← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 108

Sashe 96

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata kunya taji ta kama ta kawai ta kashe wayar ta dauki furar ta ta Shiga kitchen abinci ta hada irin na marasa lafiya marar nauyi tayi kunun gyada ta shirya komai ta dauko su ta Kai parlour sannan ta Shiga daki.

Yana kwance Yana bacci abin sa, ta wuce taje tayi wanka ta fito babu abinda ta saka kawai dan turare ta fesa kadan ta bude drawern sa ta dauko wata doguwar Riga Mai kyan gaske ta saka tayi rolling damma mayafin nata babba ne,Tazo sai tin kan sa ta zauna a bed side drawer tana kallan Shi sunkuya wa tayi tana kallan sa suna hada numfashi ta fara shafa fuskar Shi.

Tace, "audushakuru, audushakuru tashi".

Ganin ko motsi beyi ba sai ma Kara gyara kwanciya da yayi ya sauke numfashi.

Sai tin kunnan sa take ta kwalla ihu "audushakuruuuuuuuu".

Da sauri ya tashi zaune ganin ta tana dariya yasa ya diro daga Kan gadan a dari ta ta gudu tana zuwa ta rufe Shi da kofa.
tace, "kayi sauri kayi wanka Yaya beda lafiya yanzu nan ummu ta kirani".

Wucewa yayi yayi wanka ya shirya tsab ya fito tana zaune tana Shan cornflakes ya fito ya zauna a kusa da ita tare da Jan kunan ta.

Yace, "laifin ki karuwa suke basa raguwa kullum sai kin yi laifi ban Sani ba ko Babyn ki yake Kara saki kike yi laifin".

"Ouch!

Da zafi baby yace da zafi Ka sake ni please".

"Zaki Kara yi min ihu?"
"A'a bazan Kara ba".

"Zaki kara yi min laifi?"
"A'a baza ta Kara ba".

Sakin kunnan yayi.
yace, "idan ta Kara fa?"
Murmushi tayi sosai tace, "idan ta kara?

A sa Mata albarka dayawa".

Girgiza Kai yayi ya kalle ta ita Shi take kallo a tare suka furta"Allah ya shirya ko?"
Murmushi tayi shikuma ya dan Harare ta.
yace, "meye aka tashe ni haka da wuri?"
"Yaya ne".

"Yayi me?"
Sai da ta shanye ragowar cornflakes din ta, tace, "jikinne inaga ni fah".

"Kuma mune doctors ko?"
Turo Baki tayi ta ta tashi ta dauki kayan da ta hada tace, "ni nayi nan ka tashi mu tafi".

Murmushi yayi ya mike suka fita ta Shiga ta kunna motar shikuma yaje ya Bude gate, zuwa yayi zai Shiga ya ganta zata yi reverse koma wa yayi Yana kallan ta yarda take yi har ta fita ya rufe ganin ta koma wurin ta yasa.
yace, "yau fa ke zakiyi driving din mu".

"Baka tsoro?"
"Tsoron me?"
"Driving Dina mana".

"Hmmm ke ko?"
Shigowa yayi bayan ta koma ta zauna suka fara tafiya shiru sukayi sai da suka kusan zuwa.
yace, "kin yi wani laifin fa tu ba'aje ko'ina ba".

Tura Baki tafara gunguni a ciki ciki sai dai duk abinda ta fada yaji Sarai sai da ta gama.

Yace, "Biyu Kenan?"
Cikin shagwaba tace, "haba Dan Allah wai menayi ne?"
"Kinga kalli gaban ki ban shirya Zama a asibiti ba Bansan ke ba".

"Mena maka tou yanzu?"
"Kince ummu Abdallah beda lafiya kuma nasan qalau yake, Ummu ce bata da lafiya".

"Waya fada maka?"
"Oho?"
Daidai nan suka iso parking tayi suka fito shine ya dauko abincin sannan suka fito suna 'yar dramern su har suka iso dakin tsayawa suka yi suna kallan juna.

Binaif ya matsa kusa da ita yace, "kema fa ashe kin Shiga..."
Rufe bakin sa tayi tace, "kana karasa wa ina cizon bakin".

Cire hannun yayi yasa wa bakin sa alamar zip yayi shiru,hararan sa tayi tare da kwafa tana jinjina kai.

Yace, "Madam amana knocking mana".

"Ban iya ba".

"Baban Baby yace ayi hakuri".

Knocking tayi Uncle yazo ya Bude, shigewa tayi ita de ta barsu a wurin suna gaisa wa Akan gado taga Ummu tayi kuka ta gaji.

Zama a tayi a kusa da ita ta taba jikin ta taji da zafi sosai ta tashi ta fita bata jima ba sai gata ta dawo da Leda a hannun ta basa dakin sun ajje abincin sun fita.

Dakyar tasa ta taci wani abun ta bata magani ta sha sannan ta koma bacci ganin ta samu bacci yasa ta itama ta fita taje wurin Muja sun jima suna hira sai da taga kiran Mas'ud sannan suka yi sallama.

Dakin ta koma ganin basa nan yasa ta Kira shi,
be daga ba tasan maybe sun kusa dawowa Zama tayi tana kallan ummu fuskar ta tayi ja dan kuka tana nan zaune tana saka wa tana kunce wa suka dawo.

Zama uncle yayi Yana sauke numfashi Yana nishi,
yace, "na kuwa ji dadin wannan Mike kafa da nayi kace azo a sallame ni nikam kasan fa irin condition basai na fada ba".

Binaif yace, "Kar
Kadamu yanzu nan Zan kokar ta".

"yawwa haka nake so da ansa anyiwa mutum aure a kaishi gida mana yazo ya wani tare a nan ana Kula dashi".

Ummusalma tsabar kunya jitayi kamar ta nitse a wurin
ta yarda maza basu da kunya ko ta sisin kobo ce bare kuma su Saida wa wasu tana Jin su suna zancen su ganin ba shiru zasu yi ba kuma ummu ta tashi amma bata wani motsa ba kawai de tana motsi da idan ta ne.

Tace, "kun tashe ta fa?"
A tare suka juya ganin ta fara bude Ido tana cuno Baki wurin ya karasa Yana jera mata sannu.

Yace, "sannu ya jikin? me kika so?

Ina ke maki ciwo?

Zaki ci abinci?

Kin sha maganin?

Aje a siyo maki chocolate?"
Wata katuwar harara ta maka masa ta juya ta Mai baya ta rufe idan ta, sosa keya yayi ya kalli Binaif.
yace, "kaima haka kasha fama?"
Murmushi Binaif yayi yace, "nasha Mita de har yau kuma ina Kan sha".

Ummusalma ce ta matsa wurin ta ta leka fuskar ta.

Tace, "me kike so?"
Hannun ta ta kama ta rike gam cikin muryan kuka da tsantsan shagwaba kuma a hankali yarda su kadai ne kawai zasu ji.

Tace, "please Yaya don't go, uncle zai Kara kuma da zafi please".

Sai hawaye, murmushi salama tayi ta goge mata hawayen ya zauna a kusa ganin haka yasa ummu juyo wa Kara kama hannun ta tayi cikin sanyin murya da rarrashi.
tace, "kiyi hakuri haka abin yake, dauriya ce kawai zakiyi idan kika daure zaki ga kamar ma ba'ayi komai ba kinji ko?"
Matsowa yayi kusa da su yace, "nifa banyi komai kadan ne fa ai za..."
" Haba yaya Dan Allah nikam ya isa ya haka"
Binaif yace, "suna san privacy zo muje wurin doctor din maybe yazo yanzu".

Sai da yayi mata peck sannan ya fita.

Ummu de daura kanta a Kan cinyar ta ita kuma sai afkin rarrashi Basu jima ba sai ga su sun dawo da uban magani da takarda a hannun sa da'alama an Basu sallamar daman tasan za'a basu tunda uban naci yaje wurin.

A hankali take taka kafar har suka iso wurin motar su a baya tasa ta sukuma suka kwaso kayan Muja ta gani zata je pharmacy da'alama magani zata siyo,zuwa wurin ta tayi.
tace, "kinga mu an sallame mu sai wata ran kuma".

Muja tace, "aikuwa muma an sallame mu amma sai yamma zamu tafi".

"To shikenan Zan Kira ki ko zuwa gobe ne Isha Allah".

Godiya ta Kara yi Mata sannan ta kuma bata wani kudin suka tafi, baya tashi ga ta zauna ummu ta rike hannun gam kamar Wanda zata gudu.

Binaif yace, "kinga ki dawo gaba ki bar masa matar sa".

Aikuwa ummu tasa bata yi magana ba amma ta nuna bata so ai tuni ya shige gaba, sai da ya Shiga ya juyo yana kallan ta yarda ta wani narke a jikin ta.

Suna zuwa gida suka ga su Mas'ud a parlour an baje ana cin abinci da ta bar musu suna zuwa ta shige daki da ita.

Mas'ud yace, "bros gida kuka dawo ne haka?"
Sai da ya zauna yace, "to ya zamuyi da gidan Anty zamu wuce wannan yarinyar tasa kuka ita nan".

Mus'ab yace, "maybe sabida mutune ba'a rasa Wanda suka zo ba".

Zama Binaif yayi a kasa yace, "sauko mana muci abinci".

Saukowa shima yayi suka zauna suka fara ci harda na mota aka dauko suna ci.

Binaif yace, "idan ka cinye kai da Mi Amor".

"Ai daman ni ba'a sona a gidan nan kowa ni kowa ni har Karan gidan nan ma".

Uncle yace, "ai Naga alama rabu dasu kawai".

Binaif girgiza Kai yayi ya tashi ya zauna yana sha kunan uncle yace, "ya kamata muje gidan Baba Zan dauki abu buwa daga can mu wuce".

"Ina zaku yaya?"
Binaif yace, " inda Ka aike mu zamu"
Cuno Baki yayi.

Gaba ya tashi ya fara kwashe kayan ya Kai kitchen, yace, "kuma banzan yi wanke wanke ba".

"Kunfi kusa".

Gaba de yayi yaje suka yi tare da sannan suka fito.

Mus'ab yace, "yane zaka raka ni?"
"Ina din?"
"Wurin mi amor".

"Yawwa Kai jiya wai wa Muka gaisar ne?"
Murmushi yayi yace, "siriki na, kuma yau Zan koma".

"Uhm lalle Kam".

Tashi Binaif yayi ya Shiga dakin, tana kwance a cinyar ta tayi bacci, zuwa yayi wurin ta ya zauna.
yace, "zamu fita yace ki Kula da ita sosai".

Hararan sa tayi tare da murguda baki.

Yace, "ohh!

Nidin?

Zan dawo Naga alama jiya da nace nayi missing anga nayi kadan ko?

Bakomai bashi ne wannan a rubuce".

Tashi yayi zai fita yaji tace, "Ka siyo min ice cream".

Ko ansawa beyi ba bare tasa ran yaji.

Tare suka fita dasu mas'ud suka ajje su a asibiti sannan suka wuce gidan Baba sosai baba yayi mamakin ganin sa kuma wai an sallame Shi itama Umma tayi mamaki sosai amma Basu wani kawo komai a ran su ba abinda zai dauka ya dauka daga nan suka wuce gidan sa dake ring road Binaif ya Kira 'yan aiki aka share komai gidan fes yake babu wani gyara da za'ayi sune har wurin furnitures sun kuwa iya zabe kayan masu kyau dasu masu kyau dasu.

Binaif ne ya bada shawarar suje wurin Anty Safiya ta hado lefe, sunci sa'a a off take bata da aiki tare suka tafi da ita sosai akayi siyayya
a mota ya zauna sabida yanayin jikin nasa Basu suka dawo ba sai yamma likis sun gaji kuwa angama komai da ya kamata.
Chapter 96 · 0% Book details