← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 67

Sashe 64

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

jikinta sosai yace..babu wanda zai iya kwatanta halin da kika shiga sai wanda ya tsinci kansa a ciki. Abinda Izzy tayi miki ba abu bane da zamu iya mantawa da wuri. Sai dai ina rokonki alfarma yadda kike kokarin kiyaye dukkan abinda kika san ya sabawa shari'a ko zaman aure don Allah Cutie kada ki fara shi saboda bacin rai, kinji. Bata iya magana ba sai kai da ta gyada a hankali. Hawayen da take boyewa suka fara sintiri a fuskarta lokacin da yace mata a gidan Izzatu zata yi Idda. Ga kishi ga bakincinkin abinda ya faru. Hamza bai hanata kuka ba sai ma rungumarta da yayi. A hankali ya sake magana saboda yasan ranta a bace yake... Cutie nasan abinda zan fada yanzu zai kara bata miki rai sai dai ina son kada kiyi hukunci da son zuciya. Kiyi tunani a matsayinki na musulma wadda take fatan itama idan tayi kuskure a yafe mata. Rikon da tayi masa ya tabbatar masa tana jinsa.... Alhaji yasa na mayar da Izzy bayan fitarta dazu saboda haka a matsayin matata take har yanzu duk da bata san hakan ba. Na fada miki ne saboda kada kiga wani dalili yasa naje inda take tana da hakki a kaina har yanzu. Zan bari sai tayi tunanin ta gama idda sannan na sanar da ita. Hakan muna fata ya zama sanadiyar nutsuwarta. Batun girki kuma zata dafa iya na cikinta banda su Nana. Zancen Hamza har zuci ya daki Zuhra sai dai kuma tana da tabbacin son zuciya bazai taba zama alkhairi gareta ba. Shi Izzatu tayi sai gashi ita da take raina kanta da kanta ta mallaki zuciyar mutum kamar Hamza. Dago fuska tayi suka hada ido tayi saurin rufe nata....Ya Hamza in sha Allahu bazan taba shiga tsakaninka da matarka ba. Tare na ganku kuma nasan duk matsalolin nan saboda ni suke faruwa. Idan a da ban fahimceta ba yanzu nasan ya mace take ji idan taga mijinta da wata. Allah Yasa a samu abinda ake nema...ta mike tsaye tana jan hannunsa.... ka tashi muje muci abinci sai ayi wanka a kwanta. Dawo da ita yayi kan cinyarsa...dan fada min ya mace take ji idan taga mijinta da wata. Zuhra tace tabdi ai rai ne yake baci sosai. Nifa ranar da ta dawo da kyar nayi bacci. Hamza yayi dariya yace kina ta tunanin ko muna can muna.... Bakinsa ta toshe da hannunta ta tashi tana jin kunya. Kafin ya tashi ta fice daga dakin. **** Abin duniya ya ishi Izzatu sai juyi take akan gado ga wata uwar yunwa na cinta. Bata son fita ta hadu da Zuhra ko Hamza. Da wane ido zasu kalli juna? Kila Zuhra ta rinka mata dariya ma saboda yanzu an saketa. Tana wannan tunanin Raliya ta kirata. Da sauri ta dauki wayar tana son jin jawabin Ustaz. Raliya tace to ki saurare ni da kyau Izzatu. Idan kika bari wannan damar ta wuceki babu ruwana. Ustaz yace ba karamin kokari suka yi ba suka ce kiyi idda a gidan. Mutanenmu da yawa basu san cewa yana da kyau idan anyi saki daya ko biyu mace tayi idda a gidanta ba. Hakan zai sa a wannan lokacin tayi kokarin jan hankalin mijinta har ta mantar dashi dalilin sakin ya yafe mata ya dawo da ita . Sai ayi saki daya ace na baki minti biyar ki kwashe kayanki. Izzatu tace to Mum hakan dole ne ko mutum nada zabi? Raliya tace mace na da zabi amma zaman shi yafi. Kinfi kowa sanin Hamza saboda shekarun da kuka yi tare. Kinsan me kike yi ki janyo hankalinsa. Sai ki dage da ladabi da biyayya. Girki ma ko bazaici ba kiyi maidadi kiyi masa tayi. Banda saurin fushi kuma babu ruwanki da Zuhra. Idan kika yi ganganci da sauran igiyar nan zaki yi kuka da idanunki don yanzu 'yan mata ma neman miji suke ido rufe bare bazawara mara mahaifa. Haba mana Mum ya zaki fadi haka? Izzatu ta fada kamar tayi kuka. Ya bazan fada ba Izzatu. Ai mahaifar nan da kika cire wallahi ko yau ko gobe sai kin cije yatsa. Naga har yau baki fara damuwa bane. Allah Ya kyauta . Izzatu tace Amin ta tashi da kwarin gwiwa. Wanka tayi ta bata lokaci wurin gyara jikinta sosai tayi kwalliya. Wata rigar bacci ta saka shara shara ta feshe jikinta da turare ta fito ta sauka kasa. Tala har bari tayi saboda shigar da Izzatu tayi. Tayi saurin rufe ido tana tunanin yaushe Hajiyarsu zata dena irin wannan abubuwan. Ita bata taba ganinta da riga irin wannan ba duk da ta saba yawo a gidan da kayan bacci amma masu mutumci ne. Hayaniyar su Khalifa ta jiyo a falon Hamza tayi murmushi tasan yana ciki. Canja tafiya tayi ta shiga falon. Zuhra da Hamza ke cin tuwon da tayi masa da Nana wadda idonta idon tuwo. Junior da Khalifa suna ta wasa da bindigar roba. Kamshin turarenta ne ya fara sanar dasu ta iso. Junior ya kalleta baki bude yace Mummy yau kuma baki saka kaya ba kika fito daga daki? Khalifa yace kai ta saka amma irin rigar da Malam yace idan mace ta saka ta fita za'a sakata a wuta ne. Mummy wallahi babu kyau yawo a haka. Zuhra dai kawar da kanta tayi gefe don tsiraicin yayi yawa. Hamza yasa su Khalifa suka daukarwa Nana plate din tuwon yace su tafi wurin Tala. Suna fita ya juyo kan Izzatu ransa a bace. Yanzu don Allah Izzy baki ji kunyar saukowa haka 'ya'yan cikinki su ganki ba. Kila Tala ma ta ganki ko? Izzatu tayi murmushi...Babyna bansanka da zafin kishi ba. Kuma harda su Khalifa. Ni yunwa nake ji me zamu ci ne? Zuhra yake kallo ido ya cika da hawaye. Yasan dole taji babu dadi musamman da tasan ya mayar da Izzatu. Uwa uba yadda ta kunyata kanta batare da ta damu ba. Ya tashi ya tsaya a gabanta. Kinga Izzy ki bar wurin nan kafin ranki ya baci. Idan har kina so mu shirya to wallahi kada ki sake fitowa da irin wannan kayan. Sai kinyi kamar hankali ya shigeki sai ki fara wani shirmen. Meye amfanin yaro kamar Khalifa yana fada miki babu kyau irin wannan dressing din. Izzatu dai bata damu ba ko kadan. A ranta taji dadin yanayin da Zuhra ta shiga. Dole ta dage ta karkato da hankalinsa ta dawo matsayin matarsa. Karshen takaici Zuhra taji sai ta daure ta tashi ta kama hannun Hamza... Ya Hamza muje nayi maka wanka kaga dare yana kara yi. Daga shi har Izzatu baki suka bude don ko su kadai ne yasan tana jin kunyarsa. Yadda suka yi yasa sauran kadan ta karaya sai ta daure tace...muje mana Ya Hamzana. Bin bayanta yayi suka fita suka bar Izzatu a tsaye rai a bace. Ita bata ga laifin shigarta ba. Tala dai mace ce 'yar uwarta sai kuma 'ya'yanta. To cikinsu waye bai kamata yaganta a haka ba. Tabe baki tayi ta fita ta tafi kitchen ta dafa indomie kwaya daya. Indai haka ake zaman iddar ai bazata dade ba komai zai daidaita. Dakinsa ya ja Zuhra ya bude mata nata tsarabar. Kananan kaya ne da kayan bacci masu kyau. Bakin nan nata ta turo shi gaba ita a dole tana fushi tace ni a dakina zan kwana. Tana magana tana tattare kayan da ya bata. Hamza yace ai baki isa ba sai kinyi min wankan nan. Da bakinki ki fadi abu kuma yanzu ki canja. Zuhra tace ka rufa min asiri Ya Hamza ai sai ace min mara kunya. Daya bayan daya ya sauke kayan hannunta ya shafa cikinta....kinga karshen rashin kunya kuma kin riga kinyi to me kuma ya rage. Sosai taji kunyar maganarsa ta fara sunne kai a kirjinsa....ai kawai fada nayi amma ba gaske bane. Yace to ni da gaske na dauka bari ki gani...bata ankara ba ya dauketa yana cewa kin kara nauyi fa yarinyar nan. Bai ajiyeya ko'ina ba sai cikin toilet ya rufe musu kofa.
Chapter 64 · 0% Book details