← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 108

Sashe 5

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun fita tunaninta ta fara har ko yaushe ta jima a wurin sannan ta tashi ta fita, tasan yanzu suna parlour su duka saboda haka dakin Abban su ta nufa,safe ta bude taga kudin ba yawa rufewa tayi ta fito har taje bakin kofar parlourn sai kuma ta dawo tunda take bata taba Shiga dakin ba kullum a rufe,yau kam sai ta Shiga tasan yau Yana gida
maybe a bude yake ,
komawa tayi ta murda handle din aikuwa abude yake,Shiga tayi taga wardrobe ne mai kofa uku kawai a dakin sai bedside drawer guda daya, wardrobe din
ta bude taga safe
guda uku a jere,buder sauran kofar wardrobe din tayi
sauran ma haka ne aciki,
Gwada bude daya tayi Amma be budu ba sunnanta tasa namma bai budeba,tasa sunnan kowa a gidan namma haka,kuma password ne ba pin ba,sunaye tayi tasawa be bude ba,gajiya tayi kawai zata rufe wata zuciyar tace kisa ummu,sawa tayi badan tasan zai bude ba,tasawa safe din ya nuna correct,dadine ya kamata,a hankali taga safe din Yana yin kasa Yana budewa kudine aciki dayawa,kudi Bana wasa ba,da sauri ta gwada sauran Suma duk kudi aciki guda daya ce kawai taga takardu
rufe me takardar
tayi, dankwalinta ta shimfida
ta fara jidan kudin a cikin
kowanne safe,ita kanta batasan yawan kudin datake jida
ba kawai jida take,dayawa ta kwasa sannan ta rufe,ta kulle dankwalin ta fita daga dakin,Jin za,a shigo parlourn yasa ta buya a bayan labile,Abban ne yashigo,zama yayi ya ciro da wayar sa har ya Gama abinda zaiyi sannan ya tashi ya kulle dakin da tafito ya Shiga dakin sa,Yana shiga itakuma tana fita dakinta tashiga ta Adana kudin,ta kwanta.

Ranar Monday ta Gama shirinta tsab, dauko jakarta ta tayi
zuba dubu dari dayake ta kirka dari dari ta ajje duka one million ne da duba dari biyu,wayarta ta dauka ta fita,bakowa a parlourn ta sa Kai ta wuce abinta
Banki tace ya kaita,bata fada masa wanne ba kawai taga sunyi parking a access,fitowa tayi ta Shiga kasancewar da wuri tazo yasa aka Mata da wuri
account ta bude tabada dudu Dari amata transfer cikin account din,
Gobe kace tazo ta karbi atm card.

Daganan park tace ya kaita ko zata ji dadi don kwata kwata bata ra'ayin zuwa school yanzu sabida ba Neena,
Ahaka ta karashe ranar har yamma yadawo ya dauketa.

Washagari ma haka bataje ba daga karban atm park ta wuce,tayi zamanta har yamma.sai Wednesday ne taje amma badan tasan me ake cewa ba kawai tunani take ahaka de satin ya cinye kullum sai ta ba driver dubu dari ya kai banki an Mata transfer a account dinta.

Haka ruyuwa ta cigaba da tafiya a wurin Ummusalma kullum ba dadi,kullum cikin kadaici take duk da su yusseer na debe Mata kewa Amma ita kam bata gani haka,haka idan taje makaranta ji take kamar Neena zata dawo Amma kuma baita ba labarinta kuma bata Saba ba,yanzu abin kadan zata tuno sai tafara kuka, musamman idan Neena ta tuno,abin har mamaki yake bata,tayi bakin kokarinta ta daina kukan Amma inaaa bata iyawa sam.

Gashi har sun Gama waec da neco yau watan su 1 da gamawa saboda haka maganar tafiyarta kawai ake tayi.

A yanzu tunaninta ya karu kuma kwakwalwar ta takasu kusan uku da tunani na daya neman mafita nabiyu kuma abin da zata karanta na uku kuma Neena,wannan abin yabin yana damunta kwarai da gaske batasan ya zatayi ba.

Fitowa tayi kasancewar yau Friday bakowa a gidan sai ita, parlour ta sauko badan tasan me zatayi ba,idan ta Akan TV ta sauko tamanta yaushe rabon da tayi kallo hakan nan yau taji tana so,kunnawa tayi ta zanja Channel zuwa india,film din dake kallo ne ya fara Jan hankalinta,na shahid Kapoor mamanshi naso yayi police shikuma naso yayi film,wani tunani ne yazo Mata,da sauri ta tashi ta kashe kallon tasami mafita Kenan, Da daddare yaseer ya kirata yace Abba na kiranta,bayan shi ta biyo har parlour inda Abba yake zaune Zama tayi batare da ta kalle shiba,shima Bai damu ba.
yace, "wato Ummusalma kinsan mu muka haifeki,kuma kunfi kowa sanki sabida haka badan bama sanki ba zamu tura ki wani guri mai nisa ba,sai dan muna sanki kiyi karatu mai zurfi,ki taimaki alumma gaba daya kinji ko".

Kallan Shi kawai take bako kiftawa tsayawa tayi kamar statue tana kallon shi,
Mama dake gefenshi tacigaba
Tace, "muna matukar kaunarki kinji ko
ata,abinda nake sodake Shine kiyi kokari ki maida hankalinki, kiyi rayuwar ki tamkar da kiyi hulda da jama'a sosai.

Sannan kuma zaki karanci gynecologist kinji ko Shi aka samu,don har babanki ya Gama komai da komai da ya kamata har hostel kinji ko?

By: '''Hijjart''' '''_Abdoul_'''
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji_ _magana_
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023
Kawai kallansu take yi,ba ko kiftawa, idan suka ce suna Santa wani irin bakin ciki takeji,wai suna Santa.

Abba ne
ya mika Mata envelope
yace, "gashi takardunki ne da komai da komai mun ajiye copy a wurin mu,abinda nake so dake shine kiyi karatu,shine ya kaiki,banasan shirmen banza kina jina ai".

Batasan mezatace ba shiyasa ta zabi da tayi shiru,Amma har yanzu bata dauke idan ta akansu ba kallon su kawai take kallan irin kun tsaneni dinnan
"Tafiyar kuma Nanda sati daya ce kinga saura kwana takwas kenan,sabida haka sai kifara shiri kinji ko".

Muryar Abba taji ya fadi haka,
Ganin sungama magana sun dauko wata yasa ta tashi ta fita,dakinta ta koma ta zauna a balcony, envelope din ta bude ta zaro takardun ciki ta dudduba komai, su biyu ne a dakin,don har sunan dayar akwai saidai ba musulma bace daga ganin sunan,maidawa tayi ciki,ta jingina da kujerar tana tunanin tafiyar kuma da dukkan alamu ita kadai zata tafi ina laifin ma su tafi tare sai su dawo Amma zata tafi ita akadai sai kace wani namiji,kuka takesonyi ko zata ji dadin abinda takeji amma yau taga bata da alamar yin kukan,tana zaune anan bata San iya adadin lokacin da ta dauka ba tana tunani, da
yar ta tashi ta rufe kofar, alwala ta dauro ta fara sallah tana rukan Allah yasa da alkhairi a cikin tafiyar ta kuma,tare da shiriya.

Tana kwanciya bata jimaba aka fara Kiran sallah dakyar ta tashi da aka shiga sallah,tana idarwa kuwa ta koma bacci.

Ba ita ta farka ba sai sha
aya shima su yusseer ne suka zo suka tasheta zasu wuce tahfeez yau za,ayi hakan yasa akace suje goma
Amma sai suka ce sai shadaya akace
suje, zuwa sukayi suka tasheta suka Mata sallama sannan suka wuce, tashi tayi ta gyara dakin,yaukam sanyinta ta Kara karowa don Saida takusa awa daya da rabi Dana gyaran dakin tanayi tana tunani,ta wanke toilet tayi wanka,batajin zata iya wanki shiyasa ta hada takai laundry.

Lemo ta dauka da biscuit taci ta koshi, fitowa tayi ta Shiga parlourn Abba bakowa a parlourn sai tv dake aiki,dayan dakin ta shiga
kudi
ta dauko ta dawo dakinta
kirga
su tai sannan ta zuba su ajaka key din motar ta dauka guda daya Wanda yake wurinta ,sarkan gold dinta ta dauko da receipt dinsu ta hada ta dauko wani key din motar ta Wanda yake a wurinta guda daya shima ta hada.

Bayan tayi sallahn la'asar ta hada su Duka ta sa acikin jakarta, ta fito sameera kawai tagani a parlourn da'alama yau bata je islamiyya ba,wucewa tayi ta fita harabar gidan, drivern ta na ganinta ya taso da Dan gudunsa,yazo zai gaisheta saidai kafin ma karaso ta karasa wurin motar,budewa tayi ta Shiga, shima Shiga yayi sannan suka fita,inda zai kaita ta fada masa,sarkarta ta siyar,ta dawo kudin ta Mika masa,tace ranar Monday yasa Mata a account,daga nan ya kaita park,ta zauna sai dab da magriba suka dawo gida,har zata fita ta bude jakar ta Ciro mukullin motar
tace, "kasiyar da biyu ka samun kudin account".

Ta juya ta wuce.

Kallanta kawai yayi to wacce zai siyar tunda ya gane motar take nufi,Bari kawai ya siyar biyun a ajje Mata sabuwar Amma Allah yasa kar yayi laifi.

Washegari da rana gaba daya gidan suka tafi rakata shopping banda Abba,duk wani Abu da zata bukata,kayan sawa kam an jide su ba laifi,ita kawai ido ne kawai nata, daga nan suka wuce yawo Basu suka dawo ba sai tara na dare, don haka kowa dakinsa yayi ya kwanta.

Haka Mama tasa drivern gidan yake kaita gidan kawayenta acewarta tayi masu sallama,ita kuwa duk inda taje ko sallama bata masu bare kuma gaisuwar da daman can ba gaida su take ba,ko ruwa batasha bare aje ga abinci,haka zata karaci zamanta ba magana,idan kuwa zata tafi ba sallama take wucewa abinta,Haka kawayen Mama zasuyi ta kiranta suna Mata complain akan Ummusalma,ko mama ta sameta ta mata fada,bazai hana gobe ma idan taje takuma yin shirun ba,tun mama nayi har tagaji tayi shiru.

Ya rage sauran kwana biyu ta tafi ta dena fita ko'ina tana gida abinta, Mama kam ba laifi ta Mata snacks da dambun nama sai yaji dayawa, kasancewar tana San dambu da yaji,Sameera ce ta hada Mata kayanta ana gobe zata tafi,tana zaune tana kallanta tana shirya Mata kayan.

Tunanin
Sameeran take
a zuciyar ta,yanzu iyayenta bama iya iyayenta ba kadai ba mutane dayawa kallan mai hankali suke mata ga nutsuwa da kokari, gata da biyayya dai daibgwargwado, yarinya mai Shiga Rai indai har kazauna da ita zaka fahimci hakan,Amma kuma anyi ba'ayi ba wai an raka bako ya dawo, iyayenta na bata tarbiya daidai gwargwadon su amma kuma batare da sun saniba suna tufka ana warwarewa ne,ko kawaye Basu bata taba to ta tabbata samari na bata ta.sameeran ce
tace, "Yaya kuma yanzu zaki na dawowa gida?

Nodding Kai tamata alamar a,a
"Taaab har shekara shida ko?

Namma de
aga Mata Kai tayi alamar ehh,
Cigabawa tayi
"Nikam da nice gaskiya zan dawo, Nama Gama hada maki kayan bari na tafi".

Tashi tayi ta fita,tabi bayanta da kallo,har ta fice, ajiyar zuciya ta sauke daga bisani taje tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga tayi rolling tasa takalmi ta rataya jaka ta dau key din mota fita.
Chapter 5 · 0% Book details