← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 108

Sashe 20

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yafada Yana hayewa kan gadan, tambilin yayi a gadan
yace' Mama fa ta tsorata wallahi,
Kawai ya saki dariya,
Yace' wai Kai yaseer sai yaushe zakayi hankali ne ?

Baka da aiki sai dirifkiya a kan gado ko?

Du kabi ka sawa mutane ciwon jiki,banza kawai,
Ikon Allah,wai Dan Allah dame ka fini ne,da shekara dayan?

Koma da second daya ne na fika de,kuma dole a kirani da yaya Yaseer a toh,
Kai Ka sani,mutum de bazai kirani yaro ba tunda shekaru na 16,16 kuwa ai ba wasa ba.

Dariya kawai Yusuf yayi ya tashi ya Shiga toilet.

Hajiya wannan itace mai aikin naki,kamar de yarda na fada maki ita din kurma ce,tana ji Amma bata iya mayarwa,
Kallanta Hajiya tayi ganin yarda take kalle kalle yasa ta daka Mata tsawa
tace' ke kurma,
Dukda taji ta,Amma ko gezau batayi ba,kawai tana kallan girman parlourn da za'a ce kullum sai ta share tayi mopping,tunanin irin ciwon bayan da zatayi kawai take yi.

Kara daka Mata wata tsawan tayi sai
a sannan ta jiwo ta kalleta,
Hajiya tace' kinaji na ina maki magana,
Girgiza Kai tayi alamar a,ah,kallan iya ladi Hajiya tayi
tace' bacin rashin magana harda na rashin ji ma,ni kuwa bazan dauka ba ki sanar da ita tam.

Itakuwa Ummusalma a zuciyar ta tace idan nayi maganinki zakisan Bana ji Bana magana ai.

Kuma yanaga fuskarta a murtuke bata fara'a ne
ko kuma saban iskanci ne?

Iya ladi ce me bada hakuri,daga nan ta sallame ta, sannan tace ta kaita dakin ta,Wanda yake bayan jikin gidan amma kofar ta waje ce window dakin kuma daya a ciki zaka iya hango parlour dayan kuma a waje,garden zaka hango.

Katifa ce kawai a dakin sai pillow ba bedsheet bare kuma a samu blanket sai wata munafikar wardrobe
ta jikin bango siririya da ita, Allah sa Akwai toilet adakin, iya ladi ta kalla,
tace' haka Zan zauna ba abin shimfida?

Ba bargo?

Iya ladi tace' Bari naje na tambayota, naji ko za'a samu.

Batajira amsar taba ta fita,tana nan tsaye kuwa saiga ta tadawo da bedsheet sai karamin bargo mai laushi, itakam a ganinta daga bedsheet din har bargon ba Wanda yamata,Karba kawai tayi a rashin babu,kudi ta kawo ta bawa iya ladi sosai tamata godiya ta fice.

Bayan ta Kara kallan dakin,babu K'ura a ciki da'alama ana gyarashi, Ghana most go dinta tasa acikin wardrobe din, daga kasa taga tsintsiya da Dustbin karami sai parker, toilet ta shiga shima ba laifi dukda ba bathtub Amma akwai ruwa, kuma akwai kayan wankewa.

Fitowa tayi ta Kara share dakin tsab sannan ta shimfida bedsheet din,ta zauna abakin katifar,tana Zama ana kiranta,
Hajiya tace'
sunanki salamatu ko??

Daga Kai tayi, taci gaba to aikinki a gidan nan shine gyaren Parlourn nan, Dana Sama,sai abin da ba'a Rasa ba,muna da mai girki da wanke wanke, sannan Bansan kazanta ko kadan kina ji ai?

Daga Mata Kai tayi alamar ehh,
To tashi ki Bani wuri, sum sum ta tashi ta koma daki, jakar kayanta ta dauko ta ajje lungun katifar,ta bude ta Ciro wayar ta, missed calls din maman Sadiq ta gani, kasancewar sunyi exchanging phone numbers,kiranta tayi bayan sun gaisa maman Sadiq
tace' maganar gidan nan ne mai gidan yace dari takwas zai Saida,gidan kuma karami ne ,kuma dakunan a jere suke,kamar namu na da,
Ummusalma tace' Shikenan bakomai,Zan turo maki kudin idan yaso sai a mayarshi Bungalow kamar naku
Amma two Bedroom nake so,
Shikenan ba matsala,
Tace' account numbern karki manta,
Daga nan sukayi sallama,
Kwanciya tayi Akan katifar tace' tunda nake ban taba kwanan katifa ba sai yau,
Tasaba tajita a Sama tana juyi yanzu kuwa sai dai tajita a kasa idan batayi wasa Bama taji ta mirgono kasa, tana zaune
har magariba sannan ta tashi tayi alwala tazo yin sallah ba abin sallah, fita tayi ta ga bakowa a parlourn tsaki taja ta dawo ta cire dankwalin ta tayi sallahn dashi, tana nan har Akayi Isha, Jin tafara Jin yunwa yasata tashi,tana nade dankwalin, ganin kamar mutum yana zaune a garden yasata lekawa,yana zaune ya lumshe idan sa ya daura kafa akan Akan table din da dayake na gossiping chairs din, tana kallan Shi kasancewar windown da yake facing kuma da haske sosai a wurin shiyasa ma bata kunna fitila ba, matsowa tayi jikin window tana kallansa, damuwace sosai a tattare dashi, kuma da'alama mafita yakeso ganin yanda yake karkada kafarsa da kuma bubbuga hannu sa da yakeyi, bata San iya adadin lokacin da ta dauka tana kallansa ba kamar yarda shima baisan adadin lokacin da ya dauka a wurin ba,sai da yabar wurin itama ta juyo ta ajje dankwalin kanta,ta fita don cin abinci, kitchen ta Shiga tunda daman sai tabi ta kitchen zata Shiga cikin parlourn warmers din ta bude taga sauran abincin kadan ne ya rage,don haka ta zauna taci ta koshi ta kora da lemu harda cake abinta, ta koma dakinta har zata kwanta tadawo ta rufe kofar ta bar key din a jiki, kayanta ta cire tasa yar rigarta ta kunna fanka,ta janyo wayar,tana dannawa taga time 11:45,ita a tunanin ta yanzu bai wuce 9 ba haka,tayi mamaki sosai, contact ta shiga taga numbern su Yusuf batasan ta Yusuf ba batasan ta yaseer ba duka yusseer tasa masu,sai ta ummu kuma,sai numbern su chatty da glip ta 9ja,da maman Sadiq,sukadai ne daman suka bayawa ba ,sai number sahr da wurin aikinta shikenan contact dinta, what's app tayi downloading ta bude, badan komai ba sai don kawai ta ga su yusseer yasata budewa, aikuwa de tana shiga sunansu taga Dukan su online,
Batayi masu magana ba ta kashe tayi addu'ah sai bacci.

Washegari da wuri ta tashi
ta shirya ta fara aikinta, tas tas share ko ina ba ha'inci ba komai ta gyara ko ina da ko ina har windows ta buge,tayi mopping sannan tasa turaren wuta ganin burner da tayi a parlourn sama,ta rufe ko ina ta Kara fesa air freshener, ta kunna na tsinke kuma,sosai gidan ya dau kamshi mai dadin gaske,ta kunna ac, sannan ta shiga dakinta,tana zuwa ta baje a kan katifa ta gaji over gabadaya jikinta ciwo yake abinda bata Saba ba sai dai tayi kadan, janyo wayar ta tayi ta duba time ganin Tara saura yasata Kara gyara kwanciya, sai bacci,
Sosai gyaran yayiwa Hajiya kyau a zuciyar ta, abinci aka kaimata ganin tana bacci yasa aka ajje mata, bata farka ba sai shadaya,ganin abinci an ajje a gefe yasata Shiga wanka,bayan ta dau sabulun ta.

Abincin ta bude bayan ta shirya, chips da kwai da bread sai shayi,shayin kam ya huce shiyasa kawai taci chips da kwai, ta kwashe ta kai kitchen.

Ahaka tayi wata a gidan bata fita ko nan da waje sai dai zubar da ruwan mopping amma bade ta zauna ba,daga daki sai parlour shima tana gamawa take komawa daki, Hajiya kuwa zagin da take Mata kuwa ba'a magana,har wani yar Rama tayi daman gashi ita ba kiba ba, kuma kullum cikin bambamta Kaya take bata taba sa complete Hajiya tayi mitar tayi masifar a banza beyi aiki ba ,kuma idan tasa zani saita tattarshi yadawo Sama kauri a waje, ba abinda ya dameta,wataran tana Shiga dakunan su Duka
ta gyara sosai yanzu kuwa ta Saba ma da gyaran da masifar Hajiya bama Hajiya kadai ba duka yan gidan basu da mutunci ko kadan har abokiyar zamanta kuwa.

A zaman ta da Hajiya da kuma kishiyarta yarda suke abunsu babu kishi ko kadan na zahiri, ga kuma duk lokacin da suke zance suna ganinta zasuyi shiru,ranar da sukayi Baki taje kaima su lemo sunayin zance tana shigowa,sukayi shiru, bakin ne suka ce ita wannan bata sallama idan zata shigo wuri ne ko yaya?

Hajiyar ce tace' ai kurma ce bata magana,
Dayar bakuwar tace ai irinsh ake so a masu aiki,kinga ba Wanda zaiji sirrin ki,tana fita kuwa ta labe, taji abinda suke cewa,tundaga ranar take yawan Shiga dakin Hajiyar,itama Hajiya tadena wani boye boye ko ta ganta,sai wani yare da
takeyi abinta, hankali kwance.

Yau aiki take Amma ba kamar kullum ba bayanta ke ciwo sosai,alamun period dinga na gab,babban tashin hankalin ta be wuce yarda bata da pad ba,kuma ita ba magana ba, kuma bata Jin akwai wani shago a kusa,dauriya kawai takeyi, yau ko turaren da take sawa ma bata saba,so kawai take taje ta kwanta,ko zata ji saukin abinda take ji, saukowa takeyi ahankali hannunta rike da bucket din da tayi mopping, sai da taje tsakiyar steps din ta rike bayanta da dayan hannunta dayan kuma tana rike da bucket din tana cikin tafiya sai ji tayi tayi tuntube da bucket rufe ido kawai tayi tana jinran taji zafin fadowar da zatayi,Amma Jin kamar an riketa kuma ga wani sanyayyen turare da take ji yasata bude ido fes ta sauke idan ta cikin nasa, dukda ba rokota yayi ba,tokareta
yayi da hannunsa Duka biyu,
Kallanshi kawai take kamar yarda shima ita yake kallo, babban abinda yasa bata fita kenan bata so su hadu,dukda ita tana yawan ganinshi a garden
, shikuma tunani yake me yakawota gidan su,mekuma takeyi?

Dukda kallan da sukeyiwa juna hakan be Hana su wannan tunanin ba, yayinda zuciyar ta ta fara abnormal bugawa sakamakon wani yanayi da ta tsinci kanta aciki,shima hakanne a wurinsa, sun jima suna kallan juna yayin da idan ta kifta ido sai yaji an tafi da numfashin sau dubu, Baiki su dawwama a haka ba,
Hajiya ce fa fito don zuwa kitchen ta hado Breakfast ganin su ahaka yasata ta saki wani ihu tare da salati,
tace' na Shiga uku ni Hafsatu mezan gani??
Chapter 20 · 0% Book details