← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 108

Sashe 8

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahaka sukayi sati biyu suna suna ci
gaba da zuwa lectures abinsu idan tayi Mata clashing sahr na koyamata yarda ya kamata,kuma balaifi tana ganewa sosai don a satin da suka fara lectures a satin ta afara karatu,kuma karatu sosai takeyi,tana googling abubuwan da ba'a musuba ma,sosai take karatu bakadan ba hada course is not easy amma kuma hausawa sunce _sa Kai ya fi bauta ciwo._
Yau Friday Basu da psycho Amma ita tana da lectures,shiryawa tayi ta fita,da wuri tana so tayi karatun course din don bai taba zuwa ba amma tasamu abubuwan da zai koya masu kuma ta karanta sosai kamar an koya Mata,bakowa a class din samun wuri tayi ta zauna ta baje littafai tana karatunta hankali kwance abinta,tanayi har aka fara taruwa dahaka har kowa yazo,ita de karatunta kawai take dukda tana Jin hayaniya amma bata dena ba don bata hanata karatu,tana cikin karatu taji anyi shiru,ba'a surutu,a hankali ta dago taga meke faruwa,
agowa da zatayi taji zuciyar ta tayi wata irin buguwa,bata Jin komai sai sautin bugawa da kirjinta keyi,mezata gani BABA??(mutumin da ta zana)Amma kuma wannan yafi Baba haske kuma bashi da tsufan Shi,sh
ikuma Baba a yarda taganshi bashi da wadata,duk bayanin da yake bata ji koda kalma
aya ce da yake fa
a ba bata ji komai ba,sai tsinkayo muryarsa da taji Yana fa
ar sunansa ABDALLAH ABDALLAH,daga nan bata karajin komai ba sai sautin bugawa da kirjinta keyi,tunda ya shigo take faman kallansa,bata kuma
auke kanta ba gashi ita ba sauraran komai take ba bayan sunansa saidai ta lura yayi shiru Yana sauraren wani abu sakamakon gya
a kan da yake faman yi, bata Ankara a taji ta gabanta na fadin sunanta da garin da tazo dakuma meyasa take San karantar business, har an gama da kowanne row saura row dinsu,a halinda take ji batajin zata iya magana,bata gama tunaninta ba taji ta gabanta nacewa ta tashi, ita ka
ai tasan yatakeji a jikinta,gani take kamar kowa yasan halinda take ciki,a zahiri kuwa ba abinda ake gani,tattare da ita,
Ganin anyi shiru ba'a cigaba da maganaba yasa Shi
agowa karaf suka ha
a ido daman ita shitake kallo,yana
agowa suka ha
a ido,kallanta kawai yake,wani irin sanyi yaji yana ratsashi na musamman ,a take zuciyarsa tadena bugawa na wani lokaci,a hankali yasaki wata
oyayyiyar ajiyar zuciya,sannan
yace, "am listening, your name?

Kallanshi kawai take,batare da tace komai ba,shima ita yake kallo,ganin bata da niyyar magana yasa ya tambayi
aya daga cikin class members
in, Wanda aka tambaya kuwa ca.

Yaace, "ai tunda ta zo babu Wanda ta tabayiwa magana
haka take, su suna tunanin ma kurma ce tana ji Amma bazata iya amsawa ba.

Kallan sa ya mayar wajen ta.
yace, "haka ne,?

Batasan ma me akace ba kawai daga kai tayi alamar ehh, yace ta zauna,Zama tayi akaci gaba da fada,har aka Gama daganan ya fara abinda zaiyi, Ummusalma da kyar tayi nasarar kwabar kanta ta fuskanci abinda ake masu dukda cewa tasan abinda ake Amma kuma rabi gwara ta Kara ganewa ai,sosai kuwa ta gane,suna gamawa ta dawo hostel kafin tadawo sahr ta dafa abinci ta fice,itama abincin taci Amma duk wani iri take ji,bacci tayi har lokacin sallah ya gota,ta tashi wanka tayi ta tayi sallah ta shirya kamar kullum cikin doguwar Riga tayi rolling ta fito,fita tayi tana zagaye gari,wani
an shago ta gani na kayan pente pente taga kuma yarda mai shagon yake Zane,kayan zanen ta siya ta bada address din campus har dakin su,haka ta gama Dan zagayenta ta dawo,tana zuwa kuwa taga kayan da tasiyo a kofar daki bude dakin tayi ta Shigar da su ta ajje a balcony,ta dawo d
kin ta ,zauna sahr haryanzu batadawo ba,hutawa tayi tafa masu abinci,tayi sallah,Rasa abinda zatayi tayi Dan haka ta je balcony ta zauna tana kallan kasa yarda mutane ke hada hada abinsu, dauko kayan zanen tayi ta hada komai yarda yaka Mata sannan ta fara Zane batare da tasan metake zanawa ba,abinda tasani kawai tana tunanin AA ne(Abdallah Abdallah)koda ta Gama zanen Shi tagani ta zana sanye da bakaken suite yarda yake a tsaye haka ta zana Shi,zana wani ta kuma yi sannan ta zana Baba,a kusa dashi,kalla take tana so tagane menene bambamcin su saidai bataga wani bambanci ba,daukowa tayi ta dawo daki,cikin bedside drawer ta zuba su ciki.

Sai bayan magriba sannan sahr ta dawo, Kallanta tayi
tace, "ina kikaje?

Sai da ta zauna
tace, "naje gidan uncle ne,shiyasa kuma wannan matar tashi tasani aiki wai sunyi Baki".
arashe tana ya tsine fuska, kallanta kawai Ummusalma keyi batayi magana ba, abinci ta kawo masu suna ci sahr na Mata Santi,duk sanda sahr tayi santin abincinta babu Wanda take tunawa kuma sai yusseer Allah sarki ko ya suke?

Haka rayuwa tayi ta tafiya cikin kwanciyar hankali ta jima da siyan simcard Amma bata ma sa numbern su mama ba bare ta kirasu,in fact bata da numbern ba kowa sai ta sahr ita kadai gareta.

Sahr kuwa a bangarenta tana mamakin umsalma tunda tazo bata nemi gida ba,abin na bata mamaki sosai,sai kuma abinda ta lura dashi duk dare tana karanta wata paper kafin tayi bacci haka idan tayi bacci ta tashi sai ta karanta ta,ko karatu zatayi tana karanta papern,ita kanta ta karanta papern ya kai sau ba adadi ita bataga amfanin karantawa ba,tunda indai haddacewa ne to ta tabbata ta haddace ta.

Kuma tasan dole wata Rana zata bata labarin ta kamar yarda itama ta bata labarin ta ahaka.
_~Nigeria~_
Tunda suka dawo daga raka Ummusalma su yusseer suke kuka,sunki suci abinci,sunki cin komai, suna ma dakin ta Akan gadanta sun rungume juna sun tukuikuye wuri daya suna razgar kuka,mama tayi fadan tayi fadan ta gaji,Basu taba rabuwa da ita koda na kwana daya bane, da can ma dakin ta suke kwana daga baya ne da tayi rashin lafiya suka dena kwana,har dare suna dakin ko sallah basuyi ba bare su tashi suci abinci ,haka har bacci ya dauke su,idan sun farka suyi kukan su suyi bacci,ga yunwa na cinsu Amma inaaa baza su iya ci ba.

Bayan anyi Isha Mama ta fadawa Abba abinda ke faruwa,idan ransa yayi dubu to yabaci sosai ya fusata ya dau charger ya fita da ita sai dakin Ummusalma Yana zuwa lokacin bacci ya dauke su gashi daman sun galabaita,baiyi wata wata ba ya zula musu,wata rin zabura sukayi suka Kara rungeme juna maimakon su gudu inaaa sai suka Kara tukuikuyewa wuri guda takaici ya Kara kama Abba baisan sanda yayi ya tafakar suba suna ihu suna kuka,Mama na gefe don itakam daman abin nasu ya isheta,ahaka yayi ya gaji ya fita,mama ma ta bishi, dakyar Yusuf daman shine mai Dan wayo ya tashi ya tashi ya zauna ya janyo yaseer Yana rarrashinsa lemo ya tashi ya dauko masu da cake da Chocolate,yanaci yana bashi ahaka suka ci dayawa idan suncinye sai ya Kara masu har suka koshi,tashi yayi ya daura kan yaseer a cinyarsa
yace, "Yaya bazata taba dawowa ba".

Kallansa yaseer yayi
yace, "a,ah zata dawo dazu ta fada min cewar kar na fadawa kowa zata dawo ai".

"A,ah bazata dawo ba ta fada maka zata dawo ne Amma ba dawowa zatayi ba".

Cike da tausayi yake maganar kana ji kasan Yana cikin kunci ne,
"Taya kasan bazata dawo ba ita ta fada maka ne???

"Ba ita bace mama naji tanan fada".

"Yaushe??

Ya tambaya cike da zakuwa
"Dazu ta shigo kana bacci lokacin ta shigo tace, indai Ummusalma ce bazata taba dawowa garemu ba har abada kuma sai mun manta da ita a kwakwalwar mu".

Ya karashe da kwalla na zuba daga idonsa, yaseer ma kukan yake,
"shikenan yanzu bazata dawo ba??

Kana ganin zamu manta da ita ne?

Zamu manta da ita idan ta mana wani abun.

"Mezata mana to?

Kallanshi yayi yace, "ina abokin mu da ya manta da mamanshi?

Ka tuna Shi?
aga masa Kai yayi yaci gaba yace, "to da ya fa
a min abinda yasa ya manta da shima lokacin da ta tafi ta barshi kuka yayi tayi shine antyn Shi(matar babanshi) taba Shi wani abu yasha tace inji mamanshi tace a bashi yace tunda yasha shikenan be Kara tunawa da ita ba sai da ya gan maman tasa.

To itama mama Shi zata bamu bazamu Kara tunawa da yaya ba".

Kuka yaseer yasa don ya tuna wahalar da abokin su yasha kafin yaga mamanshi kulluma idan suka biya islamiyya zasuga Yana aiki idan suka tambayeshi ina mamanshi sai yace' Shi baida mama.kuka sosai suka Kara sakawa daga karshe, Yusuf
yace, "idan mama ta bamu Abu kar mu karba kuma kar musha,idan ta bamu muce munsha,kuma mudena Zan can Yaya a gabansu ko???
aga masa Kai yaseer yayi ya rungume Shi,shima rungume Shi yayi
yace, "kanina yau bamuyi sallah ba,
Dago yayi ya kalle Shi kawai sai yayi dariya
yace,"Yayanah ehh haka nefah".

Dariya suka tuntsire da ita, yaseer
yace, "taabbb wai Kaine yaya taaab ko a mafarki bazance ma ba,
Yusuf shima dariyan yake yace,"Ka tuna sanda Yaya tace kana cemun yaya ??

"Ai naga baka girmen ba da zance maka wani yaya,tsayinmu
aya dai".

"Amma ai na girmeka a shekaru ko ?

"Laaaaaa shekara dayan?

Dayace fa kuma Zan biya Ka kadena cewa Ka girmen".
daga haka suka tashi sukayi sallah tun Azahar har la'asar kayansu suka je suka cire sannan suka dawo suka kwanta sunayi auna hiran yayar su,
Washegari kamar ba abinda ya damesu suka tashi sukayi wanka,wai su yanzu andena masu wanka,suka sa Kaya iri daya abinsu sunyi kyau kallo suka kunna yaseer yaje ya karbo masu abinci sukaci suka koshi,suka fita wasa,koda mama tace masu abinci fa, sukace sun koshi,
Washegari Monday ma zuwa sukayi suka ci abincin su sukace sun wuce,
Haka rayuwar su tacigaba da tafiya ko mama ta tambayesu yaya cewa suke babu wata yaya
agidan idan ba sameera ba a tunaninta abinta yaci saidai kuma ba haka bane Sam don Basu manta da yayar suba.......

By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023
A bangaren Abba kuwa,yaji takaicin bada motar da tayi,Amma ba yarda zaiyi tunda ta Riga da ta bayar.
Chapter 8 · 0% Book details