← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 67

Sashe 4

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tace duk su je su canja kaya tana zuwa. Nura yace harda ni Mama? Ta harare shi ban sani ba. Dakin Alhaji ta shiga ta tarar da Hajiya a zaune a kan gado tana kuka. Mama tace haba Hajiya kukan iyaye ga 'ya'yansu bai taba zama alkhairi ba. Hajiya ta share hawaye da gefen dankwali. To ya zanyi Kaltume? Yaron nan ko kadan ban goyi bayan zuwansa Canada karatu ba amma Alhaji ya dage. Karshe yaje ya hadu da mata itama tashin can. Mama tace shekara hudu fa kawai suka yi da babanta yaje aiki. Hajiya tace to ai dai ta zauna ko. Gabadaya sun dauko wasu al'adu daban da namu. Wadanda basu dace da addinmu ba. Kina kallo duk shekara sai sunyi party nasu da na yaransu. Sati kusan uku da suka wuce ba ya kawo mana laces ba wai na Mother's day. Na Alhaji kuwa na Father's day ai kinga bamu taba gaya masa dalilin bayarwa ba kila da zaginsa zaiyi ma. Duk wata rana da turawa suke bawa mahimmanci Yaya da matarsa suna yi. Ko da ba kowanne muke gani ba amma munsan anayi. Su a dole rayuwar turawa sukeyi. Mama tace kiyi hakuri yanzu zan kira shi a waya yazo. Dole mu sake masa magana ko mu hadashi da Alhaji. Wannan karon sun wuce gona da iri tunda suna son batawa yaranmu tarbiya. Hajiya tace Allah Ya shirya mana. Amma don baki ji yadda raina ke baci ba idan su Khalifa na kirana Granny dinnan. Mama ta kwashe da dariya. Ai gara naki ma. Nida ake kira Grams fa. Yau da bamuyi boko ba ai da mun sha kunya tunda sai kiyi musu magana ma amma su amsa da turanci. A dole sai an bambanta su da 'ya'yan yan uwansu.

Sani masinja ya dauki wayar landline din office dinsu da aka kira. Muryar mace yaji tace matar Hamza ce. Ji yayi tana kuka tace ya fada masa Junior ya fado daga kan kujera ya karye a hannu. Sani ya tashi da sauri sai ya tuna meeting din da suke yi mai mahimmanci ne. Har ya koma ya zauna ta sake kira a fada masa yanzu ya taho gida. Ta kira wayarsa a kashe. Dole Sani masinja ya shiga hall din da ake meeting din.

Architect Hamza Nasir Hamza ya juyo a fusace yace meye haka Sani? Manyan baki gareshi turawa masu son hadin gwiwa da kamfaninsa na zane da ginin gidaje da hotels da sauran manyan gine gine. Sani masinja yace ranka ya dade uwargida ce ta bugo tace Jiniya ya fado daga kan kujera ya karye a hannu. Hamza ya tashi da sauri....what? Ya dubi bakinsa yace da turanci kuyi hakuri dana ne ya karye a hannu. Sun tausaya masa suka ce zasu dawo a karasa meeting din. Amma ya daure yasa hannu a takardar shaidar amincewarsa da sharudansu. A gaggauce ya karanta ba tare da ya fahimci kalma ko daya ba yasa hannu a duka biyun. Daya tasu dayar ta kamfaninsa. Sunji dadin amincewarsa sosai suka tashi. Yana ta sauri a hanya wayar Mama ta shigo. Ya dauka a gigice a zatonsa Izzatu ce. tace Yaya kana ina ne? Mama ke ce? ina hanyar zuwa gida. Tace to maza kazo ina son ganinka. Yace Mama Izzatu bata kiraku bane? Junior ne ya karye a hannu. Yana hango wani dan sanda ya nufo motarsa saboda yana amsa waya yana tuki da gudu yaja motar kafin a bada hannu har ya kusa karawa wani. Mutane suka bishi da zagi da bakaken maganganu.

Mama ta dubi Hajiya tace bamu ga ta zama ba wai Junior ya karye a hannu. A tare suka fito daga dakin suka kiran Nura yazo ya kaisu gidan Yaya. Hamida tace Mama me ya faru? Junior ne ya karye a hannu. Yanzu yayanku yake fada min. Adabiyya tace ba gaske bane. Jiya ne Anti Izzatu tace bata san da yadda zata sa Yaya ya baro office da wuri ba. Partyn surprise take son yi masa. Bai san komai game dashi ba. Ana haka wata makociyarsu da aka bawa aikin meatpie ta shigo take cewa danta ne ya karye kuma ya kwana da zazzabi shiyasa bata aiko ta karbi kayan yin meatpie din ba. tana fita ne shine Anti tace ta sami idea din abinda zata fada masa. Hajiya ranta ya kara baci. Mama kuwa ashar ta dannawa Izzatu saboda yadda zuciyarta ke mata zafi. Ta kalli su Hamida duk sun saka material ne da mayafansu manya tace Nura ya kaisu amma ya fadawa Yaya tana son ganinsa komai dare.

Sai bayan fitar bakin sakataran Hamza yana hada takardu ya duba wadda ya saka hannu a kai. Jikinsa ne ya fara rawa ya soma salati. Wani cikin yan office din yace menene. Inuwa Sakatare yace ai bana jin oga ya karanta takardar nan da kyau. Ta nuna ya amince ya karbi kudin da suka bashi saboda haka nan da wata shida duk ribar da aka samu tasu ce. Daga wani wata shidan kuma sai su rinka raba ribar gida uku. Su kaso biyu shi kuma daya.
[9/25, 2:41 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿7

Batul Mamman(Mrs)💖

Alhaji Nasiru Hamza dan kasuwa ne mazaunin Kano amma asalin iyayensa mutanen Kumo ne na garin Gombe. Sana'ar siyar da shanu da tumaki ya fara wadda a hankali har ya fara fitar da fatar dabbobin kasashen waje yana sayarwa. Shiyasa ma aka fi saninsa da Nasiru maifata. Halima wadda suke kira Hajiya ya fara aure yar kanwar babansa. Sun fara zama a Kumo kafin kasuwancinsa ya bunkasa ya dawo Kano. Lokacin ta haifi danta na fari Hamza suke kiransa da Yaya. Suna zamansu lafiya da mijinta. Kuma suna yawan zuwa gida ganin iyayensu. Hamza na da shekara biyu ta haifi Ibrahim sai Mariya. Alh Nasiru ba karamin soyayya yake nunawa yaransa ba. Yana da amini kuma abokin kasuwanci Alh Sabiu. Kowa ya sansu tare hatta iyalinsu suna mutunta juna. Matan Alh Sabiu biyu. Kaltume ce uwargida sai Sahura. Kaltume bata taba haihuwa ba a shekarun da sukayi da mijinta. Tana dai karatu a lokacin. Ita kuwa Sahura 'ya'yanta shida. Da kamar gaske suke zaman lafiya. Sai daga baya Sahura ta rinka daukar zigar yan uwa da kawaye ta fara yiwa Kaltume habaici da gorin haihuwa. Tun bata kulawa har dai ta fadawa mijinsu akan ya yiwa Sahura magana sai cewa yayi ai ba matsayinsu daya ba. Idan taji haushi ta haihu mana. Da kadan kadan suka juya mata baya. A lokacin tayi shawara ta sanar da Halima halin da take ciki lokacin tana da ciki na hudu. Ita kuma sai ta fadawa mijinta. Ko kadan Alh Nasiru baiji dadin faruwar hakan ba. Ya zaunar da abokinsa yayi masa nasiha. Sai dai duk a banza. Wata rana Kaltume zata tafi makaranta ta shirya ta rufe dakinta sannan ta leka dakin Sahura tace ta fita. Tana dawowa da yamma ta tarar da Alh Sabiu da Sahura har da wasu makota a kofar dakinta. wasu samari ne suke kokarin balle kofar. Kaltume duk ta rude ta tambayi abinda ke faruwa. A madadin amsa sai mari da duka da Alh Sabiu ya rinka kai mata. Sahura na kuka tace muguwa saboda baki haihu ba shine zaka kashe min nawa 'ya'yan. Tunda kika fita nake neman Ihsan banganta ba. Sai dazu kawai naji kukanta a dakinki. Ba yadda banyi ba na kasa budewa, tun tana kuka har muka ji shiru. Ta cigaba da kuka ina jin ma ta mutu Alhaji. Shi kuwa sai dukan Kaltume yake har sai da aka bude dakin. A kwance suka tarar da Ihsan yar wata takwas. Sahura tace ai kawai ta mutu ko ta suma. Alhaji Sabiu ya cire babbar rigarsa yana ta dukan Kaltume. Babu mai hanashi har Allah Ya kawo Alh Nasiru. Yayi ta rokon abokinsa amma sam yaki dena dukanta. Alh Nasiru ganin babu yadda zaiyi ya ja hannunta. Sahura tace shikenan Alhaji dama tunda yake kare mata kwartonta ne. Ji yadda yake rike mata hannu a gabanka. Alh Sabiu yace ko Sahura, to ke Kaltume na sakeki saki uku in kin gama idda ki auri kwarton naki. Kai kuma Nasiru bani ba kai. Da haka abokan suka rabo. Ashe mukulli Sahura ta sata na Kaltume ta durawa yarta maganin bacci ta kaita dakin.

Halima taji tausayin Kaltume sosai barin ma da aka rinka yadawa a gari abokin mijinta ne kwartonta. Gashi ya gujeta bayan aurenta ya mutu. shi kanshi sai da abin ya shafi kasuwancinsa. Sai da ta kai ko makaranta ta dena zuwa. Har yan uwanta wasu suna kyamarta. A wannan halin ne Halima ta bawa mijinta shawarar ya auri Kaltume domin ta tsira da mutumcinta. Da kyar Kaltume da Alh Nasiru suka yarda. Bayan anyi auren saboda Halima ta lura Kaltume na son 'ya'ya ta dauki Hamza da Mariya ta kayansu ta mayar dakin Kaltume. Wannan abu ya kara musu zaman lafiya sosai. Kaltume har kullum bata yiwa Halima kallon kishiya sai yar uwa. Haka suka zauna lafiya Halima ta haifi Jidda. Daga nan Kaltume ita ta sami ciki ta haifi Nura da Adabiyya. Sannan Halima ta haifi auta Hamida. Gidansu abin sha'awa saboda kan 'ya'yan a hade yake. Daga baya asirin Sahura ya tuno Alh Sabiu yaji tana bawa yarta labari. Har gida yazo bawa Kaltume hakuri domin ya gane bai kyauta ba. A yanzu ma dai komai ya sukurkuce musu shi da Sahura don yaran babu wani mai abin kirki gasu har su shadaya.

Tun daga farkon layin gidansa yake hango motoci. Hankalin Hamza ya sake tashi sosai. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai yake fada. Shikenan Junior ya rasu.........jikinsa duk a mace yayi parking din motarsa daga can baya ya fito. Sai kawai ya kasa karasawa gidan. Kifa kansa yayi a saman motar. A wannan yanayin Ibrahim ya iso. Yana neman gurin parking don layin ya cika ya hango yayansa a tsaye ya kifa kai. Ibrahim ya fito da sauri da matarsa Ummahani da yaransu uku.
Chapter 4 · 0% Book details