Sashe 20
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka rayuwa ta kasancewa Zuhra a gidan Hamza. Kullum safe, rana da dare duk zaa kawo mata abincin marowata kamar yadda take kiransa. A kullum zata yi waya da iyayenta. Idan bata kira ba zasu kira ta. Idan aka tambayeta Hamza tace yana nan kalau. Bata taba tunanin fadin komai ba domin Anti Faiza tace zaman gidan miji yana bukatar sirri. Ko Hajara ta hanata ta sanarwa komai na dangane da gidan aurenta. Hamza dai yasan ana bata abinci saboda haka bai taba damuwa da sanin yawansa ba. Idan ta fito sauka da kwanunkan abinci suka hadu da Izzatu zata gaisheta a ciki ciki. Itama da kyar take amsawa. Don Hamza yayi mata fadan baya son gaba ne da ko kallon Zuhra bazata yi ba. Shi kuwa matsalar kamfaninsa tasa shi a gaba, bashi da lokacin gidansa sosai.
Ranar alhamis da safe Tala ta kawo mata abinci kamar kullum. Tea ne a dan karamin cup irin mai saucer dinnan wanda kurba biyar zuwa shida zai kare. A plate din kuma sliced bread ne guda uku. Wani irin kallo Zuhra ta yiwa abincin. Ta dauki bread daya taji shi a bushe da tauri. Murmushin yake tayi... Tala yau kuma bushasshen brodi kike kawo min. Tala ta dawo ta dan durkusa gabanta amarya ai wannan tos ne. Tala zata yi sa'ar Izzatu ko ta girmeta da kadan. To...to me? Zuhra ta fada tana yamutsa fuska. Tala tace tos. A tosta ake sakawa sai kiga ya fito ta sama kamar an jeho shi. Har dan bota na shafa miki don kiji dadinsa. Zuhra ta gyada kai, naga alama. To nagode.
Bayan fitar Tala tayi ta juya bread din a hannunta. Tunda tazo gidan breakfast dinta na farko ne kawai ta taba koshi. Kullum sai dai rage hanya, gashi bata taba ganin alamar za'a fara aikin nata kitchen din ba. Ba yadda ta iya a dole ta fara cin bread din. Kana ganin fuskarta kamar mai shan madaci. Ko rabi bata ci ba ta shanye tea din. Ta sake kai bread din bakinta Hamza yayi sallama ya shigo batare da ya jira ta amsa ba. Zaune take da tray a gabanta kanta babu dankwali. Doguwar riga ce a jikinta ta wani material. Dinkin dai yayi kyau sai dai wadda tasa kayan ce sai a hankali. Sunkuyar da kanta tayi kasa tace ina kwana?
Bai amsa ba yana daura agogo a hanunsa ya dubi plate din gabanta. Ashe ma zaki iya ci. Dama naga toasted bread aka yi nayi tunanin baki saba ci ba a baki wani abincin. Zuhra tayi sauri ta tofar da na bakinta akan tray din. Wallahi bana iya ci, hakan ma dauriya ce kawai.
Hamza ji yayi kamar ya amayar da abinda yaci. Wannan wace irin kazanta ce ta gama jika bread a bakinta ta dawo dashi. Fuskarsa na kallon gefe yace naga saura biyu da rabi ki cinye. Tashi tsaye tayi tana karkade hannuwanta...wallahi dama uku ne. Dan murmushi yayi...haka Izzatu take bata son ayi abinci da yawa, a cewarta zasu yi kiba suyi loosing shape. Farkon aurensu har rama ya rinka yi. Daga baya sai yake siyan biskit da cake a ajiye a office. Kyalesu zaiyi, kila idan Zuhra ta dan horo zata nemi komawa gidan iyayenta. Sai ya saketa cikin sauki. Ba tare da ya kalleta ba yace zansa a kawo miki wani abincin. Da ya juya zai tafi yaji tace adawo lafiya, Allah Ya kiyaye, Ya bada sa'a, Ya tsare kuma Ya kare dukkan sharri. Adduar tayi masa dadi yace Amin a hankali. Wannan adduar kullum Umma sai tayiwa Baba idan zai fita wurin sana'arsa.
Tunda ya fita bata ga alamun abinci ba sai uku saura aka kawo na rana. Cikin kankanin lokaci ta tayar da abincin. Ta fito daga toilet kenan Tala ta shigo tace amarya kinyi baki. Shikenan anzo wurin.....kullum addua take yi kada tayi baki saboda bata san me zata basu ba, yau gashi wasu sun zo. Tunani ta soma yi lokaci guda idea ta zo mata. Kanta ta rike da hannu biyu ta rufe ido. Tala kaina ciwo yake min sosai kamar zai tsage. Tala tayi saurin karasawa ta riketa har bakin gadonta. Sannu amarya ko na karbo miki magani wurin Anti Izzatu? A'a Zuhra tayi saurin dakatar da ita. Nima ina da shi. Kice su hawo nan bazan iya saukowa ba. Tala duk tausayin Zuhra ya kamata tace ba komai amarya. Kafin ta fita Zuhra tace ki dan taimaka musu da ruwan sha don Allah.
Tana fita Zuhra ta gyara kwanciya. Bata san ko su waye ba amma dai tasan gidan amare ana son a bawa baki dan abin kusa da baka. Ita kuma bata da komai, idan za'a bata ma karba zata yi.
Ba jimawa yan uwansu na Ajingi suka shigo. Kirikiri Zuhra taki tashi tana ta langabewa ita mara lafiya. Da muguwar rawa gwamma kin tashi. Anti Faiza ce ta rako su. Suna ta mata tsiya ko har an fara laulayi ne na kwana biyar. Ita dai sai murmushi take yi a dole taji kunya. Tala ta kawo musu ruwa harda lemo a jug da kofona. Basu dade ba suka ce gobe zasu koma Ajingi. Tayi musu godiya ta rakasu har kofar daki. Sai da suka sauka kasa Anti Faiza ta dawo da sauri take tambayarta yaya zaman nata. Kuka Zuhra tasa mata ta sanar da ita ko abincin kirki ba'a bata. Anti Faiza tace kiyi hakuri gobe za'a kawo gararki. Akwai kudi ne a wurinki? Zuhra ta share hawayenta tace eh Baba ya bani. Duka ta debo ta bata Anti Faiza ta dauki dubu goma a ciki ta bata sauran. Zanje kasuwa gobe kafin azo kawo garar zan zo in sha Allah. Ta dafa kafadarta...ki kara hakuri kuma kada ki bari Izzatu ta san ba kya jindadin zaman. Daga ita har mijin nata so suke kiyi abinda zai sakeki. Kuma In sha Allah kinzo kenan, yadda iyayensa suka yi miki kokari kema ki dage nemawar kanki wurin zama a zuciyarsa. Zuhra ta tura baki ni me zanyi dashi Anti? Ai kawai idan ya gaji ya sakeni. Anti Faiza toshe mata baki tayi. To banza na sake jin zancen saki sai na fasa miki baki. Biskit ta dauko guda biyu a jakarta ta bawa Zuhra sannan ta sauka kasa suka tafi.
Fitarsu ke da wuya Izzatu ta shigo tare da Tala. Zuhra tana kwance akan kujera ta gansu. Tashi tayi zaune tace lafiya cike da tsiwa. Fuskar Izzatu a daure tace ke kika ce Tala ta bawa bakinki ruwa da juice a jug dina? Zuhra ta kalli Tala tayi tsuru tsuru. Kiyi hakuri na zata mijinmu ne ya saya shiyasa nace ta taimaka ta kawo. Izzatu ta soma fada rai a bace...mijinmu fa kika ce? Yanzu Zuhra don baki da kunya sai ki hada baki da inlaws dina ki auri mijina kawai don kinga ina sakar miki fuska. To Tala mai aikina ce ni kadai kuma kada ki sake taba min kaya. Ignorant fool yadda kika zo haka zaki fita ki bar min gida. Zuhra tayi yar dariya ko na kwana daya ne Izzatu kin taba zama da kishiya a tarihin rayuwarki. Izzatu ta tsaya tana kallon Zuhra..dama bata da kunya? Kwafa tayi sannan ta fita tare da buga kofar da karfi. Tala ta dauki tray din Zuhra na bata hakuri tace babu komai. Ita sai mamakin wannan aure na ubangidanta take da yadda suke wulakanta amaryar. Zuhra tayi murmushi ko ba komai yau ta dan gasawa Izzatu magana taji dadi.
Daren ranar ba'ayi girki ba ana jiran Hamza ya kawo abinci daga tantalizers. Da yake bai fito office da wuri ba abincinsu ya kare sai snacks ya siyo. Yana wanka Izzatu ta rabawa kowa banda Zuhra. Shima burger yaci ya kwanta a zatonsa an aikawa Zuhra nata. Tala tana son tambayar na amarya tana tsoro don ba karamin fada Izzatu tayi mata ba.
Har shadaya da rabi babu abinci babu dalilinsa. Dole Zuhra ta karasa sauran biskit din da Anti Faiza ta bata ta shiga toilet ta sha ruwa sannan ta kwanta ciki na kukan yunwa.
[9/25, 3:52 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 34
Batul Mamman(Mrs)
Kafin Hamza ya dawo daga raka su Mama mota tayi saurin shigowa ta hayewarta sama tana murza hannunta wanda ya matse mata harda hawayenta. Tala tana kwashe trays din da aka yi amfani dasu Izzatu ta tsaya mata a ka. Nace Tala ko kin gaji da aikin ne? Ido ta zaro a'a Hajiya wani abin ne ya faru? harara Izzatu ta jefa mata. Jiya banyi miki magana akan yiwa bakin yarinyar nan amfani da kayana bane? Tala tace Allah Sarki ai naga harda maman Alhaji shiyasa na dauko musu. Kiyi hakuri. Izzatu tace ba mamansa bace kishiyarta ce. Kuma na karshe kenan da zaki taba min kaya da sunan karrama bakinta. Wallahi ranar zaki koma kauyenku. Daga nan ta juya ta koma kan kujera ta zauna tana huci. Yadda Mama da su Mariya suka ki amsa gaisuwarta ke damunta. Kwafa tayi inma suna rawar kafa ne sun koma bayan amarya zata bar gidan ne da wuri. Su basu san wasa bane ko abubuwan nishadi da har zasu ji haushin abinda tayiwa Zuhra asa mijinta aurenta. Tana ta karkada kafa tana mita a ranta Hamza ya shigo yayi hanyar sama. Da bibbiyu yake tsallake steps din. Murmushin mugunta tayi Allah Yasa daga nan ya saketa kowa ya huta.
Zuhra na tsaye gefen kujera tana hawayen yadda hannunta ke zafi tace kuma Allah Ya isa na....dawa kike taji Hamza ya fada yana shigowa dakin. Duk da ta tsorata cike da tsiwa fuska duk hawaye da majina harda murguda baki tace da wanda ya tsargu. Baki Hamza ya saki lallai yarinyar nan bata da kunya. Shi saboda yadda yaki jinin raini shiyasa baya shiga sabgar autarsu Hamida. Itama tsiwa ce da ita....