← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 108

Sashe 54

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Comments
By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
Cwthrt
BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
Dagowa sukayi suka kalle Shi Dan
murmushi yayi Wanda iya fatar bakin ya tsaya beje ko ina sannan ya samu wuri ya zauna ya Dan kurbi lemu, gaban Shi faduwa kawai yake,
yace'
sannu fa,
Namijin yace' Hi,
Karar wayar Shi yaji yasa Shi daga wa ganin ita ce,
Tace' banga kana wani abuba sai San lemu Allah zamu tafi mu barka,
Adan wayince ya juyo ya kallesu,ya juyar da kansa,
yace' sannu fah,
Namijin yace' ina de lafiya?

Sameera tace' Kawai kazo Ka samu a gaba?

Tace' baeb mu tafi abimmu,
tashi sukayi
zasu tafi
Yana rike da
hannunta ta gaban Shi suka zo zasu wuce mesan what comes his mind ba yade ba daga zuciyar Shi shawarar ta fito
sai gani yayi ya rike hannunta, juyowa tayi ta kalle shi,
tace' wai Kai lafiya?

Namma shiru yayi Shi kawai hannunsa yake kallo da ya rike Yama kasa magana,dakyar ya samu kalma biyu,
yace' yi hakuri,
Cikin fasifa tace' sake min hannu ko na zabga maka Mari a nan wurin mu jawo 'yan kallo,
Sakinta yayi
yace' am daman a wannan Kaduna,
Wayarsa dake hannunsa tayi kara message ne ya shigo kafin ya dago ya gansu sun gifta Shi, binsu yayi Yana Kara Karanta abinda ke ciki,
ta kusanta ya je,
yace' am daman fa a Kaduna na sanki,nazaci wacce nasani ce shiyasa ma har na rike Mata hannu,kiyi hakuri fah,
Namjin yace' Kai tafi a anan wurin ba ita bace,
Besaurare Shi ba don beda abinda zai fada masa, shiyasa yayi shiru sai,,
yace' kiyi magana mana koba Sameera bace?

Ja tayi ta tsaya tabbas kuwa ya Santa Amma ita batasan Shi ba ai, shima tsayawa yayi ya Dan kalli wayarsa,
yace' Nasan kece wacce nasani ai, bazaki tuna ni ba ai, Amma ni nasanki,
Namijin yace'kar ki Rena min wayo mana, Sarai kin San Shi Ashe daman bani daya kike kulawa ba ko?

Message yaga ya shigo wayarsa,
yace' ni zan tafi sai wataran Kenan?

Bejira amsar ta ba yayi gaba ina ruwan Shi abinda aka sashi yayi besan cewa fada tasa Shi hadawa ba,
Sameera tace' aww daman kana tunanin Kai daya nake kulawa?

Nasan cewan kana da 'yam Mata kalata sunkai goma ko fiye dahaka bakai daya bane,
Yace' Naji karki Kara kulani tunda ke mayaudariya ce kuma zaki sane kinyi Dani,
Tace' nasaba Jin Kalmar nan a bakin mutane da yawa,wato ga banza ko?

Kai kuma mene?

Har gwara ni Bana lalata da samari Kai fa?

Meye bakayi ?

Waye besan halin Kaba?

Kowa ya kama rabansa medame ni ba, banza kawai shasha,
Tasa Kai tayi gaba abinta,shikuwa Yana tsaye kamar gunki tunda yake da mace sai dai ya gama amfani da ita ya yar a bola bolarma wacce za'a Kona bazata anfanu ba, Amma wannan babu abinda yayi da ita niyyar Shi yau yayi duk abinda
yi da it gashi yanzu komai ya wargaje beje ga komai ba, beyi tunanin ma bata sanshi haka ba,tunda suke bata taba daga masa murya ba sai yau, shima tafiya yayi ya bar wurin,
Yana zuwa ya samu waje ya zauna Yana sauke ajiyar zuciya nishi kawai yake Kai kace yayi gudun tsere ne, a zaton Shi zasu haushi da fada shiyasa ma ya kulle idan sa, so bega abinda yake faruwa ba a tsakanin su,sai da suka tafi Ummusalma tace' ya kamata a Nemo wannan mutumin bazai barta haka ba,
Uncle yace' to amasa me kuma?

Bacin kina gani de da'alama sun rabo,
Tace' ehh da'alama ba?

Amma Shi bazai kyaleta ba ai, idan Ka lura sanda ta tafi kamata yayi acd shima ya tafi amma sai ya tsaya yayi wani Dan tunanin kadan, ayarda suke fadan zaka San beji dadi ba Ka gane?

Yace' na fahimta,
Kallan mas'ud tayi tace' Chatty kafa
Kayi kokari fa sosai da sosai Allah ya Kara jarumta,
Ba shiri ya bude ido yace' Kai haba da gaske?

Kice nazama expert Kenan ho ni ho hoho, na bar wani a Baya first time in history nayiwa mace magana Bama maganar komai ba maganar soyayya na bar wani wallahi,
Mus'ab yace' ji banza waka Bari din?

Ai ni de kasan Zan iya wallahi,
Ummusalma tace' meye maganar soyayyar tukunna ma wai?

Kana nufin wannan abun daka fada Mata shine love din?

Dariya suka sa masa,shikuwa kumbura Baki yayi, dayake mus'ab ne marenin wayan sa shi ya tashi zai buga aikuwa suka fara gudu wannan yayi ta nan Wannan yayi tannan,
Murmushi fal fuskar uncle bazai iya fassara yarda yajiba Amma kuma dadi yaji meyasa aka raba su?

Kwalla yaji zata fito daga idansa bema sani ba sai Jin hannu yayi Ya share masa kwallar hannun yabi da kallo yaga Binaif Yana masa murmushi,
yace' kayi hakuri kowanne bawa da irin tasa kaddaran ku taku sai tazo da sauki Allah yasa kun hado,amma ni tawa,
Murmushi yayi Mai ciwo,
yace' har yau banyi wani Abu ba,Bm Akan neman mahaifiya taba ( a lokacin da aka bada labarin uncle Yana cikin damuwar labarin da aka bashi to besan sunyi zancen ba kawai jinsu yake bazai ce ga me aka fada ba),
Uncle yace' kayi hakuri komai zai wuce kaji ko?

Murmushi kawai Binaif yayi bece komai ba beda abinda zaice shiyasa ya zabi da yayi shiru,
yace' kalle su Ka gani?

Kallan su yakai wurin da suke guje guje har Ummusalma suna dariya kamar wasu yara tun sunayi su kadai har suka gayyato yaran wurin Suma suka fara
dole wai sai Mas'ud ya kama su ya nada sai kace wani ubansu, sukuma sunki shine yara ma akazo,
Binaif yace' Shekaru hudu Baya da muka hadu da su bata magana bare tayi dariya, bacin na taba ganinta tana yin hakan,
Uncle yace' ni Zan fada maka,ko presentation ne fah batayi ance min kurma ce shiyasa sai na bata assignment a maimakon shi,Ashe ba kurma bace tsantsan rashin son magana ne,
Murmushi binaif yayi yace' Ina San farin cikinta ina san ta kasance cikin farin ciki a koda yaushe bansan bacin ranta, bansan tayi ta tunani idan ta zauna ita daya,
Uncle yace' idan haka ne why not ku zauna tare dasu?

Binaif yace' wannan daman shine ra'ayi tun kafin nasan Zan yi aure, ko Dan suji suna rayuwa cikin 'yan ci, suji suna rayuwa acikin gidan su,tunda suka taso suke fuskantar matsala, tafiyar su Spain ya Dan lafa suna dawowa komai ya cigaba, daga karshe suka dawo gidan Kakar mu ananne suka Samu freedom bayan an koresu daga can gida,
Murmushi kawai uncle yayi Yana cigaba da kallan su,
Wani Abu ya fito da Shi a cikin Dan box box din ja ce mai ba'a kuma ganin abinda yake ciki, ya mikawa Binaif
yace' wannan abun shine abinda aka gani acikin towel din da aka yar Dani bayan sun duba sun gani Ka rike Ka hada Shi da takardun wajenka, maybe zaiyi amfani gaba,
Meyasa Kai bazaka rike ba?

Inaji kamar wani Abu zai faru,kamar wani Abu zai sameni, godiya ta ga Allah dayace dayasa na ga 'yan uwana da yasa nasan gaskiyar komai, Ka rike Shi a wurinka abun Yana da mukulli amma babu key din haka suka ga abun, ko ya fadine Basu sani ba, box Mai kyau gashi karami kamar na zobe na zobe ma yafi girma karba yayi yasa a aljihu bekara magana ba daga nan, suka zuba musu Ido suna kallan su.

Waya akayiwa ganin Baba yasa Shi dagawa,
yace' Baba an wuni lafiya,
Daga can ummu tawaikwayi muryan Baba irin shine din nan,
tace' Lafiya qalau yarona,
Yace' ummu ranki zai baci, fa
Tace' Uncle saban labari su besties sun dawo fah tunda safe sai ga su sunzo Amma fa Wanda yasa ce su ne ya kawo su sannan kuma Ance kar Abie yaji donmma Kar yayi wani bincike kasan halin Abie da Dan Karan bin kwawwafi daga karshe de yaushe zaka dawo, Amma idan zaka tafi can London tana nan zaka wuce sannan kuma Kai daya zaka koma Allah sarki My Uncle,
Yace' kekam Ummu bazaki canza ba ko?

Daga dawowar su har kindawo normal,yanzu bakin Anty zai fara ciwo,
Laaa kaga ni bazan iya Bama kwasar su zanyi inkai su gidan Hajja yalwa itace babu ruwanta ko fada bata maka idan kayi lefi sai dai
tace' yanzu Kaine kayi kaza kayi kaza to kar ka kuma Zan Zane Ka idan kayi,
Cikin sanyi take maganar shiyasa itama tayi magana yarda takeyi,
Murmushi yayi yace' hmmm ba ruwan keda Umma idan taji ki,
Yaushe zaka dawo de,
Gobe Insha Allah zuwa rana haka?

Zan dawo
Tace' Haba de Rana ai yayi nisa dayawa ina laifin zuwa safe haka kayi break fast anan dakaina Zan girka maka abinda kake so,
Shikenan Zan duba nagani,idan nazo akwai labari dayawa,
Kai Amma naji dadi sosai sai kazo idan Ka zo kamin waya da wannan wayar Baban, Amma kace ni kake nema Kar Ka Kira Shi ku fara gaisawa kaji ai?

Numfashi yaja yace' Naji second mom din na,
Sannan sukayi sallama murmushi fal fuskar Shi,
Ummusalma ce tazo ta zauna tace' nagaji dayawa,nayi gudu, tana sauke numfashi,
Mus'ab ma zuwa yayi ya zauna shima, mas'ud kuwa wasan sa yayi tayi da yaran sai da Iyayen su suka zo suka dauke su sannan shima ya dawo yana Nishi,
Binaif yace' ku tashi mu tafi gida magariba ta gabato,
Mas'ud yace' sai da kukaga nazo Zan hutar sannan za'ace a tashi a tafi gida?

Wannan in justice ne, daman nasani ba'a Sona ku Duka kuwa,
Babu Wanda ya kula Shi Dan sun San halin sai uncle shikadai ne ya masa magana sannan ya tashi, sai da sukaje inda sukayi parking Binaif ya juyo ya kalle su,
yace' kubi bros ku tafi baza'a takura min ba, a tafiya na rage hanya a komawa kuma bazan rage ba,
Kallan juna sukayi sukace' mekenan?

Ummusalma kuwa bata ma San me yace ba Dan har ya Shiga mota abinta shima shigowa yayi ya kyalesu suna sun hangame baki,
Tace' yanaga Baka shigo da suba?

Yace' kyalesu sun fiye sa Ido ganawa zanyi da mi precioso,
Shiru tayi ta kyale shi bata San mezata ce ba,
yace' Kinyi shiru lafiya?

Tace' uhm
Uhm kadai?
Chapter 54 · 0% Book details