Sashe 95
A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Taya kika sani?"
"Ta yarda kika yi magana mana".
Murmushi tayi tace, "freshyo dinki ce bansamu ba shine Anty ta Bani fura na kawo maki nikumana hado da Hollandia.
"Wow nakuwa gode taho muje
kafin wancan uban hadar da da rani yazo ya shanye mu".
Daukan basket din ummu tayi tayiwa Muja sallama ta wuce, a hankali suke har suka iso dakin suna zaune su uku Binaif da su yusseer ne kawai a dakin sai Shi shikuma idan sa a rufe yana kwance da sallama Ummusalma ta shigo ita kuma ummu a bayan ta kanta a kasa.
Yaseer yace, "Antyn mu harda dake ashe ina wuni?"
Bude idan sa yayi ya hango ta sabida Ummusalma ta matsa shiyasa ya ganta lokacin ta maka wa Yaseer harara tare da irin kallan zamu hadu murmushi yayi kawai ya kuma rufe idon sa.
Binaif yace, " mu tashi muje dubiya ko ya kuka ce".
Ummusalma tace, "abinci fa?"
Yana tafiya yace, "banji yunwa".
Tashi sukayi suka fita ita kuma ta tsaya kikam a tsaye, girgiza Kai Ummusalma tayi sannan taja hannun ta har gaban gadan ta Zaunar ta daura hannun ta Akan m hannun sa sannan ta dauki abin cin ta ta fita.
Jin shiru taki tace komai kuma bata cire hannun ta Akan
nashi ba yasa ya Bude Ido ya kalle ta kallan hannun su take bakin ta na motsi alamar takasa cewa komai kuma tana San fada.
Yace, "ba gaisuwa ba sannu da jiki ko?"
Maida kanta kasa tayi tana Mai Jin kunya, ta girgiza Kai, murmushi yayi sosai yace, "Uncle nifa ko kaga wasu wai suyi taji kunyar Uncle dinsu ni kuwa bana Jin kunyar ka kuma bazan ji ba kaji bazan Mata ji ba kuma ko naji to Ka tuna Zan cire ta Dan banga me zanyi yiwa kunya ba ko haka ne ai".
Ware ido tayi ta kalle Shi ta tashi zata fita da sauri ya riko ta.
yace, "oush!
Hannu na kin fama mun wayyo hannun na?"
A rikice ta dawo ta fara jera masa sannu tana rike da hannun shikuma be Dana ba tsabar rikice Vail dinta ya kunce bata sani ba dayake doguwar Riga ce tasaka sai tayi rolling da mayafin rigar sai hula data sa, kallan ta kawai duk tsawan shekarun yaune kawai yake mata kallan da ba
na 'ya ba kallo ne na irin mijin dake San matar sa ganin Dan abinda ya same Shi Amma tabi ta riki ce, ita kuma ganin har yanzu Yana rike da hannun yasa kawai ta rungume Shi ta fara kuka.
Dayan hannun ya fara sha Mata kanta dashi Dan be zaci haka daga wurin ta ba yasan da wuyane tayi kuka sai dai kukan tabara sosai yake shafa ta ya cire hular kanta ya lumshe Ido yana jin kukan ta ita kuma dadin shafar data ji Bata San sanda ta hau gadan dakyau ba tayi shiru tana Jin yarda yake shafa ta bata San sanda bacci yayi gaba da ita ba daman jiya bata yi wani baccin kirki ba.
Fuskar ya leko yaga tayi bacci gashi yamma ce besan tashin ta yasa kawai ya barta duk da kwanciyar bata masa ba Yana Jin wani iri a jikin Shi babu dadi wani Abu na tsarga masa haka ya daure ya kyaleta.
"Alhaji Sai fa Ka biya kudin nan su goma ne masu aikin nan tun jiya nake binka Ka Basu kace sai kaje banki yau kaje Baki amma shiru".
Abba yace, "kefa kika ce abinci ya kare na siyo komai da komai yarda zai isa ya Dade ana amfani dashi yanzu ni banki na miliyan daya ne ya rage ashi zanyi hidi mar biki, idan kin yarda ga dubu hamsi nan ki raba musu ina laifi?"
"Wai ni Alhaji tsaya ina safe din gidan can kawai Ka dauka a fasa ta a kwashe komai mana".
"Ban fada maki daman?"
"Kace min me?"
"Barayi sun shiga gidan sun kwashe komai daman ba wani kayan kirki bane Wanda yayi saura to sun hada da na dakin nan sun dauke ranar da sukayi kuma gobara ta kama a gidan Alhaji Sammani to ya taba gidan shima kusan rabi ya kone na zaci na fada maki ai".
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un yanzu hakan ta faru baka fada mun ba?"
"Yanzu kin sani".
"Taab nikam bazan iya Zama a wannan takaicin ba".
Banza yayi da ita ya ya tashi ya dauko dubu hamsin din ya ajje Mata yace, "idan kiga dama ki Basu daga nan kuma ki sallame su banda kudin bawa masu aiki".
"Nikuwa bazan iya ba wannan ai cin zarafi ne da tazorci wallahi, ina bazai taba iyu wa ba".
Har wani huci take tsabar takaici da haushi.
Abba yace, "ai kina da kudi zaki iya cigaba da daukan su amma nikam nayi nawa nagama bazan iya ba".
"Haba Mahmud Bama Alhaji ba,
wannan abun fa abun daba wa ne ya kamata a duba lamarin nan da kyau wazai ke Shara,wanke wanke, wanki, share tsakar gidan nan ma kadai aiki ne, ga wurin wasan su Yusuf ga gyara dakin su du waye zai ke yin wannan?"
"Hmmm sunana ne daman, su zake yi mana waye zai musu kiyi abinda zakiyi su karasa sauran nagama magana".
"Hehehe Mahmud Kenan Ashe kuwa na kusa barin gidan nan wallahi cab Allah ya sauwake".
"Ameen".
Yace, "kinga yau za'a zo auren neman auran Sameera" .
"Na Hana su zuwa ne?
Ko kuma nace Kar a zo?"
"Fada maki nayi ne kawai karki ga wai sunzo anyi magana, na kuma Kira abokai na Wanda zasu tsaya mata".
"To".
Ya kauda kansa yana Jan carbin
sa ya rabu da ita dan Shi Kam ya Gama abin da zaiyi karta sa jinin sa ya hau ya samu yasawa zuciyar sa salama abu Daya ya yanke duk sanda ta nemi takardar saki to zai bata babu takura babu takurawa.
Ita kuwa tashi tayi ta bar wurin tana masifa bayan ta dauki kudin da ya ajje mata.
Tana Shiga suna zuwa abokan nasa sosai ta tarbe su yasa aka kawo musu abun motsa baki sabida ya tana da saboda su, suna zuwa sai ga su Daddy Suma sunzo ba'a wani yi doguwar magana ba tunda harda Baba sai mijin Anty ummi sun san juna babu wani bukatar bincike Daddy ya nema da asa nanda wata biyar Abba yace hakan yayi dan ita ma zata karasa makarantar ta daga nan aka Shiga 'yar hira sai daf da magariba kowa ya tafi hakan yayi wa Abba dadi sosai baka dan ba".
Basu suka bar asibiti ba sai dare anan suka ci abinci sannan suka bar ummu su yaseer suka je suka dauko Mata kayan wayan
acewan Anty, da zasu tafi ummu kamar tayi kuka.
Tace, "Yaya salama wai ni Daya za'a Bari ne?"
"Ummu kiyi hakuri ki zauna kinji ko?"
Uncle yace, "Binaif wai yaushe za'a sallame ni nifa nariga da na warke".
Binaif yace, "da saura hannun Ka be karasa warke wa ba".
"Hakkun Naga alama".
Murmushi kawai Ummusalma tayi ta fadawa ummu abun a kunne sannan suka tafi.
Sai da suka sauke su yusseer sannan suka wuce gida.
Ummusalma tace, "yunwa nake ji muje a siyo min fura, furan dazo yamin dadi sosai".
Binaif kuwa beyi kwanan gidan su ya Mike ya dau hanya.
Mas'ud yace, "wallahi kede sai addu'a wannan ci naki dame yayi kama eh?
Kinga yanzu kin koma kin cin abinci sau goma a rana".
"Kai chatty Bana San sharri har wani goma a rana".
"To me nace Dan nace goma, fav ringa kirgawa kaga da safe idan ta tashi sai ta sha cornflakes ta dama custard ta sha fa kuma da yawa cemin daya,
Mus'ab yace, "Daya".
"Kaji Daya?
Tam tazo idan zamu ci breakfast nan ma taci ce biyu".
"Biyu".
"Tazo ta idan angama ci fa ana jima wa kadan befi da awa ba sai tace yunwa taje ta dafa indomie taci ba uku ko?
Tazo kafin aci na rana ta sha fruit salad, hudu Kenan aci na rana da ita..."
"Chatty Bana San sharri Naga tare da Kai muke sha muci komai kayi dani bari naje nayi alawar madara Naga wani yace zai sha ko aka min sintiri a kitchen".
"Haba Anty salama kinsan Bama haka kece lil sis na my sweet kauwa love you Lodi lodi irin Daya wanan".
Mus'ab yace, "baza'a Baka ba din nasan ni za'a bawa kasa Banda magana kamar Kai".
"Baka da maganar kamar chatty amma kafi chatty tsegumi da kini bibi ai?"
Dariya Binaif da Mas'ud suka sa, mas'ud harda rike ciki Dan mugunta.
Yace, "maganin Ka ai wayace ma ana yiwa wannan aljanar kwanin ta".
Shiru tayi ta kyalesu ganin yayi parking a wani wuri harda su kaza zai fita tace, "a hado da kaza da ice-cream sai kasiyo furar da yawa daga na a hado da fresh milk itama da yawa chatty kuje Ku taho da kayan".
Tsak Binaif ya tsaya Jin wannan Batu nata, a hankali ya juyo.
yace, "du waye zai sha yaci wannan din?"
Dan murmushi tayi ta Ka fara wasa da abin hannun ta tana cigaba da murmushi, Kai kawai ya girgiza ya karasa fita, sune suka je suka kwaso kayan da ta bukata babu abinda Mas'ud yake sai mita da jaraba an asha aiki Dan ba iya abinda ta ce kawai ba sun Karo abun da yasan tana sha.
Da safe karfe shida tana parlour tana aikin shan fura tana danna waya gashi furan tayi sanyi dai-dai tana shan abin ta.
Ganin Kiran Ummu tayi gaban ta ya fadi ta furta "Lafiya?"
Gaban ta na faduwa ta daga wayar tana daga wa taji shashshekar kuka...
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt
A BAKIN WAWA
_Akanji magana_
Gaban ta taji ya kuma faduwa. tace, "Ummu meke faruwa ne?"
Cikin kuka ummu tace, "yaya kizo yaya wallahi..."
"Kinga
Ummu ki fada min meke faruwa lafiya?
Wani Abu ya samu uncle din?
Kiyi magana".
Ji tayi yace, "ni lafiya nake, ta damu wai sai kinzo shine ta Kira ki tun dare take son Kiran ki na hanata shine yanzu kuma take kuka".