Sashe 37
A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yace' Umma ba jimawa ba zamuyi ba,yanzu zamu dawo,
Umma tace' ina ruwana to,mude a zamanin mu idan aka Kai mace gidan mijinta ko leka kofa batayi sai tayi shekara cis a dakinta, Kai wata ma sai ta haihu,wata kuwa bata haihuwa sai ta shekara biyu,uku,hudu Kai har shida ma sannan wasu zasu fita shima sai an zubda wanka,kuma idan mace ta fita a ranar take dawowa gidan ta ba irin yanzu ba,
Yace' Haba Umma da kikace da da dayanzu ai ba daya bane komai ya canza,
Tace' Allah ya Baka hakuri fada maka nayi ai,ko kaima zaka yiwa matar haka, sai kun dawo.
Ummusalma tace' sai mun dawo,
Shikuwa ko magana beyi ba,
Ya Riga zuwa hakan yasa ya bude mata kofa shima ya zagaye ya bude ta Shi,Shiga tayi tana mamakin wannan labarin da Umma ta basu,anshe da sun shade wahala.
Bayan sun dau hanya ta fada inda zasu,suna tafiya shiru babu mai magana ita tana kalle kalle shikuma yana tuki, katse shirun yayi da cewa'
' Kinsan wani abu?
Sanin da ita yake ta girgiza Kai,
yace' anfa Bani shawara,kuma shawara ce mai kyaun gaske nake fada maki,
Ganin kamar Yana so yaja da magana,kuma da alama de bayansa shirun nan nata,
tace' Wacce shawara ?
Yace' ahh wacce Umma ta Bani mana,
Tace' dayaushe?
Yace' yanzu da zamu fito,kinga daga yau bake ba fita sai kin haihu,
Kallanshi tayi dakyau tace' sai na haihu kuma?
Yace' yes,of course,idan kin haihu a shekara daya to kina so ki fita idan ma kin haihu a shekara biyu Kinsan fita,Amma Baki haihuba a wannan shekararun bake ba fita,wasu ma har sun manta dake,
Kumewa tayi tace' wai maganar nan dakeyi daga zuciyar Ka take fitowa kokuma daga bakinka,nakasa fahimta,
Yace' zuciya tamana sannan Baki na yake fada ,kinsan ana cewa abinda babba ya hango ko ya hau ina ne bazai hango ba,
Banza tayi ta kyaleshi,har suka karaso unguwar
yace' kinde San ni ba aljani bane da Zan San ko ina ko?
Da hannu ta fara mai kwantance,samun wuri yayi,yayi parking
Kallanshi tayi dakyau
tace' lafiya?
Yace' Naga kin Zama kurma,ni kuma banzama ba,shiyasa gwara kawai mu zauna haka,
Tace' amma de kasan ai yamma tayi yanzu ko,kuma yanzu magariba zatayi daman bamu fito da wuri ba,
Yace' to Ashe kina magana haka,
Bata yi magana tama juya tana kallan wani wuri,motar ya tada,
yace' Madam ina muka nufa,
Nuna masa hanya ta fara yi har suka isa, fita tayi ta Shiga gidan da yake opposite dana Maman Sadiq, Sallama tayi aka amsa sai da suka gaisa,
tace' maman Sadiq ce ta aikonj Zan amsa key Zan dau sako,
Zasuyi sa'anni da matar gidan,
tace' eh ta fada min Amma meye sunanki?
Tace' Ummusalma,
Tace' ina zuwa,
Koda Shiga sai ta Kara Kiran maman Sadiq ta shaida Mata, sannan ta dauko key din ta bata,
Fitowa tayi janye da
trolley dinta da kuma wata jakar a hannun ta, fitowa yayi daga mota ya zo ya ansa jakar ita kuma ta maida key din,
Gidan dake kusa da na Maman Sadiq ta kalla da ta Shiga gidan Maman Sadiq taji haniyarsu da'alama ball suke a tsakar gida, mota ta Shiga ta zauna,
yace' kinsan masu gidanne?
Gida nane,tace
Kuma Baki Shiga ba,tace' su yaseer ne fa a ciki,
Kunna motar yayi ya fara tafiya,
A cikin wani store taga sunyi parking,
yace' zaki Shiga ne?
Girgiza Kai tayi alamar a,a, fita yayi ya shiga,har ya shige tana kallansa, sannan ta maida kanta jikin kujera ta rufe Ido, ita abin ma Mamaki yake bata wai itace da Miji abinda batayi tsammani ba, gashi kuma ko kadan daga cikin mission dinta bata kammala ba, dole ta dage idan har tana so ta cimma burinta, amma taya zatayi hakan?
Kamar ance Mata ta bude ido ta
juyo wurin windown ta, idan ba gizo idanta ya Mata ba Neena tagani fa, ai da sauri ta bude kofar ta fito sai dai kafin ta karasa har ta fice ta hau a daidai ta sunyi gaba tsayawa tayi tana kallan masu adaidaitar tabbas Neena tagani,dawowa tana mamakin ganinta da tayi Ashe hassashenta daidai ne Kenan ba barin garin sukayi ba,suna nan acikin garin amma ai gari da fadi a,ina ??
Security din wurin ta samu,
tace' don Allah wacce ta wuce yanzu nan daga ita babu Wanda ya fito tana zuwa nan wurin sosai ne?
Securityn yace' taya za'ayi na gane Wanda suke zuwa fa dayawa,
Tace' ehh nasani amma idan mutum Yana yawan zuwa dole zaka Santa,
Yace' munsan wasu ma dayawa Amma gaskiya itade bansanta ba,
Numfashi taja tace' to ku nawane masu shifting din nan wurin?
Mu uku ne,daya bezo ba ga daya can kuma daga ciki, godiya ta masa ta nufi wurin na cikin,Yana zaune taje tayi masa sallama
tace' am wacce ta wuce nace don Allah ko kasanta ?
Tana yawan zuwa haka?
Yace' Wacce Kenan Aminatu?
Ita kadai ta wuce ai,yanzu sai kuma Maza da suka fita yanzu,
Tace' ehh Kasan tane?
Yace' ai unguwar mu daya da kafin su tashi, ni kuma ana nake aiki, to gaskiya kwanan ina yawan ganinta tana zuwa kuma indai tazo tana zuwa mu gaisa,indai ina nan.
Tace' to shikenan yanzu zaka Bani numbern Ka duk ranar da na samu lokaci Zan kiraka,
Numbern Shi ya bata tasa a wayarta,ta Ciro kudi ta bashi,sosai yayi godiya mota ta dawo ta zauna har yanzu be dawo ba,
Ji tayi an bude kofa an shigo,gani Shi da ya ajje kayan hannunsa a baya,
Tace'
ice cream,
Yace' da kinsan kina San ice cream kikayi shiru ban siyo ba kuma bazan koma ba, kuma kema bazaki fita ba,
Kumbura Baki tayi tace' da nace Zan fita ne?
Batasan a fili tayi maganar ba,
yace' me kika fita yi?
Naga kina magana da wancan security din?
Tace' Neena na gani fa, Amma ban Mata magana ba ta hau abin hawa ta wuce, shine na tambayi security yace tana Dan zuwa akai akai kwanan, shine na amsa numbern sa watakila yasan inda suka koma ko?
Gingina Kai yayi yace' hakan yayi,Amma kar ki sake magana da wani sai da izinina kinji ai?
Daga masa Kai kawai tayi, alamar taji,
Suna tafiya aka fara Kiran magriba, suna zuwa gida wasu masallaci sun idar,Kayansa ta kwasa ta fita da su,bakowa a parlourn sai Tv shikuma masallaci ya wuce daga nan,
Itama sallah tayi ta zauna tana Azkhar bayan ta Gama kuma ta tashi ta Shiga wanka tana fitowa Yana shigowa da akwatinta bata ma lura dashi ba ita sai da tazo tsakiyar dakin ta ganshi, murtuke fuska tayi ta janyo hijabinta a Kan gado ta rufe jikinta, ta wuce wurin mudubi,
Yace'
ikon Allah, to mene na rufe jikin kuma?
Ke kina sani de,ya ajje mata Jakarta har zai fita sai kuma ya dawo ya bude ledar da ta shigo da Shi, comp ya dauko da main kitso da ribbon yazo ta bayanta
yace' tunda Allah ya hadani da wacce batasan gyaran gashi,ni Bari na gyara mata,
Ta jikin mirror take kallansa bata iya musu ba,ita kuwa zata ga ikon Allah Namiji da gyaran gashi.....
By:'''Hijjart Abdoul'''
Cwthrt
A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
Yana Jan Jan Dan ya taje, ta rike hannunsa,sabida wata irin masiffan zafine daya ratsata,
tace' a hankali fa ake bi,
Yace'
Madam a hankali fa nayi,
Wanne hankali kasa duka karfin Ka kaja,sai kace Ka damu gashin doki,
Yace' to naji sake min hannu, zanbi ki a hankali bazan yi da zafi,
Promise?
Promise,
Sake masa hannun tayi,tana kallansa yarda ake kunshe dariya,aikuwa ta Kara hawa gashi yace Mata Madam, ahankali yake bin Kain yarda bazata ji zafi har ya taje Shi tsab,ya kawo mai ya shafa Mata,ya kuma tajewa,ya dauko ribbon,
yace' to ki juyo mana a kulle kinsan bazai dauro ta haka ba,
Batayi musu ba ta juyo shikuma ya daure Mata kai,
yace' kinma fi kyau haka,kyanta kitso aka min,a yarda suke haka sai sun fi kyau,
Tace' ban taba kitso ba.
Yace' to juya kiga yarda na iya gyaran gashi na tabbatar ko ke bazaki iya ba,
Juyawa tayi ta kalli kanta a jikin madubin ta kalle Shi yarda yake murmushi irin nayi abin arziki
nan,
Tace' sai kace wata yarinya zaka min three babies?
Ashe shiyasa yace da kitso ne sai yafi kyau, kallon Shi tayi,
tace' wannan ai damuna zasuyi,
Shidai Yana tsaye Yana kallanta ta jikin mudubin, yarda take cuno baki tana kumbura Baki,shifa abin arziki yayi a ganinsa Ashe na yara ne, kuma fa tasan tayi kyau amma take kushewa shikam Allah ya hada Shi da Mata, a Dan zaman da sukayi da ita ya gane 70% a halayarta.
Sunkuyowa Yayi daidai fuskarta suna kallan juna ta cikin madubi,
yace' kinyi kyau mi precioso,
Ya kaimata peck a kumatu ya fice, murmushi kwance a fuskar Shi,
Kallanta ta dawo dashi wurinsa har ya fice,ta dawo da kallanta ga madubin murmushi tagani a fuskar ta har dimple dinta duka biyu ya lotsa, shafa inda yayi mata peck din tayi tana mai kallan kanta a madubi, Idan aka ce Mata zatayi murmushi nan gaba to zata karya ta mutum,bare kuma ace tayi dariya?
Ada tana tunanin yaushe zatayi Kara Jin farin ciki a tattare da ita, sabida
damuwar da take ciki kuncin da bakin cikin da take ciki, shekara bakwai ta ta wuce,a tunaninta ma tayi bankwana da dashi, sai kuma yanzu rana daya kwatsam wani daban yasata dariya alokacin da bata shirya a lokacin da batayi zato ba, dukda shima Yana cikin damuwa ahaka yake danne damuwarsa don yaga annashwarta to ita Akan me bazata danne ta ta damuwar ba itama ta dawo kamar kowanne mutum??