← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 67

Sashe 58

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alh Nasiru bai damu da yadda Mal Bashir ya canja ba. Abinda yafi haka ma yana da ikon yi akan 'yarsa. Babu uban da zai zuba ido yaga ana wulakanta masa 'ya'ya komai talaucinsa. Alhaji ya sake fada musu abinda Izzatu tayiwa Zuhra a daren jiya. Kuka ne ya kwacewa Umma sosai ta rungumo Zuhra jikinta har rawa yake. Da da ajali a kusa babu abinda zai hana sojojin nan harbe Zuhra. Hajiya ma wani kukan take tayata. Hakika duk da rashin wadata sosai amma gidansu Zuhra gida ne mai cike da soyayya a tsakanin iyayen da tilon 'yarsu. Baba ma idanunsa ja suka yi sosai. Alhaji yace na zabi fada muku gaskiya saboda halin rayuwa. Ba don mai aikin gidansu ba da tayi tunanin sanar damu da karshenta yau labari yasha bamban. Mal Bashir ina mai baku hakuri da neman afuwarku. Wallahi idan Yaya ya dawo zan dauki mataki akan shegiyar yarinyar nan.

Mal Bashir ya kalli Zuhra yace babu wani abu da ya sameki ko? Tayi masa murmushi Allah babu komai. Yace to Alhamdulillahi sai mu jira Hamza ya dawo lafiya ya baki takardarki. Yau ko akuyar gidan nan kike bazan yarda ki koma inda akayi miki wannan diban albarkar ba, bare 'yata. Alhaji kuyi hakuri amma bazan bari ku koma da ita ba. Ita kadai Allah Ya bani idan ka duba da wuya idan bamuyi sa'anni da kai ba amma sai a kanta haihuwa ta tsaya tsaya mana. Wallahi duk kawaici irin na mutumin kauye bazan iya dauke kai ba idan abu ya shafi uwata. Gara na aurar da ita a kauye da ta fuskanci rayuwa irin wannan. Umma ta nuna ta goyi bayan mijinta.

Alhaji da Hajiya suka shiga bawa su Baba baki amma kememe Baba yace shi fa bazai yarda ba. Ibrahim yace Baba idan bazaka damu ba ka bani damar magana. Baba yace ina jinka amma bazan canja kudirina ba. Murmushi Ibrahim yayi sannan ya sanar dasu irin canje canjen da ya gani tattare da dan uwansa bayan aurensa da Zuhra. A takaice abinda iyayensu basu sani ba dangane da irin taimakon da tayi masa bayan durkushewar kamfaninsa a dalilin Izzatu duk sai da ya fada musu. Mamaki sosai suka yi Zuhra ta sake samun masauki a zuciyar surukanta. Ibrahim yace shekaranjiya yazo har office ya sameni ya sanar dani komai yace wasiyyace ya barmin saboda yanayin tafiya idan har bai dawo ba kada na taba bari ta wulakanta a duniya.

Wannan jawabi na Ibrahim ya sanyaya zuciyar iyayen Zuhra ita kumq yasata kuka sosai tare da dagewa wurin yin addua Allah Ya bashi sa'a kuma ya dawo dashi lafiya. Alhaji Nasiru yace bukatarsa daya a wurinsu kada su taba cewa sunsan inda Zuhra take domin Izzatu da hannunta zata girbe abinda ta shuka.

****
Mama da su Hamida ta tafi gidan Hamza. Ihun su Khalifa Izzatu ta ji suna murnar ganinsu ta fito daga kitchen a tsorace. Ba dai can Zuhra ta tafi ba. Ai kuwa tasan Alhaji sai ya bata mata rai. Ga Mama itama wata mara son nata. Gashi uwa uba bata san takaimaimai inda Zuhra ta tafi ba. Har wayarta ta gwada kira bata samu ba.

Da dan cokalin miya Izzatu ta fito tana murmushin da bai kai zuci ba tayi musu sannu da zuwa. Mama ta amsa fuskarta a sake tana tambayar ya suka kwana. Izzatu tace lafiya kalau Junior yace amma yau tun safe bamu ga Maama ba. Inata kiranta bata amsa ba. Izzatu ta make shi sannan tace tana dakinta kila bacci take yi. Mama tayi 'yar dariya tace su Hamida su duba mata. Dama da wata jaka mai dan girma da Adabiyya ta sako cikin hijab. A gaggauce suka debo mata kayan sawa, 'yan ciki da na bacci suka sauko. Hamida tace Mama da gaskiyar Junior Anti Zuhra fa bata dakinta..

Cokalin hannun Izzatu ya fadi don tsoro tace au na tuna tun safe ta tafi gidansu tace a can zata yini.

Adabiyya da Hamida suka kalli juna suna dariya kasakasa. Mama ta dauke kai kamar bata gansu ba tace to ga wannan dama Alhaji ne yace na duba ku. ..dubu biyar ta bawa Izzatu...idan Zuhran ta dawo ki gaidata. Daga nan suka fita suna mamakin karyar da Izzatu tayi musu.

Suna fita tayi ajiyar zuciya hankalinta ya kai karshen tashi. Yanzu idan Zuhra bata dawo ba ina zata fara nemanta? Dole ta kai cigiya wurin 'yan sanda tun kafin a kara dawowa nemanta.

****
A gidan Zuhra ta yini sai dare Nura ya dawo ya dauketa saboda washegari zasu tafi Ajingin da suka fasa zuwa a yau.

Tana zuwa gidan wayarta tayi chaji. Sakonnin text goma ta gani na Hamza masu nuna damuwarsa da rashin samunta a waya. Wurin shadayan dare ya sake kira lokacin suna masaukinsu a wani hotel. Ba karamin dadi yaji ba da ya sameta. Tayi ta bashi hakuri akan cewa wayar ce ta fada kasan kujera a motar bata ganta ba. Hirarsu suke ta masoya har Hamida da Adabiyya suka bar mata dakin suna tsokanarta don ta dage ita wurinsu zata rinka kwana. Alhaji yace kada ta nunawa Hamza komai yanzu saboda kada ya kasa yin abinda ya kaishi. Ta nuna masa tana gida kamar yadda yake tunani.

****
Haka rayuwa ta kasancewa Zuhra a gidan Alhaji babu irin gatan da su Hajiya basa nuna mata. Haka sauran 'yan uwan Hamza ma. Umma da Baba kullum sai sun kirata a waya. Lokacin da ta cika sati biyu ne suna kitchen ita da su Hamida suna aiki Zuhra tana wankin nama taji zuciyarta na tashi. Abu kamar wasa ta fara cewa naman yayi karni da yawa Adabiyya tace ai kuwa yana da kyau. Bata kara magana ba ta soma amai kamar kayan hanjinta zasu fita. Kofar kitchen din ta baya ta fita tayi aman tana yi tana kuka. Hajiya da Mama aka kirawo suka shigo kichen din. Ita dai Hajiya tana ganin aman da Zuhra take yi murmushi kawai tayi ta ja da baya, Mama ta wuceta ta taimakawa Zuhra. Yadda take aman har kirjinta na amsawa yasa take kuka. Mama tace oh ni Kaltume haka kike yiwa Yaya wannan kukan shagwabar? Gaskiya Umma Atine ta shagwaba mana 'ya. Hajiya na daga gefe tace don ba tare muka je gidan dake ba da kinsha kallo. Yadda kika san ta shige ciki. Zuhra duk kunya ta kamata ta tashi da gudu. Mama tabi bayanta da sauri tana dakatar da ita...haba Zuhra yanzu kuma ai lokacin tattalin jikinki ya kama sai kinbi a hankali. Bari na kira Nura a waya yazo ya kaimu asibiti don a tabbatar mana da abin alkhairi. Kan Zuhra a kasa ta kasa cewa komai. Itama tana zargin abinda Mama take fada saboda 'yan alamun da ta gani daga irin hirar 'yan mata da kawayensu. Da yamma suka je asibiti aka tabbatar tana da ciki wanda ke cikin watansa na biyu. Tun a hanya Mama ta kira Hajiya harda Alhaji tayi musu kyakkyawan albishir. Siyayyar 'yan kayan kwadayi tayiwa Zuhra wadda don kunya ta rufe fuskarta da mayafi.

Shima wannan labarin bata sanar da Hamza ba a lokacin da sukayi waya. Tafi son ya gani da idonsa. Sai dai suyi ta hira yana tambayarta me tayi yau. Kulawa kuwa a wurin 'yan gidansu sai godiyar Allah.

****
Izzatu sam bata da kwanciyar hankali a gidanta. Ga Tala ta tafi gida ga yara su dameta. Junior da Nana sunki yarda ta saka musu pampers ko ta saka musu sai sun cire. Dakinta har zarni yake saboda fitsarin da suke mata a kwance. Kafin ta gama girki kullum sai Nana tayi kuka saboda ta riga ta saba da kin dorawa da wuri. Idan ta zuba musu anjima kadan suce yunwa tunda bata zubawa da yawa. Duk wannan bai dameta ba kamar rashin sannin inda Zuhra take. Hamza dai ya dena tambayarta Zuhra shiyasa take mamaki. 'Yan kwanakin nan har mafarkinta take yi. Don tsananin tashin hankali ko shara bata yi a gidan ga uba wanke wanke ta tara. Tunani ne ya isheta wata rana bayan ta dauko su Khalifa daga makaranta ta wuce airport. Ya zama dole ta fara neman Zuhra tun kafin Hamza ya dawo kashinta ya bushe.

Daga bakin gate tayi parking ta fito ta tafi wajen masu karbar kudin shiga ta tambayesu ko sun ga wata mata da bata wuce shekara ashirin da daya ba sati biyu da suka wuce da daddare. Wanda ta tambaya yace ranar bashi bane da aiki amma bari a tambayi sojojin saboda yawanci a nan suke.

Da tafiyarta ta 'yan gayu ga takalmi mai tsini Izzatu tabi bayansa zuwa wurin sojojin. kafin su karaso yawanci duk sun taho wurinsu. Mutumin ne ya tambayesu abinda Izzatu tace ai kuwa wani gabjeje a cikinsu ya daka mata tsawa yace tayi kneel down a nan. Kamar ta saki fitsari don tsoro tayi abinda yace tana rarraba idanu. Ya kalleta sama da kasa yace...chege kaine ka bar kishiya a nan ko?

Izzatu tayi saurin girgiza kai alamun ba ita bace.

Wasu mutum biyu suka nunata da bindiga tayi saurin cewa nice, wallahi nice.

Katon yace dama kaine kawai zaka ki zuwa nemanta sai bayan two weeks. Mugu yau sai munci ubankaaaa. Ya fada yana wata irin dariya mai ban tsoro.

A take Izzatu taji saukowar fitsari daga mararta saboda tsabar kidima.
[10/23, 5:48 PM] +234 806 611 3313: AL'ADUN WASU 75

Batul Mamman(Mrs)

Wani soja musulmi wanda baiji dadin lokacin da suka sa Zuhra cire hijab ba, don babu yadda zaiyi ne saboda yadda ake amfani da hijabi ana cutar mana da addini da sauran musulmi. Muguwar harara ya dankarawa Izzatu sannan yace banda kneel down ta daga hannu sama. A dole tabi umarninsa babu inda baya rawa a jikinta. Tana daga hannu mayafinta yayi sama sai ga shatin fitsari a jikin zanin shaddarta. Kafin ta ankara ta rufe wurin sun gani suka rinka dariya. Sauran mazan dake gefe ma dariyar suke yi. Izzatu yau taga wulakanci irin wanda bata taba gani ba.

Daga nan suka rinka yi mata fada akan me zata bar yarinyar mutane a airport da tsakar dare. Ita dai Izzatu babu bakin magana bare ta tambayesu ina suka ga yarinyar tayi.
Chapter 58 · 0% Book details