← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 67

Sashe 13

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata tsawar ya sake yi jeka ka dauko min copy din contract din. Inuwa jiki na bari ya bude wata drawer a cikin office din Hamza ya dauko masa. Karantawa yake yana maimaitawa. Ya dago idanunsa da suka yi ja yace Inuwa garin yaya nasa hannu a takardar nan? Inuwa ya tausayawa ogansa yace ranar da Junior ya karye ne. Nima bayan ka fita na sake karantawa shiyasa na turo maka da text a daren. Hamza yayi saurin dago kai. Text kuma? Eh text na sake maka bayanin contract din ko zaa gyara tun kafin abin yayi nisa. Kuma ka tabbatar min ka karanta. Don kace Hajiya ta sanar da kai na bugu waya ma. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Izzatu kin kasheni shine abinda Hamza ya iya fada a hankali.
[9/25, 3:40 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿20

Batul Mamman(Mrs)💖

Lokacin da suka isa gidan cike yake da mutane tamkar ana biki. 'Yan gidansu Izzatu har da mamanta duk sun zo. Ga kawayenta da makota da wadanda ma ba'a sansu ba 'yan cin ta tsotse. Kannen Hamza kuwa Mariya ce kadai taje sai Ummahani matar Ibrahim. Su Hamida suna Kumo ita da Adabiyya da Nura.

Gidan ya tsaru sosai kana gani kaga gidan babban architect. Sama da kasan ko'ina mutane hawa sukeyi ana kallon yadda aka kashewa gidan kudi. Zuhra sai rakube rakube take yi ita tazo gidan surukai. Anti Faiza tana mata dariya don Hajara ta tsegunta mata zancen kanin Izzatu.

Izzatu na ganinsu sai murna tasa aka shigo da meatpie din aka hada shi cikin kayan rabo. Zuhra ta mika mata kayan sanyi tace bari na dauki miki kudinki. A kunyace Zuhra tace ta barshi. Tayi murmushi ta fita bari a kawo muku abinci.

Hamza ta fita ta kira tana rokonsa yazo gida Mummynta tana son ganinsa. Muryarsa a dashe saboda tsananin bacin ran da yake ciki yace mata ya kusa karasowa gidan. Da sauri ta koma dakin da ta bar su Zuhra tace mata dan sake gyara fuskarki muje. Anti Faiza tace ina zaku ake magana bama ganewa? Izzatu tace sirri ne. Kawayenta na dakin kuwa sun gane suma dariya suke yi. Yan kayan kwalliyar jakarta ta dauko ta sake shafa hoda da janbaki. Fuskar nan ta fita daban da sauran jikinta saboda kyallin foundation. Tun a dakin kannen Izzatu da yayarta Zeenatu ke dariya kasa kasa. Ita kuwa uwar gayya ko a jikinta tace da Anti Faiza yanzu zata dawo su tafi.

Mamaki Hamza yayi yadda gidan ya cika da mutane haka. Yadda yake ji idan Izzatu bata yi da gaske ba zai iya marinta. Sanadiyar bin al'adun wasu ta janyo masa asara mai girma. Ita ta tada masa hankali yasa hannu a takardar ba tare da yasan me yake yi ba. Kuma ta goge masa messages. Tsaki yayi ya shiga gidan ta baya. Wani karamin falon ya shiga shiga ya kirata a waya. Bata kawo komai a ranta ba jin yanayin muryarsa. Burinta kawai taga yadda zasu kwashe da Zuhra idan sun hadu. Its Zuhra zaman jiran da take yi a falo ya fara isarta don ma da mutane.

Da sauri Izzatu tazo da tray a hannunta dauke da juice da soyayyan nama a karamin plate ta mika mata. Muje ku gaisa ku tafi Faiza duk ta damu. Zuhra ta dan gyara mayafi ta karbi tray din. Sai da suka je kofar falon duk taji kunya kamar kada ta shiga. Izzatu ta turata tare da komawa falo tana sanar da mutane su shirya dariya zata yiwa wata April Fool. Mariya na jin haka ta mike da sauri tace da Ummahani kila yarinyar nan ce. Na rasa abinda ke damun Izzatu. Bata kara magana ba suka ji karar fashewar tangaran.

Lokacin da Zuhra ta shiga falon da sallamarta. Hamza ya taso a fusace yana cewa Izzy kinsan abinda kika jawo min yau? Zuhra tayi saurin daga kai suka hada ido, bata san lokacin da ta saki tray din ba. Mutumin nan da ya kusa marinta ta gani. Bakinta har rawa yake tana cewa yayi hakuri ta durkusa tana tsince sauran jug da kofin da ya fashe. Dama a harzuke yake yace me ya shigo dake falona? Waye ya bude miki? Duk ta kidime tace Anti Izzatu ce. Zuwa lokacin kofar falon ta cika da yan gidansu Izzatu har da ita. Sauran mutane ma jin ana daga murya suka zo kallo. Hamza yace ita Izzatun ce ta bude miki falona tace ki shigo. Zuhra tace eh. Hamza na daga murya yace ba kece mara kunyar yarinyar nan ba, wato sata kika zo yi. Da sauri ta girgiza kai tace a'a wurin Hamza nazo.

Daga shi har Zuhra babu wanda hankalinsa ke bakin kofa bare su ga yadda mutane ke kallonsu. Yan gidansu Izzatu da suka san komai sune suke dariyar yadda jikin Zuhra ke rawa. Yace Hamza? To nine Hamzan ya akayi? Zuhra tace ba kai Hamzan ba. Kannin anti Izzatu ne yace yana sona shine yake min tes. Ita tace na zo nan yana jirana wallahi. Hamza ya runtse idanunsa yace idan na bude baki bace min a wurin nan ba sai na bata miki rai. A gigice ta juya ta hango Izzatu. Ta karasa gabanta tace yi hakuri na fasa miki kaya. Amma ni ban gane ba mijinki yace shine Hamza. To waye kanin naki? Wata irin dariya taji sun kwashe da ita suna cewa APRIL FOOL!!!.

Ko da bata gane me suke nufi ba amma dariyarsu tayi mata ciwo sosai. Hawaye kawai take yi ko gani bata yi sosai yadda hawayen ke zubo mata tace Apre..me? Kanwar Izzatu ta sake cewa April Fool. Da wannan fuskar taki kike tunanin yin saurayi dan gayu. Ina ji kuna hirar da matar da kuka zo. Anti Faiza tace Izzatu wai me yake faruwa ne. Na zata kuskure kikayi da kika ce a nan kanin naki yake jiranta. Ba sai kiyi musu bayani ba. Da kyar Izzatu ta tsayar da dariyarta tace ni nake yin text din.

Hamza kallon Izzatu yake yi tana dariya ita da yan uwanta. Sauran mutanen wurin kuwa kadan ne abin ya basu dariya. Sauran tausayin Zuhra suke yadda rashin sani yasa ta fuskanci wulakanci. Anti Faiza ta rungumo Zuhra wadda bata san inda take jefa kafafunta ba. Sautin dariyar da aka yi mata kawai take ji a kunnuwanta. Izzatu ta cigaba da cewa april fool nayi mata na rinka tura mata text din soyayya. Ta zata saurayi tayi har ta amince. Ta dafa kafadar Zuhra ta sake cewa april fool. Kada ki damu it was just for fun.

Saukar mari taji mai kamar wuta a kumatunta kafin Hamza yace kowa ya fice masa daga gida. Mata suka tsaya kallonsa ya daka musu wata tsawa. Ba shiri suka fara bacewa.

Izzatu na dafe da kumatu ta juya taga ba Hamza, Zuhra da Anti Faiza.

Anti Faiza jan hannun Zuhra kawai take yi har suka fita daga gate din gidan. Ummahani ce tayi musu horn Mariya na gaban motar suka ce su shigo. Anti Faiza tace su tafi kawai. Mariya tace kiyi hakuri ku shigo kada a rinka kallonta kinga an fara fitowa..

Anti Faiza tana ta cewa su tsaya zasu sauka a hanya amma Ummahani taki tsayar da motar. Mariya tace ki kwantar da hankalinki zamu kaiki inda za'a bi muku hakkinku. Anti Faiza ta cije lebe tana kallon yadda Zuhra ke zubar da hawaye tace Allah zai isar mana ku ajiyemu kawai ba sai munje wurin yan sanda ba. Ummahani tace gidansu Hamza zan kaiku. Ni matar kaninsa ce, wannan kuma kanwarsa ce. Sai a lokacin Zuhra tace ku ajiye mu don Allah. Mariya ta juyo ta kalleta. Dole Zuhra ta baka tausayi. Wannan karon Izzatu ta wuce gona da iri. Kiyi hakuri mun kusa zuwa gidan. Anti Faiza tace kunga bama son wani wulakancin ku barmu kawai. Ummahani bata tsaya ba sai a cikin gidan don tayi saa an budewa Alh Nasiru gate zai fita kenan suka shigo. [10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [9/25, 3:40 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿21

Batul Mamman(Mrs)💖

Ummahani na tsayar da motar Mariya ta fita da sauri ta tari Alhaji. Su Anti Faiza kuwa fita suka yi daga motar suka yi hanyar gate zasu fita. Muryar dattijo suka ji yace don Allah su tsaya. Kuka Zuhra ta cigaba tana jan hannun anti Faiza. Mariya ta zo gabansu tace don girman Allah ku tsaya. Ba yadda zasuyi dole suka biyo bayanta. Amma duk yadda aka yi Zuhra ta kafe bazata shiga cikin gidan ba. Kukan da take yi yasa Alh Nasiru yace Anti Faiza da ke mata fada ta kyaleta. Sai a lokacin Zuhra ta kalli dattijon. Ko ba'a fada ba tasan shine baban mijin Izzatu saboda sunyi kama. Da sauri ta durkusa har kasa tace ina wuni? Lafiya kalau ya amsa fuskarsa dauke da murmushi. Kallonta yake yadda take goge hawaye da majinar fuskarta da dankwalin kayanta. Sannan ta nade kanta da jikinta da katon mayafi.

Suna nan tsaye Mama da Hajiya suka fito tare da Mariya. Hajiya tace yanzu Mariya ke fada min munyi baki kuma wai sunki shigowa. Anti Faiza da Zuhra suka gaishe su. Mama ta ce ya naga bakuwar na kuka Allah Yasa lafiya. Alhaji yace Mariya ta dan soma fada min. Ku daure mu shiga ciki. Mama ce tazo ta kama hannun Zuhra ta tayar da ita suka shiga cikin gidan ba don tana so ba.
Chapter 13 · 0% Book details