← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 108

Sashe 86

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai Mas'ud yazo ya Kai Ku"
" Da dan albarka ma lafiyan Shi qalau da ban ma magana ba,
Tunda tace Ka bata Ka bata mana, ko bakin cikin samun ladan kake min ne?"
Key din ya Mika Mata,ya tashi ya wuce dayan parlourn ya zauna, itama tashi tayi ta dauko hijabin da jakar, Umma kuwa Mayafi aka yafa, suka fito, Mas'ud
daya fito yagan su,
yace'' Umma ina zuwa"
"Za muje duba marar lafiya ne a asibiti"
Yace'' to a dawo lafiya"
" Allah yasa"
Yana kwance ya shigo ya same Shi, zama yayi a kasa, Yana sunne kai,
Yace'' bb"
Bude idan sa yayi ganin Mas'ud a kasa yasa Shi tashi zaune,
yace'' lafiya nagan Ka yau a kasa?"
Kara sunne Kai yayi yace'' da..ma..n..daman am..."
" Kaga meye kake tawani daman daman me?" Nade San ba kunya ta kake ji ba, bare nace wani abu"
Kara sunne Kai yayi ya fara shafa keya,Yana ta motsi da Baki"
Dariya ya bawa Binaif sosai, Binaif yace'' karde kaje,garin sunne Kai,Ka kifa kanka a kasa"
Shiru ya kuma yi sai Dan murmushi murmushi da yake yi,
" kaga nifa ba ca nace Zan Baka, 'ya ta ba,bare kuma kazo kana wani Jin kunya ta, abinda bamma taba gani ba kena, Mas'ud da kunya"
Yace'' daman fah''
Tsaki yayi ya kwalla wa Mus'ab Kira, Mus'ab da yazo a kujeran da Binaif yake ya zauna,
yace'' bb gani"
" Yawwa tambaye Shi, me zai fada min, sai wani sunne Kai yake yi, Yana Jin kunya, idan ya fada maka Ka fada min"
Kallan sa Mus'ab yayi yace'' wonders, yau Kai ne
haka?

Kunya fah Kenan"
Mintsi nin Mus'ab yayi a kafa, mus'ab
yace'' kut, lalle ma me na maka?

Waya akayiwa Binaif ya tashi yace'' kunfa ni na fita, idan ya fada maka, Ka fada min"
Yana ganin Binaif ya fita shima yayi sauri ya tashi ya dawo kusa da Mus'ab ya lankwashe kafa daya, daya kuma ya sauke ta a kasa yake facing din mus'ab,irin zaman da yake so Kenan, musamman idan zai zuba surutu Baya Zama normal a kujera,
Yace'' Kai dalla,Ka kusa cemin Yaya Mas'ud, Kai da waccar Aljanar, very soon zaku fara"
Mus'ab yace'' to sai Ka samu ai"
" Kai bama yaya ba, na kusa Zama BABA?

No ba Baba ba Baba old fashion ne, ABBA?

No ba Abba ba, shima ya zama old fashion,
DADDY?

No ba daddy ba,muna da Daddy, to wa?

Yawwa PAPPI, yes pappi ko PAPA, ehh su sun danyi haka ma za'a cemin"
" Wai walili ce ta kusa haihu wa?"
" Mtsww da ita wannan ko cikin tana da Shi ma?

Ai sai na haihu yarinya ta ta girma tayi wayo ko yaro na sannan zata haihu, Kai aure fah zanyi Nanda wata hudu kyawawa hehehe na girma na bar wani kasan ance mutum sai yayi aure ko me ko ya cika mutum ko me oho de, shine ma fa yanzu nazo na fadawa bb aje ane ma min
auren ta"
Ya fada tana Dan dariya irin ba Yana din nan, Mus'ab shima din dariya yayi Yana dariya,
yace'' Kai yanzu aure zakayi?

Shine kake wannan uban lissafin, har Ka fara tunanin samun Yara tun kafin ma asa Rana"
" Kai fa banza ne wani sa'in idan kana abu kamar marar ilimi, Sam Baka da ganiya"
" Fadi komai, kuma zaka San Wanda zeje ya fada wa bb din, bakinsu kace min ma marar hankali din na yarda wallahi na hada maka wani abun"
" Wayyo Dan Allah kayi hakuri, Yaya Mus'ab na manta kai ne, lo siento mucho( am so sorry)"
Dawo wa kasa yayi,yayi kneeling a kasa ya hada hannun
sa yana rukan sa, shikuwa mus'ab Dora kafa Daya yayi Kan daya, Yana Kar kada wa, daga karshe ma tashi yayi,
yace'' kaga ni tafiya ta, na wuce asibiti"
Tashi yayi ya wuce,yana tasi shima ya tashi,
yace''
wallahi sai dai muje, tare baza Ku barni ni daya a gida ba, sai kace tsohon maye nayi ta tunanin mi amor dina"
Tsaki mas'ud yaja,yayi gaba ya barshi, sun fito har sunje gate,
Mus'ab yace'' haka zaka bar musu gidan Baka rufe gidan ba?"
" Mtsww har wani ni Zan..."
Sai kuma yace'' aww ohh to ni, Minti Daya ma yayi yawa ina zuwa"
Ya fella da gudu yaje ya dauko key din su, ya dauko wallet din Shi, sannan ya rufe gidan ya fito, Yana haki yazo ya rufe gate din suka tafi, suna tafe Yana zuba masa surutu sa'a sukayi suka mi abi hawa suk hau suka tafi.

" Ai ina San idan ana tafiya Dani ake tafiya a hankali Ashe kema bakya gudu, safiya itama bata gudu, amma Ida aka ce Miki audushakuru da Baban su, ko Adamu ba'a magana Ida suka shararo motar nan ba'a magana"
Ummusalma shiru tayi Dan bata San me zata ce bare ta
ci cigaba da magana shiyasa,
tace'' ai yafi dadi rashin gudun"
Parking tayi tace" Umma Bari a sai fruit"
" To jeki mana, zance Kar kije ne"
Fita tayi taje wurin Mai Saida kayan, shikuma Yana yiwa wata yarinya fada baza su wuce sa'anni ba,
Yarinyar tace'' kayi hakuri Dan Allah wallahi haka nake dashi,marar lafiya Zan bawa"
Shikuma yace'' ina ruwa na da wani marar lafiya sai kin ciko min kudi na,da kin san Baki zaki ce a yanka miki, ba zaki tafi ba sai kin ciko min"
Ummusalma tace'' yimin hadan dubu Daya da dari biyar, kasa lemu da Dan yawa"
Yana hada wa Yana masifa, yarinyar gwanin tausayin har ta fara matsar kwalla, tausayi ta bawa Ummusalma sosai kana gani zaka san tana cikin hali na taimako, dauke Kai tayi daga kallanta, tana kallan yarda yake hada wa Yana Bala'i, sai da ya Gama ya cika Leda baka da yellow tab sannan ya miko Mata, bata Karba ba ta zaro dubu uku ta bashi,
tace'' nawa ne kudin Ka na yarinyar nan?"
Yace'' dari uku ne"
Tace'' Ka dauka, Ka Kara Mata, sai Ka bata canjin ta"
Tana fada ta karba ta wuce,kafin ma yarinyar tayi godiya har ta wuce, ta biyo ta Dan ta Mata godiyar kuma sai taga har ta Shiga mota taja tayi gaba daman ba kashe wa tayi ba, tsayawa tayi ta sauke ajiyar zuciya ta dawo tace da Mai lemu,
" Ka dauki kudin ka, Ka Bani sauran kudin,Bana San Karin naka"
Zaiyi magana de sai kawai ya Mata dubu Daya da dari biyu abinta, ta karba, ta wuce ta hau napep tana Mai Jin dadi, da yanzu a kasa zata taka,takuwa ji dadi sosai,
A kusan tare suka je du asibiti Daya ne, ward ne ba Daya ba, su suna dakin dai dai ita kuma tana Mai hada a male ward,
Suna Shiga Umma ta Kira Anty safiya tace'' wanne daki ma kika ce ne?"
Anty safiya tace'' daki na shadaya"
Umma tace'' na goma?

Koba na goma ba?"
Anty safiya tace'' shadaya idan kinzo ki tambaya"
Kashe wayar tayi tace'' keni naji goma kika ce,Lamma gomar ce bansani ba ko me, nasani Daya da zero mana, ga kuma Salamatu"
Ummusalma tace'' Umma wanne dakin suke, wai na goma"
" To shikenan Umma Bari ni zanje ganin likita, idan nagama sai nazo"
" To shikenan nanne nasan nan suke zuwa"
Ta fada tana nuna Mata wurin da hannu,
Sannan kowa ya kama gaban sa,
Umma a hankali take tafi har wurin daku nan babu kowa sai wani da ta gani,
tace" bawan Allah ina ne daki na goma"
Nuna mata yayi sannan ya wuce, itama wuce wa tayi tana dogara sandar ta, tana tafiya,har ta iso, tura wa tayi ta bude a fili,
Tace'' mtsww bakowa a dakin sai su bar marar lafiya Shi kadai"
Kara sowa tayi ta Shiga cikin dakin har bakin gadan,gyara glass din idan ta tayi dakyau yaga de Sarai Namiji ne, a kwance,
Tace'' a,a to ko ba nan bane ba"
Fitowa tayi ta Shiga dakin dake opposite,Yana zaune a Kan kujera Amina na zaune a kasa tana cin abinci, ta shigo da sallama, juyowa sukayi suka amsa Mata,
Umma tace'' Kai jama'a wai Yana ke ta mantuwa ne, nifa daki na goma aka ce min,Ashe ba Shi bane na shigo nan ma, da'alama ba Shi bane"
Baffa yace'' Mama inaga kinyi mantuwa ne,nan na tara ne"
Shigo wa tayi tace'' Kai ni nagaji,Bari na zauna, na huta sai na tafi"
Kujera ya tashi ya Mika Mata,ta zauna tana sauke numfashi shikuma ya dauko wata ya zauna, waya ta dauka ta Kira Anty Safiya,
Tace'' ke ni,kinga sai bata nake yi, wanne daki kika ce"
Tace'' daki na shadaya fah"
"Awww ai ke kikayi shirmen Bani ba"
Kashe wa tayi tace'' Ashe daki na shadaya tace, to sannun Ku ya Mai jiki?"
Baffa yace'' da sauki alhamdulilla"
Amina tace'' ina yini"
Umma tace'' ina wuni de ko?" Wani ina yini?

"
Murmushi tayi kawai bata ce komai ba, Umma tace'' Bari na tafi,
Baffa yace'' da kin Bari ta raka ki kawai Naga ta Gama ma ai"
Tashi tayi tace'' Bari na raka ki Kawai mama"
Sannan suka tashi suna tafiya har taje dakin tace'' gashi nan, Allah ya sauwake"
Da ameen Umma ta amsa ta Shiga ciki,ita kuma ta juya ta koma, tazo Shiga dakin su, tace'' su wannan basa rufe daki ne?

Kome?

Wayar tace tayi Kara shiyasa bata rufe ba,sai kawai ta koma ta fita ma daga ward din gaba Daya, tana daga wayar,
Tace'' ya aiki barrister?
Chapter 86 · 0% Book details