← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 108

Sashe 23

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi dariya tace' ni mantawa ma nake dashi wallahi,bafa number ta na bayar ba, numbern Inna na bayar kasan kuma Inna ba turanci take jiba shikuma be iya Hausa ba,kaga shikenan anyi run da come,
Amma Baki da mutunci wallahi,
Yusuf yace' wallahi kar ki bawa kowss numbern ki, taam nidai ba ruwana atoh,
Babu Wanda ya Kara magana har suka je suka je school din, parking sukayi inda suka saba,kamar kulluma yarda suke tafiya yauma hakan ce ummu a tsakiyar su,sukuma a gefen ta, Dukan idan Ka kallesu zaka ce bahaka suke ba,don a school basa magana ma da wasu,Basu da kawaye sai dai course mate, suna tafiya ummu ta matsa kusa da Yaseer,
tace' kaga in-law dinmu,tana jiran mu,
Besamu yayi magana ba amma yayi Mata alamar ya gani,saboda sun karaso,Sarai Yusuf yajita Amma be ko tanka musu ba,idan da sabo ya Saba da wannan yarinyar da ta makale masa dukda bata ce tana sanshi ba Amma alamar hakanne da ita, shikuma sai wani basarwa yake,sabida kwata kwata baya san dizgi ita kuma akwaita da wannan,
Ummu ce tace' Fati, yau ma kin rigamu zuwa Kenan, nikuwa Naga ranar da zamu rigaki zuwa,
Wacca aka Kira da fati tace' aikuwa bazaku taba rigani zuwa ba,kufa komai kukeyi nikuwa yimin ake,tafada suna Shiga lecture theatre din.

Sai da suka Shiga suka tuna cewan basuyi assignment ba, shikuwa yusuf Ko a jikinsa, Dan yayi nasa,kuma Yana sane yaki tuna masu,to Allah yasa su lecturer baizo
b.

Sai 2 suka gama, sun fito don tafiya fati,
tace' idan Baku manta na tuna maku kunce zaku je gidanmu yau,kuma ummu ke kika fada,Dan haka tare zamu tafi,
Yusuf wani irin takaici da haushi suka darsu a zuciyar Shi, Sam bayasan wannan yarinyar amma ummu da Yaseer baza sudena kulata ba,mtswww yaja tsaki a zuciyar shi, badan bayasan karya alkawari ba da babu inda zashi shikam, suna tafiya har suka iso wurin motar tundaga nesa ya budeta suna zuwa kuwa yaga ta shiga gaba su kuma sun Shiga baya, wani murmushin yayi shima ya shiga, yana Shiga kuwa ya yatada motar, sai dai be tafi ba sai ma kifa kansa da yayi,ganin shiru shiru Basu tafi ba yasa Fati cewa Yaya lafiya kuwa?( Yarda suke cemasa a makaranta)
Girgiza Mata Kai yayi yace' kaina ke ciwo kice yaseer yazo ya ja,
Yaseer yaji abinda yace kuma yasan bawani ciwon Kai, kafin ma tayi magana ya fito ya bude kofar ta
yace' ki koma baya Zan ji dashi,
Bata yi musu ba ta koma baya kusa da ummu,itama umma da tasan kwannan zance batayi magana ba, suna Shiga kuwa yaja motar ya suka tafi,zoo road tace,bayan sunje kuwa ita ke nuna masa hanya har suka iso horn yayi aka bude masu gidan, parking yayi suka fito, parlour ta Shigar dasu,ta wuce kitchen ganin Ummusalma a kitchen din yasata cewa ke kurma yau ke kike abincin?

Mai abincin?

Bata nan ne?

Daga Mata Kai Ummusalma tayi alamar eh,
Tace' to ki kaiwa Baki ruwa da abinci suna Parlour, ta juya ta fice, da wata irin uwar harara ta bi bayanta ta tace'" zaki ci uwarki ne,
Ta kofar baya ya shigo ganin ya kwankwasa dakinta bata nan yasashi zuwa kitchen ko zai ganta haka kawai yaji Yana san ganinta shiyasa ya fito takanas don ya ganta,
Kalmar karshen ne ya bashi dariya sai kawai yayai murmushi ya gyara tsayuwar Yana kallanta, yarda take zuba abubuwa a plate sai kace Wanda aka ce Mata mutane goma ne suka zo, ta fita don ta Kai,sai dai Jin muryan take kamar tasan masu muryan, sai dai murya daya zata iya cewa tasani dayan tajinta take kamar tasan irin ita, a haka de ta karasa parlourn sai dai bata je ga Shiga ciki ba ta hango ummu a sukwane ta juyo ta koma da kitchen da harda hadawa da gudu,tana Shiga ta sauke wata ajiyar zuciya Allah yasa Basu ganta ba,ajje kayan tayi, Yana nan be fita,
yace' kinga Wanda kika sani ne?

Kallanshi tayi da mamaki,da'alama ya jima Yana kallanta bata Kula dashi ba,
Murmushi yayi yace' karki damu kawo nakai
maki,amma sai kin fada min suwaye su a wurin ki.

Yafada Yana shigowa cikin kitchen din, numfashi taja ahankali cikin muryan da shikadai ne zaiji
tace' kannai na,kuma Bana san su ganni,don na tabbata yanzu nemana sukeyi.

Murmushi yayi yace' to shikenan anything for you,
Yafada Yana daukan tray din.

Yana fita kuwa ta tafi dakinta ta Shiga wanka,Da murmushi dauke a fuskarsa ya fito
ajje masu tray din,
yace' sannunku,
Yusuf ne ya tashi ya Mika masa hannu suka gaisa ,sai yaseer shima ya Mika amsa,ummu ta gaidashi,ya amsa ganin yarda Yusuf yake cika yake batsewa yasashi kallansa dakyau,
yace' abokina lafiya kuwa?

Zo muje waje kasha fresh air,
Yafada Yana yakamo hannunshi,shima Yusuf din beyi musu ba ya bishi ta kitchen ya bi dasu, a garden suka zauna , sanan yaje ya zubo masu abinci da lemo, don yau ji yayi Yana san cin girkinta dukda be taba ciba amma Yana da yakinin zaiyi dadi, ya ajje masu a tsakiya yace' bismilla,
Yusuf kallan abincin yake dambun couscous, an barbadeshi da dambun nama, baisan sanda wani murmushi yayi escaping lips dinshi ba, Yana mai kallan abincin, Banaif kallansa yayi,
yace' lafiya kuwa?

Numfashi ya sauke Yana mai Kara murmusawa yace' lafiya qalau kawai dai na tuna wani Abu ne,
Can u share with me?

Yafada Yana Kai loma bakinsa,
Murmushin ya kuma yi,
yace' Favourite food din Yaya tane, idan kana so kayi bribing dinta to Ka kawo mata dambun nama,ko na couscous,
Amma fa idan na dambun couscous ne to sai Ka barbada masa dambun nama,
Wata yar kwallace ta taru a idansa ya gogeta sannan yayi murmushi,
Yana cigaba da kallan abincin, shima ajje spoon din hannunsa yayi dukda Loma daya yayi kuma abincin yamasa dadi sosai,
yace' ko zan iya sanin me Yaya
tafi so da wani abu daga cikin labarin ta?

Ya tambaya da murmushin da yake karawa mutane nutsuwa,
Kara goge kwallan idon sa yayi sannan ya Kai loma daya bakinsa,wani murmushin ya kuma yi
yace'
lokacin I was 10 Amma idan yaya tayi girki to nasan girkinta saboda dadin Shi,nida yaseer mukanyi mamakin inda ta iya girki haka lokaci guda,
Yaya tana san wasa,zuwa park,ice cream, biscuit, drawing, games, basketball, da sauransu,Amma tana san surprise
tana so a mata itama kuma tanayi,
Shiru yayi ya budi Baki zaici gaba yaji wani kamshin turare ya daki hancinshi,lumshe Ido yayi ya bude yace har yau bansan sunan wannan turaren ba amma nasan irin shi Yaya take sawa,
Shiru yayi yakuma yin wata lomar zaiyi magana yaji yaseer nacewa" idan labarin Yaya ne bazai taba karewa ba,
Ya karaso shima ya zauna, yacigaba, ya kalli Binaif,
yace' meyasa kake San Jin wani abu daya danganci yayarmu?

Murmushi yayi yace' saboda tana San abinda nake so,tana san favourite food dina kuma ance yawancin masu San abinci iri daya, to halin suma zai zo daya haka ne?

Kallan juna sukayi suka yi wani murmushin da iya su kadai suka san shi, yaseer,
yace' bamu Sanka ba, amma koma meye kana San Jin wani abu daya daganci yayar mu hakan na nufin u mean alot to us,muna San duk wani mai San yayar mu,
Shiru yayi Jin muryan Shi zata fara rawa, Yusuf yacigaba,
yace' idan muka baka labarin Yaya daidai yake da kaima Yayane a wurin mu, amma bamu San ya zaka dauki maganar Tamu ba.

Shima daga nan shiru yayi,ganin sunyi shiru yasa Shi cewa" to yanzu ina Yayar take??

Wani irin murmushin takaici Yusuf yayi yace' muma bamu sani ba,karshen ganin mu da ita yau kimamin shekaru shida da wata daya da kusan Sati Kenan,babu ita babu labarin ta,
Lomar abincin da Kai bakinsa ce ta makale, yaseer ya bashi ruwa ya kora,
yace' bangane ba?

Zaka gane ai,
Yaseer yafada sannan ya cigaba da cewa'' tunda ta tafi makaranta London bamu Kara Jin labarin ta ba,sai ranar da zata
dawo Nigeria suka hadu da ummu wacce muka zo tare ita, ta bata sakon gaisuwa sannan tace ta amsa numbermu, har yau muna jiran kira daga gareta har yau babu labarin zata ma kiramu din, sai dai tunda ta amsa munsan zata Kira,
Zuwa yanzu kanshi ya kulle sosai ,yama rasa wanni tunani zaiyi, kallansu kawai yake baikara masu wata tambayar ba gudun kar ya kuma fadan abinda zai Kara sashi cikin wani yanayin bayan Wanda ta saka Shi aciki again ga kannanta sun Karasa shi aciki, kallansu yayi yaga suna cin Abincinsu hankali kwance sunayi suna kora da lemo, ummu yazo,
tace' kutashi mu tafi,na gaji wannan budurwa taka ta fiye surutu wallahi,duk surutuna ta fini, ta dameni ta shanye ai wannan ga shegen iyayi, ni bazan iya ba kutashi mu tafi bakuma zamu Kara zuwa gidan nan ba a toh kuna jina ai?

Ganin sun Mata banza yasata cewa da'ace na iya mota wallahi bawanda ya isa ya kawo min raini ban taka shiba,har wani ina cewa ku tashi mu tafi kunsamu gidan mutane wato kuna zira abinci sai kace gidan ku ko?

Yusuf yace'kin dame ni fah,idan zaki ci ki zauna kici nasan yunwa kike ji,
Kumbura Baki tayi ta samu wuri ta zauna spoon din da ya ajje ta dauka tana cika Baki, binaif kallanta yayi,
yace' daman fadan yunwa ce Hala ?

Ita sai anan ma ta lura dashi,wani irin kunya ne ya kamata
Girgiza Kai kawai tayi,ganin ya Basar ya jasu da hira yasa itama ta sake tana zira abinci, sosai suka ci suka koshi, sannan ya raka su wurin mota, ko sallama basu yiwa Fati ba Saida suka fito sannan ummu ta kirata ta fito sukayi sallama suka wuce, lokacin anyi kiran sallah la'asar don haka suna zuwa gida suka wuce sallah, da suka dawo kuwa wanka sukayi suka saka kayan shan iska,suka fice kasan layin su inda ake ball,
badan suyi ba sai dan suyi kallo...

Da yamma ta fito ta zauna tana tunanin yarda zata fara aikinta hankali kwance lokaci yayi da zata fara gudanar da aikinta, lokaci yayi da zata nunawa duniya itace mai kudi ba wani Wanda ake cewa shine ba, lokacin mai da martani yayi,batare da sun sani ba.
Chapter 23 · 0% Book details