← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 67

Sashe 21

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ke, dani kike? Share shi tayi ta cigaba da matsa hannu. Tsawa ya daka mata ke ba kya jina ne. Nace ni kike yiwa Allah Ya isa? Waige ta soma yi hagu da dama ita a dole bata san da wa yake ba. Ransa ya kara baci yayi kanta. Da gudu ta kara shigewa cikin dakin sai da ta kai jikin bango. Kafa yasa ya buga kofar da karfi daidai da bugawar zuciyarta. Sai rarraba idanu take. Wani irin kallo yake mata kafin ya sake cewa wai kina ji ina tambayarki kin kasa bani amsa saboda ki nuna min ban isa ba. Tsoro kam ta gama ji amma ta rantse bazata yi shiru ba tace au dama dani kake? Maganar ta sake sosa masa rai ya biyota har inda take tsaye jikinta ya soma rawa. Tana cigaba da hawaye tace to ai ke naji kace ni kuma da aka haifeni Baba saniya da rago ya yanka ya rada min suna Fatima. Dayake sunan Innarsa ne da kuma Ummana shine ake kirana Zuhra. Ta turo baki sai ka zabi daya a ciki ka dena ce min ke kamar wata...yan lips din nata ya kama da yatsunsa biyu. Taji zafi ta fara kokarin cire hannun nasa. Idan kika ki tsayawa tsinkesu zanyi sai naga na tsiwar . Idanunta duk sun firfito sai hawaye sharrr.

Sai lokacin ya kare mata kallo. Ba wani tsahon kirki gareta kuma tana da jiki madaidaici. Kalar fatarta bata da haske sosai amma kuma ba baka zaa kirata ba. Akwaita da idanuwa masu kyau ga hancinta da baki duk yan madaidaita. Banda rashin iya kwalliya da itama zata shiga jerin matan da basu da muni. Hijabin jikinta ya kalla duk yasha hawaye da majina. Sai lokacin yaji kyankyami ya sakar mata lebe. Ta karkace baki ta sake cewa Allah zai saka min. Kan gadon ta haye zata zagaye shi ta gudu. Yasa hannu ya fizgota ta saki kara. Da karfi ya manna ta da bango ta runtse idanunta tana jira ya sake kama leben. Dalli taji masu zafi guda uku ta sake cewa Allah Ya....wani ya kara mata da yafi sauran zafi. Nan da nan ta soma kuka mai sauti. Irin kukan da idan ta fara a gida har makota sai sun leko an bata hakuri take denawa.

Hamza huci kawai yake don bacin rai. Me zaisa Alhaji ya hadashi aure da wannan mara kunyar yarinyar. Gashi ta kafeshi da idanu kamar wani sa'anta. Yi min shiru ya fada da karfi. Tsaf ta hadiye kukanta. Ina so kisan cewa ba'a min rashin kunya. Sannan kika kara cewa Allah Ya isa sai na dirje miki baki. Kina jina? A hankali ta gyada kanta domin taji zafi a bakin da ya dalle. Good ya fada, me yasa baki fada min za'a kawo gara ba? Kuma a ina kika sami abinda zaki bawa bakin? A hankali tace Anti Faiza ce ta kawo. Ga gidan yunwa ko, shine abinda za'a bawa baki ma sai kin roka don ki jawo min magana ace bana kula dake. Hannu tasa ta rufe bakinta sannan tace nima bansan zasu zo ba sai jiya. Kuma ban ganka ba bare na fada maka. Ni duk abinda kuke yi min banji haushi ba sai....sai me ya tambaya da yaga ta kasa karasa maganar. Ba komai ta sunkuyar da kai. Zare mata ido yayi bazaki fada ba sai na kara dalle bakin. To ba kaine jiya kace zaka aiko min da abinci ba amma naji shiru. Da daddare ma kuka barni na kwana da yunwa. Wani iri yaji a jikinsa...kika kwana da yunwa??? Nufinki ba'a kawo miki abinci ba. Zaka ce baka sani bane.....auuuu, tayi saurin rufe kanta da hijab kada ya sake mata wani abin. Ga mamakinta shiru taji tana dago kai har ya bude kofa sai ya juyo. Da sauri ta sake rufe bakinta. Key din kitchen din ya jefo mata gashi nan zansa a hada miki gas cooker. Bai kula ba yayi tafiyarsa. Key kuwa a goshinta ya sameta ta soma tsalle tana ihu. Allah Ya isa ta fada a hankali.

Kasa ya sauka ya sami Izzatu tana kallo. Tana ganinsa ta taso Baby....hannuwanta ya ture da take shirin taba shi. A wane dalili ne jiya baki bawa yarinyar nan abinci ba? Wani irin kallo ta masa Why do you care? Saboda matata ce hakkinta ne na ciyar da ita. Matarka fa kace Hamza? Har Zuhra takai matsayin da zata hada kai dani. Wallahi sai ka saketa a yau....wayarsa ce ta soma ringing. Yana dubawa yaga manajan bankin da ya tura Inuwa ne ya karbo kudi a cigaba da aikin ginin da suke yi. Izzatu sai fada take yana daga mata hannu tayi shiru taki.

Mr Oscar ya gama tsorata tunda manajan yace bari ya kira Alh Hamza ya tabbatar ko shi ya aiko shi. Ya gama hango kansa a matsayin korarre daga aiki kila ma a rufe shi. Bayan sun gaisa manaja yace Alhaji dama na kira ne domin confirming ko kai kayi authorizing cheque na 10 million. Gefe Hamza ya dan matsa amma Izzatu har nan ta biyo ita wallahi ko ita ko Zuhra. Daidai sanda manaja yace ka turo Mr Oscar Hamza baiji ba amma tunda yasan ya turo Inuwa sakatare sai yace eh ya ajiye wayar. Ya juyo ransa ya gama baci Izzatu ki shiga hankalinki dani wallahi. For God's sake ya kike so nayi da rayuwata ne. Daga ke har yarinyar da kika yi sanadiyar zuwanta gidan nan bakwa gabana. Duk kin birkita min lissafi lokaci guda. Da kamfanin zanji ko masifarki? Come on get out of my way ya tureta ya fice don ya kusa makara masallaci.

Mamaki ya kama Mr Oscar lokacin da manaja ya bada order a bashi kudin. A tsorace ya karba jiki na rawa yana ta tunanin kada ace ya dawo dasu. A daidai bakin gate suka hadu da Inuwa sakatare. Cikin Mr Oscar ya murda sosai ji yake kamar ya saki zawo don firgici. Inuwa yace Oscar kaima ashe kana banking a nan. Nima sauri nake kada su tashi kasan yau Friday Oga ya aiko ni. Kai kawai Oscar ya gyada yayi gaba yana kankame jakar kudin.

Inuwa bai kawo komai ba ya shiga bankin. Shima wurin manaja aka kaishi saboda yawan kudin. Manaja yace kuma kaga yanzu wani maaikacin kamfaninku ya karbi the same amout na 10 million. Hala babban project ne a gabanku. Inuwa sakatare yace Oscar ma kudin kamfani ya karba? Manaja yace eh har da Oganku nayi confirming. Inuwa yayi mamaki dai amma sai ya karbi kudin ya tafi. A iya saninsa shi kadai Oga yake aika banki.
[9/25, 3:52 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 33

Batul Mamman(Mrs)

Washegari Jumaa tun bakwai da rabi Hamza ya fita zuwa site din da suke wani gini. Dama a daren Izzatu ta kai masa karar Zuhra wai tayi mata rashin kunya. Da safe ta sake tuna masa yace idan ya dawo zaiyi maganin abin. Yau bakin shayi da bread aka kaiwa Zuhra a matsayin breakfast. Bata nuna damuwa ko kadan a fuskarta ba da Tala ta kai mata. Tasan Izzatu na neman suyi fada ne ita kuwa bazata biye mata ba. Bayan ta gama sha ta dauki kofin ta sauka kasa.

Junior ne ya tareta a kofar kitchen din...Zuhra meyasa kika dena cin abinci tare damu? Shafa kansa tayi babu komai nafi son zama a daki ne. Hannunta ya rike to nima zan rinka zama a dakinki. Khalifa ya taho da sauri ayi hirar dashi suka hada ido da Izzatu. Ba shiri ya koma dakinsu don yasan ma'anar wannan kallon. Tsawa ta dakawa Junior tace ya bar wurin. Ya buga kafa a kasa ni Mummy ki kyale ni Zuhra is my new fiyend(friend). Karasowa tayi gabansu ta kalli yadda suka rike hannu. A sakar min hannun yaro ko. Zuhra ta durkusa a gaban Junior. Kaga tunda Mummy tace ka tafi to ka zama yaron kirki kaji. Watarana har goyaka zanyi,amma yanzu idan kana rashin kunya babu ruwana da kai. Murmushi yayi wanda ya kara fito da kammaninsa da Hamza. Pyomis(promise) ya fada yana tsalle. Dariya kawai tayi don bata gane abinda yake nufi ba. Ga mamakinta dage yayi ya mata kiss a goshi tunda durkushe take a gabansa. Izzatu ta fizgo shi tana fada. Muje nayi maka brush, ji yadda ka taba wannan kazantar da bakinka. Ta gallawa Zuhra harara, ita kuwa bata tanka mata ba har suka shige ciki. Mamaki take yadda dan karamin yaro ya iya iskanci a cewarta. Kiss ai sai marasa kunya.....

Bata bar wurin ba Anti Faiza tayi sallama. Da sauri ta tarota ganinta da kaya niki niki. Kwalayen juice ne guda hudu, ruwa guda biyu da cake da biskit duk na kwali. Sai da suka gama hawa dasu Anti Faiza ta sake fita ta dauko wata katuwar kula da taimakon mai adaidaitan da ya kawota. Zuhra tace Anti Faiza wannan kayan fa? Bari na sallami mutumin nan ina zuwa.

A falo ta jirata ta dawo. Sai da suka gaisa Anti Faiza tace kudin da na karba a wurinki dashi na siya. Kinga anjima zaa kawo gara sai ki bawa baki. Sauran ki ajiye kiyi amfani dasu. Ta nuna kular can kuma meatpie ne da spring rolls shima sai a basu. Da kuka Zuhra ta rungume Anti Faiza tana godiya.

Hayaniya Izzatu ta soma ji ta fito falon. Mata ta gani wadanda bata sani ba zazzaune suna ta hira. Ana yan ciye ciye, yan uwan su Zuhra ne da wasu makotansu harda Maman su Anti Faiza. Basu jima ba sai ga su Mama , Mariya, Jidda da Ummahani matar Ibrahim. Cike da kunya Zuhra ta gaishe su. Mama tace duk kannenki ne kike durkusa musu. Tashi abinki kinji matar Yaya. Kunya sosai take ji yadda Mama ke janta a jiki kamar wata yarta. Su Umma sunyi matukar kokari kayan garar da suka hadawa Zuhra. Mama ta basu tukwici suka fara shirin tafiya saboda kada a rufe tituna tunda Jumaa ce. Izzatu komawa tayi daki ba tare da ta sauko sun gaisa ba ta dauki waya ta kira Hamza.
Chapter 21 · 0% Book details