← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 108

Sashe 26

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama bata tsaya Jin ba'asi ba ta fita waje wurin mai gadi,
yace' ai Hajiya Bansan sun fita ba sai karar bude gate danaji ko da na fito har sun tafi sun bar gate a bude nama zaci wani ne ba lafiya shiyasa,
Aikuwa ta fara surfa masa ruwan bala'i wani abinmma batasan tana fada ba,dakyar su ummu sukayi controlling dinta suka maida ta ciki,waya ta dauka ta kira Abba ta fada masa, bai
wani dade ba ya karaso, sosai shima hankalin sa ya tashi kafin kace me gari ya karade ana neman yaran 'ya'yan M & M da U & U,
sai
dai babu su babu labarinsu, babu kuma wani evidence da suka bari ko kadan ba, kuma ma dadin dadawa har motar aka dauke, a iya bincike Yan sanda sunce sai dai idan barin garin sukayi tunda gashi ko me irin kalar motar su babu, dajin haka
kuwa yan jarida suka fara tambayoyi akan me zai saka su gudu?

Shin me aka musu zasu gudu su bar garin, batare da ansani ba?

Abba dukda yasan an sanshi a gari Amma baizaci haka kowa yasanshi ba infact baimasa cewan ansan yana da yaya ba sai da wannan abu ya faru, Idan hankalinsa yayi dubu to ya tashi yarasa inda zai sa ransa yaji sanyi.

Yana daki aana kwance yaji wayarsa tayi kara alamar shigowar sako, kamar bazai daga ba sai kuma yadago ko labarin 'ya'yan sa ne sai dai abinda ke rubuce a jikin message din ya fi ma batan 'ya'yan nasa tada masa da hankali, zufa ce take karyo masa ta ko ina babbar rigar dake jikinsa ta jike sharkaf da gumi, Ya karanta sakon yafi a kirga, bawani Abu bane da sakon Amma Shi a ganin sa wani abu ne, Mamace ta shigo ta ganshi da kuma waya a hannunsa batayi magana ba ta karbi wayar ta ga abinda ke jiki,
tace'.

Alhaji banga komai a cikin wayar nan ba dazaka kara tada hankalin Ka,
Kallanta yake irin bakisan me kike fada ba, kallanta yayi na kallan Baki da hankali kallo na ma'anoni daban daban bema San ya fassara kallanta ba,gani yake ma idan ya bata amsa Yana da lokacinta,
Ganin kallan ya ki karewa ne ya sata,
tace' haba Alhajina yanzu me aka rubuta a jikin wannan Abun?

Abinda ya dace shine mu nemo 'ya'yan mu daga baya sai mu nemo wannan,nasan wanda ya sace su to tabbas shine zai turo wannan sakon, mene na tashin hankali kuma?

Shi baimayi wannan tunanin ba tabbas ya yarda da ake cewa mace tana da hikima kalakala amma ake cewa sune masa karamar kwakwalwa,dukda haka dai bayarda yayi ba don shi wani tunanin ya dauko Wanda yasa ita bata kawo Shi a ranta ba,kuma bazai fada mata ba har sai ya tabbatar da gaskiyar lamarin.

Beyi mata magana ba ya cire babbar rigar ya tashi ya shiga bayi, wanka yayi ya fito ya shirya ya kuma fita,
don jin labarin ko an Samu wani abun kuma, sai dai har dare babu su babu labarin su.

Mama kuwa idan ta kwanta to batasani ba don ko shingida batayi ba abinda take cewa kawai shine yaranta ina suke? ( Sai kace Wanda akace Mata an San inda suke anki fada ).

Tana komawa gida tun daga bakin gate ta saki wata uwar Kara sai da yasa kowa ya fito tana karasowa kuwa parlourn ta zube tana kuka, tana cewa an sace su an sace su shikenan an yanka su,sun mutu, sai da Anty ta tsawatar mata tukunna tayi musu bayani, tana gamawa kuwa ta kuma zubewa tana kuka, daga karshe ma hotunan su ta rungume a kirjinta a haka tayi bacci, sallah kawai yake tada ita daga inda take tana parlourn a rakube kallo daya zaka Mata ta baka tausayi sosai. ( Allah sarki ummu).

Yau ta tashi cikin wani irin farim ciki dukda fuskarta tana nan kamar kullum ba fara'a amma ita a yarda take ji wani irin dadi da nishadi ne yake kwasarta, batasan dalili ba, musamman idan ta tuna Mr lizard ( Binaif), akan abinda ya faru jiya,sai ta samu kanta da murmushi ga kuma su yusseer wanda basu zo ba a jiyan, a haka ta gama aikinta taje taci abinci tayi wanka, koda ta fito gidan bakowa tsit yake, lokacin har sha biyu tayi kasancewar yau bata tashi da wuri ba, kitchen ta shiga ta daura abinci ta dauko silalliyar kaza ta daura ta don ta narke ta soya,tunda tazo ake cin dafaffiyar kaza yau kam ko suna so ko basa su sai sun ci soyayyiya tunda ita tana so, sai da tayi ta soya ta, ta bade ta da yaji, ta dauki na dauka ta rufe sauran a flask, Naman rago ta dauko ta wanke ta daura,tuwo ma zasu ci yau.

Sosai tayi tuwon semo da miyar kubewa bushshiya Tasha manja da nama, Saida ta gama ta kuma gyara kitchen din, bude Fridge tayi ta dauko lemo mai sanyi ta dauko namanta ta fito bakin kitchen din da kofar dakinta tasa takalmi ta baje tana cin nama tana korawa da lemo tsabar dadi har wani lumshe ido take irin yaushe rabo, zuwan shi kenan don yasanar da ita abinda ke faruwa ganin wani sinadarin farin ciki a tare da ita yasa Shi tsayawa Yana doubting ya fada mata ne ko mar ya fada, gashi yanzu sai cigiyar yaran ake, tunda yazo ta lura dashi amma tayi kamar ma bata ganshi ba, karaso wa yayi ya tsaya akanta,dago Kai tayi ta kalleshi, ta maida kanta ga naman da take ci,kujera ya dauko ya zauna yana kallanta, tashi tayi ta Shiga kitchen bata jima ba sai gata tafito dauke da kwano a hannunta tuwo ta zubo masa da naman da ta soya, beyi musu ba ya karba, ta zauna ta cigaba da ci, shima sauka yayi daga kujerar ya zauna a kasan tiles din wurin ya nade kafa yafara zirawa,sosai yaci Saida ta lura ya kusa koshi,
tace' inaji meke tafe da Kai?

Sosai yayi mamakinta, Kenan tasan da magana a bakinshi,
sai da yacinye tuwon tas ya kai kayan kitchen ya dawo ya zauna
yace' bansan ta ina xan fara ba ai, cewa zanyi an sace Kannan ki ko ya zance?

Kallanshi tayi tace to me Zan masu don an sace su sai me??

Ni zaka fadawa kome ko kuma nice ubansu kaje can ka fadawa babansu amma nani ba,
Dukda cewa ahankali take magana amma sai yaga kamar ranta ya baci daya fada mata din dan yayi wani iri bacin rai yake hangowa karara a tare da ita, tashin da tayi zata Shiga dakinta ya sashi saurin riko hannunta a sukwane ta juyo zatayi magana ya riga ta
Yace' meyasa?

Meyasa zakiyi haka?

Why?

Fada maki nayi fah don kisan halin da ake ciki amma shine zaki min haka?

Bata Kula Shi ba tace' menace ma game da rike mun hannu?

Sakinta yayi ta wuce ta tafi ta barshi a tsaye ,ya rasa yazaiyi da ita yana so su Saba kodan tarin tambayoyin dake kansa ya sauke mata su.

Tana Shiga ta kwanta a katifa tana tunanin.

Tana Jin
ya tafi
tazo ta kwashe plate, wanke kayan da suka bata tayi,ta koma bata Kara fitowa ba gudun kar su Kara haduwa dashi, tana Jin yan gidan suna mitar tuwon da tayi Amma bata fito bama bare a zagi iyayenda bata san su ba.

Washegari da yamma ta shirya ta fito kasancewar Yan gidan basa nan ta lura jiya da yau basu zauna a gida ba, kuma Basu dawo da wuriba,hakan yasa itama kulle dakinta ta fita,tana fitowa taga mai adaidaitar ta fada masa inda zai kaita tayi, tana masa kwantance har kofar gate din, cewa tayi ya jirata tana fitowa ta tura gate din,a bude kuwa yake, sai dai ganin mota da tayi a wurin yasata tunanin tabbas zuwa akayi shiyasa ma taji gate din a bude, zuwa tayi wani lungu ta makale tayiwa mai adaidaita message cewar ya jirata a bakin layin, sannan ta dauko wata Nokia key pad tayi message,ta mayarda ita cikin jakar ta,lallabawa tayi ta Shiga gidan,kallan gidan take tamkar batayi rayuwa acikin sa ba,wani irin tsanar gidan take ji Yana taso mata,dukda ba mutane Amma yana samun gyara akai akai, Jin motsin tafiya yasata saurin buya a dining wurin wani dan lungu ta makale, leko da kanta tayi taganshi yana saukowa, yakara kiba da fari,kana ganinsa zaka san Yana cikin daula da kwanciyar hankali sai dai kuma daga jiya zuwa yau ya zabge ya rame, kallansa takeyi tana tuna abubuwa da dama,Jin ya kusa saukowa yasata saurin Kara labewa har ya sauko ya fita,Yana fita kuwa ta tattare hijabinta da wani iri gudu ta haye sama dakinshi ta Shiga don taga dalilin zuwanshi gidan da suka tashi suka Bari batare da sun zuba yan haya ko sun saida gidan ba, dakin sa ta Shiga sai dai bakomai a dakin hakan yasa ta fito ta Shiga dayan,Yana nan yarda tasan Shi banbamcin kawai ansake
wardrobe ne, Shiga tayi ta bude taga wannan safe din zata bude Kenan taji Yana waya ashe be tafi ba, wani dokawa kirjinta yayi,cikin sauri ta shige bayan wardrobe din data ganin wani dan space, Allah ya taimake ta bata da kiba, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali,tare da numfashi, ji tayi Yana,
cewa' yanzu million ashirin fa zan Kai, akan yaran nan million ashirin fa,ba yarda za'ayi a kama Wanda yasace ne?

Bataji me ake cewa ba Amma tasan da Mama yake waya, jitayi yace' kinga ni ina
tsohun gidan mu duk abinda za'ayi saidai ayi don kira zanyi ayi hacking din wannan password din,Naga menene acikinta nagaji da zaman jira sai yaushe ne wannan lokacin da zaiyi million ashirin wasa ce ne akace maki?

Daga nan kuma bataji me yace ba alamar ya gama wayar, sai taji kuma Yana wata wayar daban Yana bude wardrobe din,da turanci yake, Yana fadar yarda safe din take da iya adadin letters din da take dauke dashi,sai taji kuma Yana cewa yanzu de sai Friday zaka iso Kenan?
Chapter 26 · 0% Book details