Sashe 23
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hamza na ganinta yayi saurin ture Izzatu tare da yi mata tsawa. Idan kika kuskura kika ce iskanci sai na dalle miki baki. Kina hauka ne zaki shigo mana daki babu sallama. Izzatu ta sake rike shi ni na kirawota baby. Rigarsa ya dauka ya saka gaba a baya saboda kunyar da yaji Zuhra ta ganshi a haka. Sabon raini zai shigo kenan.
[9/25, 3:53 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 36
Batul Mamman(Mrs)
Bakin kofar Izzatu taje ta riko hannun Zuhra suka shigo cikin dakin. A gefen gado ta zaunar da ita, mugun kallon da Hamza ya watsa mata yasa tayi saurin zamewa kasa, dama a darare ta zauna. Wasu yan siraran hawaye Izzatu ta soma yi tace Zuhra don Allah ki yafeni. I played a cruel joke on you. Zuhra tace eyye...play kuma? Kawar da kai Hamza yayi yayi dan murmushi. Yana ganin da kyar idan Zuhra ta fahimci abinda Izzatu ta fada saboda yadda ta soma yaken karfi da yaji. Izzatu ta cigaba da magana, nasan ban kyauta ba amma don Allah ki yafe min.
Babu komai Zuhra tace idanunta na cikowa da kwalla. Ta dai yafe amma bata jin zata taba manta irin dariyar da Izzatu tayi mata a gaban mutane. Tashi ma tayi zata koma nata dakin Izzatu ta dan taba Hamza, baka bata hakuri ba. Ni kuma??? A wani dalili? Dan marairaicewa Izzatu tayi, shi kuma yana kallon Zuhra da ta tsare shi da ido. Dena kallona ya fada yana harararta. Kanta ta sunkuyar dama tasan bazai bata hakurin ba. Izzatu dai da fara'arta tace ni na baki hakuri a madadinsa. Kai Zuhra ta gyada kawai, Izzatu tace to tunda kin hakura ina fata zaki amince ya SAKE ki. Ta juya ga Hamza, daga shi har Zuhra kallon mamaki suke mata. Zuhra tace dama abinda kike so kenan shine kika rinka yi min kirki dazu? Duk abin Izzatu sai da taji kunya. Hannuwan Zuhra ta rike, nasan kema auren nan dole ake yi miki kamar yadda aka yi mana. Ki amince ya sakeki ki koma gida ki auri miji daidai da ke wanda zai so ki. Nasan idan da bakinki kika fadawa Alhaji ke kika nemi sakin bazai ga laifin Sweetyna ba. Sai ta kalli Hamza ta kalli Zuhra duk tunani suke yi. Dan gyaran murya Hamza yayi duka suka mayar da hankulansu gareshi. Idan kin amince da sakin bazan sake ki yanzu ba sai nan da kamar wata shida ko shekara daya saboda Alhaji bazai taba yarda ke kika nema ba. Izzatu ta bata fuska habaaaa Hamza, wata shida is too long. Hankalinsa yana ga Zuhra yana karantar yanayinta saboda ta zurfafa a tunani. Zaman gidan nan ba nata bane saboda babu mai kaunarta. Itama kuma ba son mijin take ba, son kyautatawa iyayenta da nunawa Izzatu kurenta yasa tun farko ta amince. To yanzu idan aka saketa yaya Baba da Umma zasu ji? Waye zai yarda ya aureta idan aka ji aurenta ya mutu bayan wata shida. A sanyaye ta dago kanta suka hada ido da Hamza, saurin kawar da kanta tayi kamar ba itace mai tsare mutane da ido ba. Na yarda amma don Allah kada ku bata min suna idan anyi sakin saboda iyayena....hawaye ne suka zubo mata tayi saurin rufe fuskarta da mayafinta ta fita. Tana jiyo ihun murnar Izzatu ta sake danewa jikin Hamza.
Shima duk jikinsa yayi sanyi don baiyi tunanin zata amince da wuri haka ba. Dole ya sami dalilin da zai fadawa iyayensu yadda baza'a ga laifin kowa cikinsu ba.
Izzatu yaji tana kokarin cire masa riga yasa hannu biyu ya rike abarsa. Meye haka? Dazu kinzo kinyi hugging dina a gaban yarinya. To meye ta fada tana jan rigarsa. Ai tasan abinda yafi haka ma munayi. Tana dariya tace Baby we need to celebrate bari na samo mana juice mai sanyi da cups muyi toasting. Duk da wata shida is a long time amma ba komai. Fita ta sake yi ta barshi yana tunani. Kamata yayi ya yi murna da amincewar Zuhra sai dai a kasan zuciyarsa yasan abinda suke niyar yi bai kamata ba.
Ba jimawa ta dawo da apple juice a wata roba mai kyau ta tsiyaya musu a glass cups. Hamza zai kai nashi baki ta rike hannun, I said lets toast ta kashe masa ido. Tare suka dan buga cups din suka yi yar kara. Izzatu tace TO FREEDOM.
[9/25, 3:53 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 37
Batul Mamman(Mrs)
Kwanaki biyu a tsakani Zuhra na zaune a falo don yanzu Izzatu tace ta rinka zama tana sakewa. Hatta su Khalifa tana bari su zauna da ita. Wurin karfe biyar na yamma Hamza ya shigo maigadi ya biyo shi da ledoji. Kofar inda ya kamata ya zama kitchen din Zuhra yace ya ajiye masa. Su Junior da Izzatu suna ta yi masa sannu da zuwa Zuhra ta mayar da idanunta ga kallon tv. Ita yanzu da tasan matsayinta a gidan tana ganin yi masa sannu da zuwa kamar shishshigi ne. Shima a nasa bangaren bai kulata ba suka tafi dakinsa shi da Izzatu. Ba jimawa ya fito da shirt mara nauyi da dogon wando, da gani wanka yayi.
Abinci ya zauna ci suna ta hira da Izzatu. Sai da ya gama ya tashi ya bude kitchen din Zuhra sannan yace ke zo. Da farko tayi niyar sharewa sai Izzatu tace mata jeki mana Zuhra kayan miya ya siyo miki. A hankali take tafiyar har sai da yaji haushi. Ya nuna mata kayan da hannu alamun ta dauko. Wato kace na dauka da bakinka ne kake ganin asara....Allah Ya sauwake ta fada a ranta. Dauka tayi gabadaya hudun ta shigar dasu kitchen din. Kallon mamakin da yayi mata yasa ta tuna maganarsu dasu Anas da suka ce mata maza basa son mata masu karfi. Sai kuma ta tunawa kanta ai Hamza ba mijin da zasu so juna bane.
Kwalin gas cooker dinta ya farke ya sake fita. Bai dade ba ya shigo dauke da karamar cylinder. Daga can gefe ya ajiyeta sannan ya hada mata gas din. Ya koma kan fridge din shima dan madaidaici ya jona mata. Ita dai tana gefe tana binsa da ido. Sai da ya gama tsaf yace ga kayan miya nan da nama sai ki saka a fridge kada su lalace. Daga yau ki rinka dafa iya abincin da zaki ci. Idan akwai abinda babu a cikin kayanki sai ki fada a siyo. Tsananin farinciki da taji yasa ta washe baki da gaske kake don Allah....daure fuska yayi, na taba wasa dake ne? Nagode, nagode, nagode ta rinka fada tana bude ledojin. Ji tayi yace kuma ki kula kada ki bata wurin nan kinga tun asali ba kitchen bane. Ya nuna mata sink shi kadai zan iya sawa idan kin tafi sai a cire amma bazan miki wani kitchen kabinet ba. Duk da haka ma nagode ta fada cike da murna. Yau zata dafa abinci son ranta taci ta koshi. Hango kanta take da kwano ba ma plate ba shake da abinci.
Wannan irin farinciki da take yi yasa shi jindadi. Ko ba komai yana ganin ya tsira daga laifin tauye mata hakki a ganinsa. Zuhra tana susar kai tace uhmmm....yes ya amsa don yasan akwai abinda take son fada. Dama...dama... gajiya yayi da inda indarta yace dama me? Uhmm nace shi gas din ya zan rinka kunnawa? Au dama baki iya kunnawa ba aka kawo ki dashi. Turo masa baki tayi to mu a gida ba da itace muke yi ba ko risho. Ganin ya daga hannu tasan a bakinta zai sauke shi tayi saurin ja da baya. Nufi na fa ban saba dashi ba amma cikin kayana akwai risho din sai na fito dashi. Hannu ya daga yana nunata, ki fito da me? Wallahi kada kuskura ki kunna min risho a wurin nan in ba so kike ki sake min sabon fenti ba. Kinji ko! Gyada kai ta rinka yi kamar kadangaruwa da taji ya fara daga murya. Sai kuma yace matso ki gani..kunnawa yayi sannan ya gwada ragewa da kashewa duk tana gani. Idan kin kasa ki kira Tala ta nuna miki don naga alama kin fita kauyanci. Ni ba yar kauye bace ta fada tana kara turo bakin nan nata. Biyota Hamza yayi zaiyi maganin rashin kunya ta juya da gudu. A bakin kofa suka ga Izzatu tana dariya. Ai tunda naji kana daga murya nasan kun fara fada shine nazo kallo. Ta kalli Zuhra bai dake ba ko...babu wanda ya bata amsa ta cigaba da dariyarta ta kama hannun Hamza suka fita.
Tuwo Zuhra tayi niyar yi Izzatu tace kada tayi girki an riga anyi abincin dare da ita. Har ranta bata ji dadi ba amma haka ta daure taci abincin.
Inuwa sakatare yana ta hada wasu files zai kaiwa Hamza saboda meeting din da zasu yi sai gashi ya fito daga office dinsa rike da waya da makullin mota. Inuwa yace ranka ya dade fita zaka yi ne? Akwai meeting fa biyu da rabi. Ba jimawa zanyi ba Inuwa in sha Allah. Zanje banki ne tun friday kaga yau alhamis banji alert ba na kudin da ka ciro. Inuwa yace to Allah Ya kiyaye adawo lafiya. Amma ranka ya dade yaushe Oscar yace zai dawo ne muna bukatar sa hannunsa a wasu takardu. Hamza yace nima duk na damu ko jikin mahaifiyar tasa ne sai dai ban same shi a waya ba. Bari nayi sauri na dawo sai muyi maganar dai. Koda ya fita jikin Inuwa sakatare yayi sanyi....Allah Yasa abinda zuciyarsa take kitsa masa ba gaskiya bane.