabawa sai gashi kun cika mana gida da ihu. Adabiyya tana dariya ta turo Zuhra da ke makale jikin kofa kinga bakuwar da muka yi. Mama ta taso itama tana mata sannu da zuwa. Kasa Zuhra tayi duk ta gaishesu. Ina Yayan naku Mama ta tambayi Adabiyya. Yana wajen dakinku. Fita Mama tayi tace Adabiyya kaita dakinku zata fi sakewa ki kai mata abinci.

Idon Zuhra na kan Hajiya tana bare albasa zata hada ruwan miya. Gabanta ta karasa a kunyace tace Hajiya kawo na yanka miki. Itama Hajiyan ta rasa dalilin da yasa taji kunyar Zuhra kamar yanzu Yaya ya fara aure. Barshi kuje daki da Adabiyya idan na gama zanzo mu sake gaisawa. Adabiyya ta gama hada cup da lemo a tray tace zo muje Antinmu. Zuhra ta mika hannu don Allah Hajiya ki kawo na tayaki. Me zaki dafa nayi miki? Na iya girki fa. Hajiya tayi murmushi tana kallon Zuhra. Mayafinta ta cire ta jefa saman kofar kitchen din. Adabiyya tace don Allah kizo muje idan kika sha ruwa sai mu dawo. Ki tayani zama a nan kawai muyi girki. Ta karbi albasar Hajiya kije ki huta. Sosai Hajiya taji dadi sai dai kuma girkin saboda Alhaji da zai dawo daga Kumo yau take yi. Amma yadda Zuhra ta langabe mata kai yasa ta hakura ta fada mata tuwon semovita zata yi da miyar danyar kubewa wadda tuni Hamida ta gurza. Tana fita Adabiyya tace gaskiya ina taya Yaya murna yanzu yayi aure. Zuhra bata ce komai ba sai dariya tace ta bata roba zata yi rude. Sai ga Hamida da littafi a hannu tace ayi hirar da ita. Sunso sa mata hannu tace ita dai su tayata zama. Komai ta nema zasu nuna mata haka tayi tuwonta wanda ya tuku sosai yayi kauri. A leda ta kulle sannan ta bar ruwan miyar wajen awa daya yana dahuwa wutar kasa kasa yadda Umma ke yi. Hamida tace ita kamshi ya dameta a kada miyar yau tuwo zata ci ba indomie ba. Suna ta barkwancinsu har ta gama hada miyar kitchen din yana ta kamshi.
Chapter 26 · 0% Book details