← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 108

Sashe 43

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'''Hijjart''' '''Abdoul'''
Cwthrt
Washegari
koda ya fita ya gansu a parlour babu Wanda yayiwa magana,
sune da suka ganshi suka gaida Shi sai dai ko kallo Basu ishe Shi a bare ya su samu ya amsa ya wuce su yayi tafiyar sa,
Mas'ud yace' Hajjaju wai ku mayar masa da matar sa mana kinga ni tunda nazo banga yaci abinci na kar ulcer ta kamashi,
Umma tace' naci kwal uban gidan su baza'a mayar ba,olsar ta kamashi a haka zai kare shegiyar zuciyar Babansa(usman) ne duk zuciyar ubansa bekai ubansa Adamu
ba sai kace shine ya haifo shi,
Mus'ab yace' Allah sarki Umma wallahi ni tausayi ma yake Bani,da'alama Yana san matar Shi,
Umma tace' kunga meye aciki Nanda sati uku mai kyau za'a bashi ita, ya cinyeta.

Wannan da zaima iya ce Mata Yana sannata ne,
Mas'ud yace' a,a fah ai irin wannan sun fi iya soyayy....

Rufa min Baki marar kunya kawai,
Tafada tare da wurga masa ludayin
hannunta da take Shan kunu,
Mas'ud yace' haba Hajjaju da yanzu Bana roba bane da tuni kin min asarar Dan Baki nan nawa,kin rage min farashi,
Ummu tace' na lura Kaine Ka koyawa waccan dinkimkim din rashin kunya idan Ka kuma magana wallahi rainka zai baci tam,
Shiru sukayi Basu Kara magana ba har suka gama cin abinsu.

Koda ya fita gidan Shi yaje yaga ankarasa gyaran da yakamata ayi komai angama daga nan kuma sai ya wuce company shima Wanda tuni an kusa gamawa befi kadan ba aiki sune bana wasa ba, duk inda ya kamata
gyara an gyara hatta sunan companyn an canza ya koma UMMU LTD.

Yafi so Nanda
wani satin sun gama, anfara aikin da yakamata na sarrafa madara da sugar dayake da iya madara ce yanzu kuma harda sugar yake so ayi, da zai sai companyn harda gonar shanu ya hada ya saya.

Sai da ya Gama zagaya ko ina ya dawo cikin office da yake Sama window ya bude dayake na glass ne kuma babba Yana ganin komai abinda ke faruwa a kasan office din na iya yankin wurin, dawowa yayi ya zauna, ya dauki waya ya Danna Kira,
yace' nasan yanzu hankalin sa ya kwanta,kuyi duk abinda ya dace,
Bejira amsa ba ya kashe wayar sa, jakarsa ya dauko ya bude takardun Yana neman na company tunda company biyu ya gani sai gidaje da fili, Yana cikin dubawa ne wani rubutu yaja hankalinsa
janyowa yayi yaga rubutun kadanne ajikin wata paper anyi stapling dinta da ta fili Zuwa ga Dana Umar Muhammad da date sai kuma signing date din daya gani yanzu shekaru talatin Kenan, numfashi yaja ya zaro takardar ya ajje ta a gefe cigaba da dubawa Yayi ganin Ummu yasa Shi dakatawa ya tuna da ya taba dubawa du haka yagani yawanci a takardar Kara Nemo na Company din da yake nema yayi sannan yayi copy guda daya yazo yaciga da dubawa Yana mai nazartar takardun wasu Basu Kai wasu tsufa ba dukda Duka sun tsufa sai dai kuma yanayi na ajjiya mai kyau yasa Basu ji jiki ba, biro ya dauko ya rubuta Umar, Ummusalma, mas'ud da mus'ab,
Azuciyarsa yake tunanin,Umar Shi aka fara Haifa sai Mas'ud da Mus'ab sai Ummusalma kenan, numafashi yaja a fili ya furta yace' Tabbas haka yake amma mene dalilin rubuta wannan abun?

Yana nan Yana tunanin bashi ya tashi ba sai yamma sai da ya Kara lekawa ya tabbatar da komai normal sannan ya dau hanyar gida babu abinda yaci sai malt da yasha guda biyu restaurant yaje yaci abinci ya dau hanyar gida gabadaya kewanya yake kwana daya kacal be taba tsammanin hakan zaiji ba,Ashe jiya kadanne,Akan yarda yake ji a yanzu da zai koma gida ya tarar bata nan,yana zuwa kuwa ya gansu sun sata a tsakiya suna zuba,ko kallan inda suke beyi don haushin su yake ji,sune suka masa sannu da zuwa wuce su yayi ya Shiga ruwa ya watsa sannan ya fito ya tafi masallaci be dawo ba sai da aka idar da sallahn Isha sun Riga Shi dawowa don har sun zuba abinci suna ci,
Suna kallon film din da Umma ke kallo karangiya ta kalli film din saj tari ba adadi amma duk sanda sukeyi sai ta kalla tana cin dariya abinta, Yana shigowa ya dauki remote ya canza zuwa tashar labarai kallanshi ta budi Baki zatayi magana taji anacewa
Ayau ne mukayi hira da wannan sharar mai companyn wato M & M Wanda ya aka masa tambayoyi game da sace 'ya'yansa da 'yar sa wacce ya tura karatu tsawon shekaru har yau babu ita babu labarin ta ance de waka a bakin mai ita yafi dadi,
A safiyar yau ne mukayi hira da Alhaji Mahmud Isah wato mai company nan na M & M da kuma U & U Wanda muka tambaya sai dai kuma be bamu amsa gamshashiya ba,
Abba aka nuna sanda ya fito daga company ranar da ya saidashi,suna masa tambayoyi,
Dan jaridar ya Kara dacewa sa'an nan kuma munji jita jita cewan yaransa Basu mutu ba yayin da wasu suke cewa yaransa sun mutu,wasu kuwa suka Kara dacewa har gawarsu sungani, 'yar sa kuma wacce ya tura karatu yace beda wata 'ya yaransa uku ne kawai a yarda kukaji yace sai dai kuma Wanda suka je karatu dasu nan gida Nigeria sun tabbatar da tare sukayi karatu da ita kuma tare ya kamata ace sun dawo, tambayar da mutane suke yi anan shine shin
tayi aure me acan?

Ko kuma de dagaske ba 'yarsa bace?

Ko kuma 'yar Dan uwace da ta tafi kuma sai ta koma wajen iyayenta?

Wannan tambaya mutenan suke ta yadawa muma baza muce a gaskiyar lamarin ba, ni Bilal Abdullah nake cewa mu hadu a shiri na gaba,
To kunji de yarda wannan abu ya kasance sai dai muce Allah ya kyauta,
A jiya kuma aka nemi yaran minister aka rasa acikin garin Kaduna sunzo ne ziyara wurin 'yan uwa sai dai kuma ba'a gansu an neme su ko Sama ko kasa anrasa sun bace bat kamar allura, Allah de ya kyaut.

Umma da ta bude zatayi magana sai
sakinsa tayi tana kallo ganin ikon Allah, Suma kansu sunji mamaki sai dai basuyi gigin tambaya ba tunda basuga fuska ba, ko da suka dau wayar su duk zancen ake tun Basu fahimta har suka gane inda zancen ya dosa sai dai kuma Basu San gaskiyar lamarin ba,
Shima be tashi ba sai goma idan wannan tashar labarain sun Gama sai ya Kai wata kuma duk sai anyi labarin Abba kowanne kuma da irin abinda zai fada ahaka ya tashi ya koma daki, don ya kwanta sai dai Yana kwanciya baccin yaki zuwa tunanin ta kawai yake, ganin baccin yaki zuwa yasa Shi tashi ya bude wardrobe dinta ya janyo akwatinta ya bude takardu ya kwaso Duka ya daura Akan gado, ya baje su Yana bi Yana gani ya kwashe tsawon lokaci Yana ganin wannan takardun wasu
gabadaya ya mallakawa 'ya'yansa harda Wanda Bana kasar ba kalilan ne nashi Dana matar,na matar sa ma yafi nashi yawa, ya jima sosai daga nan ya tashi ya dauki paper yayi rubutu a ciki ya dauki takardan da zai dauka ya maida sauran papers na sketching yagani a jakar yace'" ita kuma me takeyi da wannan?

Kamar ya bude sai kuma ya
Maida yayi ya rufe,Yana kwanciya bacci ya dauke Shi.

Da safe da ta tashi ba kowa duk Basu tashi ba har yaran gidan,part din Anty safiya ta gyara tsab( dayake tana da abokiyar zama?) Ko ina ta kunna burner tayi turaren, dayake jiya taji suna zancen Dan wake zasu ci yasata,kwabawa tayi tayi
masu tare da dafa kwai ta Kai parlour inda sukaci na jiya ta ajje, har lokacin Basu tashi ba wanka tayi ta shirya cikin kayanta na kullum, doguwar Riga, tashin Nafisa tayi dakyar ta tashi lokacin ma shadaya saura, wayarta ta dauka ganin game a wayar ta tasan kila jiya yaran suka tura game din ta hauyi tana cikin yi sai ga Anty safiya tazo,
tace' sannunkin fa da aiki irin wannan aiki haka?

Gaisawa sukayi sannan Antu tace' fito muje muci abinci to,
suna tafiya Anty tace' Ai da weekend Bama tashi da wuri sai mu Kai shabiyu muna bacci abinmu muna tashi kawai abincin Rana za'a daura kuma har yaran,
Karasawa
sukayi suka zauna a wurin dining sai dai ba'asa dining ba a kitchen ta ga ansa Shi, Ummi ma ta tashi har an Mata wanka,Basu jima ba sai ga Nafisa tace' Ina kwana tana kallan Ummusalma,amsawa tayi, tace' Mommy ina kwana,
Anty safiya ta kalleta tacet yau kuma kece da gaidani Haka?

Tace' Kai Mommy kema de kinsa ai mantawa nake shiyasa ai,
Anty safiya tace' Ai bakya manta da gaida babanki ko?

Ai wannan special ne ina zan manta dashi?

Ohh nikuma ba special ba ko?

A,ah kefa ta dabance,
Kinga zuba mana abinci ba wannan surutun zamuci ba,
Tana kokarin zuba abinci, tace'
Anty yau mun tashi da wuri ko Dan muna da bakuwa kar tace mana makararru shiyasa tana tashina na tashi,
Anty safiya tace' yanzu ma hakanne don ba abinda kikayi ai du ita tayi wannan aikin har abincin da kike zubawa, wani ana tashin ki da bansan hali ba de,
Shiru tana cuno baki irin haba din nan agaban bakuwa kuma?

Ummusalma kallansu kawai tun jiya idan suna dramar su, ta lura akwa shakuwa
sosai a tsakaninsu ko ajiyan sai da ta tuna Mama a lokacin da take taken shagwa arta sai dai kuma a yanzu tasan tayi bankwana da wannan abu, sai dai ina a lahira idan anayi, suna cikin ci wani
yaro ya shigo ya girmi ummi sosai don zaiyi shekara goma,ummi tana ganinshi ta hade Rai karasowa yayi,,
yace' mommy ina kwana,
Anty safiya tace' lafiya qalau Ka tashi lafiya,
Yace' laaa Momy ina zanci ,
Tace' Baka gaid a bakuwa ba,
Juyawa wurinta yace' ina kwana, da lafiya ta amsa,
Ummi tace' Kai kullum kullum sai kazo ko ba makaranta ko?

Yace' eh din sai nazo din wurinki akace nake zuwa kome?

Ko gaida ni bakiyi zaki fara ko?
Chapter 43 · 0% Book details