Sashe 44
A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai na mauje maki Baki marar kunya kawai,
Shiru tayi tasan yanzu tsab sai Anty safiya tasa yamata duka don babu reni a tsakanin yara gidan batasan dalilin dayasa reni ya Shiga tsakinta da Yaron ba,
Babu Wanda ya Kara magana har suka Gama sai da suka Gama Nafisa ta kwashe kayan ta Kai kitchen ta wanke su tas, tace' Bari taje ta gaida mutanen gidan, da to kawai ta masa mata, parlour suka dawo suka zauna suka kunna kallo suna yi, Ummusalma ta kalli Anty safiya
tace'
Anty safiya maman Shi fah,
Kallan Anty safiya tayi
tace'
laa wai Ahmad, Ahmad Cousin din Ummi ne gidan Suma ba a jikin gidan nan yake kuma akwai kofar da ta shigo tana shiyasa kullum Yana nan idan banfita aiki ba shiyasa,
Ummusalma tace' Anty safiya shifa,
Wakenan?
Ehhm Bi...bi...bi...na..nai...f
Numfashi taja tace' nagane,
Hannunta taja suka je daki hotuna ta dauko ta ajje mata Akan cinyarta,Zama tayi a kusa da ita cikin nuna halin nadamuwa,
tace' Binaif be taba tambayar mahaifiyar shiba, Bansani ba ko ya tambayi Rukayya wacce ya tashi a wurinta,
Shiru tayi sannan tace' ki bude hotan mahaifiyar sane,
Bude hoton tayi wata budurwa tagani fara da ita kyakykyawan kallo daya zakayi Mata Ka gane hakan,idan Ka kalli idan ta kuma zakace Mata bafilatana,suna kama da Binaif sai dai idanshi ba irin ta bane nata kana ne na Fulani shikuma idansa ba madaidaici ne,bakinta yafi nashi pink shape dinne irin daya,kallon take sosai tana kare matar kallo hannunta kuma rike da jariri kallanta ta dawo kan Anty safiya wacce take kallanta,
tace' to tana ina?
Kwallace ta taru a idanta ta share,
tace' babu Wanda yasani,ko ta mutu?
Ko tana da Rai?
Bamu sani ba Sai Allah,
Da'alamar tambaya ta juya kallan kallonta,
tace' bangane ba?
Anty safiya tace' bazaki gane ba idan ba bayani aka maki ba,
Tace' zaki iya Bani labarin ?
Ganin tayi shiru alamar tunanin yasa Ummusalma kamo hannunta, tace' don Allah,
Asalin mu mu 'yan kauyen Alkaleri karamar hukumar Bauchi, mu hudu iyayen mu suka haifa Dan Lami shine Mahaifimu Amma asalin sunasa Ahmad Bansan dalilin da yasa ake fada masa haka ba, Ada can ma Shi Dan kasuwa
ne kuma Yana tafiye tafiye da ada tafiyar tana daukan lokaci kafin aje inda za'aje a kuma dawo, mahaifiyar mu Zainab wacce ake Kira da Hajja Abu wasu kuma suce Mata mai tagwayen suna, Hajja Abu tun tana karamar ta take da masifa rashin hakuri,rashin gani ta kyale komai ta hada ba ruwanta da Kai ko waye, dayake a da ne kuma ana yiwa Mata auren wuri shiyasa aka Rasa me aurenta sai Dan Lami Wanda yake Dan uwa a gareta,kwata kwata halinsu bezo daya ba,Amma da yake Shi mutum ne mai karamci iya Zama da mutane
yasa Shi Jan ra'ayinta suke zaune, Dansu na farko Usman sai da aka shafe kusan shekaru hudu Allah yabasu Adam, Usman da Adam kusan tare Baba yasa su a makaranta dake cikin garin Alkaleri,Shi beyi ba shiyasa yasa 'ya'yansa, dukda za'a iya cewa usman kusan halin Baban Shi ya dauko sai dai Sam Shi magan a baya dame Shi gashi kuma da dankaren zuciya, shikuma Adam tun Yana yaro yake da Jan magana shiyasa basa jituwa shida Umma, sai kace ba halinta ya biyo ba, har sun fitar da ran Kara haihuwa
bayan shekaru goma aka haifeni a lokacin suna Usman Yana da shekara sha biyar Adam nada goma Usman Yana makarantar secondary sannan kuma Yana koyar da primary dayake da haka akeyi idan Ka gama Zama koyar kafin Ka tafi jami'a, Nima koda na taso sai ya kasance halina dana Adam ba daya ba,nafi sabawa da Usman a haka muka taso sai nayi shekara uku aka haifi Ruqayya itakuma sai ya kasance Adam ke dawainiya da ita komai shike Mata sai da shekara shida aka sani a makaranta lokacin tana Shekara uku itama sai da tayi shida aka sata, mun taso cikin so da kaunar junanmu tare da tarbiyar
iyaye sai de kuma bamu da wani lokaci Wanda ya wuce na karatu,muna tasowa daga boko zamu tafi ta Allo dayake da duk shi akeyi, har gwara mu muna da Dan lokaci Amma su Basu da wani lokaci idan ba dare ba shima sai can dare suke dawowa saboda sana'ar dasukeyi don su taimakea kansu su ragewa Baba wani abu, bayan wani lokaci
Yayinda Usman yasamu wani aiki a Ilorin na man fetur kawo lokacin akwai mota jefi jefi,shima kuma Adam yasamu aiki a Kano na koyarwa dayake Shi fanin education ya karanta,yayin da nikuma bami cigaba ba, Aikin da suka samu Baba beso ba sai dai kuma Jin Adam
a Kano yake yasa Shi Jin damadama,Yayinda Umma tayi tsalle ta diri tace Adam bazaije Shi ba yayi nesa da gida a gida ma tana fama inga ya fita wani wuri, duk yarda akayi da ita ki tayi kawai sai Baba yace mu tafi tare tunda Yana zuwa acan yayi ya cigaba da sana'ar Shi, wannan shine dalilin tasowar mu daga cikin dangi muka dawo nan kano Yana aikin Shi koyar a gidan da aka bashi Wanda akwai komi da komi aciki ba bukata daga nane Baba ya fara sana'ar Shi kuma ta karbe Shi don har gidan kansa yayi,muna cikin haka mane ma suka fara fitowa inda Baba yace Yana so ne mu karanci bangaren lafiya, Adam ne ya samu mana nursing a BUK anan muka fara karatu, a Yayinda aka yiwa
Adam transfer ya koma Alkaleri kuma aka Kara masa matsayi, ba yarda Umma ta iya ta hakura ta barshi bewani jima ba aka kuma maido Shi,Yana dawowa kuwa ya yace' ya Sami matar aure Amma yaran Giwo ce,ba haka Umma taso haka de ta hakura tayi shiru Amma ba tasan auren nan Allah Yana ya gani bayan anyi aure ta jima bata haihu ba, sannan kuma bata zuwa gaida Umma ita kuwa Umma daman can basanta take ba shiyasa ko bi takanta batayi, Sai da ta shekara uku ta haifo 'yarta mace,a haihuwa ta biyu ma mace ta haifa, anan kuma aka masa transfer ya koma Adamawa aka kuma Kara masa matsayi saboda haza karsa a wurin aiki zuwansa Adamawa a inda yake aiki ya hadu da wata zulai
Ihat, dayake mutanen da akwai rike amana ganin sa mutum kamili da Shi yasa suka bashi aurenta
sannan kuma aka taho da iayenta, a tunanin sa umma zatayi wani Abu sai dai kuma ganin ta nuna bakomai yasa Shi Jin dadin haka satinsu guda anan gidan su sukace zasu koma Suma su Umma suka biso don ganin wuri, Babu ta inda yasamu matsala sai a wurin matar Shi Hajiya Kenan tayi borin ta kada ta Raya Amma a banza, zulaihat yarinya ce mai hankali da girmama na gaba sa'ar Ruqayya ce shiyasa komai nasu yafi zuwa daya ba ta da matsala ko kadan kowa Yana santa, sai alokacin Usman yace' zaiyi aure,dayake Baba bame matsawa haka ma Umma ita dai kawai barta a fada kosa ya shaida da wannan musamman idan kayi Abu baka nemi shawarta ba, a lokaci ne kuma mutuwar Baban Umma ya riske mu gabadaya muka tafi a motar Usman bayan wani lokaci aka daura auren Usaman da matar da ya gani acan kauye a kauyen aka daura ya dau matarsa suka tafi Ilorin,
A bangaren zulait da Umma babu zancen zaman lafiya amma babu Wanda yasani sau uku tana yin Bari daga nan kuma bata sake yin wani cikin ba, Amma Umma tace ya daukota ya dawo da ita kusa da ita, a lokacin mun Gama makaranta mun gama ba jimawa Nayi aure, na tafi bagan aurena da wata biyar Allah yayiwa Baba rasuwa mutuwar ta girgiza mu kuman dauki hakuri, bayan wata uku matar Usaman ta haihu Dan ba Rai kuma bata da lafiya a dole Umma ta ta shirya tace zata je karma a dagawa Yan uwa hankali Ruqayya da Zulaihat suka koma gidan
Adam da zama Zuwan Ruqayya
ne yasa kowa sannin halinda ake ciki Ashe bakar azaba Umma ke ganata Mata ganinta mai hakuri a, koda Umma ta dawo Ruqayya tace baza ta koma ba zata Kula da Zulaihat tunda kamar ga ciki nan a jikinta batayi musu ba ta barta, sanda aka zo neman Ruqayya da aure sai dai idan an daura auren zata tafi kasar waje ne mijin kuma ba ita kadai bace itace ta biyu,ta nemi alfarmar a Bari sai zalaihat ta haihu sai ayi auren haka aka kuwa aka Bari sai ta haihu.
A ranar da ta haihu a ranar tayi rubutu a paper ta ajje ta tafi, bamu Kara ganinta bamu Kara Jin labarinta ta tafi ta bar danta, babu wanda yasan dalili sannan kuma Adam ya sauyawa Ruqayya kwata kwata dukda ita tace rike da dan da ta haifa ta Bari taki ta bawa kowa Haka Hajiya tayi tayi tabata amma a banza bata bata ba,ko Umma bata bawa bare ni,haka ta rike Shi gam ta Hana kowa Shi ko bandaki zataje dashi take tafiya,
Adam kuwa yayi neman duniya babu ita babu labarin ta har Adamawa yaje Amma shiru babu ita Suma sun tabbatar da bata zo ba Yayanta shima Wanda yake zaune a kano ya tabbatar da bataje gidan saba sosai abubuwa sun rikice cikin kuwa harda canzawar Adam kwata kwata ya canza ya dena walwala,
Bayan sati har Anyi nema an gaji kowa ya hakura ya fawwala Allah kuma har lokacin Ruqayya bata yarfa da kowa ba Ya dauki yaron ba ko huduba mahaifin Shi bemasa ba Usaman da yazo shine ya masa babu Wanda yasani, duk yarda Adam yayi da San ganin dansa taki yarda bata bawa kowa Shi bare a dauka,sai da sati yazo kowa yasan sunasa Abdulshakur,Wanda ta masa lakabi da Binaif ko taron suna ba'ayi ba don firgicin da ake ciki, bayan wata uku kuwa aka daurawa Ruqayya aure sai dai ko kafin a daura sai da tabbatar wa mijinta cewam tare da Binaif zata tafi,kuma ya yarda sannan aka daura auren.