Sashe 25
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuhra ji tayi jikinta yayi sanyi saboda yanayin da taga Hamza. Da gani yana cikin damuwa Allah Yasa ba wani laifin tayi masa ba. Plate din tuwo kuwa sai da suka sude shi tas ita da yarta Nana sannan aka tashi aka wanke hannu.
Bayan yayi wanka Izzatu ke tambayarsa ya aiki. A hankali yake magana yace Alhamdulillah. Tana zaune akan kujera tana masa kallon tuhuma tace Hamza ko ka fara sonta ne? Bangane ba shima a zaunen yake don baya jin zai iya cin abinci. Banda damuwar da yake ciki hannun Zuhra yake hangowa miya na binsa ta gefe tana kai lomar tuwo. Yarinyar ta fiye kazanta. Izzatu ta dan sha kunu Zuhra nake nufi. Lokacin da ka shigo ita ka fara kallo kuma ka danyi murmushi. Izzatu kenan,yanzu baki bani komai nasa a baki ba kike tuhumata. To idan naso ta laifi ne? Matata ce fa. Sosai ta daure fuska bana so, Hamza bana son irin wannan wasan. Nan da wata shida zata koma gidan iyayenta mu cigaba da zamanmu yadda muka saba. Daga nan sai kuma ta soma murmushi baka ga yadda take cin abinci ba dazu. Baka ce dan bakin nan tana zai dauki abinda take tura masa ba. Idan ka fita yau pizza zaka siyo mana Baby a matsayin dinner. Ko sau daya bata damu da rashin walwalarsa ba. Hmmm kina bani mamaki Izzy...me kuma nayi Babyna? Murmushi take masa tana kashe ido. Fada mata ma bata lokaci ne don karshenta ta fadi abinda zai kara bata masa rai. Babu komai bari na dan kwanta kaina na ciwo. Tashi tayi to bari na kawo maka magani. Amma kafin nan ga wannan....ta dauko cards har kala hudu na biki. Ni duk matsalar Zuhra yasa na manta next week za'a fara bikin Mardiya cousin dina ta kaduna. Yar Uncle Jibril kanin Dad dinmu. Wai matar da miji ya fadawa yana ciwon kai kenan. Ga naka na daurin aure, ni a son raina ranar saturday na tafi kadunan saboda muna da shirye shirye a gabanmu. Kasan dani suka dogara tunda na zauna a Canada suna son ayi abin da tsari sosai. Kije Allah Ya kiyaye hanya ya fada a takaice....bargo yaja ya rufa har kansa. Bashi da kwarin yi mata fada ko fada mata abinda ya kamata. Sai da ta gama yi masa lissafin kudin da take bukata sannan ta dauko masa magani da ruwa.
Sai la'asar ya tashi jikinsa ya danyi kwari sannan kan ya dena ciwo. Masallacin kusa da gidansa yaje yayi sallah ya dawo yaci abinci. Yana gama cin abincin ya dauki key din mota....Izzy ni zan fita ki fadawa yarinyar nan kada tayi abincin dare zan taho muku da pizza din in sha Allah. Duk maganar a sanyaye yake yinta, wani salihanci yake ji tunda Oscar ya dibga masa sata. Tace harda Zuhra kuma? Ba kayi mata siyayyar kayan abinci ba. Yace nasan nayi amma as long as tana gidan nan zanyi kokarin sauke nauyinta. Tabe baki Izzatu tayi to shikenan sai ka dawo. Har bakin mota ta rakashi ya tafi gidansu. Nan ya zauna suka sha hira da kannensa kamar bashi ba. Hajiya taji dadin ganin ya sake ba kamar dazu ba.
[9/25, 3:54 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 40
Batul Mamman(Mrs)
Takwas da rabi a gida tayi masa ya shigo da ledar pizza har hudu manya. Ya riga ya kudurce a ransa daga yau siyayyar abincin alhamis ta kare sai lokaci lokaci kuma. Itama Izzatu zai bata kudi taje bikin ta dawo sannan ya sanar da ita halin da yake ciki tunda bata tambaya da kanta ba. Ita da yara suna ta murna da ya dawo ta karba ta rarraba. Yanka biyu ta sakawa Zuhra a plate Hamza yace ta kara mata daya saboda big size ce. Tala ta kirawo ta kaiwa Zuhra daki saboda tun bayan magriba bata sauko ba. Tala ta fito daga kitchen hannunta duk kumfa tana gogewa da tsumma. Hamza ya mika hannu bari na kai mata saman zani. Plate din ta mika masa tana tambayarsa a ina zai ci tasa yace ta kai masa falonsa yau baya son hayaniya.
Zuhra na kwance akan doguwar kujerarta tana kallon wani film din Hausa na marigayi Rabilu Musa dan ibro tana ta dariya. Tun daga bakin kofar dakin Hamza yake jin dariyarta. Yarinyar nan bata da kamun kai ya fada a ransa. Ji yadda take dariya kamar ba mace ba. Sallama yayi ta tashi da gudu ta dora hijab a jikinta. Plate din kawai ya mika mata zai fita sai yaji tace ina wuni? Tunawa tayi dazu tana cin tuwo bata gaishe shi ba. Jiya kuwa dama basu hadu ba. Da ya juyo ya amsa sai yaga plate din take karewa kallo. Ta dan kalle shi....shi kuma wannan menene? Pizza ce, baki taba ganinta bane? Tace eh, Allah Yasa da dadi dai. Sai da yayi murmushi sannan yace ci ki ji mana. Yanka daya ta dauko gashi da girma ta dan lankwasa shi biyu ta tura a baki ta gutsiri rabi. Sai da Hamza yasa hannu a bakinsa don mamaki....tabdi! Ke bakinki zai iya yagewa idan kina katuwar loma haka. Dan gayun nan na mata ma baki iya ba. Wani irin dandano taji da bata taba ji ba. Abin dai bazata iya kwatantashi ba. Bata san lokacin da ta furzar da na cikin bakinta ba, wanda bai sauka a ko'ina ba sai kafar Hamza.
Wayyo Allah, Wayyo Allah, Wayyo Allah shine abinda yake ta nanatawa ya dage kafar tare da kawar da kansa gefe. Idan ya kalli kafarsa yasan dole ne yayi amai. Kamar yayi kuka saboda da takaici. Yana girgiza kai yace ke kuwa me nayi miki zaki tofa min abin baki. A tsorace ta dago kai zata bashi hakuri. Sauran ya gani a gefen bakinta da habarta. Dan danne fushin da yake yi ne ya gagara ya daka mata tsawa....Goge bakinki mana. Da hijab dinta tayi saurin gogewa sannan ta sake cewa kayi hakuri, shi kuwa sake hade fuska yayi yana ta yatsina hanci....kai so disgusting yace yana rike hanci.
Irin kallon bangane ba tayi masa sannan tace SO kuma? Ni yaushe kaji nace so? Ba cewa nayi ina sonka ba hakuri nake baka. A wane dalilin zan ce ina sonka? Mamaki ta bashi ya rasa daga ina taji kalmar. Sai daga baya ya tuna yace SO DISGUSTING. Dariya sosai abin ya bashi, yace anya kin taba shiga aji kuwa? Sosai ma kuwa, har SS3 na kai a sakandire. Tana magana ta durkusa zata goge masa na kafar tasa da hannunta. Saurin jan kafar yayi tare da yin tsaki...kazama da hannu kuma zaki goge, ni bani tissue. Eyye me kace? Ya sake maimaimatawa. Dan murmushi tayi na ta gane zancen. Toli fefa kake nufi, wallahi bani da ita. Jin kafarsa yake kamar ya yanke ta yace to dauko min ta toilet dinki da sauri. Ya dan kalli kafar....Oh God I hate this.
Gani yayi bata tafi ba ya dan daga murya nace ki dauko ta toilet kin tsaya kina kallona. Baya ta dan sake matsawa na fada maka babu. Iko sai Allah, yanzu ko a toilet babu? To da me kike amfani. Dariya ya bata ji wata irin tambaya.... tace da tawul mana, ni bansan ana goge jiki da toli fefa ba. Jin bata fahimce shi ba ya kara bashi haushi. Ni ba cewa nayi a goge jiki ba. Shiru yayi saboda kunyar abinda zai fada. Da kyar yace kafin kiyi tsarki nake nufi. Kanta ta dan juyar a kunyace tace tsarki da toli fefa kuma kamar wata arniya.
Yarinyar nan duka take so...kwafa yayi sannan yace ke a kazantarki idan kin gama abinda kike a toilet hannu kike sawa? Shi kam Izzatu ta cuce shi da tayi sanadin auren nan. Gaskiya ke kazama ce ta karshe ya fada yana toshe hanci. Hanyar toilet dinta yabi zai wanke kafarsa sai wata zuciyar ta hanashi. Karshenta yaga wani kayan kazantar. Da jan kafa ya fita daga dakin ya tafi nasa. Ya shiga toilet ya sakarwa kafar ruwa. Sai da yaga babu komai a kafar sannan yayi wanka ya fito.
Ita kuma Zuhra gyara wurin da abin pizzar ya bata tayi ta sauka da sauran a plate. Izzatu ta kaiwa suna cin nasu dasu Khalifa tace bazan iya cin wannan abin ba. Izzatu tayi dariya dama shi ya dage sai ya baki. Tana karba ta bude plate din da ta saka masa nasa ta kara da sauran biyun na Zuhra. Tana kallo Zuhra ta wuce kitchen dinta ta dumama tuwo ta haye sama zata ci.
A bakin bene suka hadu yace mhmmm haka kika iya, ki cika kwano da tuwo. Bata amsa ba ta bashi wuri ya sauka. Izzatu ta biyoshi falonsa da nasa abincin. Biyun saman wanda aka yi da naman kaza ya cinye yace ya koshi. Izzatu tace kuma kai na ajiyewa mai beef(naman saniya) din don nasan shi kafi so. Ruwa ya dauka a cup yana sha tace ashe rabonka ne mai chicken din da Zuhra ta dawo dashi wai bata.......kwarewa yayi sosai tun kafin ta gama maganar ya soma kakarin amai. Idanunsa har ja suka yi saboda wahala yace yanzu Izzy ragowar yarinyar nan kika bani. Tace to meye ai bata ci ba, hannu tasa tana shafa masa baya. Sannu kaji my darling shiyasa ba'a son magana idan an cin abinci.
[9/25, 3:54 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 41