← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 67

Sashe 66

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AL'ADUN WASU 80 Batul Mamman(Mrs) Yau kwanan Junior uku da rasuwa amma kullum jinta suke kamar lokacin aka yita saboda yaro ne mai shiga rai. Zuhra bazata taba mantawa ba shi ya fara cewa zai zama abokinta a gidan. Ga Nana idan tayi wasa ta gaji sai ta fara neman shi ko Khalifa kamar yadda ta saba. Idan kaga Izzatu dole ka tausaya mata a wannan lokacin. Ta rame sosai duk da cewar da wuya ka ganta tana kuka. Mafiya yawan lokaci ita ke rarrashin Zuhra saboda ita akwai raguwar zuciya. Abin kuka baya mata kankanta. Yadda ta koma ya bawa duk wanda ya santa mamaki tare da zama abin burgewa saboda ta dauki qaddarar da tazo mata hannu bibbiyu. Suna zaune a falo Raliya tana kallon Zuhra da Izzatu suna karbar gaisuwa. Wata mata cikin 'yan gaisuwar tace wace mahaifiyar yaron ne a cikinku? Izzatu ta nuna Zuhra. Matar ta rinka bawa Zuhra hakuri akan ta rungumi qaddara ta sami lada. Batan san kukan Zuhra a wannan lokacin ba na rasuwa bane. Tana jinjina yadda Izzatu ta nunata a matsayin maman Junior ne. Wannan abu akan idon Hajiya akayi da Raliya. Sunji tausayinsu sosai. Raliya tace a ranta lallai kowane rashi daga Allah baya rasa alkhairi a tattare dashi sai dai ba kowa yake ganin wannan alkhairin ba bare ya amfana dashi. Misali mutane da yawa suna wa'azantuwa da mutuwar wani makusanci su daina akaita barna da sukeyi a da. Wasu kuma imaninsu ne yake karuwa idan suka yi rashi. Wasu kuma abinda idonsu ya rufe da basa gani sai su fara fuskantarshi a wannan lokacin. Ga mai hankali mutuwa ayah ce mai ishara ga barin mummuna da komawa ga kyakkyawa. Rasuwar Junior tayiwa kowa ciwo amma Raliya tasan shine ta zama sanadin shiriya ga 'yarta. Saboda irin tarbiyar da suka bawa 'ya'yansu Izzatu ta tashi da irin halin nan na bature daga ni sai iyalina makusanta wato miji da 'ya'ya. Duk wanda yazo a bayansu ana iya rayuwa batare dashi ba. Hakan yasa ta kasa fahimtar mijinta a lokacin da yaso ta gyara halayenta don su zauna lafiya da 'yan uwansa. Sannan kuma 'yan uwan nasa suma suka ki ta saboda ta kasa barin al'adun da ba nata ba ta shigo musu da bakin al'amura. Babbar matsalarta kuma shine bata daukar abubuwan da take da mahimmanci shiyasa ko sun nuna fushinsu sai ta ga kamar hakan ba komai bane. Ajiyar zuciya Raliya tayi tana addu'ar Allah Yasa ta dore a haka Ya yafe musu kuskurensu wurin bawa 'ya'yansu tarbiya. Dama haka Allah Yake hukuncinSa. Abinda ka raina baka dauke shi laifi ba sai yayi sanadiyar bata tsakaninka da mahaliccinka. Abinda kuma ka raina a matsayin aikin lada sai ya kaika ga rahmar Allah. Allah Yasa mu dace. Amin **** Da yake Junior yaro ne gidan baya cika sosai. Hamza yana waje inda yake karbar gaisuwa daga makota da abokan aikinsa. Cikin masu zuwan ne kawai yaga wani mutum ya shigo rabin fuskarsa duk a rufe yasa bakar jacket da bakin wando gashi kansa da hula. A gaban Hamza ya durkusa ya cire bakin glass din idonsa yace Sir I am very sorry about your loss. May his soul rest in peace. Ba Hamza ba sauran 'yan office dinsu da suke wurin tuni suka gano muryar Mr Oscar. Wurin mutum biyar suka yi kansa harda masu zagi. Hamza ya tashi da sauri ya hanasu. Inuwa sakatare ya harzuka yace haba yallabai Mr Oscar ne fa. Babu wanda zai ce ya manta halin da ya jefa mu sanadiyar satar da yayi maka. Shine har zai shigo gidan nan hankali kwance. Hamza yayi dan murmushi yana rike da hannun Oscar....idan har rashin da mukayi zai sa yazo gidan nan duk da cewa yasan nemansa nake yi to lallai dole ne nayi hakuri. Har kun manta abinda ya tara mu a nan? Mutuwa ce fa mai daukar babba da yaro talaka da mai kudi.... Ya mayar da dubansa ga Oscar....nagode sosai da nuna damuwarka gareni a wannan lokacin. Mr Oscar ya soma hawaye yace...Oga nasan nayi kuskure ina neman afuwarka. Ka yafe min domin nayi nadama. Tsoron abinda zai faru yasa na kasa zuwa na sameka. Inuwa yace abinda zai faru bai wuce na kira 'yan sanda suyi gaba da kai ba. Shege arnen banza. Bata rai Hamza yayi sosai yace haba Inuwa. Kada fushi yasa ka sakawa mai laifi da tsiya. Ko baka san maganganunka zasuyi tasiri a zuciyarsa ba ya sake tsanar Hausawa da musulmai....kaga Mr Oscar nasan naji ciwon abinda kayi min amma yau godiya nake da kazo min taaziya saboda haka kaje kawai. Cheque Mr Oscar ya dauko daga aljihunsa... Oga kayi hakuri nayi kokarin mayar da kudin kamar yadda suke amma na kasa. Na yi amfani da miliyan daya da duba dari takwas kuma bani da hanyar maido maka da kudin nan. Ka bani lokaci ko aiki idan na samu zan rinka biyanka a hankali. Godiya Hamza yayi ga Allah sannan yace babu komai kaje na yafe maka. Ba kowa bane zai iya abinda kayi. 'Yan office dinsu basu ji dadin yafe masan da Hamza yayi ba sai dai kuma Mr Oscar ya basu mamaki. Shima mamakin yayi yadda Hamza yayi saurin yafe masa yace..Oga haka duk musulmi suke da saurin yafe laifi? Hamza yace a'a amma haka musulunci yace mu rinka yafiya ga wadanda suka cutar damu. Mr Oscar yace indai kuwa haka ne to na yarda wannan addinin naku akwai adalci. Zan iya zama musulmi dan uwanku yanzu? Wani cikin mutanen wurin ya tuna lokacin da Umar Farouq Mukhtar ya musulunta a masallacin unguwarsu. Yaji ance yaron har ya auri wata yarinya Ruqayya wadda tayi sanadiyar musuluntarsa. Kabbara suka yi abin alkhairi ya samu aka musuluntar da Mr Oscar. **** Daga ranar aka gama zaman makokin duk 'yan uwa suka koma gidajensu. Wata Juma'ar na zagayowa Hajiya ta dawo gidan. Ita da bata zuwa gidan 'ya'yanta sai da dalili mai karfi shiyasa suka yi mamakin ganinta. Ibrahim ne ya kawota ya zauna a falo saboda Hamza baya nan. Izzatu da Zuhra basa kasa Tala tace mata suna sama Zuhra ce bata jindadi. Waya Izzatu ta saka a speaker tana magana ga kofin tea a hannunta Zuhra ta kwabe fuska kamar zatayi kuka. Izzatu tace...Baby har yanzu taki shan tea din fa. Ga idonta ya cika da hawaye. Ni tsorona kada ta haifa min baby mai kuka. Daga office dinsa Hamza yace kyaleta idan na dawo dura zamuyi mata irin na jiya. Zuhra tace don Allah kuyi hakuri. Zan sha da kaina. Hajiya tana tsaye a kofar dakin Zuhra tana jinsu. Zuciyarta cike take da farinciki mara misaltuwa. Sallamarta ce tasa Izzatu tayi saurin kashe wayar duk suka gaisheta suna yi mata sannu da zuwa. Hajiya da fara'arta ta amsa tace su zauna wurinsu tazo. Izzatu tace bari na kawo miki abinci Hajiya. A'a dawo ki zauna nagode. Zuhra Hajiya ta kalla tace ki shanye tea din sannan muyi magana ko. A yadda Hajiya ta tsareta da ido dole ta karbi kofin ta fara sha. Izzatu tayi dariya bari na dauko miki bread kada ruwan tea ya kulle miki ciki. Kamar tayi kuka haka ta rinka tura bread tana kurbar tea kamar magani. Sai da ta shanye tea din sannan Hajiya ta bukaci su bata hankulansu tana son yi musu magana ne. A nutse ta fara magana duk su biyun sun sunkuyar da kai kasa suna sauraronta.... Nasan zakuyi mamakin zuwana gidan nan a wannan lokacin duba da cewa ba abu bane da na saba yi. Yanzun ma dole ce tasa ni zuwa domin akwai shawara da nake son baku. Tun kafin rasuwar Sunusi nake kula daku a asibiti har zuwa kwanaki ukun da mukayi muna karbar ta'aziyya a gidannan. Tabbas canjin da nagani a wurinku ya sanyani matukar farinciki. Nagode Allah Yayi muku albarka. Sai dai akwai kalubale a gabanku. A lokacin da kishiyoyi basa zaman lafiya idanuwa basu fiye zama a kansu ba dama shaidanun mutane burinsu su ga ana tashin hankali. Amma daga yanzu da mutane suka kula yanayin zamanku ya canja to 'yan gulma da hada fada daga danginku ko na mijinku zasu kawo muku farmaki. Da sunan soyayya wata zata wargaza muku farincikin da kuke kokarin ginawa. Abubuwa da yawa sun faru a iya zamanku a gidan nan tun daga lokacin aurenki Izzatu har zuwa yanzu da kuka zama ku biyu. A da can ki sani mu ba kinki mukeyi ba sai dai halayen da kika zo dasu ne bama so. Munyi kokarin ganin kun canja tun a baya sai ya zamana shima maigidan naku ya biyewa irin wadannan bakin al'adun. To babbar matsalar da kika fuskanta shine duk inda ake aure to idanu sunfi yawa akan mata. Komai munin halin miji indai matarsa tana da kyawun hali sai kiga ba kasafai ake damuwa da halinsa saboda mace ita ce gida kuma da ita aka fi hulda. Haka komai kirkin namiji idan matarsa bata kyan hali to nan ma gabadaya gidan za'ace basu da hali saboda ita mace ita take nuna irin gidanta a waje. Alhamdulillah tunda har Allah Yasa idanuna sun gane min irin zaman da kuke yi yanzu ina so don Allah ku zauna lafiya. Ku yafewa juna abubuwan da suka gabata ku rike juna da zuciya daya. Idan ance ki zauna da kishiya da zuciya daya wata zata ji tsoron cutarwa daga kishiyar to ki sani duk abinda tayi miki na cuta kuma tayi nasara dama Allah Ya kaddara hakan sai ya faru. Kada tsoron muguntar kishiya yasa kema ki zama muguwa. Ni da Mama ba karamin toshe kunne da hakuri da juna yasa muke irin wannan zaman da kuke gani yanzu ba. Dole sai anyi hakuri sosai. Idan mace taki kwantar da hankalinta kina ji kina gani watarana miji zai sakeki kuma ya barwa kishiya 'ya'yanki ko ta rike ko ta cutar dasu idan baki da karfi dole kiyi hakuri daga inda kike kina jin labari mara dadi game da 'ya'yanki. Ko kuma rai yayi halinsa kishiyar nan dai da bakya so ki bar mata 'ya'ya da mijin baki daya. Kunga kenan har gara ki fahimceta ku zauna lafiya ko don gaba. Allah Ya kara rufa mana asiri Ya baku zaman lafiya. Shima zanyi masa nasa fadan
Chapter 66 · 0% Book details