Sashe 15
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko kazar da kwai ya fashewa a ciki zata fi Hamza kuzari. Daga kafa yake kamar ba'a jikinsa take ba. Ko da ya koma gida dakinsa ya shiga ya rufe. Izzatu tayi bugun har ta gaji. Bai fito ba sai da aka kira magariba. Yayi wanka ya canja kaya. Ba don kuncin da zuciyarsa ke ciki ba sai ka zata sabon ango ne....kodayake ya kusa zama angon!
Masallaci ya fara zuwa yayi sallah sannan ya wuce gida. Alhaji da Ibrahim ya gani a shirye suna jiransa. Mama har bakin mota ta rakosu tana musu fatan alheri. da ta shiga gida Hajiya tace wato duk gidannan kinfi kowa farinciki da wannan abin. Mama tayi dariya Hajiya bazan taba manta abinda Izzatu tayi mana ba. In Allah Ya yarda yanzu Yaya zai san yayi auren yar da ta dace da addini da al'adarsa.
Yadda Ummahani ta kwatanta masa haka Ibrahim ya bi. Hamza yana gaba kamar ruwa ya cinye shi. Alhaji da Ibrahim sai hirarsu suke yi. Daga bakin layin suka ajiye motar Ibrahim yace daga nan na manta kwatancen, Yaya ya ma sunan yayartawa? Wata muguwar harara Hamza yayiwa Ibrahim kafin yace zanci.....Alhaji yayi gyaran murya don yasan karshenta zagi Hamzan zaiyi. Yau ya zama a lallaba auren zamani. Ibrahim dai dariya yayi sannan ya kira Ummahani ta tuna masa sunan. Da tambaya suka sami gidan domin ba wuyar ganewa.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [9/25, 3:42 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿24
Batul Mamman(Mrs)💖
Wurin goma da rabi na safe kukan Nana ya tashi Izzatu daga bacci. Tana bude ido ta kalli agogo. Da sauri ta sauko daga kan gadon ta dauki Nana da ke kawo karar Junior ta tafi dakin Hamza. Abin mamaki a rufe taji dakin. Ta tsaya tana bugawa Khalifa yace Daddy ya fita. Ranta ne ya baci. Tunda suka yi aure ranaku kadan ne suka taba kwana daki daban shima sai da dalili mai karfi. Amma akan abinda bai kai ya kawo ba shine jiya yaki tashinta daga bacci ta koma dakinsa kuma yau harda kulle kofar daki. Kwafa tayi zai dawo ya sameta ne. Bayan tayi wanka ta sauko kasa. Tala ta gyara gidan tas kamar ba'ayi taro a cikinsa ba. Hatta su Khalifa duk tayi musu wanka. Da yake asabar ce babu makaranta. Sabon dakin wasansu suka tafi suna ta tsalle tsalle. Tala ce ta rugu da gudu ta kawowa Izzatu wayarta da ke ringing a daki. Bakuwar number ta gani ta dauka suka gaisa. Da jin gaisuwar kasan bata san da wa take magana ba. Mama tace Haj Kaltume ce daga gidan Alh Nasiru uban mijinki. Izzatu ta dan ji kunya tace yi hakuri Mama bangane ba. Mama tace ah ai babu komai idan kina da lokaci kizo nan gida Alhaji ya bayar da sako. Kafin Izzatu ta amsa Mama ta kashe wayarta.
Duk da babu mutane sosai a office din saboda weekend ne amma can Hamza yaje. Tunani ne yayi masa yawa bai iya yin baccin kirki ba. Shawara daya ya yanke zai basu ribar kamar yadda suka bukata sannan zaiyi kokarin hada kudin da suka bashi ya biyasu. Yana wannan tunanin Izzatu ta kira shi tana sanar dashi kiran Mama. Yace taje shima zai je anjima kadan. Har zai ajiye wayar yaji tace sweetyna kayi hakuri da duk abinda nayi ba daidai ba. Sai yaji ta bashi tausayi. Basa iya dogon fushi da junansu. Babu komai Izzy, love you. Tace love you more.
Dakin Mama ta wuce kai tsaye tunda ita ta kirata. Hamida tana gyaran wardrobe din Mama taji sallamar Izzatu. Wata sabon gani. Anti Izzatu dama kina nan, yaushe rabonki da gidan nan? Izzatu ta dan sunkuyar da kai. Ita kanta tasan tafi wata biyar rabonta da gidan iyayen mijinta. Ko da Mama ta karye kunya da tunanin basa sonta ya hanata zuwa. Kuma Hamza baice taje ba. Mama ta fito daga toilet tace Hamida bana son rashin kunya ko sa'arki ce da zaki zauna ki titsiyeta. Tashi ki fita magana zamuyi. Ki kawo mata dan abinda zata ci. Izzatu ta sami wuri ta zauna tace ki barshi a koshe nake. Hamida ta tabe baki tayi gaba.
Mama ta dubeta, gabadaya Izzatu ta fice mata a rai. Mun sami labarin abinda kuka yiwa yar mutane jiya a gaban jama'a. Izzatu na jin haka tasan kila fada za'ayi mata tace Mama don Allah kuyi hakuri. Itama yarinyar zan kirata na bata hakuri. Maybe bata ji haushi ba saboda bata yi kama da mai daukar abu serious ba. Mama tace ga mahaukaciya ko, dole kice bata daukar abu serious. To sakamakon abinda kuka yi jiya Alhaji yaje neman aurenta wurin iyayenta. Izzatu ta zaro ido harda dafe kirji. Yanzu Alhaji Zuhra zai aura? Karamar yarinya ce fa da kadan zata girmi Hamida. Ikon Allah ai da Nura ya nemarwa aurenta. Mama ta tsaya kawai tana kallon Izzatu ranta na kara baci. Ba shi zai aureta ba mijinki ya nemawa aurenta kamar yadda kika fada mata. What? Tashi Izzatu tayi a gigice... Mama don Allah da gaske kike? Hajiya ce da ta shigo dakin a lokacin tace da kuna yar wasa ne da ita. Kan kace meye wannan Izzatu sai kuka. Ta durkusa gaban Hajiya don Allah ku bawa Alhaji hakuri wallahi bazan iya zama da kishiya ba. Bazan iya sharing mijina ba. Daga Mama har Hajiya kallonta suke yi tana kuka wiwi. Mama tace don baki da kunya Izzatu mu kike gayawa bazaki iya sharing miji ba. In sha Allah aure kamar anyi an gama. Tana kuka tace dama kirana kuka yi kuyi min wulakanci.
KE IZZATU MEYE HAKA. Ta yi saurin juyawa wurin Hamza daya shigo dakin shima. Rungume shi tayi tana kuka. Kaji abinda suke cewa wai Zuhra za'a aura maka. Duk kunya ta kamashi yana kokarin tureta tana dada kankame shi. Ya daka mata tsawa sake ni mana... iyayen nawa kike cewa suna miki wulakanci? Ba kin iya kiranta ki fada mata Hamza na sonta ba. To zan aureta kinga bukatarki sai ta biya. Idanu sharbe da hawaye tace ni kake fadawa haka Hamza....sai kawai ta fice.
Mama tayi murmushi sannan ta nuna masa kofa bita kada tayi wani wurin. Ya yi hanyar kofar Hajiya tace Alhaji yace na fada maka lallai kaje gidansu Zuhra yau ku daidaita. Tsayawa yayi kamar gunki yana kallon yadda su Hajiya ke nishadi saboda za'a kakaba masa auren da baya so. Bai ankara ba yaji tashin motar Izzatu. Da sauri yabi bayanta. Hajiya tace an dai ji jiki. Wallahi Alhaji yayi min daidai. Su Mama za'ayi surika, Allah Ya tabbatar da alkhairi. Mama tace Amin Hajiya tana fadada murmushinta.
[9/25, 3:42 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿23
Batul Mamman(Mrs)💖
Yaron da ya rakasu gidan har soro ya shiga dasu sannan ya karasa ciki ya fadawa Baba yayi baki har su uku. Dama a shirye yake shi da baban su Anti Faiza ne a tsakar gidan suna jiran zuwan suriki. Basu san wainar da ake toyawa ba. Baba yayi wa yaron godiya yace da Umma ta dauko juice din nan da ya tanada domin bakon. Manyan kwalin happy hour ne guda biyu sai ruwan roba babba daya. Akan tray ta jera da cups hudu ya mika hannu zai karba babansu Anti Faiza da ake kira Malam yace haba Baban yara bari na dauka.
Tabarmi biyu Baba ya dauko suka shigo soron. Da yake akwai wuta yana ganin bakin yadan ji faduwar gaba. Irin wadannan mutanen da gani masu arziki ne. Anya sa'anin auren Zuhra ne kuwa. Ibrahim yayi sauran karban tabarmin ya shimfida musu. Suka zazzauna suna gaisawa. Alh Nasiru ya sake dasu sosai suna ta barkwanci kamar sun dade da sanin juna. Idon Hamza kyar akan dungulmin hannun Baba. A ransa tunani yake Allah Yasa ba kuturu bane. Kodayake ya gama tsara yadda zaiyi ya gujewa auren nan. Alh Nasiru ne ya fara magana. Alhamdulillah tun kafin muyi abinda ya kawo mu kunyi mana tarba mai kyau. Wannan yasa naji dadi nasan yaron nan baiyi zaben tumun dare ba. Malam yace in sha Allahu. Ai Zuhra yarinya ce mai ladabi duk layin nan ko ince unguwar nan babu wanda bai san gidan Mal Bashir ba. Baban yara ake kiransa saboda dan kowa nasa ne. Bakin gwargwado kuma yayiwa tasa yar tarbiya. Alh Nasiru yace haka ake son duk uba nagari. Ni sunana Alh Nasiru Hamza amma anfi sani na da Maifata saboda sana'ar sayar da fata nake yi sannan yayi musu bayanin asalinsa. Ya nuna Hamza da Ibrahim duk ya gabatar dasu. Sai ya nuna Hamza shine mai neman auren Zuhra. Baba ya sake kallonsa yace nagodewa Allah. Dana Allah Yasa kai abokin rayuwa ne na kwarai ga Zuhra. Ita kadai Allah Ya bani kullum adduata ta sami miji nagari. Tun farkon lokacin da ka fara turo mata sako a waya babu abinda ta boye min. Ni kuma a lokacin na yaba da tarbiyarka nake ta addua. Allah Yasa ayi a saa. Kowa yace Amin. Baba yayi musu bayanin matsayin karatunta da sana'ar da take yi yanzu. Alh Nasiru yace duk babu komai. Zai sanar da yan uwansu na Kumo nan da sati biyu idan ya amince sai a kawo kudin aure ayi maganar sa rana don baya son a dauki lokaci. Hamza dai sai yake yakeyi zuciyarsa na zafi. Ya rasa ta ina zai fara kokarin tattaro rayuwarsa da ke neman rugujewa lokaci guda. Suna mota Alh Nasiru yace yanzu da bamu zo ba ai alhakin yarinyar nan kila har jikoki sai ya bika Yaya.
Zuhra na dawowa Baba ya sanar da ita Hamza da mahaifinsa sun zo. A zahiri ta nuna musu farincikinta amma a tsorace take da abin. Gashi baban Hamza ya roketa ta rufa masa asiri kada ta fada a gida. Anti Faiza ma tace ko Hajara kada ta fadawa. Haka ta shiga daki ta kwanta tana jin iyayenta suna tattaunawa akan bikinta.