Sashe 39
A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Babu yarda ta iya ganin ranshi ya baci haka nan kawai taji bata san ya kara jin wani haushin, tashi tayi taje takunna ta dawo ta kwanta ta rufe Ido
kasa baccin tayi
juyi kawai take
ta juya nan ta juya can
ta mirgina nan tayi can har karshen gadan take kaiwa daga nan ta dawo inda take, duk idan ta a rufe yake,daga karshe bargo ta Shiga ta rufe har kanta tukun ta samu tayi bacci,
Yana kallanta kamar zai kashe wutar,sai dai bai kashe ba juyin da take kamar yarinyar da take rigima da bori ga gashin kanta ya tattaso, ajiyar zuciya ya sauke sanda yaga ta rufa da bargo, bedena kallanta ba sai da
ya tabbata tayi bacci sannan hankalin sa ya koma ga system dinshi,yaci gaba da aikinsa, yana nan har har karfe bakwai sannan ya tashi
ya Shiga wanka
cikin bakaken suite ya Shirya ya dauki abinda zai dauka yasaka a jakar Shi, har yazo kofa zai fita sai kuma ya dawo yaga window a
rufe sabida acn da taka kunna jiya Amma bata saki labulen ba,dukda dai gari ya gama wayewa
dawowa yayi ya sakar mata labulen ya kunna Mata ac ya kashe fankar,dukawa yayi saitin da take ya bude bargon da ta rufa dashi ganin dan gumi a gaban gashinta yasa shi saka hannu ya goge mata ya ida cire mata bargon aikuwa ta kudundune a wuri daya Zama yayi ya ya dauko biro da takarda
yayi rubutu ya ajje akan bedside drawer, ya sunkuya
yayi pecking dinta a goshi da bakinta dan motsi tayi alamar an dameta murmushi yayi ya kuma pecking dinta ya tashi ya fita tare da kashe mata wutar dakin.
Anyi komai da komai da ya kamata ayi na siyar da company din Abba guda daya Abba Jin kudi ninkin wanda ya bayar yasa shi saurin amincewa,
yace' sai dai kuma ban taho da takardun ba,sai zuwa gobe Insha Allah zan kawo maka,
Binaif kallansa ya dawo gareshi wani killer smile yayi yace' ai bakomai an zama daya,
Shidai Abba harga Allah Baya San wannan murmushi nashi tunda suka zo ace mutum yake fama da murmushi da kuma yayi tunanin ko haka nature din shi yake sai ya basar,
Abba yace' to shikenan hakan ma yayi tunda ga shedu sun shaida komai mai saukine,
Binaif yace' ya kake ganin zuwa Monday
kafin nan zamu iya fara namu aikin?
Abba yace' ehh badamuwa tunda kaga weekend zamu shiga ba?
Jinjina kai kawai Binaif yayi beyi magana ba, tashi sukayi suka fita dashi da lawyern sa guda biyu sai kuma wani shima, bayan sun fito sukayi wurin da sukayi parking motar su Barr Aliyu
yace' Wato Binaif kana ganin hakan ba matsala bace?
Binaif yace' babu wata matsala ai,
Dayan barristern Barr Ibrahim dattijo ne don yama kusan retired
yace' Abinda nake so na fada maka kenan,kaga fa mu mun bashi kudin mu amma kuma ba'a bamu takardun ba, kuma yakamata mu da mukazo siyan abu a zagawa da mu ko ina mu ga yarda ake aiki,muga ma'aikatan da sauran su,
Binaif yace' ai Baffa wannan duk nayi wancan lokacin da nazo kuma naga komai da komai yarda suke aikin su ba matsala,batun kuma takardun ba komai tunda yace gobe?
Ai ina ganin
kawai ba matsala,koba gobe ba yace ni mai iya jinkiri ne,
Bar Aliyu yace' to shikenan ni zan tafi ina da aiki a office,
Musabaha sukayi sannan kowa ya shiga motar sa yayi gaba amma Shi Binaif me makon ya tafi da ya fita daga cikin company n sai ya samu can tsallaken titin yayi parking,waya ya daga yayi kira daga can dayan,
yace' ku karaso daga kusa,
Ya kashe wayar ya jima a wurin yaga motar da yaga Abba yazo da ita ta fito sai kuma 'yan jarida suka baibayeshi kamar jira suke ya fito kuma ba damar ya tafi don gaba daya suka baibaye motar tashi,ganin haka yasa shi yin gaba abinsa
ya tafi,
Abba kuwa yana ganin 'yan jarida yasan za'a rina don tun sanda aka sace su Yusseer ake zarya ko an maido masa dasu kome wani ma tambayarsa bata da amsa shikan besan tsakanin lawyer da 'dan jarida wanda yafi tambaya ba, zuge glass dinsa yayi nanfa kowa yayi korarin yi masa tambayoyi kallansu yayi yarda kowa yake masa tambaya,
yace' yanzu tambayar wa Zan fara amsawa?
Ku min a hankali mana daya bayan daya na baku Minti ashirin zuwa talatin, wani daga cikin Dan jaridanne yayi karaf,
yace'
ance wai an kashe 'ya'yan shin haka ne?
Wani kuma yayi sauri
yace' ance kuma Ka Kai kudin kimanin naira Millon dari shin haka ne,shiyasa ma ka saida wannan company?
Wadannan tambayar ta ruda Abba iya rudawa bai kai ga magana ba kuma wani,
yace' ance kana da yarinya wacce zatayi kimamin shekaru 23 ka tura ta karatu yanzu shekara shida kenan.
Wanda yayi tambayar farko yace' kuma munji labarin bata taba zuwa gida ba kaima baka tana kai mata ziyara ba shin ya abin yake ne?
Wata irin zufa ce ta ketowa Abba betaba tunanin wannan tambayar ba Shi yama manta da batun wannan yarinyar Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yake furtawa,cikin wata irin dakiya wani Yana shirin yi masa wata tambayar,
yace' mekuke cewa ne?
Kunce ance kunga kena ba abakina ba, yarana kuma ba mutuwa sukayi ba sannan ba wani kudi da aka karba a hannuna game da yarinya kuwa banganta ba bamma Santa ba,ni yarana uku ne,
Cikin wani irin sauri Wanda yayi tambayar farko,
yace' an tabbatar mana da yaranka hudune biyu Mata biyu Maza ita kuma sunanta Ummusalma hakane munsa da wannan labarin,
Wannan Karan bai iya basu amsa ba don bashi da tacewa yasashi cewa lokacin ku ya cika, wani yace' a,a ranka ya dade da saura fa.
Sai dai ko Jin shi ma baiyi ba ya zuge glass yayi gaba abinsa, tashin hankalin da ba'a sa masa rana.
Karfe tara ta tashi ganin dakin ba haske dayawa yasata kallan dakin dakyau ta juya dayan barinta amma bayanan ita zatonta yana toilet,shiyasa ma tafara gyara dakin fita tayi ta amso mopper da tsintsiya wurin mai aiki tare da duster tazo goge side drawer taga Papern da ya ajiye mata dauka tayi taga menene aciki,
_The beautiful morning dew and the lovely morning hue are symbolic of mi amor for you.
Good morning mi precioso_ .
Rubutun yafi komai burgeta yarda aka tsara shi daki daki kai kace gasar rubutu yaje, numfashi ta sauke ta nade ta ajiye a wurin kasan pillow ta cigaba da aikinta sai dai kuma tunaninta yafi karkata ko yama ci abinci ya fita?
Ko ina zaije bai sanar mata ba oho?duk yarda ta so yakice abin ya ci tura ta kasa . ko da tagama wanke toilet tayi,tayi wanka
ta fito kallan kanta tayi yarda gashinta ya taso wannan three babies din da ya mata kuncewa tayi ta taje kanta dukda tasan ba tajewa zatayi kamar yarda ya taje mata ba haka ta taje Shi ta kulle a tsakiyar Kai, sai da ta shirya tsaf cikin doguwar Rigar ta kamar kullum ta yafa mayafi ta fito harta fita ta dawo ta dau wayarta ganin missed calls dinsu mus'ab rututu yasata Jan tsaki
tace' yanzu haka damuna zasuyi da surutu bazan kiraba,
Umma tana zaune a parlour tana kallo,gaisawa sukayi Umma tace' kije kice abinci,
Tashi tayi taje taci abinci ta dawo ta zauna suka ci gaba da kallo,Hausa film suke kallo ita ba ma'abociyar kallan Hausa film ba amma wannan da akeyi yaja hankalin ta sosai tana kallo sai dai kuma rabin hankalin nata yana kan kofar shigowa ita gani take bajimawa zaiyi ba, gaba daya kewansa ya addabeta yau kadai gashi bata da numbern sa,idan ma tana dashi tace masa me?
Umma taji
tace' Salamatu ungo nan danno min waccen 'yar zaki ga
ansa filawa da kan mutum sai mota guda daya, yawwa donnuta naji shiru kuma ga rana tana neman yi,
Karban wayar tayi tana cikin dubawa taga numbern sa dayake ta taba kiranshi a wayarta, number ta kalla har zata dauka a wayarta sai kuma kawau ta hardace ta tanemo mata ta danna kira, wayarta ta dauka tasa numbern shi tayi saving,
Suna zaune sai ga wata Mata tazo gaisawa sukayi gaishe da ita Ummusalma tayi Umma tace' ai wannan itace take bin Adamu baban audushakuru Kenan
sunanta Safiya daga ita sai Rukayya Allah ya jikan rai itace auta, Kara gaidata tayi, sannan ta tashi ta basu wuri tare da daukan yarinyar da suka zo tare dukda katuwa ce zatayi shekara biyar.
Numfashi Goggo Safiya tayi tace' Amma yarinyar nan da'alama Umma tana da nutsuwa,
Umma tace' hmmm amma bata fara'a ba?
Batayi magana ba don tasan halin kayanta shiyasa tayi shiru,
tace' Umma bari yazo ya bada kudin lefen matar shi,
Umma tace' shashanci banza Kai wanne kudi kuma, dhi Wanda ya daura auren ne ai zai bayar dhi yace yana santa ne ko kuma shi yace a daura masa aure da ita ehh?