← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 67

Sashe 46

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

********
Wasu matasa ne su uku duk da bakaken kaya harda abin rufe fuska suka shigo cikin kauyen da gudu da cikon na hudun a kafadar wanda yafi sauran girma. A kofar wani katon family house suka ajiye na kafadar wanda yake ta zubar da jini sakamakon harbinsa da aka yi a cinya suka gudu. Da yake tsakar dare ne babu wanda ya kula dasu. Sai can wasu maza biyu suka zo wucewa a buge suka ga mutum a kwance a kasa. Da har zasu gudu sai daya ya haska shi da touchlight, da sauri ya karaso giyar da yasha ta fara barinsa yace sa dayan kazo mu taimaka masa Felix ne kanin Mr Oscar miloniya.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 67

Batul Mamman(Mrs)

Cikin hanzari suka burkito fuskarshi suna ganinshi duk suka razana "mr.oscar yau kaine ahaka?
Afili hakkin hamza yafito,mr.oscar yana kuka yanacewa kutaimakeni na cuci hamza mutuwa zanyi wayyo Allah na.

Nidai nawa tunanin kenan,kekuma wannene naki

Gabadayansu ba karamin tashin hankali suka shiga ba. Da sauri Hamza ya koma dakinsa ya dauko wata doguwar riga ya sakata gaba a baya ya dauko Izzatu. Zuhra ma hijab ta burma ta bi bayanshi da gudu da wani mayafi da ta gani a dakin Izzatun domin a suturta mata jiki. A kasa suka tarar da Tala da Nana zata hada mata tea. Idanunta ne suka bi Hamza dauke da Izzatu ga jini a jikinta. Zuhra tace mata ta kula da gidan da yara zasu je asibiti.

Gudu Hamza ya rinka yi cikin dan lokaci suka isa asibitin. Maaikatan asibitin suka yi masa jagora zuwa emergency inda aka bukaci su tsaya a waje shi da Zuhra. Haka suka rinka kai kawo a wurin sai gashi an turo Izzatu akan gado an wuce dakin operation da ita. Hamza ya tambayi wani cikin likitocin menene ya sameta. Likitan yace bari mu fito zamu yi maka bayani. Ku dai kuci gaba da addu'a.

Sun kusa awa biyu a corridor din babu wanda yake iya yiwa wani magana. Kowa da abinda yake sakawa da warwarewa a zuciyarsa. Zuhra ce tayi karfin halin cewa Hamza ko zai yi waya gida ya sanar dasu Hajiya, jikinsa duk a sanyaye yace ya barota a gida. Itama Zuhra tace bata dauko tata wayar ba. Suna magana likitan ya fito yace Hamza ya biyoshi office. Ga mamakin Zuhra sai taji ya kamo hannunta suka tafi tare.

Ko zama basu yi ba Hamza yace don Allah ka fada min halin da take ciki. Likitan yace to ka zauna mana, Zuhra ya zaunar tare da rike mata hannu gam. Likita yace kaine mijinta ko? Hamza ya gyada kai. Ya cigaba da cewa to sai dai kuyi hakuri bamu iya saving din abinda ke cikinta ba.

Bangane ba doctor? Kana nufin tana da ciki ne.

Kwarai kuwa don har ya kusa wata biyu. To matsalar da aka samu shine mahaifar bata da kwari kwata kwata. Don ita da abinda ke cikin tare suka fara fitowa.

A gigice Hamza yace fitowa kamar yaya?

Ina nufin bari tayi wanda har mahaifarta ta fara fitowa saboda rashin kwarinta. Shiyasa muka ga dole muyi mata virginal hysterectomy saboda ceto rayuwarta.

Kokari Hamza yake kada ya rasa nutsuwarsa yace kayi min bayani a yaren da zan gane. A wane hali Izzatu take?

Likita yace yanzu tana bacci saboda anyi mata allurar anasiziya. In sha Allah nan da kamar awa daya zata farfado. Abinda nake nufi da hysterectomy shine mun cire mata mahaifa saboda ba karamin lalacewa tayi ba.

Wata muguwar faduwar gaba Hamza yaji wanda hakan yasa shima ya zauna. Zuhra ta sake kankame hannunsa saboda firgici. Yace doctor kana nufin yanzu bazata sake haihuwa ba.

Haka nake nufi amma don Allah kayi hakuri bamu fara sanar da kai ba kafin mu aiwatar da nufinmu. Yanayin da take ciki ne baya bukatar bata lokaci. Idan ta tashi ita tafi cancanta da ta fadi maganin da tasha ya illata mahaifar haka. Bazamu iya yanke komai ba sai munji daga gareta. Tashi likitan yayi ya barsu a office din bayan ya gama yi musu bayani.

Yana fita Zuhra ta rungume Hamza tana kuka. Kayi hakuri Ya Hamza duk laifina ne. Ganina ne ya bata mata rai har hakan ta faru. Da hannunsa ya share mata hawaye...ki dena fadin haka Cutie kaddara ce da bata wuce kowa. Amma shima a kasan zuciyarsa gani yake kamar laifinsa ne tunda Izzatu ta fada masa ranar zata dawo, sai abin ya zama kamar cin fuska ma.

Sabon dakin da aka kai Izzatu suka je. A nan ya bar Zuhra yace zaije gida ya fada musu tunda baizo da waya ba.

******
Daga Hajiya har Mama babu wanda labarin yayi masa dadi. Duk sun tausayawa Izzatu. Mama tace watan cikin nawa? Ni ban san dashi ba Hamza ya bata amsa. Sai a lokacin ta kula da rigarsa tace ya gyara ta. Kunu da kayan tea suka hada ya daukesu ita da Hajiya da Adabiyya ya kaisu asibitin sannan ya dauko Zuhra suka tafi gida. Har lokacin Izzatu bata farfado ba.

Saboda yanayin da suka fita maigadi da Tala suna ganinsu suka fara tambayar ya mai jiki. Zuhra ce take iya basu amsa tana cewa da sauki. Wanka duk suka yi sannan Zuhra ta sauko ta hada masa abinci. Da kyar ta samu yasha tea yace zai koma asibitin. Damuwa ce tayi masa yawa yana tambayar kansa ta ina zai samo kudin asibitin Izzatu? Bashi da sauran kadarar da zai sayar sai wani fili da ya siya a Kumo wanda yanzu kafin a samu mai siya ma aikine guda. Shi ko irin budewa yara account dinnan bai taba tunanin yi ba saboda basu hango rana irin wannan da zasu fuskanci matsin rayuwa ba.

Zuhra na kallon yadda ya zurfafa a tunani ta dan dafa kafadarsa. Ya Hamza kaine fa kake cewa kaddara ce abinda ya faru. Don Allah kayi hakuri. Idan ka bari damuwa tayi maka yawa waye zai rarrasheta idan ta farfado? Murya a sanyaye yace babbar damuwata yanzu inda zan samo kudin asibitin Izzy. Kinsan halin da nake ciki bansan inda zan samo kudin ba indai ba kudin kamfani zan dauka ba. Zuhra tace idan ka dauka aikinku zai sami rauni. Kuma kace har kun kusa kammala daya. Ta mike tsaye ina zuwa....

Bata dade ba ta dawo da wata karamar leda mai kyau a hannunta. A tafin hannun Hamza ta ajiye ledar yace koma meye ki rike kayanki zansan yadda nayi na sami kudin. Ko bashi ne sai na nema. Idonta fal hawaye tace yanzu ka gwammace ka nemi bashi akan ka karbi abinda kake da iko dashi? Wannan abin da na baka kai ka siya fa? Idan ka karba ai ba yana nuna gazawarka a matsayin namiji bane. Jarabawace Allah Ya dora maka.

A hankali ya bude ledar ya ciro wata yar roba mai murfi. Sarka ce da dankunne da zobe na gwal a ciki. Saurin rufewa yayi ya dora mata a cinyarta. Cutie ki dauke kayanki bazan sayar miki da sarkarki ba....abinda ya kasa fada shine ko pant bai siya mata ba a lefenta. Komai Alhaji ne yayi. Hannuwanta biyu tasa ta rike kumatunsa tana kallon fuskarsa mai dauke da tsantsar rashin kwanciyar hankali. Tunda nake ban taba saka gwal ba a rayuwata don an sayar da wanan bazanji komai ba. Duk irin wadannan abubuwan dama ai saboda rana irin yau ake tanadin su. Ni a abinda su Baba suka koya min wannan shine aure. Taimakon juna a lokacin bukata batare da mun fita waje mun tonawa kanmu asiri ba. Su Alhaji ne baka son sanarwa halin da kake ciki to ni din da na sani ka bani damar taimakonka mana. Sarkar da hannunta ya hada ya rike sosai sai kawai taga hawaye ya fito daga idonsa. Lallai rayuwa bata da tabbas, babu wani yanayi da bawa zai tsinci kansa yace wannan yanayin zai tabbata a ciki har ranar busa kaho. Yau kana da arziki gobe waninka ne. Wa zai taba tunanin akwai ranar da Architect Hamza Nasir Hamza zai karbi taimako a hannun Fatima Bashir? Yarinyar da ko certificate din shaidar tayi secondary school bata dashi,ga kazanta ga rashin wayewa. Ikon Allah kenan, kada ka taba raina bawa domin baka san abinda Allah yayi masa na arziki ba. Arziki kuwa ko da ba na kudi bane. Hawayen da Hamza yake yi ya karyar mata da zuciya ta soma kuka. Haka suka rungume juna na tsawon lokaci. Daga baya Hamza yace ta tashi su koma asibiti tace a'a yaje kasuwa ba'a rasa masu bude shago ranar lahadi ya sayar. Ita kuma zata kara yin saka zuwa la'asar ko bai dawo ba zata yi girki ta tafi asibitin da kanta. Sai da ya kwashe kusan minti biyar yana kissing dinta sannan ya fita. Bai san da yaya zai gode mata ba. Tunda ya shiga mota har ya isa kasuwar ALHAMDULILLAH yake ta nanatawa saboda godiya ga Allah da Ya azurta shi da mace tagari a lokacin da rayuwarsa take tsaka da rushewa.

A dalilin mugun tashin da dollar tayi wanda muke ta addu'a Allah Ya yafe mana Ya kawo mana sassauci sai da Hamza ya sami dubu dari uku da tamanin da hudu a matsayin kudin sarka, dankunne da zobe. A haka ma don mutanen sun kula kamar a matse yake da ya sayar.
Chapter 46 · 0% Book details