← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 108

Sashe 82

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda suka fito Basu tsaya ko ina ba sai company ana suka tsaya sukayi breakfast Sannan,
Binaif yace'' yanzu de ya kuke ganin za'ayi?''
Barrister Ibrahim yace'' Insha Allah Mune da nasara"
Barrister Aliyu yace'' komai ya kare daga gobe inaga, yanzu zai fara neman mutanen da ya siyarwa ne, yanzu ya za'ayi?"
Binaif yace'' ba damuwa, Allah ya kaimu goben"
Barrister Ibrahim yace'' Bari na wuce, sai dai idan mun hadu goben"
Sallama sukayi shima ya wuce,
Coffee ya hada ya tashi ya koma cikin office ya fara aiki, sannan ya Kira Felix shima sukayi magana Akan zasu wani satin daga nan kuma suka fara tsare tsaren su, Baya sunyi sallama ya jima Yana aiki har lokacin sallah sannan yayi sallah, ya dawo ya zauna zai cigaba kawai Ummusalma ta fado masa,ture aikin yayi ya kwashi kayan sa ya fice zuwa gida.

Ya fito Yana tafiya sukayi gware, dagowa yayi yaga dawa sukayi gware haka?

Mas'ud yagani sai mulmula wurin da ya bige yakeyi Yana wani shishi da Baki kamar yasha yaji, besan sanda tsaki yayi escaping daga bakin sa ba,
Yace'' Baka ganin gaban Ka?"
Marairaice fuska yayi tare da yin kalar tausayi yace'' Taya Zan gani, waccan aljanar ta Bani sako wajen dubu wai na siyo mata nikuma har ga Allah na manta na farko ma bare na tuna"
Wani tsakin yaja yace'' kuma Ka Kira Ka tambayeta mana"
" Nine nan naki,sai da tace ta maimaita min, nace Allah ya sauwake ai ni din ba na karshe nakeyi a aji ba, ta kuma cewa to tunda sakon dayawa na rubuta maka, nace daman ai ita ta Saba zuwa ta karshe a aji shine na taho kuma wallahi gashi yanzu na manta komai, sakon kuma tun goma ta Bani Shi, yanzu kuma har Azahar tayi, bansan ya zanyi ba, please my sweet bb Ka taimaka min Dan Allah"
Binaif yayi wani murmushi na irin Ka Rena ni, sannan yace'' idan baza ka Kira ta ba, Nima bazan Kira ba,har wani tayi ta bin kanka ma?

Kace wani meye meye,harza ce Mata dakikiya har sau biyu kuma kace na taimaka maka, you must be kidding"
Yasa kafa ya fara tafiya wurin motar Shi,bin Shi ya farayi Yana rukonsa,
" bb Haba bb ya zamuyi haka, wallahi bance Mata ba, kasan Allah kuwa, Haba Dan yaya naaa? matar Ka ce,ni kuma kauwata ce, yama za'ayi haka, please mana"
Sai da yaje wurin motar sa ya Shiga shima mas'ud din da sauri yaje ya Shiga ya zauna a gaba, Sai da ya tada motar ya fara tafiya, bedana masa magiya ba, Can,
Binaif yace'' da Sharadi"
" Mene sharadin?

Ni indai baza ta Rena ni ba ai shikenan"
" Mtsww, kamin shiru"
" Nayi "
Waya ya dauko yayi dialing numbern ta,
Tana kwance tana tunanin inda Mas'ud ya tsaya gashi Baya picking call dinta, kawai tunanin ya tafi ko wani abun ne ya same Shi, ta dafa farar shinkafa batayi miya ba, tana jiran yadawo tayi miya, har tayi bacci ta farka ta sake wanka shiru, tana cikin tunanin taji karar wayarta ganin sun Binaif yasa ta daga,
tace'' Hello!

Yace'' ya gida?"
" Lafiya ba lafiya ba"
" Me yafaru?"
" Manta kawai,Ka kusa dawowa?"
"Ehh!

Mezan taho maki da Shi?"
" Komai ma"
"Kamar me ?"
" Dayawa fa,kaga ko miya banyi na,na aiki Chatty har yanzu be dawo ba"
" Kyale wannan,waya ce maki da ana aikin Shi, sai yamma zaki ga sakon ki idan bakiyi sa'a bama ya manta, ya tafi wurin abokai, ko ya sami majalissa ya zauna kawai kimin message din abinda za'a"
" To shikenan nagode, sai Ka dawo, take care"
Kashewa tayi, Dan kallan mas'ud yayi yace'' sharadin shine zaka Mata hakuri"
A sukwane ya juyo ya kalli Binaif yace'' am..am..daman,shine sharadin?

Imagine nine Zan bata hakuri"
Samun gefen hanya yayi yayi parking yace'' then go"
" Haba bb wasa fa nake, ai Zan bata ma, ai kauwata ce,aww yaya ta, Anty Ummusalma Walilin Inni, Zan bata ai"
" Better"
Message din tayi mas'ud yayi sauri ya bude yaga ni sai ca yace'' mtsww Ashe ma wannan abun ne, ai na tuna ma, harda wani ice cream a karshe baza' a siyo din ba "
Kallan Binaif yayi yaga driving kawai yake hankalin sa ma kamar ba a kunsa yake ba, ya kuma hade fuska irin ba wasa nan, yace'' bb to Ka saki fuskar mana,Naga de shan kunun ya kare tunda nace Zan bata hakuri"
Ko ehem bece masa ba, be daddara ba ya kuma cewa'' Haba de mutum sai kace ance gobe zai mutu?

Sai cika yake Yana batsewa ai shikenan"
Be tanka Shi ba sai suka je kasuwa,yayi parking ya dauki wayar sa yace'' jeka siyo kayan ina nan ina jiran Ka, idan Ka dade nayi tafiya ta"
" To bani wayar na ga abinda za'a siyo"
" Nazaci Ka tuna,kana bata min lokaci"
Dakyar ya bashi yaje ya siyo abinda tace, sannan ya Karo masu fruit dayawa, ya taho da Kaya Niki Niki, ya bude boot yasa,
ya zauna
yace'' bb nagaji wannan matar akwai sa aiki"
Banza yayi dashi ya yaja motat suka tafi, a wani shagon Sai da ice cream ya tsaya yace'' fita"
" Nayi me fa?

" Ice cream zaka siyo Mata"
Wani idi turo Baki yayi ya fara gunguni sannan ya bude motar ya fita, ya siyo ya dawo, Yana dawowa kafin ma ya Shiga motar yasa Shi a seat din baya, sannan ya zauna, be Kara magana ba har suka iso gida.

Tana nan kwance shiru sai kallo da ta kunna tana yi,da sallama suka shigo tashi tayi taje ta tarbe shi ta ansa kayan hannun sa,
Mas'ud yace''
ni kuma fah?

Wata hararan ta wurga masa, tayi gaba, abinta yayi shima da kayan Yana mata magana tayi banza dashi, sai da ta ajje ta fitar Dana fitar wa tasa a fridge ta dauki Wanda zatayi amfani dashi kawai, Shi kuma ya samu waje ya zaune Yana zuba, yana kuma cin guava,
tace'' Ka wanke kazar Ka gyara Ka daura, a takaice de kayi miya, na wuce ni"
A sukwane a sauko daga inda ya zauna yace'' ke kuma meye aikin ki?

Ina zakije?''
" Zanje na Kula da Mai house ne"
Ta wuce ta barshi a wurin ya saki Baki Yana binta da kallo sai da ta fita daga kitchen din yace'' marar kunyar banza mijin da ba'a San Shi,Kode tana san shi?

Oho de su suka sani"
Koda taje dakin sa yana wanka shiyasa ta fito parlour ta zauna ta kunna kallo tana yi,
Jitayi ya daura kanta a kafadar sa, yace'' me kike tunani haka?

Kallansa tayi tace'' ina tunanin sameera ne"
" Me tayi?''
Gyara kwanciyar ta yai sosai tace'' she's fall for mas'ud"
Ajiyar zuciya ya sauke, yace'' then?

" Gashi ya rabu da ita, yama yi blocking sim dinshi"
" Rabu dashi akwai lokaci"
Shiru sukayi suna kallo babu Wanda yayi magana, sai can ya bata labari abinda ya faru a kotu sai da ya gama,
tace'' Kar Abba yayi wa PA wani abu, ya kamata a buya har zuwa gobe"
" Good idea"
Ana zuwa ko parking ba'a Gama ba, ya fita ya Shiga cikin gida, Mama na zaune tana kallan TV ga ganshi ya fado kamar Wanda aka jefo Shi Yana neman faduwa,da sauri ta taro Shi tana tambayar sa lafiya?

Babu abinda yake cewa sai ya cuce ni,ya ci amanata, ya ha'ince ni,haka kawai yake cewa, yana girgiza kai.

Mama tace'' wai Alhaji waye haka?

Waye ya cuce Ka ne?"
Cikin wata masifa yace'' waye kuwa idan ba Inuwa ba, Inuwa PA da kika sani, shine yaja min komai, shine ma inaga yayi komai, ke shine ma"
" Haba Alhaji wanne Abu ne haka kami biyani dalla dalla mana,sai nafi ganewa ai"
Numfashi yaja sannan kuma ya koma ya jingina da kujera sannan ya bata bayani abinda ya faru kaf a kotu,
Huci ta fara, zuciyar ta wani irin tafasa take yi, tashi tayi ta goya hannun ta a Baya ta shiga zagaya wurin da suke,
tace'' almajirin yaran?

Yaran da beda cin yau balle na gobe?

Yaran da ko karatu be iya ba?

Amma yanzu shine yayi wannan aikin, tabbas ya zama mutum ya gina kansa, wannan Shi ake Kira da daga taimako!

Wuri ta samu ta zauna tace'' Bari muga?

Waye zai yi nasara mu ko su?"
Waya ta dauka ta kira Amma bata Shiga ba, dayar kuma ba'a daga ba, ajjewa tayi tana Kara Jin mamaki gami da jimama min wannan abu,
Dun kule hannun ta tayi tana jinjina Kai tare da bubbga kafa daya tace'' sai na koya maka hankali, sai na koya maka hankalin da ko masu kudi Ka gani zaka gudu, sai na sa maka tsoron mu a cikin zuciyar Ka yarda ko maka mantan sunan mu aka an bata sai Ka razana, ba'a taba ba,kuma baza'a fara ba"
Tashi tayi ta wuce Sama ta dauko wata wayar ta, ta Dan jima tana yi sannan ta ajjeta ta fito, kana gani zaka san abun ya Mata zafi sosai.

"Ina taya ki murna kin samu transfern lettern ki, kije ki karba a wurin barrister Ibrahim,
Amina da taji dadi sosai tace'" Nagode sosai yanzu Insha Allah zanje na karba"
Yace'' bakomai haka zaman taren yake ai, Kar a yar da zumunci de"
Murmushi tayi sosai tace'' Insha Allah baza'a yar ba, Ka gaida min da ummu"
Dariya yayi yace'' ohh Ummu de zata ji,amma tana 9ja sai dai na gaida Madam"
To Ka gaida ta nagode"
Ajiyar zuciya ta sauke Bayan ta kashe wayar ta, tattara abinta ta fara yi masu amfani sai da ta gama sannan ta fito ta Shiga office din barrister Ibrahim suka gaisa sannan ya bata ta fito.

Tana zuwa gidan kamar kullum suna zaune Yana de bewa Inni kewa Yana bata labari masu dadi yana kuma taya ta aikace-aikace, sallama tayi ta karasa shigowa,
Baffa yace'' Amina lafiya kuwa?
Chapter 82 · 0% Book details