← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 108

Sashe 19

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata barshi yayi magana ba ta dinga Jan hannunsa,bata yarda janshi take,juyowa yayi kawai suna tafiya don yasan komin dare yadawo sai sun gaisa shiyasa kawai ya zabi su gaisa din yama huta da mitarta,
Tunda ya juyo ya fara tahowa suka kalli juna suka zuba masa ido, bako kiftawa har ya karaso gabansu ya Mika masu hannu Amma basu san ma Yana yi ba sai da, ummu ta tabosu tukunna, Yusuf ne yayi dan yaken da kana ganinsa zaka san
iya fuska ne kawai,ya bashi hannu,
yace' Yusuf,kawai iya cewa don maganar ma kakarewa tayi,
Murmushi yayi yace wannan duk ganin nawa yasa kuke kallo na haka?

Kamar na maku kama da wani?

Ya fada Yana mikawa yaseer hannu,maimakon ya Mika masa sai ya zuro hannu a aljihunsa ya ciro hotonta da sauri ya bude ya dauko guda daya,shidai kallansa kawai yake kuma bai dauke hannun nasa ba ganin abinda ya dauko yasa Shi kallan
hoton, yaseer kuwa tashi yayi ya
Kara hoton a fuskar Shi,
yace' haba ummu Yama zakiyi kice wannan basa kama,suna kama wallahi, kece Baki ga kamar ba, Yusuf mekagani,
Yusuf bai iya magana ba don Shi tashin ma yakasa yi,ummu ce ta matso,
tace' laaa uncle kuma fah hakane kuna kama wallahi,
sai kawai tayi dariya, girgiza Kai AA yayi ya amsa hoton a hannun sa
yace' muga da wacce nake kamar,
Kallanta yayi a fili ya furta
student?

Kasantane?

Ummu ta tambaya,ehh nasanta mana a school din da nake lecturing take karatu,bata magana yarinyar sai da na ganku a airport kuna yi ,ashe ta warke yanzu tana magana,
Amma fa ni banga kama ba anan,ya fada Yana kallansu,
Yusuf yace'daman Kai ai bazaka ga kama ba,Amma kuna kama fah.

Yaseer da har yanzu yake kallansa yace' dole akwai alaka a tsakanin ku da ita,
Kallan yaran yayi yace' Ba kune Kannan taba taya kuma zai Zama da alaka a tsakani na da yarinyar nan, ina da nawa iyayen da suka haifeni,itama kuma tana da nata iyayen tunda har tana da kannai.

Yusuf da ya tsani yaji an alakanta ta
da ace iyayensu su suka haifeta,ya tashi cikin wani hargagi ,
yace'
IYAYE ??Wanne iyaye,?

Wanne iyaye take dasu?

Bata da wani iyaye.

Wanne iyayen ne zasu nemi tura yarsu karatu batare da an Kara waiwayar taba?

Wanne iyayenne zasu nemi halaka yarsu?

Wacce uwa ce wannan da bazata bawa
'yarta tarbiya ba?

Wacce uwa ce da zata tura 'yarta wani wuri tace tana so 'yan uwanta su manta ta?

Wacce uwa ce wannan?

Idan ita ba 'yarta bace Shi kuma uban
fa?

Ai Shi 'yarsa ce ko?

To Wanne irin ubane wannan da zai tura 'yarsa
karatu batareda yana tura Mata kudin da zata bukata ba?

A yarda yake da wadata meyasa bazai je ya ganta koda sau daya bane ba a shekara?

Wanne irin ubane da 'yarsa zata tafi tayi wannan adadin shekaru batare da yaji daga gareta ba kuma hankalin shi bai tashi ba?

Fada min sune zata Kira a matsayin
iyayenta ??

Kawo yanzu kuka yaci karfinshi, dauriya kawai yake yi kar hawayen su zubo sai dai kuma bai San
da cewar tunda ya fara ba yake zubar da hawayen ba, Saida ya Gama ya zauna,ya dafe kansa Jin yana Sara masa, yaseer ne ya dago dakan sa
cikin wani irin low voice
yace' da'ace nice ita da bazan kirasu da marikana ba,sun san basa santa meyasa suka reneta,sun san basa Santa meyasa Basu wurgar da ita ba,meyasa Basu kaita gidan marayu ba ta tashi acan,meyasa basu bada ita ba ga mai so?

Sun manta cewa 'da na kowa ne?

Ka fada mana yakayi shiru uncle??

AA kuwa tunda suka
fara maganar yake kallansu,sai yanzu yasan menene matsalar ta, rashin iyaye,
Zama yayi,
Yana kallan ummu yace itace wacce kika bawa Anty labari?

Daga masa Kai tayi,don itakam sun kulle Mata Kai,ai basuyi wannan maganar da ita ba,koda yake bakomai bane daman zasu fada Mata ba,kuma yanzu taji,.

Kallan Yusuf yayi yace' naji bayan daga wurin ummu tana bawa Anty labari,kuma naji kunce zaku nemota can I join you guys ??

Basu Kai ga magana ba Anty ta fito don fadawa ummu taje tayi gyaran daki,Amma sai ta tarar Yusuf na fadan wannan maganar, kuma basu lura da ita ba,
tace' Idan ba damuwa Nima ina cikin wannan tawagar can I??

Tafada da guntun murmushin a fuskar ta,bawai tayi murmushin bane don kanta,kuma baikai zuci ba,can kasan zuciyar ta tausayin Ummusalma take tare da tausayin su kansu besties din,tasan halin da suka Shiga to itama zata Shiga ko bai Kai Rabin nasu ba, murmushin tayi don kawai ta kwantar masu da hankali.

Daga yaseer har Yusuf kallansu kawai suke Basu iya magana ba, ummu ce tayi magana dukda itama tana tausayawa besties dinta da wani irin murmushi a fuska ta
tace' wooww my mom?,my uncle?

Kawai tayi dariya
tace' daman mama kina son mu haka?

Amma kullum sai kin mana fada Ashe kina sonmu,
Ta karasa tareda rungumo mamanta,
Uncle kawai murmurshi yayi don kullum idan aka masu
fada sai tace ba'a San su, dukda labari yake ji,kuma wataran ana Mata fada a gabanshi.

Tashi yayi
yace'ni Bari na koma daki na kwanta don tafiya kam na fasata, Zan fadawa su umma.

Anty tace' ai wani satin Suma zasu dawo, Basu fada maka ba?

Yana tafiya yace' Basu fada min ba da sai dai naje kuma mudawo.

Itama bata Kara maganaba ta dawo ta zauna, kasancewar a three seater suke da space a tsakanin su,Zama tayi a tsakiyar su ta daura kansu a shoulder dinta tana shafawa
tace' kudena damuwa Insha Allah komai zai wuce,kamar ba'ayi ba ,kowa da irin kaddaransa,kuma bazamu iya tsallake kaddaran mu ba,duk abinda kukaga yafaru da bawa an rubuta zai faru dashi ne tun kafin yazo duniya, bacin ga haka kaddara tana cikin rukunan Imani, kun tuna da haka?

Bata jira amsar suba taci gaba da cewa,walau me kyau ko marar kyau,idan kuka ga bawa Yana da kudi,kada kuyi tunanin Allah ya fifita Shine Akan wasu a,a Allah Yana jarabtar sane yaga taya zaiyi amfani da kudin?

Ta hanya mai kyau ko akasin haka, idan kuma kuka ga Bawa Yana cikin talauci shima jarabtace,shin zai iya rike talaucin sa ko kuma zaiyi wani abun da zai sabawa Shari'a.

Allah Yana jarabtar mu ta hanyoyi da dama, batare da munsani ba, Idan Allah ya jarabce mu da kowacce iri ce fatanmu mu mutu Mina masu dacewa .

Haka Allah yasa kuma Haka yaga dama , Allah yasan hakan Shi yafi alkhairi,Amma acikin 100% kalilan ake samun masu fada.

Abinda nake so daku shine ku kwantar da hankali ku kunji ko?

Bana San hankalin ku ya tashi,ina sanku tamkar 'ya'yan da na Haifa a cikina, daku da ummu duk daya ne a wuri na, a haka ta cigaba da lallashinsu tun suna kan shouldern ta har suka zame suka kwanta a cinyarta,wata nutsuwa na Kara Shigar su tanayi tana shafa kansu har sukayi bacci.

Hakan yasa ta kalli ummu Wace ta zauna a kasan kafarta ta daura kanta kan center table itama tayi baccin.

Ajiyar zuciya ta sauke ta jingina da kujeran ta rufe idanta, wata kwalla taji tana zubo Mata,aduk sanda ta tuna da wani babban al'amari,tasan duk Daren dadadewa dole Gaskiya zatayi halinta.

Hannu tasa ta share hawayen,ganin lokacin na tafi yasa ta ajiye kansu a hannun kujeran, ta tashi ta Shiga kitchen don daura abinci.

Basu farka ba sai bayan Azahar, bayan sunyi sallah suka ci abinci,sosai suka ware kamar ba abinda yake damun su, sai da magariba sannan suka koma gidan su,suna Shiga suka ga Mama tana zaune tana kallo kuma tana
waya, Zama sukayi Suma suka Dan fara kallan, Mama ta kallesu,
tace' ya hakuri kuma?

Yusuf ne yace' hakuri an gode Allah mama,
Yaseer kuwa kawai kallansa yake me yafaru kuma, Yusuf kuwa ganin irin kallan da yake masa na irin karka bada mu,beyi aune ba yaji yaseer nacewa" mama kin ga yarda yayi mutane kuwa, Kai mama Allah yasa muma muyi
kyakykyawan karshe , daman fa Shi ba ruwansa, kuma Yana Karatun Qurani ya rasu, gashi ma kuma, maraya ne Akayi adoubting din shi iyayensa sukayi, amma haka suka rike Shi tamkar dansu, Koda suka haifa nasu, sun cigaba da sansa, Hmmmm ai ba'acewa komai mama,
Kallansa tayi tace' Ya sunansa kuma,
Abdul sunan sa ai, munji mutuwar nan ta girgiza mu,
mama, ni har na fara komawa ma ga Allah,yaseer yafada,
Yusuf yace' kuma mama wallahi idan kinga yarda suke sansa ca zakice dansune,muma bamu saniba sai a wurin mutuwan nan mukeji,munyi mamaki sosai, Akan wani shikuma da ajimmu da rikonsa ake,
Ya kalli yaseer yace bata labari,
Yaseer kuwa
yace' ai mama ko wallahi mutane suke Jin tsoron Allah,shikuma wai fa rikonshi fa ake don kawai babansa da mamanshi
sun
rasu, sai ya koma gidan kanin mahaifin Shi to matar gidan bata bashi tarbiya, ta batashi ga kashe kudi,tun muna js2
ya fara shan taba, yanzu kuwa tsabar abin yayi nisa har club yake zuwa abinsa,kuma ba kullum yake kwana ba a gidan, ai lamarin Shi gaba yakeyi, ga yanzu india zai tafi,hmmm Mama tsoron duniyar nan nakeji,
Yafada Yana dan share hawayen kamar gaske,
Mama kuwa tunda yaseer yafara take hada wata uwar zufa, taab ashe itama ta tafka kuskure fa a rayuwar ta, ita har mantawa ma takeyi da abinda ta aikata,koda yake bazata taba kiranshi kuskure ba, ba abinda ma ta aikata ai.

Kallan juna sukayi Yusuf
yace'
Mama lafiya kuwa??

Ko Baki da lafiya ne ?

Bata ji shiba ma itakam ai ta lula duniyar tunanin shin daidai ne abinda tayi ko ba daidai bane?

Suma tashi sukayi suka Shiga daki suna Shiga yaseer
yace' wai ca kace wa mama mutuwa akayi ne?

Yace 'ta shigo kana wanka tace me yafaru taga idona yayi ja haka kamar Wanda nayi kuka?

Shine nace mata ai wani abokin mu ne ya rasu shine fah,abinda nace Mata,Kai kuma da tuni ka kwafsa mana dan ma dai ka iya tsara zance da Kai da waccen parrot din Bansan wa fi wani ba.
Chapter 19 · 0% Book details