Sashe 28
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kansa ya bude mata gaban motar ta zauna ya rufe. Yana tayar da motar ya kunna AC, ko minti biyar basu yi da fara tafiya ba ta soma gyangyadi. Dan bugun kujerarta yayi, kinji sanyin AC ko, to idan kika yi min bacci jefar dake zanyi a titi na huta. Gyara zamanta tayi tace amma dai wasa kake yi ko? Gabansa yake kallo ki yi baccin sai mu gani wasa ne ko gaske. Waje ta koma kallo. Da shirun ya isheta tace Allah Sarki su Nana suna hanya ko. Kaduna babu nisa sosai tun dazu suka isa ya bata amsa. Daga nan motar tayi tsit ko rediyo bai kunna ba.
Motar na shiga layinsu Zuhra yara suka fara binsu ana ga Zuhran baban yara. Hannu bibbiyu ta rinka daga musu. Har su Anas da Sani kowa ta gani sai ta daga hannu. Haka kawai Hamza sai abin bai masa dadi ba. Tana dagawa Munkaila mai shagon kusa da gidansu hannu Hamza yace kika kara daga hannu sai na dalle miki baki. A islamiyya ba'a koya muku kamun kai bane. Turo baki tayi to kuma sai ka hanani zumunci da mutane. Rai a bace ya juyo sai dai ko motar bata jira ya kashe ba ta fice da gudu.
Umma na kwance a falo taji an fado mata a jiki. Tana kokarin tashi Zuhra ta soma kuka. Umma tace to meye haka kuma. zuciyarta cike take da farincikin ganin yarta. Baba da ke daki fitowa yayi da jin muryar Zuhra. Shima makale shi tayi tana kuka. Umma tace wai kukan na meye ne? Hamza ne ya shigo dauke da manyan ledoji guda biyu yace kukan shagwaba take yi Umma. Baba ya tarbe shi, har kasa ya durkusa ya gaishesu tare da ajiye ledojin a gaban Baba. Umma tace kai kuwa baka gajiya da wahala. Duk zuwa sai kayi dawainiya. Dan sunkuyar da kansa yayi albarkarku muke nema Umma. Zuhra mamaki tayi wai dama yana zuwa gidansu. Kawai sai taji ya kara girma a idonta. Zata yi kokarin dena yi masa rashin kunya.
Hira sosai suka yi da Baba ita kuma suka shige daki da Umma. Duk dadi ya kama Umma taga kamar Zuhra ta nutsu. Zuhra tace sai bayan hutu zaki dauko Safara'u ne? Umma tace eh ance sun kusa fara jarabawa. Zuhra tace yace daga nan gidansu zamu je. To me zaki kaiwa surukan naki? Sai a lokacin tayi tunani ya kamata ace ta kai wani abu tunda yana yiwa nata iyayen. Umma bata jirata ba ta fita kitchen. Kayan kamshi da kayan kadin da kanwarta ta aiko mata da yawa ta zuba a leda ta bata. Da zasu tafi bayan sunyi sallar laasar Baba ya bata wani turare mai kyau yace ta kaiwa Alh Nasiru. [10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [9/26, 12:31 AM] +234 803 244 1205: AL'ADUN WASU 46
Batul Mamman(Mrs)
Ba shiri ya saketa, yana yarfe hannu. sake bude baki tayi zata yi ihu a hankali yace ke nine....ajiyar zuciya tayi da karfi sannan tace da tsoratani kazo yi kake min sanda a daki? Kaima baka da fitila ne? Dukan da tayi masa ya kulle masa ciki gashi ta dame shi da surutu. Da waya na shigo karama bansan inda kika jefar min da ita ba. Yayi kokarin dukawa ya lalubi wayar yaji zafi a cikin....auchhhh. Zuhra tayi saurin matsawa kusa dashi menene ta tambaya a tsorace. A duhun ya harareta naushi na fa kikayi a ciki ga cizo sai kace wata yar dambe. Duk hanyar mugunta kin sani. A wahale take jin muryarsa na fita ta mika hannu tana sannu taji ta taba cikinsa....kamar wadda aka tsikara tayi saurin janye hannun tana cewa yi hakuri. Shima hakan yaji amma bai so ta dauke hannunta ba. Dakin yayi shiru na dan lokaci...Hamza ya kasa gane dalilin da yasa ko yaya jikinsa ya taba na Zuhra sai abin yayi affecting dinsa sosai. Dan gyaran murya yayi bazaki tayani neman wayar ba? Kamar jira take ta durkusa tana rarrafe tana shafa hannu a kasa. Abu taji ta taba tayi saurin janyowa ashe hannun Hamza ne shima yana duddubawa. Da yake da karfinta taja shi kuma baiyi tunanin hakan zai faru ba sai ya fada kanta. Bakon yanayi duka suka tsinci kansu a ciki. Kunya kamar Zuhra ta nutse a wurin, kamshi ne mai dadi yake fita daga jikin Hamza.
Yana fadawa ya gane daurin kirji ne a jikinta...a hankali ya soma yi mata magana. Nifa bana son daurin kirji don Allah ki dena. Wai ita yake hadawa da Allah....saurin dawowa tayi hayyacinta ta fara kokarin ture shi. Yana ji ya sakar mata nauyinsa yana mata dariya.....wai kema kina son jin dumin mijinki shine kika janyoni. To saboda ina tausayinki bazan miki fada ba mu kwana a haka. Wayyo Allah, karshen kunya Zuhra ta gama ji. Har wata in'inar karfi da yaji ta fara. Al'Quran....Al'Quran ba...ba haka bane. Ko kadan bashi da niyar tashi don ya soma jindadin tsokanarta yace to yaya ne? Abinda kika ga munayi da Izzy kike so nayi miki? Wani karfi ne yazowa Zuhra ta dage ta ture shi. Tana ji yana dariya ita kuwa sauran kadan ta soma kuka. Bata dade da matsawa ba yaga wayar ya dauka ya kunna tare da soma haska dakin.
Can bakin kofa ya ganta ta takure harda jan bargonta ta rufe jiki. Koda ya matso harda dan hawayenta. Kusa da ita ya koma me kuma nayi miki kike min kuka? Sai da ta dan matsa sannan tace ba kaine kace wai...wai...wai....kwafa tayi ta kasa karasa maganar. Dariya shagwabarta ke bashi, dazu fa aljani kika kirani banyi kuka ba sai kece mai arhar hawaye zaki min kuka daga wasa. Kin kallonsa tayi saboda kunyar ganinsa babu riga. Yace kinga fito daga bargon nan kisa rigar bacci bana son daurin kirji. Tana kumbura baki tace ni a haka zan kwana. Mikewa yayi to ya rage naki...wai ma kinyu wanka kuwa kafin ki kwanta. Tsami nake ji a dakin nan....dama zuciya na kusa ta fara kuka wallahi bana tsami. Yace to kinyi wankan..tsakaninki da Allah. Rufa tayi har ka sannan tace banyi ba. Rufe bakinta ke da wuya ya janye bargon gaba daya tana kuka ko kulata baiyi ba. Lokaci daya ya yankewa kansa shawarar abinda zaiyi ya taimaka mata kafin su rabu.
Kan gadonta ya jefa bargon sannan ya shiga toilet dinta. Babu komai sai sabulun wanka da omon wanki da wanke toilet. Ficewa yayi ya barta a duhun baiyi magana ba. Ga tsoro tana ji ita kadai amma bata son binsa.
Bayan kamar minti biyar ya dawo da wata fitila mai haske wadda tafi karamar wayar tasa. Shima a babbar bashi da chaji sosai. Wani abu ta gani a hannunsa kamar toothpaste tace ina da makilin fa. Wannan ba makilin bane yar kauye zo nan. Baya ta dan matsa tace yi hakuri. Fitilar ya ajiye a kan dressing mirror dinta sannan ya jawota ya zaunar da ita kamar ranar da yayi mata kwalliya. Duk ta tsargu da daurin kirjinta, shi kuwa ya saka kayan bacci marasa nauyi yanzu. Yana zaunar da ita ya kama hannunta duk da yadda yaji ya daga. Allah Sarki Zuhra sai hawaye...ashe dazu bata ga komai a kunyar da Hamza yake shirin bata ba. Kokarin sauke hannunta tayi ya sha kunu zan matseki idan baki tsaya ba. Kuma kinga mu kadai ne a gidan babu mai taimakonki. To me zaka yi min? Yace sa ido ki gani bana son surutu kuma ki hadiye kukan nan. A hankali take hawaye tana gani ya bude abinda ta zata makilin ne ya zuba a wani abu kamar cokali mai dan fadi ya soma shafa mata a hammata. Ji tayi kamar cakulkuli ta soma dariya....girgiza kai yayi kina da matsala, daga kuka sai dariya. Bata dena dariyar ba har ya gama yace ta bar hannunta a bude. Dayan hannun ya daga ya shafa a nan ma. Wurin minti biyu yana dube dubi a dakin har yaga inda ta ajiye turaruka da body spray din lefenta. Tace wai a haka zan zauna ne? Sai da ya dauko wurin kala biyar sannan ya dawo ya dauki yar robar da tisssue a hannunsa ya kwashe duka gashin. Zuhra ta wage baki ....lahhhh kaga gashin ya cire. Hamza murmushi kawai yayi..yar kauye bata san shaving cream ba. Fes ya share mata sannan ya mika mata shaving stick har uku. Shiga toilet kiyi shaving sannan kiyi wanka ina jiranki a nan. Ya Salam yau Hamza so yake ta tona rami ta boye kanta don kunya.
Kasa shiru tayi tace can kasa wai yau kunya kake son sani ji? Bata san yaji ba yace yes idan baki wuce ba zanzo nayi miki da kaina. Fitilar ta dauka da sauri ta shige harda murda key. Murmushi Hamza yayi ya dan matsa kofar toilet din...kada ki fito sai kinyi wanka sau uku. Ki tabbatar jikinki ya fita sosai don zan duba. Idan baki fita ba na iya yiwa kazamai irinki wanka. Kuma kiyi brush sosai. QTo an hada Zuhra da aiki, sai da tayi amfani da duka shaving sticks din wurin gyara jikinta sannan ta shiga dirzar jiki. Allah Ya kiyaye ta bari yayi mata wanka. Sau biyar ma tayi harda goge kafa da abin kaushi duk da kafar tata bata da matsala. Brush da toothpaste kuwa sun san Hamza na dakin don sun sha aiki. Katon tawul tasa ta goge jikinta sai taji wani dadi da iska na shigarta. A hankali tace na gama. Yana kwance akan gadon nata yace to fito mana. Lallai ma a hakan? Rigar bacci yake duba mata amma sai yace to meye ya rage da zaki boye min. Shiru yaji bata fito ba ya dan kwankwasa, bude ga riga ki saka.