← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 108

Sashe 79

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Binaif yace'kana gani de karfina aka fi ai,
Tagumi yayi yace' shikenan kawai yau Banda sa'a,
Ganin da sukayi ta iya yasa suka hada Ido irin tabamu kunya fah, sai gata ta cinym Mus'ab,
Mus'ab yace' gaskiya ki Basu,Abinsu, bafa a haka,
Inaa Bama taji shiba,
Suna cikin yi su yusuf suka shigo, da sallama babu Wanda ya amsa sai ganin su da sukayi
awurin su,
Yusuf yace' taabdi idan Yaya ta fara ko,kawai Ku hakura ma, da game din, Dan abinda yafi zero ma sai Ka tashi dashi,
Yaseer yace' aikuwa de Dan yaya bala'i ce,
Ummu tace' yeeeeess daga masu sunanne,
Ke dalla can da ko handle din kin iya rikewa ne ma?

Na Shaka,Zaka San kayi dani daman yaseer Ka renani tam,
Mas'ud yace' Kai yaseer kadena Rena mutune fah,
Mus'ab yace' kaji babban yayan ana hudu ba,
Ajjewa tayi tace' nagaji, ta Shi yayi ta koma Kan kujera Binaif yazo
yace' Zan fita,
Ina zakaje?

Sunkuyo wa yayi Mata peck yace' Zan je gidan Anty safiya,
Kace ina gaida ta,kace kuma har yau banga su Nafisa ba,
Ganin kallan da yake mata irin ni Dan aikekine?

Tace'please baby?

Murmushi yayi ganin yayi murmushi ta tashi ta masa itama peck, acikin kunne tayi masa rada, tace' byee,
Sai da ya tafi ummu ta dawo kusa da ita, sukuma suna can a kasa ana fama sai iho suke, Mas'ud da Yusuf Mus'ab da yaseer,
Ummu tace' Yaya kaina ya kulle bansan ya za'ayi ba,jiya de bata fita ba, bansan yau kuma ba, kuma tana San wani Mas'ud, shine ma damuwar ta,
Kallanta tayi da kyau Jin Abinda tace, tace' kin tabbata haka ta fada maki?

Ehh yaya,
Tace' kinga Mas'ud din da take fada maki can,
Tafada tana nuna Mata Shi,
Mamaki ne sosai a fuskar ummu, tace' Amma yaya taya Kenan?

Anan tabata labarin haduwar Sameera da Mas'ud har jiya da sukayi wayar nan,
tace' yanzu abind za'ayi shine zai dena kiranta, sannan bakin ce kina da shawaran d zaki bata ba?

Bani da wata shawara yaya,na Rasa yarda zanyi ai,
Ni,ina da ita, yau Ida kinje ki taso d maganar jiya,
Shiru tayi tace' sauran maganar Kan Ku tafi Zan maki message incase ki zaki manta ko kuma kin manta sai ki duba, a wayarki kin gane?

Daga Mata Kai tayi alamar eh, tace' laa koma nasa earphone a kunne na,ko?

Hakan zai fi ma,
Kiyi de yarda nace maki, din maybe lokacin Nayi bacci, tace' to shikenan yaya.

Bata taba tunanin haka so yake ba, sai da ta afka cikin sa, bata San haka yake ba, tasan ta yanke samun farin cikin, a ganinta Wanda take so shine farin cikin mutum kuma ace shima Yana Sanka, Amma ita tasan bazata taba samun wannan walwalar ba, shiri take zata fita Amma tana tunani, dauko jakar ta tayi zata fito taga ummu a bakin kofar,
Ummu ta shigo tace' ina zaki kuma?

Kinsan Zan zo mu karasa maganar mu ta jiya ko?

Ajiyar zuciya ta sauke tace' ummu Zan fita ne, fah,
Ummu tace' aikuwa babu inda zaki je, Shi Wanda kike so din ance maki idan yaji kina yawo zai amince ne?

Yaya Sameera let me tell you the truth duk wani Wanda yace maki wannan yawon zuwa partyn da kike shine birgewa to ba makawa Yana neman saki a bata ne, ko kuma ma yasaki, yaya Sameera ki gyara tun yanzu,
Yanzu idan kika fita kika mutu fah?

Ehh?

Wa gari ya waya?

Mutune suna maki kallan Kamila kuma nutstsa me kike tunani?

Idan Baki gyara rayuwar ki tun yanzu ba sai yaushe ?

Tsayawa tayi kawai tana kallanta, fada take Mata tana daga murya kamar itace babbar ita kuma karama, zatayi magana taji,
tace' idan kina tunanin cewan su kawayen naki suna sanki ne, to kirasu kiji, ki Kira su, ki fada masu cewan kin samu wanda kike so, kiji me zasu ce,
Cikin fada itama tace' ke ummu kinsa me kike fada kuwa?

Kawayen nawa?

Zaki ce basa Sona?

Hmm to kina mamaki ne?

Ki Kira mana ai ga waya nan a hannun ki,ki rasu kiji,
Ummuu,
Call them pleaseeeee,
Zatayi magana ummu tace' please,
Wayar ta Ciro daga cikin jaka ta daga ta Kira tasa a speaker,
Daga can aka daga aka ce
" Meera har yanzu Baki zoba, zafa a fara,
Tace' kinga, Seena,bawannan ba Nayi samu wanda nake so,
And so what?

Tace' Ina San shi fah,
To meye kuma?

Ko anyi auren ina kowa Karan sa zai ci babu babbaka, kinga Idan zaki zo kizo ki taho mana da kudin Kari, a to,
Tace' seena, mekenan?

Kamar ya?

Kinga Karki bata lokaci kiyi sauri kizo, malama,
Ya kashe wayar ta,
Wayar tabi da kallo ta kalli ummu, murmushi ummu ta danyi tace' Daya Kenan, next?

Ajiyar zuciya tayi ya saisaita kanta, ta Kira wata,
Tana.

Dagawa tace' Yau ina kika nufa kuma?

Tace' kinga bawannan ba, ina fada cikin tarkon San wani shikuma Baya Sona,
Mtsww kin ban haushi, Abu Mai sauki yanzu nan ki taho mujr wurin Malamin nan danake zuwa wurinsa kawai ayi komai a Gama tuni zaiji babu wacce take so sai ke, kigama cacima ki watsar da shege,
Rufe idanta tayi tace' mekenan?

Me kuwa?

Ke ai daman bazaki canza ba, mafita ce fah na nema maki,
Kuma aikin nacun kudi da yawa ki taho da kamar 100k haka,
Tace' to nagode zaki jini sai gobe Amma,
Yawwa yar gari, sai naji ki,
Kashe wayar tayi tayi ta koma da Baya ta zauna Akan gado, ta Dafe Kai,
Ummu itama karasowa tayi tace' next?

Kiran wata wayar tayi aka dauka, tafada mata,
Tace' Haba Meera wallahi kina bada mu, da yaza'ayi ace yasoki, wannan party zaki je sai kisa wani long skirt kiyi
kawo Vail ki yafa, wataran har atampa, kawai ki ajje wannan bidi'ar a gefe kisa kayan asali, gaki da kayan aiki,kina sa kayan asali zaki fito duk shegen da ya ganki shikenan,kawai ki bada Kai bor.....

Kashe wayar tayi ta kifa kanta tana kuka, gaba kidayansu babu wacce taba ta shawarar arziki,
meye mafita?

Ummu tace' kidena kuka, Mafita Daya ce,ki kaurace
masu, kina da kawaye ba lalle sai suba, Amma idan kina tare da su to tabbas akwai aiki ja, abinda ya kamata yanzu, ki ajje batun so a gefe ki raba kanki da makiyan ki,ba ke soke soba kudin ki soke so,
Dagowa tayi tana kuka sosai tace' sune suka fara ,sune suka fara Jan ra'ayina, Ummu daman haka akeji?

Ummu
Sai kuka, Rasa abincewa tayi sai rarrashin ta da tayi sai da ta nutsu ta dena kukan, sannan
ummu tace' ki kwanta Amma ki kashe wayar ki, kiyi tunanin da kanki,ki nemowa kanki Mafita Zan tafi,
Fitowa tayi tana
tausayin ta, tabbas cin Amana beda dadi ko kadan, Allah ya kaimu gobe komai zai kare.

Sune suka yi komai yau har breakfast sune sukayi sunayi suna fada, har suka Gama sai da suka Gama Mas'ud yaje yayi knocking kofar dakin Binaif,
Yace' bb,aljana Ku tashi, yunwa mukeji,
Jin shiru yasa Shi yi da karfi yace' Ku tashi mana,
Binaif ne ya bude kofar yace' jeka dafa kaci
Gam ya rufe kofar,
Damman an tasheku,
Sannan ya wuce Yana Mita shidaya,
Bayan sun Gama breakfast, Binaif yadauko masu takardun su gaba kidaya aka baje kowa yana gani suna cikin budawa Binaif yaga wata takarda Idan be manta ba,ya taba ganinta lokacin da yafara duba takardun sanda Yana gidan Daddy, dauka yayi ya bude, ganin rubutu a ciki, aikua itace,
Yana cikin nadewa idan Shi ya sauka Akan Sunnan Ummusalma,
Dagowa yayi ya kalleta hankalin Yana ga duba wasu
abun, Mika Mata takardar yayi, bece komai ba,
Karba tayi tace' tame ce?

Ki karanta,kawai yace,
Warewa tayi dayake ya fara nadewa, ganin rubuta da yawa yasa kawai ta kalli ta kasan layin,
My lovely Daughter Ummusalma Muhammad Uthman Suraj,
Babu abinda yazo Mata Kai irin Kenan Shiyasa Amina take amfani da Muhammad Suraj??

Fara karantawa tayi.

I your father Muhammad Uthman Suraj, My dear daughter.........

By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
46
Is better to have an enemy who slaps you in the face then a brother or a friend who stabs you in the back.

My message to yoo maybe take long to reach you, I might die.

Ummusalma bakida kowa a yanzu, you have siblings, Mas'ud and Mus'ab, sun bata a aranar birthday din ki 20 june.

Mutane dake tare dake bana kirki bane Sune suka wargaza rayuwar mu, Allah yayi hakan zai faru Amma sune silan komai, ba komai yaja haka ba, sai hassada da kyashi da ganin kuma na fisu, they don't love you any more they hate You, one more thing You have to know shine akwai wani key na karamin check it out.

Daga nan ya kwashe labarin su ya bata a takaice sannan ya rubuta Mata adadin dukiyar sa, a duk a cikin Papern,
Daga karshe kuma akasa sunanta tare da wannan signing din na Ummu.

Hawayene fal idanta Amma be riga da ya zubo ba, Mas'ud tashi yayi ya dawo kusa da ita ya ansa papern ya karanta ya mikawa bb, shima ya karanta sannan ya mikawa Mus'ab, kowa shiru yayi Yana tunani can,
Ummusalma tace' Me kuka gani?

Binaif yace' kawai mu bari ya Kai mu Kara kotu ko meye sai ayi,
Mus'ab yace' yanzu fah beda komai kome?

Mas'ud yace' ehh gaskiya Dan kaga wanda aka hada businesses din dasu, suka ce baza su yarda ba sai dai companyn din ya zama nasu, to Shine suka siya fah,
Numfashi Binaif yaja yace' ba siya sukayi ba, kudin da suka zuba inaga shine kawai sukayi masu ciko ya dawo nasu,
Ummusalma tace' yanzu abinda za'ayi a raba Shi dana Abuja,
Mas'ud yace' beda komai Kenan?

Malalacin murmushi tayi tace' idan ya wayi garin beda komai din, Banda gidan Shi daya mallaka Wanda ya Gina Shi,da kudin sa zance ko da kudin babammu,
Mas'ud yace' da kudin Baffa de,
Mus'ab yace' yanzu ya za'ayi?

Mas'ud yace' kawai a tura kawu munir ya je ya saya, tunda shima ya fara yin kasa,
Binaif yace' taya hakan zai faru?
Chapter 79 · 0% Book details