← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 67

Sashe 48

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakinciki fal zuciyar Raliya saboda yadda Izzatu bata jin magana tace idan kika kuskura kika daga masa hankali nayi miki alkawarin sai na fada masa ke da kanki kika sha magani kika zubar da ciki. Kuma har asibiti kika je domin a cire miki mahaifa. Kin zauna mutane sai tausayinki suke ji basu san bukatarki bace ta biya. Izzatu ina jiye miki tsoro idan Hamza ya sakeki fa babu wanda zaiso ya auri macen da bazata haihu ba.

Hannu Izzatu tasa a kan bakinta alamun Raliya tayi shiru. Sai dai aikin gama ya gama domin Hamza da Zuhra sunji komai.

Cike da bacin rai Hamza ya sake kama hannun kofar zai bude Zuhra tayi saurin rike masa hannu saboda yadda taga fuskarsa gabadaya ta canja kamar bashi ba, jikinsa rawa yake sosai. Hannun nasa ya fizge daga rikon da tayi masa ya shiga cikin dakin.

A take Izzatu da Raliya nasu idanun suka firfito waje saboda tsabar kidimewa.
[10/10, 1:59 PM] +234 809 156 9113: AL'ADUN WASU 67

Batul Mamman(Mrs)

Yadda Hamza ya shiga dakin tamkar wani zaki. Zuhra ta biyo bayansa ta rabe a gefen kofa, bakinta a rufe da hannunta daya saboda zafin da lebenta yake sakamakon fizgar da Hamza yayiwa hannunsa ya bigeta.

Kokarin tashi daga kan gadon Izzatu take yi domin yanayin Hamza ya bata tsoro. Murmushi yake mata wanda gara ace duka ya rufe ta dashi saboda duk wanda yaga yanayinsa dole ya tsorata. Sai da yaje kusa da gadon yace koma kiyi zamanki ranki ya dade. Nazo inyi miki godiya ne saboda irin abubuwan da kike yi min. Abu daya ya rage ki karasa ladanki shine ki kasheni ki huta.

Raliya tace Hamza don Allah kayi hakuri ka tsaya muyi magana kada zancen nan ya fita.

Wani shekeke ya kalleta abinda bai taba yi mata ba. Kinga ki dauki 'yarki ku koma gida idan an sallameta. Ke haihuwa ce kika gaji da ita. Ni kuwa da kika ganni ganinki ne gabadaya bana son yi. Ba don kina gadon asibiti bane babu abinda zai hana na nayi miki abinda zaisa a kawoki asibitin.

Raliya ta hada hannuwanta biyu tana hawaye Hamza kayi hakuri kada ka saketa. Izzatu bata san meye rayuwa ba shiyasa take wannan haukan.

Indai zata yi haihuwa uku amma ta kasa sanin meye rayuwa to ina ganin har abada bazata taba sani ba. Ya bata amsa rai a bace.

Izzatu dai sai kuka take yi. Duk haukanta tasan Hamza yana son haihuwa bazai taba goyon bayanta a cire ciki ba balle mahaifa gabadaya. A hankali tace Sweetbaby am sorry. Bana son nayi ta haihuwa ka dena ganin kyau na har ka fara tunanin sake aure.

Mamakin kansa yake yi da yadda ya iya zama da Izzatu duk tsawon shekarun nan. A kokarin kyautata mata ya rinka kuntatawa iyaye da 'yan uwansa. Kansa har wani irin ciwo yake masa, fadan ma ya kasa yi yadda ya kamata. Izzatu ta cigaba da magana, Baby a da indai nayi maka laifi fada kawai kake yi min. Amma yanzu duk ka canza saboda yarinyar nan da ko kadan bata waye ba. Har me ka gani a jikinta wanda bani dashi, me ya sami soyayyar da muke yiwa juna?

Ai ta tabo wa kanta masifa tunda tasa Zuhra a ciki. Itama Raliya shiru tayi saboda irin fadan da Hamza yake yi yana gaggayawa Izzatu magana. Ke har kin isa ki hada kanki da Zuhra? To bari na fada miki wallahi ban taba son wata mace kamar yadda nake sonta ba, ciki kuwa harda ke Izzy. Zuhra tayi min abinda mata dayawa bazasu iya yiwa mazansu ba a lokacin da kike yawon gidan biki. Wannan yarinyar da kika raina ita ake kira matar rufin asiri. Kuma wallahi da ace wannan cikin da kika cire shine na farko bazaki kara komawa gidana ba daga nan sai kwasar kayanki.

Hamza ni kake fadawa haka akan wannan yarinyar? To wallahi ko saki uku kayi min babu inda zani. Ni da kai mutu ka raba. Kuma zubewar cikin ba laifinka bane? Eyye nace ba laifinka bane??? Ai an tsayar da jinin tun a Abuja amma don wulakanci nazo na ganka da yarinyar nan a kan gado kana romancing dinta....ko kunyar Raliya bata ji ba take fadan wannan magana. Zuhra ta rasa me yake mata dadi.

Shima Hamza ya manta da Raliyar a wurin yace shi kawai kika gani? Baki kula ko riga babu a jikina ba. Ki karasa bawa duniya labarin abinda kika gani a dakin mijinki sakamakon shigar masa daki da kika yi babu sallama.

Raliya da Zuhra sai kallon kallo. Yau masoyan tamkar su cinye junansu don bacin rai. Sai da suka gaji don kansu Hamza ya finciko hannun Zuhra suka fita. Sauri yake kamar ya tashi sama. A motar ma babu wanda yace kala haka yaja suka tafi gida.
Nana tana ta yi masa gwaranci ko kallonta baiyi ba ya haye sama. Yau ran Hamza ya baci fiye da yadda yaji lokacin da aka yi masa sata. Izzatu taci amanar soyayyar da yake mata. Duk abinda take yi yana kawar da kai, wannan karon ta kure hakurinsa.

Tsoron binsa daki Zuhra tayi saboda yadda taga ya fusata. Lebenta ba kasa da ya bige har dan kumbura yayi sannan wurin yayi ja sosai alamun jini ya taru. Rufawa kanta asiri tayi ta dauki Al'Qurani ta shige wurin sakarta. Ta dade tana karatu tare da addu'ar nemawa mijinta sauki daga kuncin da ya shiga.

********
Mama Agnes na tsaye akan autanta Felix tana ta zubar da hawaye. Irin matan nan ne masu tsananin riko da addini ko takalmi bata sawa. Kwance yake akan gadon asibiti ga yayyensa maza biyu da mace daya sai 'yan sanda biyu.

Dansanda daya yace a iya binciken da muka yi da kuma abinda abokan nasa da muka kama suka sanar damu sata suka je yi akan high way lokacin wasu 'yan uwanmu suna patrol shine aka harbe shi. Mama Agnes tace officer idan ya warke zaku tafi dashi ne? Yace kwarai kuwa tunda an samu bullet din ya fita. Share hawayenta tayi tace shikenan, ku zama shaida ta fada tana kallon sauran 'ya'yanta. Ko mutuwa nayi kada ku bari Felix yazo kan gawata. Na yafe shi daga cikin 'ya'yana kuma na tsinewa ranar da nayi cikinsa da ranar da na haifeshi. Cikinku idan akwai wanda yasan yayi sata to ya mayar da hakki ga maishi domin daga nan zanje Church ne. Zamuyi addua ga duk wani barawo a garin nan yayi mutuwar wulakanci da kaskanci. Duk cikin zuri'armu babu abinda muka fi kyama kamar sata.

Felix na jin maganar da babarsa keyi ya soma kuka yana bata hakuri. Tace idan ma hukuncin kisa aka yi maka to kasani sarai gawarka bazata sami bikin burial ba. Zamu binneka tare da sauran masu abin ku yar kauyen nan..barayi 'yan uwanka.

Mama Agnes na gama magana ta fice ko waige babu. Kauyensu Mr Oscar gara mutum yayiwa yarinya fyade akan yayi sata. Sata tafi kowane laifi girma a wajensu. Dayake Mr Oscar ya yarda sosai da adduar Church dinsu shiyasa ya tsorata da abinda mamansa ta fada. Kudin Hamza wanda har ya fara gini dashi su suka fado masa.

******
Bacci ne mai nauyi ya dauke Hamza sai karfe bakwai da rabi ya farka. Salati ya rinka yi da mamakin dadewarsa a kwance. Da sauri ya fada bandaki yayi alwala yazo ya gabatar da sallar magriba, kafin ya idar yaji ana isha a masallaci dole itama yayita a gida.

Har lokacin zuciyarsa babu dadi sosai shiyasa shima ya zaune karatun Qur'ani. Ya dade yana addu'o'i tare da istigfar saboda neman sauki a wurin Allah. Haka yayi ta zama a daki har shadaya da rabi babu motsin Zuhra. Murmushi yayi da ya tuna karshenta tana can tana fushi saboda shareta da yayi.

Dakinta ya fara dubawa babu kowa a ciki. Da ya sauka kasa ma tsit yaji sai karar injin saka. Da saurinsa ya bude kofar dakin da take sakar ya ganta tana yi.

Zuhra na jin ya bude kofar gabanta ya fadi. Kusa da ita yaje ya zauna yana kokarin cire hannunta daga jikin wani karfe da take turawa. Kin saki tayi sannan ta sunkuyar da kanta kasa. Ka kyale ni yanzu zan gama ita ce ta karshe. Kin sakin hannun nata yayi ya cire shi sannan ya kira sunanta cikin sanyin murya Cutie....kamar wadda aka kunawa famfo sai kawai ta saka masa kuka hawaye na ambaliya a kumatunta. Rungumeta yayi yana shafa kanta...Cutie me ya sameki? Ki bar sakar haka muje ki kwanta. Iya karfinta ta soma kokarin ture shi tana tura baki....ni ka kyale ni idan nagama zan tafi na kwanta. Sake riketa yayi haba Fadimatu fada min waye ya saka min ke kuka, waye yake son yau na hana shi bacci tunda ya taba min Cutie.

Marairaicewa ta sake yi tace ba kaine ba....Ya dan ware ido, ni da kaina Cutie? To fada min me nayi. Da yatsanta ta nuna masa lebenta da yayi ja amma yanzu babu kumburin. Ya Salam Cutie am so sorry, dazu ne a asibiti ko? Kai ta gyada yace kuma ka dena kulani duk da ina son baka hakuri akan abinda ya faru.

Shhhhhh ya fada tare da dora yatsansa a bakinta. Kiyi shiru Cutie babu laifinki a dukkan abinda ya faru. Raina ne ya baci lokacin amma hakan bai zama dalilin da zan share matata ba. Kice kin hakura.

Murmushi tayi tare da noke kafada. Yace please, please, please. Sake noke kafadar tayi yace to tashi muje mu kwanta kinga shabiyu ta kusa. Abin sakar ta kama ka bari wannan ce karshe saura kadan na gama.

Kusa da ita ya zauna har ta karasa tace gobe sai ya kai musu. Godiya yayi mata da addu'a sannan ya kama hannunta suka tashi. Jikinta duk yayi tsami saboda zaman wuri daya.

Sai da suka fito falo yace kince abinci kuwa. Tace a'a zata sha tea yanzu. Dariya yayi duk kaunarki da abinci ki kare a shan tea lallai nayi laifi. To muje na soya miki kwai kici da bread. Zuhra tayi dariya kaji ka Ya Hamza ka iya girki ne? Hannunta ya rike muje kiyi kallo yarinya.
Chapter 48 · 0% Book details