← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 108

Sashe 80

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yasan Shi fah, idan ya ganshi zai gano komai,
Tace' Ga mafita, asamu wani dake aiki a companyn dake Paris kaga idan Felix zai zo sai su zo tare kawai, inaga hakan shine mafita kawai,
Mas'ud yace' kuma asibitin sa fah,
Idan yaga beda kadara sai wannan gidan nasa shima zai sayar dashi ne ga wani,shima sai mu siya,
To wai da kike cewa ya saya ya saya,da wanne kudin hakan zata faru,
Murmushi tayi Mai kyau, tace' da kudin sa,
Binaif yace' wazaki sace?

Ba sai ansace kowa ba, sato wa zamuyi,
A'ina?

Suka fada a tare,
Tace' a gidan sa, Tsoho mana,
Yau zamuje fah Amma ko?

Ehh, duk yarda akayi,
Mas'ud yace' ga shawara kuma kawai a siye PA din Shi, shima yaji yarda akeji idan anci amanar mutum,
Kallan Shi tayi tace' woow su Chatty kanka ya fara ja fa,
Hannu ya kawo zai bugeta ta goce, kwafa yayi irin zamu hadu,
Binaif yace' sai ku karasa komai,
Daga nan aka cigaba da magana ba su suka tashi ba sai Azahar kitchen ta Shiga ta daura abinci sannan taje tayi sallama.

Ta idar zata fito taga Ummu na Mata waya dauka tayi,
tace' ummu ya akayi?

Daga can ummu,
tace'
Yaya me zan fada Mata kuma?

Ummusalma tace' abinda ya dace Shi zaki fada Mata,
Me Kenan?

Ya ilahi, ummu this time around you have do it by yourself,
Yaya bansan fah mezance ba,ni ba irin wannan abun na iya ba, kuma ni Banda kawa sai besties,
To ki tsaya da kyau Kiji, daga nan ya shiga fada Mata abinda ya dace,
Sannan sukayi sallama, Ummu tace' yawwa Bari naje na Mata dadin bakina, hahaha ho ni Ummusalma 'ya ga Faisal jikar Adamu, hehehe,
Yaseer dake zaune a kusa da ita yaja tsaki yace' mutum sai hauka,
Pillow ta dauka ta wurga masa,
tace' Wallahi Ka kiyaye ni, am I your mate?

Ehh?

Ina wasa dakai?

Hada hannunsa yayi yace' Ana aasfi ya Ummusalma,
Daure fuska tayi tace' dade ya fi, Ku tashi mu tafi,
Yusuf yace' yaushe su Anty zasu tafi ?

Tace' gobe zasu wuce,
Yace' gidan Antyn Ring road zaki koma?

Nima bansani ba,Amma de Zan tambayi Anty idan ta barni sai nadawo gidanku,tunda kace an sallamu Abba kaga Mama Kenan tana na sai Muke kwana da Yaya Sameera, Amma fah sai kun tayani tambayar ta,
Yaseer yace' zata ma Bari Insha Allah,
Tace' to ku tashi de mu tafi,
Tashi sukayi ta suka fita, gidana su yusuf suka tafi, tana zuwa taje ta Kara yiwa Abba sannu da jiki sannan ta wuce dakin Sameera, a kwance ta Ganta tayi rufda ciki idanta a rufe,
Ajiyar zuciya, ta sauke ta karasa Shiga dakin Bayan ta rufe, a bakin gado ta zauna,
tace' Ya Sameera Lafiya ?

Juyowa tayi ta gyara kwanciyar ta tace' ummu bansan ya zanyi ba?

Nakasa samuwa kaina mafita,
Ummu tace' mafita Daya ce, ki canza SIM, ki watsar da duk wasu kawayen ki, ki fara sabuwar rayuwa kamar kowa,
Tashi zaune tayi tare da yin wani murmushi takaici,
tace' kina ganin Zan iya rayuwa kamar kowa?

Bacin yanzu ma ya dena Kirana?

Daman nike kiransa wani sa'ilin, to yanzu Nima nadena ganin ni Daya nake kidana, soyayyar sa kullum karuwa take yi a cikin zuciya ta, Ummu zuciya ta nauyi take min,
Ummu tace' kiyi hakuri Insha Allah komai zaiyi sauki kuma komai zai tafi daidai, trust me,
Tace' I should trust you?

Daga Mata Kai tayi alamar tabbatar wa, tace' Amma farko dole sai kin danni San da kike masa, kin fara sabuwar rayuwa hakan shine hanya mafi sauki da zamu cimma,
Zan gwada hakan,
Fatana kiyi yarda zuciyar ki ta fada maki,ba yarda kawaye suka fada maki ba,
Shiru tayi tana sauraren ta, tana kuma kallanta, ita kuma ummu tayi ta fada Mata kurarenta data yi a baya.

Washegari Binaif Yana zaune a office aka kawo masa
sammaci ana neman sa a koto, dayake yasani kuma shima ya shirya
sai kawai ya Kira lawyers dinsa guda biyu, Barrister Ibrahim da kuma Barrister Aliyu ya fada masu, sannan ya fito ya shiga motar sa ya wuce,
A kusan tare suka isa kotun sai Basu Shiga ba,Shi yashiga shima akayi komai da komai da ya kama ta
sannan aka sa nan da Wednesday za'ayi Zama, zaman iya su ya su, daga su sai alkali da lauyoyin su sai su kuma su kadai za'ayi hakan,bayan sun fito,
Binaif ya dubi Abba yace' yanzu Alhaji haka ne daman abun?

Me kake nufi Kenan ?

Murmushi yayi sosai mai kama dana dariya, sannan ya dafa Binaif, yace' yaro Kenan haka abin yake,
sai mun hado ranar laraba,
Sannan yayi gaba zai tafi, dasauri Binaif ya sha gabansa ya Dan bubbuga kafadar Shi tare da yin wani murmushin da kana gani kasan na renin hankali ne,
yace' to what's done, chest.

Yayi gaba ya barshi ya wurin ya daskare, ya maimaita To what's done,chest.

Kenna Yana nufin
what's done is done, you've made your bed, now lie in it.

Mekenan?

Jiyayi zuciyar Shi tana bugawa da sauri, lawyern sa ne ya masa magana sannan suka tafi,
Binaif kuwa Yana zuwa ya Sanar da lawyers Dina da yarda akayi,
Barrister Ibrahim yace' Binaif inaga Zan Mika komai hannun Wani barrister Faisal, Dan lokacin nan Bana nan natafi umara, kuma bansan wannan casa din yasha ruwa dukda de muna da muhimman shaidu kuma mune zamuyi nasara Insha Allah,
yau din nan Zan Kai masa komai,
Binaif yace' to shikenan Allah ya dawo da Kai lafiya, duk yarda kayi daidai ne,
Barrister Aliyu yace' Ashe shiyasa tun farko be bamu ba, Amma bakomai Allah ya Shiga tsananin mugu Dana gari, sun jima suna tattaunawa daga nan sukayi sallama har zai koma office sai kuma ya koma gida,
Yana zuwa yaga su mas'ud suna nan basu tafi ba.....

Page 47 yayi missing kuyi hakuri sai a hankali daman.

Ina godiya sosai da yarda kuke nuna jin dadin ku Nagode kwarai
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
Suna parlour suna game ita wucewa yayi ya Shiga dakin ta ganin bata nan ya kwankwasa toilet namma shiru ya bude yaga bata nan, ya fito kallansu yayi,
yace'' ina take?

Mas'ud yayi saurin cewa'' ita
wa?

" Mtsww ita mana"
Mus'ab yace'' tana can parlour"
Wucewa yayi tare da Galla masu harara, tana kwance tana latsa waya Akan kujera, kafar ta ya sauke ya zauna ya daura kafar aka cinyarsa, tashi zaune tayi,
tace'' yau ka dawo wuri'
Balla mata harara yayi yace'' ba sannu da zuwa fah''
Murmu
shi tayi tace'' Haba Mai gidana yi hakuri tou''
Dan yatsar kafarta yaja,tayi Kara, tace'' da zafi Mai gida"
Zai Kara ja,tayi sauri ta janye kafar ta, tana dariya,
Kumbura fuska yayi yace'' yau...

" Laifi nawa nayi?

Murmushi yayi sosai yace'' Ashe kin San laifin ki"
Tace'' amma Yana ganka kamar kana cikin farin ciki"
Gyarawa yayi ya zame ya kwanta ya daura kansa a cinyarta Yana kallanta, ita Shi take kallo, hannu tasa tafara shafa masa Sumar sa,Yana kallanta, tare da kamo hannun ta guda Daya ya rike, Yana wasa da hannun ya fada Mata yarda akayi, sai da ya gama,
Tace'' amma fah Faisal Adam sunan Baban Ummu ne"
Zaiyi magana wayar sa tayi Kara ganin barrister Ibrahim yasa Shi tashi zaune sannan ya daga,
Barrister yace'' kaga ma yanzu nan na Kira shi dayan barristern yake cemun zaiyi tafiya, kawai inaga Zan zauna,
Binaif yace'' kana ganin ba matsala?

Barrister yace'' babu Insha Allah shikenan sai anjima"
Komawa yayi ya kwanta yace'' yace ma barristern zaiyi tafiya"
" Zuwa dubo uncle a asibiti"
Yace'' sai yaushe mu zamuje?

"Sai ranar da kasa rana"
" Shikenan ba rana kenan"
" Um,um''
" Ina so zanje Spain daga can sai mu wuce mu dubo Shi"
" Kana so zaka je Spain, daga can sai mu wuce mu dubo Shi, damu Kenan za'aje kodani ni kadai"
Hancin yaja, yace''
kekam ko?

Sai kace Wanda kika yi psychology"
Murmushi kawai tayi batayi magana ba, ganin Yana neman rufe Ido alamar Yana Jin dadin yarda take shafa masa Kai, ga kuma hannun ta da ya rike shima,
tace'' ita wannan Sumar ba'a askewa ne?

Buda idan yayi yace'' so nake na tara irin taki, Mai yawa, tama fita tsayi"
Ware ido tayi irin really, sai kuma abin ya bata dariya tace'' ina bazai yi ba ma"
" To kisa wasa ki gani"
"Haka kace"
Tace'' ina San fita makota mu gaisa da su"
Juyawa yayi daga kwanciyar yace'' to na hanane?

Zaki iya zuwa ko yaushe ma idan Bana gida"
Tace'' Amma gaskiya ya kamata a cire wannu sumar, idan ba haka ba Zan Kai karar Ka wajen Umma"
Juyowa tare yin 'yar Dariya yace'' so kike kawai ki tada min rigima de, Umma bala'i ce"
"Umman kake cewa bala'i?

"Kina wasa da Umma, wannan tsohuwar idan ta kara girma da matsala''
Dariya tayi tace'' to nidai badani ba,Kai da ita kuma Zan fada Mata"
"Kiyi ta fada indai nine, daman tace na tsaneta, sanda taje spain"
"Taje spain?

"Kai tab sanda ciwon kafar ta yayi tsanani wani zuwa da Mijin Anty Ummi yayi gaida ita kawai suka taho tare sai ganinta mukayi, in fada maki, daga nan Ranar da tazo ranar ta fara yi mana jaraba,Anty ummi tace na zubo mata abinci, shikenan ta fara masifa wai Dan ta rena ta yaro ne zai zubo mata abinci eh,eh wannan ai reni ne, eh, bata da kunya, ehh rashin kunyar da takeyi ashe be barta ba, eh"
Dariya tayi Sosai tace" to meye na cewa eh din"
Yace'' Rasa abin fada tayi kuma tana San yin fadan, harda cewa nima na koma dangin nasara, ai Umma Idan tana fada kawai Kar ki kulata, Shikuma Mas'ud sunfi shiri da ita shine me fassara abinda nake cewa da Spainish, sabida wani abun Yana kari"
Tace'' indai chatty ne zai aikata abinda yafi haka ma"
" Meye naji ana cewa chatty me yayi?

Wato gulma ta kuke me kuke cewa?

Karasa shigowa yayi ya zauna, a kujeran kusa da ita yace'' kina jin ina maki magana ko?

Tace'' labe Ka koma Kenan?
Chapter 80 · 0% Book details