← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 108

Sashe 102

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ganin but wait, ba kukan Pretty nake ji ba bazaki dauke ta ba?"
"Wayar Ka ce tasa ai".

"Irin wannan Marta bawa haka?

Zaki biye ni zuwa jibi ai ganin nan".

Murmushi kawai tayi ta kashe wayar mika ita mama tayi ta ansa gaba Daya sai taji kunya ta kama ta takasa shayar da ita a gaban ta.

Haka nan Mama taji yarinyar ta burge ta sabida kunyar ta.

Tace, "ki bata mana sai kuka take amma ki Dan rarreshe ta tayi shiru kadan ba'a san shayar da yaro Yana kuka Sosai ki tashi ki Shiga parlour".

Tashi ta wuce Kan ta a kasa sai da dan rarreshen ta sannan ta bata ta koshi sai bacci goya ta tayi ta fito ganin tana wanki yasa ta je ta fara taya ta wanki ba yawa da wuri suka gama.

Mama tace, "gaskiya ba lalle bane na biki Bana san wani abu ya sami yaro na".

Murmushi Ummusalma tayi kawai bata kuma cewa komai ba ta tashi zata tafi Kenan wayar ta tayi Kara ganin shine yasa ta daga.

Yace, "ina kofar gidan Ku fito".

"Ka shigo to ni ina gidan kusa dasu Ka shigo nan din me farar kofa nan please!"
"Ohh!

Keko?"
"Please".

"To ganin nan".

Dayake bayan sunyi wankin ciki suka koma ita kuma a waje tayi wayar shiyasa itama ta koma ciki sauko da pretty tayi ta kwantar da ita ita kuma mama kitchen ta shiga ta kawo Mata snacks da lemu.

Tace, "kiyi hakuri ko ruwa ban kawo maki ba".

Murmushi Jin kunya tayi tace, "laa bakomai dayake ai daga gida nake shiyasa".

Mama tace, "nikam ina Shan kunya sai kace wata sirikar ki".

Murmushi ta kuma tayi ta, tace, "Mama inaga gashi nan yazo zaku gaisa".

"Tou!

Jeki shigo dashi Bari na dauko mayafi"
Tashi tayi ta fita ita kuma tayi hanyar waje bude masa kofar tayi ya maka harara ita kuma tasa dariya kawai tayi gaba da sauri ya shigo Yana kwafa har parlour ya shiga ya zauna a kusa da pretty sannan ya dauke ta.

Yace, "kawai ki kafa ajje ta a gidan mutane salan ta fado ta fasa Kai".

Waro Ido tayi tace, "yarinyar da ko cikakken juyi bata yi?"
Harara ya balla mata, murmushi tayi murmushi kasa kasa tace, "wallahi zanyi Zama na a gida ko na tafi Adamawa nayi wayon arba'in acan sannan nadawo".

"Naji wannan".

"Yarda fa".

"Banyi ba".

Shiru ganin Mama ta fito da murmushi a fuskar ta ta karaso zata zauna Kenan ya dago dan ya gaita da ta gaisuwar da ba'ayi ba Kenan kowa ya kame ita kuma zaman da batayi ba sai ma Kara Mike wa da tayi.

Kama biyu take hangowa a fuskar Shi Daya kamar ta Daya kuma kamar Wanda ko mutuwa tayi ta dawo zata gane shi shikuma babu abinda yake hangowa sai tsantsan kamar shi ga kirginsa da yaji Yana wani irin dokawa kamar ya fito zuciyar sa wani irin sanyi sanyi yaji tana yi sai faduwar gaba haka nan yaji ya kasa dauke idan sa Akan ta itama haka.

Ummusalma tace, "Mama Zaikai ga Baban Mai sunan ki".

A tare suka maida Idan su Kan ta
kowanne da alamar tambaya a fuskar Shi.

Binaif yace, "mekike nufi Kenan?

Wannan ita ce kika Sawa pretty?"
Gingina Kai tayi alamar tabbatar wa.

Lineage Ido yayi ya Bude cikin a kanta.

Yace, "a'ina kika samu ta?

Mene hadin mu da ita".

Kanta ta mayar kasa tana wasa da hannun ta.

"She's your mother".

Ba shiri ya mayar da kallan sa ga kanta itama Shi take kallo sun jima a haka babu Wanda ya iya magana daga bisani.

Yace, "Nasan kin san komai kin kuma san dalilin barin ta ta barni bayan Anty ummi tace min ta rasu please tell me everything".

Mama kuwa takuwa wurin Shi tayi tana kallan sa hawaye na zuba a idan ta ita de ko ba dan ta bane da gaske zata ke daukan sa yaran ta har ta bar duniya, kawai ta rungume Shi shida pretty dake hannun sa
lumshe Ido yayi ya Bude su akan Ummusalma dake kallan su.

Jin yarinyar ta fara motsi alame zata tashi yasa tayi breaking hug din sai anan yani bugun da zuciyar sa take masa yaji ta dena sai wani sanyin dadi Mai kama dana Jin dadi dake ratsa jikin sa.

Ummusalma tace, "a lokacin da su Mas'ud suka bani labarin su tare da naka haka nan naji ban yarda su Hajiya ba hakan yasa na fara aiki a gidan saboda abu biyu na farko sabida Kai na Biyu kuma saboda idan ina aiwatar da komai nawa babu Wanda zaiyi tunanin nice sabida ina aiki a gida.

Zuwa gidan sai ya zama naji abubuwa da yawa Dan game da Kai da Maman ka, sannu a hankali nagane duk wata duk wata suna zuwa wata anguwa duk da wata na Daya a gidan da satittika nagane hakan sabuda zancen da suke yi ga kuma abina suke kulla maka wani zancen ba da Hausa take ba da yaren Bole take kasance war ta yare sai akayi sa'a na iya yaren sanda ina junior sosai kuma Dana ji sai naji ban manta ba duk wani abu da za suyi nasan dashi har business din da Daddy besan sunayi ba nasan suna yi ita da Anty da taimakon kawar su Bari na gidan sai ya Zama na bana Jin komai sai dabara ta fado min na nasa iya ladi aiki a gidan take dauko min maganar su idan da Hausa sukayi zata sanar min idan kuma da yaran su tayi zata yi recording ta kawo min a boye a haka har wata yayi ranar da za'a kai mata nasa Saminu Wanda suka ce su yusseer suka bita har gidan a daren kuwa aka
dauko ta aka kawo ta nan".

Shiru sukayi kowa Yana kallan ta ta dago ta kalli Binaif tace, "Sanka ne yasa ta tafi bar Ka bata a lokacin kana tsananin bukatar ta San ka ne yasa tayi haka bakomai ba babu uwar da zata haifi yaran ta ta tafi ta barshi a ranar Ka godewa Allah Ka samu Anty ummi wacce ta rike ka a matsayin uwa".

Wani hawaye ne ya digo daga cikin sa a diga akan Pretty yarinya sai ta fara kuka irin tana taya Baban ta kukan farin ciki kallan yarinyar yayi ya tashi ya kai mata ita sannan yaje wurin Maman shi ya zauna a kasa ya Dora kansa akan cinyar ta sai kuka kasa jurar kukan sa tayi ta tashi ta fice daga gidan ma gaba Daya ta koma gidan Maman Sadiq tana zuwa Ummu ta karbe ta ta goya ta Zama tayi itama ta fara ci abinci.

Neena tace, "ina kika je?"
Harara ta zabga mata tace, "inda kika aikeni".

"Haba Salma Dan Allah wai tunda muka hadu fa babu wani zancen arziki da ya taba hada mu wai laifin me nayi maki Dan Allah".

"Mtsww tambaya ma kike?

Bakiyi komai ba".

"Haba dan Allah idan dande naganki har sau dayawa ban maki magana ba kiyi hakuri komai ya wuce ai yanzu".

Banza tayi mata bata amsa ba wato har sau dayawa ma ta ganta amma ba magana hakan yasa ta Kara kume wa da ita kadai tasan tayi abin ta sai da maman Sadiq tasa Baki sannan tace ta hakura.

Mama kuwa itama kukan take ta kasa hanashi bare itama ta Hana kanta,dakyar ta samu.
tace, "kayi hakuri Abdul am sorry".

Kukan ya tsayar ya dago Yana kallan ta, goge mata hawayen yake yi itama ta fara goge masa a tare suka sakar
wa da juna murmushi.

Tace, "yaro na Ka girma ko?"
Murmushin Jin kunya yayi ya dauke Idan sa daga gare ta, ya maida kan sa cinyar ta ya kwanta yasa da'a ce Anty ummi ce Kan sa zata fara shafawa haka ma Ummusalma sun San abinda
yake so, murmushi kawai yayi ya lumshe Ido.

Tace, "bansan irin godiyar da zan yiwa matar Ka ba ban san mezan ce mata.

Amma Ka rike matar Ka dakyau ta Kai duk inda ake so mace ta Kai ya hada komai kuma ta maka komai ba kowacce bace zata ji labarin Ka ta shigo cikin rayuwar Ka ba amma ita tayi hakan, Abdul idan ka butulce mata baza ta Kara yarda da kowa ba ka, itace ta silar hada mu, tasa sunana tun kafin ta hadu dani, and Abdul Karka biyo ni halina na zurfin ciki beda amana beda dadi sai cutar da Kai da wauta da sa mutum nadama duk Mai irin halina Ka bashi shawara da ya dena".

Shiru tayi bata yi, sannan ta kawar da duk wani Abu da take ji.

Tace, "labarin Ka fa".

Murmushi yayi Idan sa a rufe yace, "labari na Mai dadin jine amma labarin ta beda dadi ji sai dai na Baki shi idan zaki ji".

"Nace bazan ji ba?

Ina san ji".

A hankali ya bata labarin ta tsab har kawo haduwar su da Iyayen su komai ya fada mata.

"Allah sarki sai gashi yanzu kamar ma ba'ayi ba haka rayuwar take".

Dagowa yay ya kalli inda take ganin bata nan yasa Shi maida kansa cinyar ta labari suka shiga yi be fada mata anty ummi ta rasu ba sai dai tana san tambayar sa amma tayi de shiru sai aka kira magriba suna nan sai dai idan an Kira sallah suje suyi tare suka ci abinci tana bashi a Baki du sai yaji wani iri be sababa Amma da matar sa wannan normal ne kawa ita din ce be sa ba sai Duka gama.

Yace, "ya kamata mu tafi nasan ana ta kirana wayan na mota ki taso mu tafi".

Baza ta iya musu musu ba tace, "to Bari na hada Kaya na".

Yace, "wanne Kaya kuma Mama?

Ki Bari kawai tunda gidan zaki Bari".

"Sabbin kaya tasa a din kamin fa kwati har uku kayan sallah ma akwati guda aka min kuma kace na barshi?"
Yace, "to muje na dauko maki".
Chapter 102 · 0% Book details