← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 67

Sashe 42

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuhra na kan riga ta bakwai Hamza ya shigo dakin da sallamarsa. Kafadarta ce ta dan rike saboda kwana biyu bata sakar ta dan tsaya tana dukan wurin. Ganin Hamza ya shigo yasa ta murmushi. Ya Hamza har ka tashi? Nayi tunanin sai ka kai karfe daya. Yace saboda ga kasa sarkin bacci ko. Murmushi tayi tace ni dai bance ba, naga yau asabar ya kamata ka huta. Maimakon yayi magana zagayawa yayi ya tsaya a bayanta sai ji tayi yasa hannuwansa yana mata tausa a kafadunta. Da farko kunya taji sai kuma ta soma dariya saboda ji take yi kamar yana mata cakulkuli. Sosai take dariya har ta fara kokarin tashi ta gudu yace ke dai kina da matsala. Kiyi ta dariya kamar shashashan madina. Da kyar take mayar da numfashi tace to ai kaine kasa ni dariya.

Daga yi miki tausa sai kice na sakaki dariya? To ajiye ki huta ya fada tare da daukan riga guda daya. Yayi murmushi Cutie ashe dai ba cika baki kike yi ba kin iya sakar. Kanta a kasa tana cigaba da aikinta tace kaima zanyi maka kafin na tafi. Amma dai yanzu ka fita idan na ganka bana iya aikin sosai. Ya dan durkusa a gaban injin yana dariya da gaske Cutie? Ko dai kin fara sona ne? Ta dago idonu a bude ni di??? Rufa min asiri Ya Hamza ina ni ina kai. Nifa har na yanke shawarar wanda zan aura idan ka sakeni.

Kamar saukar mari yaji maganarta. Harara ya watsa mata ya fice ba tare da ya sake magana ba. Da taji ya rufe kofar tayi dariya, ita tsokanarsa kawai tayi amma tunda ta ga yaji haushi ta daga hannu sama. Ya Allah Kasa shima yana sona ko dan kadan ne. Ba ita ta fito daga dakin ba sai azahar ta dafa taliya tayi sallah. Har ta idar su Khalifa basu dawo daga masallaci da Hamza ba. Ajiye musu abinci tayi ta kai masa nasa falo ta koma ta cigaba da aiki.

Bayan sallar magariba Inuwa sakatare yazo, Hamza ya sanar da ita zasu fita tayi masa adawo lafiya. Ranar gabadaya Zuhra a saka ta tafi sai sallah da girki da take tashi tayi. Wurin karfe goma ta fito saboda yunwa. Su Khalifa duk sunyi bacci Tala ta kaisu dakinsu ganin Zuhra na aiki. Abinci ta diba da ruwa ta tafi dakinta dashi saboda ko sallar isha bata yi ba. Sai da ta zauna zata ci abincin taga babu cokali. Wanko hannunta kawai tayi a toilet ta zauna taci. A gajiye take sosai ga kafadunta da baya duk suna ciwo. Gajiya da bacci ne suka tarar mata a kan doguwar kujerar da taci abincin ta dan kashingida sai bacci ko hannu bata wanke ba.

Hamza ya dawo gida bayan ya ajiye Inuwa a nasu gidan. Unguwar su Mr Oscar suka je ko akwai wanda yake da labarin inda ya tafi basu samu ba. Dakin da Zuhra ke saka ya duba ya tarar da riguna birjik a kasa ga fitila bata kashe ba ga dukkan alamu zata dawo ta cigaba da aikin ne. Bashi da niyar barinta ta cigaba a ranar saboda yasan ta gaji. Dakinta yaje ya tarar da ita tana bacci a zaune ga plate din abinci a gefenta a kan kujera. Ya duka zai tasheta ya kula da hannunta duk miya har ta soma bushewa. Da gani tana jindadin baccin sai yaki tashinta. A hankali yace Allah Sarki Cutie yasan ba karamar gajiya tayi ba. Tissue ya samo ya goge mata hannun, ya sauke plate din ya gyara mata kwanciya ya fita. Tausayi ta bashi sosai yadda ta dage tana saka ga girki tana yi akan lokaci.

Kusan minti talatin da fitarsa yaji kamar ihu daga dakin Zuhra. Lokacin bai dade da kwanciya ba. Da sauri ya fito ya ganta a tsaye ta rike hannunta na dama tana kuka sosai. Saurin matsowa yayi kusa da ita Cutie me ya same ki? Kara matsawa tayi baya tana kuka tace kada ka matso Ya Hamza ni tawa ta kare. Bai fahimci inda zancen nata ya dosa ba yace taki ta kare kamar yaya? Ki dena kukan kiyi min bayani.

Murya a shake tace abinci naci a wurin nan, ta nuna kujerar...sai bacci ya daukeni amma na tabbatar ban wanke hannu ba. Ina farkawa yanzu naga alamun an lashe hannun amma dai da saura kadan. Hannun damanta ta daga ta nuna masa. Yayi murmushi zai fada mata shi ya goge mata da tissue ta cigaba da magana. Ashe ni kuma a haka zan tafi Ya Hamza, Allah ma Ya sa mutuwa a dalilin annoba ana sakata cikin shahada. Ta sake barkewa da kuka, bera ya lashe min hannu Ya Hamza, ya saka min zazzabin lassa. Yadda Zuhra take kuka da gaske ya bashi dariya sosai. Yace banda sharrinki Cutie kin taba ganin bera a gidan nan. Tace shi bera ina ne baya shiga. A yadda naji a rediyo mutum ba wani dadewa yake ba idan ya kamu da ita.

Dariya Hamza yake son yi amma ya gimtse. Zuhra bata da dama ya fada a ransa. Hannu ya mika mata zo kinji Cutie dina, babu wani bera ki kwantar da hankalinki. Can karshen dakin ta koma kada ka tabani ka kwasa kaima. Ka barni kawai anan har lokacina ya cika. Kodayake naji ance gwamnati na bayar da magani ka sanar dasu akwai mara lafiya a nan sai suzo su daukeni. Ta sunkuyar da kai, nasan ma dakyar zan kai labari. Shi dai Hamza dramar Zuhra nishadi ma ta saka shi ya zauna akan kujerar da ta tashi tace tashi kada ka dauka anan na kwanta. Yana kallo tasa hannun hagunta ta dan tattaba wuyanta. Kaga har na fara jin zazzabin kuwa. Yace Allah ko Dr Zuhra yana murmushi. Sake taban wuyan tayi tace inajin ba zazzabin bane amma shima nasan yana kusa.

Hamza ya taso ya taho wurin da take tsaye ni zan zauna dake ko wane irin ciwo kike dashi kinji. Hannu ta daga masa alamun kada ya matso fuska duk hawaye tace Allah Sarki Ya Hamza shiyasa nake SON ka wallahi saboda kana da kirki da tausayi. Cak Hamza ya tsaya maganarta ta sauka a zuciyarsa. A hankali ya daga kai ya kalleta. Da gaske kina sona Cutie? Kunya taji har ta soma girgiza kai sai ta dena ta dago tana kallonsa. Ya Hamza idan mutum zai mutu ai babu zancen kunya da karya ko? Gara ma na fadi gaskiya na sami lada. Hamza yace wannan gaskiya ne. Zuhra harda gyaran murya tace nasan munyi daku zaka sakeni bayan wata shida to Allah Ya gani wallahi ni bansan ya akayi ba sai naji ina sonka. Ba a matsayin Yayana ba fa. Dadi Hamza yake ji sosai sai ya dan basar to a matsayin me? Sunkuyar da kanta tayi tana magana a hankali. Wallahi Ya Hamza irin na soyayya nake maka jiya har mafarki nayi ka kaini asibiti zan haihu. Amma kada kace min mara kunya wallahi ina zaman zamana tunanin yake zuwa. Kuma in fada maka wata gaskiyar ma duk sallah a sujjada sai nayi addua'a idan da alkhairi Allah Yasa kada ka sake ni. Tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha haka Hamza yake ji a wannan lokacin. Ashe ba shi kadai yake sonta ba suka yi shiru da zasu kwari kawunansu. Ya dan bata rai dazu kika ce bakya sona kuma har kin tsayar da mijin aure. Tace wallahi karya nake, irin abin nan ne na mata zan maka ashe ma bani da rabon dadewa a gidan aure.

Ko kanta ta kasa dagawa saboda yadda take jin kunya gashi zata mutu ko soyayyar basu fara ba. Takun Hamza taji ya matso gabanta yasa hannu ya bude bargon da ta rufe kanta dashi. Kuka take tana rokonsa zai kamu da zazzabin lassa. Hamza yayi mata kyakkyawan murmushi sannan ya dauketa tamkar ya dauki karamar yarinya. Da wata bakuwar murya mai dadi yace Cutie ni na goge miki hannun da tissue, ta ware masa idanunta da yake son kallo tace da gaske? Ya gyada kai. A take kunya mai tsanani ta lullube Zuhra. Hamza yayi murmushi yace bari na karasa lada na nayi miki wanka, sai na fara koya miki lesson din soyayya. Irin soyayyar da zata sa mafarkinki na jiya ya tabbata nan da wata tara. Kanta ta tura a kirjinsa don kunya ta kankameshi. Zuciyarsa cike take da son Zuhra yace kinsan wani abu? Girgiza kai tayi batare da ta dago ba...I love you too Cutie. Nima bansan yadda akayi ba sai kawai naji ina matukar sonki. Dadi ne ya mamaye zuciyarta wai ita Hamza mijin Izzatu yake furtawa so. Tafiya taji ya fara yi da ita hanyar toilet ta soma kokarin zillewa.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 63

Batul Mamman(Mrs)

A kofa toilet ya ajiyeta ya fara juyata a gabansa yana karewa kayan jikinta kallo. Kokarin rufe jikinta ta soma yi yace wai ni ta ina kika saka rigar nan? Duk na duba na rasa maballi ko zip. Ajiyar zuciya tayi mai karfi tana murna da bai gani ba. A tsorace take da Ya Hamza. Janyota yayi jikinsa ya zagayeta da hannuwansa. Daga gefen kafadarta ta dama taji ya kama zip din wanda yake boye a jikin riga ya soma sauke mata shi kasa. Duk yadda tayi ta gudu abu ya gagara. Jiki na rawa tace Ya Hamza don Allah banda wanka. Yace kin manta sunnah ne? A'a amma akwai wasu dayawa. Idan nayi wankan da kaina duk abinda kake so zanyi maka. Wani murmushi yayi mata wanda shi kadai yasan ma'anarsa yace to amaryata. Zan jiraki a daki. Sai da ya manna mata kiss a goshi sannan ya tafi.

Sai yanzu take jin tsoron Ya Hamza kuma. Wanka zatayi kawai tayi kwanciyarta. Ta dade tana kalkale jiki ta fito aka bata lokaci a gaban mudubi ana ta shafe shafe. Turaruka ta saka masu kamshi sosai da daukar hankali sannan ta daura zani ta tayar da sallar isha da bata yi ba. Tana idarwa ta cire hijab ta fara neman rigar da zata saka. Daga ita sai daurin kirji Hamza ya turo kofar.
Chapter 42 · 0% Book details