← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 108

Sashe 51

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace' eh ita, sannan ta nuna masa dakin,
Shiga yayi parlour har yayi Dan Kura danma wai ba sanyi ake ba, kofar kusa dashi ya bude yaga kitchen ya bude na opposite yaga toilet ne,sai ya bude na gaban Shi daki ne na tarkacen su, Wanda yake opposite dashi ya bude yaga dakinsu Shiga yayi yafara duba abu sai dai babu koda
Paper dayane sai hotanta, wayar yaseer ya daya gani akan gado yasashi dauka ganin ya kunna yaga bata kawo ba alamar akashe take,
a aljihunsa yasa ya fita, Basu dawo bakuwa Saida ya juna a charge sannan ya fita yin sallahn Isha sai da yaci abinci ya koshi yayi kallo zuwa 9:30 ya tashi ya kashe kallon ya dauki mukullin motar dayagani a Parlour yaje ya daukk Atm dinshi sannan ya fice zuwa store Dan siyo kayan bukata.

A wani store yayi parking yace' bazaki fito ba?

Tura Baki tayi gaba tace' ice cream,
Yace' idan Baki fito ba to bazan siyo ba,
Kara tunzura Baki tayi tare da kumbura Baki murmushi yayi,
yace' da'alama de kinsan Abu nan ma dazu ko?

Mai dadin nan?

Kallanshi tayi tace'wanne Abu Kenan?

Meye mai dadin?

Kawo kunnanki kiji rada Mata wani Abu yayi ai bashiri ta bude kofa ta fice tana murmushi Tama Riga shi Shiga store din sabida haka sai tayi hanyar ta, shima da yazo sai yayi hanyar Shi tana cikin tafiya taji tayi gware da Abu dago Kan da zatayi sukayi four eyes da uncle Baki bude take kallanshi kamar yarda shima yake kallanta, murmushi karfin hali yayi
yace' can I have your contact please?

Yafada yana Mika Mata wayar Shi,wayar tabi da kallo sannan ta karba tasaka masa, murmushi yayi yace' thank you,
Sannan yace' Ummu ta Shiga damuwa saboda rashin bestie dinga am I mean Yusuf da yaseer, bayan sun so su nemeki amma Allah beyi ba Sai kaddara ta Riga fata,
Yace' idan bazaki damu ba inasan zamuyi wata magana,
Duk maganar da yake a sanyaye yake yinta Kala kalar tausayi, a yarda ta lura ma kamar Yana cikin damuwa damuwa mai wuyar fassara wa,
Kasa magana tayi tsabar ta Zama speechless batasan haka Abu yake ba bata san zata cutar da Ummu ba da batayi ba,
wayarta ta daga ta Kira Binaif amma bedaga ba, maybe wayan na mota har ya wuce ta da sauri ta sha gabanshi tace' baka kirani ba,
Murmushi yayi yasan gudun kar ayi ta ta ta da ummu ne shiyasa tace haka, kiranta yayi taga number samun kanta tayi da Saving with Yaya,
Shikuma yayi gaba abinsa, Binaif ne yazo wurin ta Yana neman wani Abu hankali kamar ma be ganta ba sai duduba
mutene yake zuwa tayi wurinshi,
tace' lafiya?

Wa kake nema?

Rike hannunta yayi yace' Neena
Kallanshi tayi dakyau tasaki Baki shida besan Neena ba,?

Kara maimaita wa yayi,
yace' Ehh Neena nagani Amma banga fuskarta ba tana cikin store din nan,
What?.......
#team Umsha
#team yusseer
#team Mussab????

More comments
more _typing_
By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
Itama fara neman ta tayi Saida babu ita babu dalili ta gajiya tayi,
tace' Ka saya abinda zaka saya mu tafi,
Yace' nagama siyan kayana, muje ki dau ice cream dinki mu tafi,
Fitowa sukayi bayan ta dauki ice cream din ya biya kudin, tunda ta fito kafin su karasa wurin motarsu taji ana kallanta daga Baya tsaya tayi ta juyo Amma ba kowa,gaba tayi ta duba namma bataga kowa ba zuwa yayi
yace' lafiya kuwa?

Idanta ya cicciko da hawaye,
tace' indai da gaske
Neena kake tunanin Ka gani to tabbas itace kuma yanzu ma itace take kallona,idan baza zo inda nake ba nagama nemanta a rayuwa ta har a bada ko naganta Zan nuna ban Santa,
Ta karashe
tare da goge hawayenta ta tafi ta barshi a tsaye, Saida taje wurin motar Yana kallanta sannan shima ya yafi,
Sun dau hanya,
tace' taya Ka gane Neena ce bayan kuma kace bakaga fuskanta ba,
Yace' ina tsaye a wurin cashier wata tazo bazata wuci kiba a tsayi sai dai da Nikaf a fuskarta itama ta tsaya tana jiran a Gama min itama a Mata zoben hannu na ya gani,
tace' Zoben Ka yayi kyau a'ina Ka siya don Allah,
Nace' ba siya Nayi Bani akayi,
Tace' Zan iya sannin don Allah waya Baka?

Kinsan data min tambayar nan sai da ta kalleta?

Nace' meyasa Zan fada maki?

Tace' kawai ina San sanine Naga de zobem kamar na Mata,tunda yawanci irin wannan Yana zuwa da bracelet shiyasa, to bansani ba ko Kai naka yazo iri guda daya ne,
Nace' Bani akayi,kuma itama bata akayi,
Budar bakinta sai ca tace' irin na Ummusalma sak, sannan ta tafi ko gama biyan kudin ma batayi ba, sai da ta tafi wani tunani yazo min, nace' tabbas itace shine fa na fara duba
mai irin kalar hijabinta,
Yace' kuma kinsan Nima nakaina nayi mamakin yarda na zage ina zabga Mata surutu Bana tantama itace,
Murmushi Ummusalma tayi,bata ce komai ba ganin sun dawo hanyar gidan Umma yasa,
tace' lafiya?

Yana karya kwana yace' kinyi mantuwa,
Ni babu abinda na manta fa,
Idan munje zaki gani ai,
Shiru tayi don itakam yau taga ta kanta daman ma bata zo ba, a waje yayi parking, ya zagayo ya bude Mata,
yace' fito,
Tana kumbara Baki ta fito tare da gunguni be kulata ba ya shige suna Shiga parlour suka tarar da Hadaimai suna kallo suna cin abinci Basu fito ba sai da suka tabbatar da sun tafi sannan suka lallaba suka fito, sauran abincin da sukaci suka rage shine suke ci, ko kallan inda suke basuyi ba kamar yarda Suma Basu kalle su ba, sai da suka ce Saima,
tace' shegiya karuwa mai kama da ifritu,
Sairai Ummusalma taji ta kasancewar itace a Baya shine a gaba, bata tanka Mata Har suka Shiga daki, yaja
ya tsaya
tace' mena manta to?

Zama yayi Akan kujera
yace' a haka zaki tafi?

Bata ganki ba sanda kika fito?

Tace' wa?

Anty safiya,
Yafada Yana Danna wayar Shi,
tace' to daka dawo Dani mezanyi?

Yace' to shikenan Bari mu tafi idan tagano munyi wani Abu kinga gobe ina zuwa zata Bani ke, Bari mu tafi,
Itadai harga Allah bata gane Kan zancen sa ba, to me
Sakayi ganin ya Kai bakin kofa yasa ta bishi har zata bude itama ta fita wani Abu ya fado ranta, ai bashiri ta koma
ta canza kayanta data zo dashi ta fito tana tamke fuska, ta Shiga mota dariya ce cinsa Amma ya Maza yayi murmushi kawai sun fara tafiya,
yace' ai dakin koma da wancan kayan meye laifin su kuma?

Banza tayi dashi, Tama kawar da kanta daga gareshi,
yace' fine, kici gaba kinsan ba ganin ki kikayi a parlourn Anty ba ko?

Yana rufe Baki
tace' Haba Mai gida yanzu menayi?

Kawai de maganar ce ban gane ba shiyasa,
Ta karashe da yake a fal fuskarta ita dai burin ta ta ganta a gida,
Shiru yayi be Kara magana har suka kusa zuwa, yaji
tace' Ummu tana cikin damuwa sabida sace su yusseer gobe zasu koma,
Wacece hakan?

Yarinyar da suka zo gidan ku ranar nan,
Yace' ohh nagene, me dinsu ce?

Kawar suce,
Waya fada maki halinda ta Shiga,
Wanda muke nema,nafada maka daman niece dinshi ce, kuma baya ga haka ma gashi an barsu abubuwa dayawa a school, na zalince su,
Bakomai, Insha Allah komai zai daidai,kin ansa numbern Shi?

Ehh ya Bani,
Saida yaje gidan mai vadi ya bude masu suka Shiga yayi parkin,
yace' Bani numbern,
Bashi tayi yasa a wayar Shi, sai anan yaga miss called din ta, beyi magana suka fito tare da daukan kayan da ya siyo sukayi part din Anty safiya,
Dukan su suna zaune a parlourn 10:30 babu Wanda yayi bacci har Ummi suna kallan king of heart Ahmad ma yana nan sun kwalalawa tv Ido basa su seen daya ya wuce su idan ba talla aka tafi ba, Da sallama suka shigo amsawa sukayi Amma idansu nakan kallo,
Saida ta
zauna ta kalle su yarda kowa ya kwalalo Ido yana kallan yarda abin zai kasance inda roushini tayi accident Shabnap ta dauko ta Amma ba a Nuno fuskar ba shima Binaif tsayawa yayi daga tsaye Yana kallo kawai ta canza channel zuwa sofiya the first, su Duka juyowa sukayi Nafisa ce ta fara magana,cikin marairaice wa,
tace' Haba Anty
don Allah ki bayar mana ankusa gamawa saura talla biyu agama Dan Allah please kinji ?

Anty safiya ta fito tace' a,a kundawo Amma de yanzu nan don yanzu na tashi naje nayi waya,wai kar in zauna anan basa sun abinda ake fada sunayin missing word,
Ummusalma tace' yanzu nan nadawo Nayi sallama babu Wanda ya amsa shine na canza,
Binaif shima zuwa
yayi ya zauna kusa da ita,
yace' har wani yanzu kika zo ca zaki ce yanzu makazo nida mijina,
Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Sam Baya kunyat fadar wannan kalma ita kuwa nauyi take Mata abakin wai mijinta,
Anty safiya girgiza Kai kawai tayi,
tace' can gidan kikaje ne?

Yace' a,a haduwa mukayi da ita a traffic suna cikin adaidaita sahu ita da kawarta suna Rabin IV shine fa Mata waya suka dawo mota ta nake kaisu shine na kaita gidan su kawar tasu da suka Gama kuma sai yanzu tace nazo na maida ta gida,
Anty safiya ta yarda 100% da zance shi,ita kuwa Ummusalma sake Baki tayi tana kallan ikon Allah wannan zubit ma'aruf din ai,mintsinta yayi tare da Mata signal din tadena kallan Shi,
Nafisa tace' dan Allah ki mayar mana muga Wacece, kinji?

Shine ya dauki remote din ya makiwa
Nafisa yace' gashi yi kallan ki, tazo ta takura maku haka akeyi?

Ummi da ta kwalala Ido tana kallan cartoon aikuwa tasa kukan baza'a canza ba,
Yace' lala aikuwa Nafisa sai dai kiyi hakuri baza'a canza ba, mayar da Aljanunan,
Nafisa tsabar takaici harda su kwalla,tashi ma tayi ta bar parlourn ta Shiga daki,
Anty safiya tace'kin gamu da aiki kuwa na tsani wannan kallan da Baya karewa, Abu a yi tayi de bazai kare ba?
Chapter 51 · 0% Book details