Sashe 61
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****
Daga gidansu Zuhra gidan Ibrahim ya wuce ko Allah Yasa sun san inda take. Nan ma babu wani abun arziki da ya samu. Haka ya tafi gida jiki a sanyaye.
Izzatu ya tarar ta gyara jikinta sannan tayi masa girki mai kyau. Ita tunda laifin ya tashi daga kanta to babu matsala. Tana ji a ranta dai duk inda Zuhra take tana lafiya tunda har suna waya da Hamza kafin ya dawo. Idan taki bayyana kanta wannan matsalarta ce. Ko kallon abincin baiyi ba ya shige daki. Yana kwanciya Anti Faiza ta fado masa a rai ya sake daukar mukulli ya tafi gidanta. Har falo ta kaishi wurin mijinta suka gaisa itama ta nuna kamar bata san komai ba. A haka ya koma gida duk yadda Izzatu taso ya saurareta ko abinci ya ci abu ya gagara.
Washegari da safe ya bawa Tala umarnin ta gyara dakin Zuhra kafin ya dawo. Da murnarta tace an ganta ne?
Hamza yayi murmushi mai ciwo...a'a amma bana so ta dawo ta rasa wurin kwana. Yadda yayi magana yasa Tala hawaye. Me yasa iyayensa suka ki sanar dashi inda matarsa take. Sajensa duk yayi wani iri saboda rashin gyara wani gashin yafi wani tsaho.
Ruwan tea kawai yasha ya fita zuwa office din 'yan sanda da suka kirashi an tsinci wata mata. Yaje ya tarar ba Zuhra bace kafin ya fito Alhaji ya kirashi yana masa tuni gobe ne za'a kawo kudin Adabiyya da Hamida kuma za'a saka ranar aure. Shiru yayi na dan lokaci sannan yace yanzu Alhaji ni baza'a yafe min zuwa ba? Duk su Kawu basu isa ba sai nazo?
Alhaji yace kaine babba a gidan nan Yaya rashin zuwanka bazai nuna abu mai kyau ba. Kuma ina maganar Zuhra ta kwana? Har yanzu baka ce komai ba.
Ina kan dubawa Alhaji yanzu ma ina police station.
Tausayin dan nasa yaji yace ka koma gida haka gobe kuzo kai da matarka. Na sami labari ina tunanin an kusa ganinta. Bai jira amsar Hamza ba ya kashe wayar.
Cikin minti talatin Hamza ya iso gidan ya dami Alhaji sai ya fada masa labarin da yaji. Alhaji yace ya bari sai gobe idan ya tabbatar amma yazo tare da Izzatu idan an gama karbar kudin zasuyi magana.
***
Zuhra na daki tun shigowar Hamza tana kuka. A haka Mama ta shigo ta sameta sai tace abu ne ya fada mata a ido.
Idanun Mama suka ciko da hawaye na tausayi. Wurin Alhaji taje tana rokonsa ya bar Hamza yaga matarsa haka. Musamman Zuhra da take da ciki ga damuwa. Alhaji yace zuwa gobe in sha Allah zasu ga juna. Mutumci yake son siya mata.
Hamza bai taba ganin dare mai nisa kamar na yau ba. Zuciyarsa ta gama bashi Alhaji ya san inda matarsa take. Tunda ya koma gida ya fadawa Izzatu zasu je gidan za'a kawo kudin auren kannensa. Baki ta turo tana mita. Tasan aiki kawai zasu sakata.
Tun karfe takwas Hamza yayi wanka ya kuma dami Izzatu sai da tayi. Batun office dama tunda ya dawo bai waiwayesu ba. Suma sun masa uzuri saboda ya dade baya tare da iyalinsa.
Tara na safe suka isa gidansu. Lokacin mutan gidan basu gama tashi daga bacci ba. Ita dai Izzatu ranta ya gama baci amma yadda Hamza ya zama masifaffe tunda ya dawo baiga Zuhra ba dole tayi hakuri.
Kowa ya fito sai yayi mamakin ganinsu. Adabiyya ta fadawa Zuhra yazo dadi ya isheta saboda Mama ta fada mata yau zata koma gidanta. Duk wani shiri da ya kamata mace tayi anyiwa Zuhra. Hatta salon taje an gyara mata gashinta ga lalle baki da ja irin wanda Hamza yake so. Kana ganinta kaga amarya da dan karamin cikinta da yake fitowa idan kaya suka kama ta.
Ana aikin soye soyen da za'a kaiwa baki idan sun zo Mama ta kira Zuhra kitchen ta tambayeta ko zata iya girki. Zuhra tace eh saboda yanzu bata wannan tashin zuciyar. Mama tayi murmushi to maza ki dafawa mijinki abinda kika san zai masa dadi zansa ayi gadin kitchen har ki gama. Allah Yayi muku albarka. Murmushi kawai Zuhra tayi. A yadda su Hamida suka ce mata Hamza ya rame sosai kwana uku kawai sai tayi masa tuwon shinkafa da miyar taushe. Nutsuwa tayi tayi girkin yadda zaiyi dadi sosai. Ta dai sha tsiya wurinsu Mariya amma yau ko a jikinta.
****
Hamza ya gaji da jan lokacin da Alhaji yake masa amma haka ya hakura don babu yadda zaiyi. Izzatu duk aikin da akeyi tana zaune a wurinsa a falo. Su Hajiya kawai taje ta gaisar a dakunansu ta sake komawa wurin mijinta.
Suna nan zaune har su Ibrahim suka zo sannan 'yan uwansu da suka kwana a gidan maza suka fito zuwa falon Alhaji. A nan aka hadu da dangin mazan suka yi abinda ya kawosu aka saka biki bayan sallah babba.
Da kyar Hamza ya iya bari suka gama tafiya ya matsa kusa da Alhaji.
Alh Nasiru yayi dariya babana ban sanka da zumudi ba. Yau ance a kusan a gidan nan ka kwana.
Hamza dai babu amsa sai jiran bayanin da Alhaji yake dashi. Alhaji ya tura Nura ya kirawo su Hajiya da Izzatu.
Hankalinta kwance tana tunanin kwanakin da aka bawa Hamza sun kare Alhaji zaisa ya saketa.
Duk sun zauna harda su Ibrahim. Alhaji ya kalli Izzatu yace... Izzatu ina so ki dubi girman Allah ki fada mana inda kika kai Zuhra. Daga ke sai ita ne a gidanku saboda haka ko zata bar gidan na tabbatar akwai sa hannunki a ciki.
Izzatu ta firgita ta daga kai suka hada ido da Hamza. Shima kallonta yake yi ya kasa gane dalilin Alhaji na yi mata wannan tambayar.
Idanun kowa a kanta suke tace ni fa bansan inda take ba. Tashi nayi da safe kawai naga bata nan. Har nemanta naje yi banganta ba. Wallahi Baby ka da ka yarda da duk abinda za'a fada maka sharri ake son kulla min. Ba tun yau ba nasan babu mai kaunata a gidan nan. Hakuri kawai kuke yi....
Tsawar da Hamza ya daka mata ce tasa tayi saurin yin shiru. Izzy idan kina da masaniya akan batan Zuhra ki fada min tun wuri. Sama da wata biyu Allah kadai Yasan halin da take ciki.
Alhaji ya dubi iyalinsa yace ya isa haka Yaya. Kunga dai na bata dama ta wanke kanta wurin mijinta sai ta zabi tayi karya. To ni nasan inda Zuhra take amma tunda bazaki fadi gaskiya ba ku tashi ku tafi kawai.
Hamza duk ya gigice yace Izzy zan saba miki wallahi. Ki fadi abinda Alhaji ke tambayarki. Me kika sani game da batan ta?
Izzatu ta dage bata san komai ba. Alhaji yace to ni na sami labari kin hada bako da wasu sunzo har gida sun saceta ko ba haka bane Ibrahim? Ibrahim yace haka ne don akwai shaidu. So suke ta fadi gaskiya da bakinta.
Tana jin haka ta fara zare ido saboda yadda taga Hamza yayo kanta... wallahi karya ake min. Duk wanda ya fada karya yake yi. A airport kawai na barta a daren da ka tafi na koma gida ni kadai.
A ransa Hamza yaji maganar....a sanyaye yace me kike nufi Izzy?
Ibrahim yace bari nayi maka bayani kamar yadda idanunmu suka gane mana. Hamza dai har kuka yayi da yaji a irin halin da suka ga Zuhra a gaban sojoji. Shiyasa babu wanda yayi yunkurin dakatar dashi a lokacin da ya kwadawa Izzatu mari har uku.
Zaiyi na hudun Alhaji ya hana shi. Hamza ya nunata da yatsa...nasan baki da hankali wani lokacin amma bansan ke mahaukaciya bace sai yau. Yanzu da sun harbeta kina tunanin zaki cigaba da rayuwa ne? Duk abinda kike yi ina kawar da kai sai da kika kureni. Izzy har mahaifa kika cire da ciki da gangan na cigaba da zama dake. Me kike so ne a rayuwarki?
Yana hawaye su Hajiya suna yi saboda jin irin abinda tayi. Alhaji yace nayi hakuri da halinki Izzatu amma wannan karon zan nuna miki matsayina a wurin mijinki. Kai Hamza yi mata saki daya....
Gaban Alhaji taje ta durkusa tana kuka tana rokonsa yayi hakuri. Fuskarsa a hade yace ko baka ji bane?
Hamza yace na sakeki saki daya.
Alhaji yace nagode kara mata daya...
Wannan karon gabansu Hajiya ta koma tana kuka tana rokon su rufa mata asiri.
Bata bawa kowa tausayi ba duk da basu taba tsammanin haka daga Alhaji ba. Hamza ya kara cewa na sakeki Izzatu.
Alhaji yace to saura igiya daya tsakaninku. Idan kina da hankali sai kiyi tattalinta har karshen rayuwarki domin na bashi dama ranar da kika sake kwatanta irin haka ya cika miki na ukun. Allah ne yayi Zuhra na da sauran kwana a yadda sojoji ke harbi idan suna zargin mutum. Ki koma gidanki kiyi idda wannan kuma umarni ne na addini ba nawa ba. Hamza ka fada mata idan ta kuskura taki zama a gidan to sauran igiyar ma zaka karasata.
Kamar mutum mutumi haka Hamza ya zama ya maimaita abinda Alhaji yace. Zuciyarsa na can tana saka masa abinda zai faru ba don Tala tayi tunani ba.
Kukan Izzatu duk ya cika falon Alhaji yace ko tana da sauran magana tayi saurin girgiza kai. Kada yayi sanadin rabata da farincikin rayuwarta. Yace Nura tashi ka kaita gida. Nura ya fara kunkuni, yaushe zai manta yadda yaga Zuhra babu ko dankwali sojoji sun zagayeta da bindiga. Don babu yadda zaiyi ne suka fita tare tana kuka.
Suna fita Alhaji yace Yaya ka mayar da matarka yanzun nan. Hamza ya dago jajayen idanu yace Alhaji bazan iya ba. Da kanka kace na saketa.
Ni bani da burin rabata da 'ya'yanta. Ka mayar da ita amma kada ta sani sai tayi wata uku a tunaninta idda take. Kila idan anyi sa'a ta canja hali a dan lokacin. Nayi haka ne don tasan cewa ba'a wasa da ran dan Adam. Idan bazaka iya ba kuma zan mayar da Zuhra ga iyayenta.
Ba shiri Hamza yace na mayar da ita. Mama don Allah ina Zuhran take?