Sashe 59
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su Khalifa ne suka hango mamansu daga cikin mota a wannan yanayi suka soma kuka. Wani soja da yaso sata tsallen kwado ya kula da yaran ya fadawa ogansu. Ogan yace to albarkacin yaran nan ta koma motarta da rarrafe sannan sun bata sati daya ta nemo kishiyarta ko su zo har gida su tafi da ita.
Abin tausayi haka Izzatu ta rinka rarrafe akan gwiwarta duk tsadar shaddar jikinta haka ta rinka jan jiki zuwa motarta. Khalifa da Junior sun sha kuka. Itama da kukan ta karasa wani soja yana binta a baya yana zungurinta da kasan bindiga.
Tana shiga motar Khalifa yace Mummy laifi kika yiwa Uncle dinku ya saka ki kneel down?
Idonta ta share tace a'a Khalifa takalmi na ya tsinke shine na gwada yadda muke yi da muna yara.
Motar ta tayar sai dai ga mamakinta sojoji biyu ne suka shiga wata motar a bayansu suka bi bayanta. Zuciyar Izzatu har bugawa take don tsoro tace yau na shiga uku. Maimakon ta tafi gida haka tayi ta yawo a titi. Tun su Nana na kukan yunwa har duk suka yi bacci don wahala. Man motar har kusan karewa yayi ta shiga gidan mai. Motoci wurin goma ne a gabanta amma bata damu ba. Burinta kawai wadannan sojojin su gaji su dena binta. Lokacin da ta fito daga gidan man tayi sa'a bata gansu ba. Sai biyar na yamma ta isa gida jikinta ya gama tsami. Har kusan faduwa tayi da ta fito daga mota ga yara sunyi bacci. Dole ta dauke su daya bayan daya ta shigar dasu gida. Wannan rana ta kafa tarihi mai girma a rayuwar Izzatu.
****
Bayan kwana hudu Zuhra na kwance a daki taji wayarta na ringing. Hamza ne ya kirata ta dauka tana murmushi. Har yanzu bai san halin da ake ciki ba. Idan ya kira hirarsu suke yi sosai. Wani lokacin suyi ta turawa juna hotuna. Gaishe shi tayi yace ni dai na gaji da gaisuwar nan Cutie. I miss you so much. Dan bakin nan na tsiwa yayi min nisa.
Tana jindadin kalaman Ya Hamzanta ta gyara kwanciya...saura wata daya da 'yan kwanaki kazo ka hadu da dan bakin. Ji nake kamar na jawo su Ya Hamza. Har rashin lafiya nake yi saboda rashinka.
Hamza yayi dariya yace ashe dai na siye zuciyarki...wayarsa ya dan cire ya kalla. Karo na uku kenan da Izzatu take kiransa tun bayan sunyi waya dazu. Ya rasa dalilin kiran ya danyi tsaki yace Cutie bani minti biyu zan sake kiranki. Ba jimawa ya kira Izzatu yana tambayarta ko lafiya.
Murya cike da kissa tace Baby dama ina son fita ne anjima to Zuhra ta fita dazu tace gidansu zata je. Ka kwatanta min gidan nasu idan na dawo sai na biya na daukota.
Har cire wayar yayi daga kunnensa ya sake kallo don ya tabbatar da Izzatu yake waya. Wai zata biya daukar Zuhra??? To ko sun fara zaman lafiya ne bai sani ba. Sake magana Izzatu tayi sai yayi mata kwatancen. Sai da yayi kuma ya fara tunanin ko wani abin zata je yi. Yace yaushe ta fita ban sani ba?
Izzatu tace to ai tunda ka tafi tana yawan fita nima bansan inda take zuwa ba. Matar taka gwanar yawo ce.
Shi dai hankalinsa bai kwanta ba har ya ajiye wayar.
Zuhra ya sake kira ya tambayeta yaushe ta fita bai sani ba.
Gabanta ne ya fadi da farko sannan ta dake tace ita tana gida. Yasan bazata masa karya ba shiyasa bai daga zancen ba. Amma sai da ya sake kiran Izzatu yace bai yarda taje dauko Zuhra ba. Idan har ta fita ta dawo da kafarta.
Tuni zancensa yabi iska. Lokacin da ya sake kira ma ta kusa fita daga unguwarsu.
****
Umma na kwashe kayan wanki Izzatu ta shigo da sallama tare da yaranta.
Tarba mai kyau Umma tayi mata sannan tace sai dai banganeki ba.
Izzatu sai yatsina fuska take. Gaskiya gidansu Zuhra basu da wani arzikin azo a gani. Tace sunana Izzatu matar Hamza.
Umma ta hade fuska tana dana sanin irin tarbar da tayiwa matar dake son kashe mata 'ya. Har zata fara fada ta tuna Alhaji yace kada su nuna sunsan abinda ya faru. A dole Umma ta kirkiri fara'a ta fara kiran su Khalifa tana tambayarsu sunayensu. Izzatu ta harare su suka koma suka zauna.
Umma ta dan waiga tace tare kuke da Zuhran? Ina fata dai lafiya.
Toh fa...Izzatu tayi tunanin samun Zuhra a nan gashi ga dukkan alamu iyayenta basu san abinda ke faruwa ba. Murmushi tayi ta mike dama hanya ce ta biyo damu shine nace bari nazo mu gaisa.
Umma tace Allah Sarki, kin kyauta. Nagode sosai zan fadawa Baban Zuhra idan ya dawo.
Kamar wadda ake kora haka Izzatu ta fita daga gidan tana tunanin daga nan kuma ina ta nufa. Kwanaki sai gaba suke yi, me zata fadawa Hamza idan ya dawo?
A bangaren Umma kuwa Izzatu na fita tayi dariya sannan ta kira Zuhra ta fada mata.
****
Bayan sayi biyu su Zuhra na cin abinci a falo ana dan taba hira. Hankalinsu yana ga labarin da Nura ke basu na sabuwar buduwarsa mai son kudi tunda iyayen nasu basa falo suka ji horn din mota.
Dariyar da suke yi duk suka dena Adabiyya ta fita waje da sauri. Murya suka ji ta daga da karfi tana cewa oyoyo Nana. Hamida ki fito ga su Junior da Khalifa. Jin haka Zuhra ta tashi ta shige ciki da gudu. Dakin Hajiya ta shige ta rufe kanta a toilet.
Izzatu ta shigo tare da su Khalifa. Ita da yaran duk sun rame. Ita damuwa da fargaba ke damunta su kuma rashin kula da basa samu daga gareta. A falon ta zaune jiki a sabule tana tararrabin abinda zai faru. Police station yafi goma taje duk ba'a tsinci Zuhra ba. Tayi zurfi a tunani bata ji sallamar su Mama ba sun dawo daga makota jaje.
Sai da Hamida ta taba ta tayi firgigit ta gyara zama. Har kasa ta durkusa ta gaishesu. Suma basu nuna komai ba suka amsa mata. Hajiya tace ina 'yar uwar taki?
Mama tace nima tambayar da zan mata kenan. Kwana biyu su Hamida sunce basa samunta ko a waya.
Cikin Izzatu har 'yar kara yayi sai kuma ga Alhaji ya shigo yace wayar waye ba'a samu?
Hamida ta amsa masa...wayar Anti Zuhra ce bama samu.
A ranta Izzatu tace munafukai wato har waya sukeyi da ita amma ita basa ko yi mata text. Junior ya tafi wurin kakansa ya rungume shi sannan yace nima bana ganin Maama tunda Daddy ya tafi.
Izzatu ce tayi saurin katse shi tace kai Junior ba tana bacci ba lokacin da muka fito. Har ka manta? Su Izzy an fara kwarewa a karya.
Khalifa yace nima dai bana ganinta maybe da Daddy suka shiga aeroplane.
Ji take inama bata zo gidan ba. Sai murmushi take kamar sabuwar shashasha tace Alhaji don't mind them. Tana gida. Bari mu tafi dama zuwa nayi mu gaisa.
Mama tace da sauri haka ko ruwa baku sha ba?
Izzatu tace babu komai ta tattara yaranta suka yi waje.
Tun kafin ta fita su Adabiyya ke dariya Hajiya tace bata son rashin hankali. Daki suka bi Zuhra suna bata labarin karyar Izzatu.
Washegari Tala ta dawo daga kauye. Izzatu kamar ta cinyeta da fada. Duk bakincikinta na wata daya da kwanaki akan Tala ta saukeshi banda tulin aikin gidan da ta tara mata. A haka har akayi azumi da sallah.
****
Sati daya ya rage Hamza ya dawo wanda yayi daidai da kwana sha daya azo kawo kudin auren Hamida da Adabiyya. Kannen Mama mata biyu ne suka zo daga Maiduguri. Mai binta Falmata sai autarsu a mata Yagana. Sun zo da wuri saboda akwai siyayyar da suke son yi na bikin sauran namijin gidansu da baiyi aure ba. Kwanansu daya da zuwa Mama ta kira Zuhra ta hadata da Yagana...ga 'yata nan Yagana so nake kafin ku nan da ranar da za'a kawo kudin nan ni kaina kada na ganeta. Ki hada min ita ciki da waje amma ayi min hankali da dan jikalle a cikin. Duk abinda kike bukata zan baki kudi kuje kasuwa a siyo.
Zuhra ta sunkuyar da kanta kasa cike da kunya. Yagana tace kwantar da hankalinki Ya Kaltume. Irin gyaran da zan mata ko Adabiyya da Hamida sai kin saki kudi zan musu irinsa. Tun jiya da kika bani labarinta na kudiri niyar sai na banbanta ta da wannan karan sigarin Izzatu. Mata tana tafe kamar an sawa taliya riga da zani.
Falmata ta kwashe da dariya. Yagana baki da dama wallahi. Kiyi aikin da aka saka ki kawai ki fito mana da 'ya.
Kafin sati aikin Yagana ya fara nunawa a jikin Zuhra. Dama ga hasken da ciki ya kara mata. Ita kanta tana jindadin gyaran don ma laulayi yasa ba komai ake yi mata ba.
Hamza ya koma kirgen kwanaki kuma a lissafinsa zai dawo lokacin da Zuhra ke da girki. Don murna har fada mata yayi yana sanar da ita irin tarbar da yake so da irin abincin da zata dafa masa. Har tausayi ya bata saboda tasan zai dawo ya tarar da sabanin abinda yake tsammani.
Izzatu dake gidan ta kasa nutsuwa tayi wani abu na murnar dawowar mijinta. Kwatakwata bata da nutsuwa. Kwanakin dawowarsa na matsowa tana kara firgicewa.
****
Karfe biyu da rabi jirgin su Hamza ya sauka a filin jirgi na Malam Aminu Kano. Da kansa yace kada Zuhra tazo saboda yasan da kyar idan zai iya hakuri da tabata indai ya ganta ko da a gaban mutane ne. Ibrahim ne yazo ya dauko shi. Ya kara haske yayi kyau kamar ba wanda yaje karatu ba. Farincikinsa baya misaltuwa.
Gidansa yace Ibrahim ya kaishi idan yayi wanka zuwa anjima zaije gidansu. Nan kuwa son ganin 'ya'yansa da Zuhra ne a ransa.
Motar Ibrahim na tsayawa maigadi ya soma kiransu Khalifa ga babansu ya dawo. Da gudu yaran suka fito suka dafe jikin babansu.
Yadda cikin Izzatu ya tsirga saboda tsabar tsoro da gudu ta shiga toilet. Gudawarta ta tara kenan tunda gari ya waye ko wanka bata yi ba.