← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 67

Sashe 16

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hamza bai sami komawa gida ba sai kusan shadayan dare. Dakin Izzatu ya shiga ya sameta a kwance tana bacci. Hmmm kina jindadinki ya fada kafin ya koma nasa dakin. Yunwa yake ji sosai don rabonsa da abinci tun safe amma baya sha'awar komai. Kitchen din kasa ya sauka ya tarar da kulolin abinci kala kala ga wasu ko budesu ba'ayi ba. Kitchen din tsamin abinci kawai yake yi. Duk da cewa ba'a gama taron ba ya watse amma anyi almubazzarancin abinci. Tea ya hada ya koma daki. Tunanin sa na farko yadda zai biya turawan nan kudinsu gaba daya ya fasa hadin gwiwar dasu. Kudaden kamfanin yanzu da yawa an fara ayyukan ginin dake gabansu. Daya a Jigawa ne dayan kuma a Abuja. Kowanne sai sunyi rabin aiki za'a biyasu gashi duk zasu ci kudi sosai. Nasa kudin kuma ya kashewa gidansa don komai sabo ne a gidan. A gefe daya kuma ga zancen auren yarinyar nan. Gashi iyayensa duk fushi suke yi dashi. Ji yayi kansa yana sarawa saboda tunanin da yayi masa yawa ya tashi ya dauro alwala yana ta nafilfili da adduar samun sauki akan dukkan matsalarsa. Mama ce zai iya fadawa matsalarsa ta bashi shawara to itama yanzu basa dasawa kamar da. Izzatu kuma damuwarta akan abinda ya shafeta ce kawai.
[9/25, 3:45 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿25

Batul Mamman(Mrs)💖

Gidan kanwar Mamanta inda suka yi masauki Izzatu ta tafi. Ko rufe motar bata yi ba ta shiga cikin gidan tana ta rusa kuka. Ana ta tambayarta abinda ya faru taki bada amsa. Sai da kanwar Maman tasu tayi mata tsawa sannan tana shesshekar kuka tace Alhaji ne yace Hamza sai ya auri yarinyar da nayiwa April fool jiya. Anti Larai kanwar Raliya tace kai amma Allah Ya sakawa Alh Nasiru da alheri. Ni dama kinsan duk wannan shirmen naki ba zuwa nake yi ba saboda na rasa wace irin rayuwa kuke yi ke da mijinki. Tun jiya da aka bani labarin abinda kika yi raina ke kuna. Ta mayar da kallonta ga Raliya...Wallahi duk laifinku ne Yaya Raliya. Rayuwar turai ai ba hauka bane. Yara kusan shekara tara da dawowarku kasar nan amma sunki yarda su yar da al'adun da ba nasu ba. Yanzu wa gari ya waya. Raliya ta sunkuyar da kanta kasa. Tasan tabbas gaskiya kanwarta take fada. Ta kalli Izzatu da take ta kuka...sai ki rungumi kaddara tunda ke kika jawowa kanki. Ni bazan shiga zancen nan ba kuma daddynku ma zan fada masa babu ruwansa. Allah Ya baku zaman lafiya. Izzatu tace haba Mum haka ma zaki ce. Raliya tace to ai tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ke duka. Daki Zeenatu ta Izzatu tana rarrashi. Kinga Izzatu kiyi hakuri yayi auren nan tunda dama yan gidansu basa kaunarki. Idan kika nuna bakya son auren suna iya sawa ya rabu dake. The way I see it wannan yarinyar bazata kai ko'ina a gidan ba zai saketa. Da haka tayi ta rarrashin Izzatu har ta hakura ta dauki wayar Hamza da yake ta kiranta ta fada masa inda take sannan ta kusa dawowa gida.

Bayan ta koma ne suka yanke shawarar yaje gidan su Zuhra kamar yadda Alhaji ya bukata. Maganar auren tasa fushin da yake da Izzatu akan matsalar kamfaninsa ta ragu.

Wani light blue din yadi ya saka da aka yiwa dinki mai kyau amma simple style ba ado da yawa. Yasa hula mai ruwan madara da light blue. Yayi kyau sosai don ma bai fiye sa manyan kaya ba. Ya sha turare sannan Izzatu ta daura masa links a hannun rigar da agogo. Yana saka takalmi tace cikin shagwaba ni gaskiya kayi kyau da yawa kamar kada ka fita. Murmushi yayi mata. Kada ki damu bazan dade ba.

Da tambaya ya iso gidan domin zuwan su na dare ga ransa a bace ko kallon hanya baiyi ba. Yaro ya tura yayi masa sallama da Zuhra. Yaron na tafiya yabi bayansa ya tsaya a soron inda suka zauna da Baba.

Yaron na sallama Zuhra ta amsa. Ita kadai ce a gidan Umma ana la'asar suka tafi kai garar Hajara. Baba ma ya fita tun safe bai dawo ba. Tana gaban murhu zata fara tuka tuwo. Da murmushinta tace Isuhu daga ina haka? Isuhu yace wani mutum ne a waje wai Hamza yace kizo. Wallahi baki ga yadda ya hadu ba Zuhra, motarsa ma abin kallo ce. Ga wani kamshi dan ubansu yana fitarwa. Tunda Isuhu ya fara magana gabanta ya fadi. Ba yadda za'ayi ta yarda da auren nan. Rokonsa kawai zata yi su fadawa iyayensu basa son auren. Ina ita ina wannan mutumim, ita tsoronsa take ji. Isuhu ta kalla kace masa ina zuwa tuwo zan tuka na kwashe. Babu kowa ne a gidan. Duk maganar da sukeyi Hamza na jinsu. Bashi da niyar dadewa a gidan saboda haka dan aiken nasa na fitowa naira hamsin ya bashi shi kuma yayi sallama ya dan shiga daga cikin tsakar gidan.

Zuhra bata gama tantance sallamar waye ba taga mutum ya soma shigowa. Gashi ta zuba garin alkama ta fara tuka tuwon. Da sauri ta fara cewa kai dakata kada ka shigo mana. Wani tsohon zani ne a jikinta da koriyar t-shirt sai dankwalin zanin da ta daure kanta tamau dashi. Hamza bai kula ta ba ya shigo har tsakiyar tsakar gidan tana ta kokawa da dankwalinta tana son bude shi ta rufe jikinta. Wani irin kallo ya bita dashi mai wuyar fassara. Kinga yi aikinki ni ba zama nazo yi ba. Magana nake so muyi ina sauri ne. Fuskarta a turbune tace don kana sauri ko sallamarka ban amsa ba ka fado mana cikin gida. Kuma ko lullubi babu a jikina. Dan karamin tsaki yayi, kwantar da hankalinki baki da abinda zai daga min hankali don na ganki ba mayafi. Maganar ta bata haushi sai ta danne tace ina wuni? Kafin ya amsa ta cigaba da tuka tuwonta.

Kallo ya bita dashi yadda take zaune gaban murhu zafin baya damunta. Bazaki bani wurin zama ba? Ko juyowa bata yi ba tace na dauka ba zama kazo yi ba. Can gefe ya sake matsawa saboda wutar ta fara hayaki. Ita kanta Zuhran yana damunta ta fara hawaye da majina. Tasa gefen dankwalinta ta goge fuskar ta cigaba da aiki. Da kyar ya hadiyi yawu saboda gabadaya kyankyaminta ne ya kamashi. Gara yayi abinda ya kawo shi ya fita kafin zuciyarsa ta fara tashi.

Ji tayi yace Ke,wai baki da saurayi ne?....ta murguda baki duk da ta juya masa baya ni ba sunana ke ba. Kuma ina ruwanka da samarina. What ever taji ya fada da turanci. A ranta tace ban yafe ba idan ka zagen. Alhaji yace yana so na zo wurinki atleast sau uku kafin a kawo kudi. Za'a tambayeki kafin ranar idan kin amince da auren, ina so kice ba kya sona. Mun gama magana da Izzatu tace kina da saukin kai zaki amince. Izzatu da ya fada ya kara bata haushi. Ko kadan bata son sake jin sunan matar. Kinga ni bana sonki kuma idan kika aureni wahala zaki sha. A tsarina mace daya ta isheni. Tunda bana jin kina da saurayi akwai sakatare na Inuwa zanyi mishi tayinki. Idan ya amince kinga shikenan. Ko ba komai na taimaka miki. Kuma nayi alkawarin yi miki kayan daki idan kin tashi aure.

Murmushi kawai Zuhra keyi ta gama tuka tuwon ta rufe tukunyar sannan ta gyara wutar. Wato mutumin nan ya raina mata hankali. Shi iyayensa su yabe shi ita kuma ace bata da kunya. Wai har cewa yake zaiyiwa wani tayinta. Ko na sati ne sai ta aure shi ta bata masa rai daga shi har masoyiyar tasa Izzatu. Da wannan shawarar ta dago kanta amma bata hada ido dashi ba. Tace shikenan abinda ya kawoka? Hamza yace eh ko kudi kike so zan iya biya kice ba kya sona kinji. Wannan karon tamkar mai magiya yake magana. hanyar dan karamin falonsu ta kama. Zanyi tunani a kan maganar, ka gaida gida. Shigewa tayi ta barshi nan a tsaye yana mamakin wai itama ta iya jan aji. Ya kada kansa ya fice daga gidan. [9/25, 3:45 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU26

Batul Mamman(Mrs)

Washegari Hamza ya koma gidansu Zuhra. Soro ta fito ta same shi. Yau zama yayi yana lissafa mata irin mawuyacin halin da zata iya shiga muddin ta yarda aka yi auren. Kanta a kasa har ya gama bayaninsa ya juya ya tafi. A waje ya hadu da Baba yana dawowa gida. Yara ne sunfi goma suke biye dashi yana rarraba musu alawa. Hakan ya bawa Hamza sha'awa. Karasawa yayi suka gaisa da Baba cikin ladabi sannan ya tafi. Yau dai ya karewa hannun Baba kallo ya kula yankewa aka yi ba kuturta bace ta cinye yatsun.

Saboda matsalar office dinsa sai bayan kwana biyu ya sake komawa. Umma tasa tayi kwalliya irin wadda ta saba yi tana ta yabon kyan tilon yarta. Zuhra tace don ma banyi wanka ba Umma ai da sai nafi haka kyau. Umma tace to sakarai sai kin fada da karfi yaji yasan cewa ke kazama ce ko. Bata rai tayi haba Umma ki dena ce min kazama. Baba yace na kile. Ai fa naga alama, to wuce ki tafi kin barshi yana jiranki.
Chapter 16 · 0% Book details