← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 108

Sashe 34

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty ta kalli Baban Ummu tace' Abu Abdallah ina tausayi yarinyar bakadan ba, kaga fa yarda ta koma zaman daki, da ita idan ta fito ita da daki sai kwanciya kullum tana parlour idan karatu ne to tana waje,amma yanzu gaba dayanta ta kulle kanta a daki,
Shima numfasawa yayi yace' Nima na lura da hakan,sai dai bansan yarda zanyi ba,duk wata hanya da zanyi,nayi na bi Amma shiru nikuma bawani mutunci muke da iyayen yaran ba, bare su fada min halinda ake ciki don nasan yanzu de duk yarda akayi an sanar dasu me ake ciki,
Anty tace'
fatana Allah yasa de lafiya suke, dakuma ace anga gawar su da abinda sauki ma,ansan sun mutu.

Bekara magana ba,itama ganin haka yasata yin shiru suka cigaba da cin abinci su.

Ummu kuwa a Mota shiru kawai tayi tana tuna ranar Monday dazasu je makaranta dramar da sukayi tayi Akan su koya Mata mota, har suka iso bata San sun iso ba sai dataji Yana tambayan ta ina zasuyi, Ashe fa driver be taba kawo ta ba,hanya ta nuna masa har suka isa, lecture theatre din ca tace ya jirata gata nan fitowa.

Tafiya take amma gabadaya batajin dadi sabon kewansu take ji,ji tayi hawaye na zuba a idanta hannu tasa ta share sannan tacigaba tafiya,kowa kallanta yake Wanda suka san ansace su su tausaya Mata wasu sukuma da Basu saniba suce ko ina yan uwanta oho,
Koda ta shiga bata zauna inda suka saba Zama ba sai ta tafi can Baya taje ta zauna abinta babu Wanda tayiwa magana, handout ta Ciro tafara karantawa dukda a takure take Amma ahaka tade ta daure take karatu, ta jimaba a wurin sannan lecturer yazo shi.

Allah ya taimaketa Dan abinda ta karanta ya wasu sun fito wasu kuma tayi da kanta ta hada, Gashi awa dayane kuma ba laifi tana da saurin note kuma uku za'a amsa sai dai kuma gabadayan su suna da 'ya'ya.

Itace zata fara forwarding gaba haka yasa tayi ta fito bata jira sai kowa ya Gama bayarwa ba.

Bayan sunyi sallahn Isha, mai aikin Umma wacce take Kula da ita ta kawo masu abinci, suna zaune suna kallo Umma
tace' sai yanzu kikaga dama wato ko?

Tun dazu inajin yunwa sai yanzu ne zaki kawo mana abinci ko?

Ita dai mai aiki shiru tayi don tasan tayi lefi,ganin Umma ta fita yasa itama ta fita kuma batayi abinci ba sai da ta dawo bayan magariba.

Itama Umman shiru tayi batace komai ba,ta fara cin abinci,
tace' salamatu ki matso muci tare kinji ko?

Matsowa tayi zataji Binaif da yake Ka kujera ya diro,
yace' a,a kamar ya ku matso kuci tare?

Mutum da matar Shi ai tare zaiji da ita ko?

Ni ko tayin ma ba a min ba wannan ai ba adalci bane.

Ko kallanshi batayi ta lura shima wannan beda ta ido zata kuwa nuna masa itama bata da ta idon,ita kuwa Ummusalma kunya ma taji daga yin auren,ko kamar ko a jikinsa yarda ma ta gani kamar son auren yake, ita kunyar shima takeji shiyasa ko kallansa bata Kara yiba,
Ganin sun fara cin abinci su hankali kwance yasa Shi Kara matsowa shima
ya dauki spoon ya fara ci, ita gaba daya takura tayi tama kasa sakewa don haka kadan taci dukda yunwar da takeji kuwa sai kunun ayar da tasha,
Umma ce tafara Mita,
tace' arasa me za'a min sai abincin yara,yanzu wannan abinci ne iye?

Binaif yace' Taliya ce abincin yaran?

Yo itace mana kawai a kafa barina da yunwa?

Tace ni na koshi ma, tafada tana cire hannunta daman da hannu take ci sune suke ci da spoon.

Babu Wanda ya Kara magana har ya Gama shima
ya tashi ya tafi gida,kwashe kayan tayi itama takai kitchen inda taga mai aikin ta fito.

Umma tace' kije ki kwanta,kuma kinga ya tafi ai da ya kawo maki kayanki,Kai wannan Mantuwa, kinga kirashi a waya ta kinji ko?

Mika Mata wayar tayi ta karba,
tace' mene sunan?

Ni nasan me aka samin, zade kiga kan mutun guda biyu da mota bata sha wahalar ganin sa ba kuwa, dannawa tayi ta Mika Mata, sai da takusa katsewa yadaga tace' Ka taho Mata da kayanta da motar Adamu, baji mezai ce ba ta kashe,
tace' kinga ni na fara Jin bacci,kama ni na tashi na tafi daki,idan yazo ki Shiga dakin kusa Dani wannan ki kwanta wancan dakin ta nuna wani daki dake gefe nasu Yan albarka ne( mas'ud da mus'ab) sunma wai kusa dawowa
haka suka ce de.

Tashi tayi ta kamata ta,har daki ta rakata sannan ta dawo ta zauna tana channel ta canza ta Kai Bollywood suna Dhoom 2 suke dukda taga film din Amma tana San Kara gani,hakan San ta Mike kafa Akan kujera tana cigaba da kallo.

Har suka gama
bashi ba alamar suka fara series tana nan zaune ba lefi series din ya Mata kyau,shima suka gama suka fara wani,tayi bacci.

Shikuwa da yaje gida kayansa ya fara hadawa masu muhimmanci yazuba a karamar trolley,kayansa na sawa kuma dayake a goge suke kawai zubasu yayi a cikin katuwar trolley dukda haka Basu cinye ba sai da ya Kara da wata,ya kwashe komai masa masu amfani sai abinda ba'a Rasa ba,ya Kai mota,sai da ya Gama komai lokacin shabiyu ta Gota Shi Yama manta da zancen ya kaimata kayanta sai da ya fito har ya Shiga zai tafi ta tuna,fita yayi yaje ya bude motar da Daddy ya fita da ita,ganin bude yasa ya dauko Jakarta.

Dakanshi ya bude gate din don yasan zuwa yanzu mai gadi yayi bacci,Dan ma ya fada masa zai dawo kar ya rufe,shiyasa ma yaga gate din bude sai dabya shigo ya tashi mai gadin da ya rufe, kayan ya fara jida Yana kaiwa ciki,yasan dayan dakin su Mus'ab ne don haka ya kai kayansa dakin kusa da Umma sai da yagama kwashe kayan tas sannan ya zo don kashe kallo da rufe kofa yaje ya kwanta,ganinta da yayi Akan kujera tana baccinta hankali kwance
ta daura hannunta daya tayi pillow dashi dayan kuma Akan cikinta, murmushi yayi ganin cute bakinta ya Kara tsukewa, film din da take gani ya kalla Nafsi Al'akhar, ganin yarda ya dauki macen yasa Shi ware ido ya kalle film din ya kalleta har suka tafi talla Hannunsa yasa cikin sumar kansa
yace' to ai su film ne,nikuma gaske ne, Yama za'ayi na fara daukanta,taaab ai bazan iyaba ma.

Kuma Shi de bayasan tashin ta,komawa yayi ya leka dakin Umma ganin tana baccinta ga kuma mai aikinta nan itama a gadanta yasa Shi komawa,ya Duka a hankali wai karba ta tashi, dauketa, itakuwa tunda ya dauketa ta tashi amma bata bude ido ba,gabanta kawai taji ya gudun tsere Akan gadan dakin ya ajjeta ahankali, harda su furta yawwa bata tashi ba,jere akwatuna yayi a gefe guda Allah yasa ma yayi wankan Shi daga can gidan, wardrobe din dakin ya bude yaga blanket da bedsheets da'alama anan Umma ke ajje su, lafiyyayu ya jawo guda biyu tare da bedsheet guda daya, Akan gadonya durasu sannan yaje ya janye center table din dayagani a gaban kujera yayi shimfidar sa ya yaje ya kulle ya kashe kallo tare da kulle kofar ya dawo ya kashe masu haske sannan ya kwanta, gaba daya ya gaji kuma gani yake daukanta da yayi yasa masa ciwom kafada( sai kace Wanda ya dauki buhun shinkafa
), addu'ah yayi ya shafe jikinsa,sai dai kuma ya kasa bacci juyi kawai yake ga gajiya ga kwana a bakon wuri gashi kuma a kasa, dakyar bacci ya dauke Shi.

Tana jinsa duk abinda yake sai da taji yayi bacci tukun itama baccin ya dauke ta........

By: '''Hijjart Abdoul'''
Cwthrt
A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
21
Da asuba ta rigashi tashi,itama ta Dan makara don har anshiga masallaci dakin ba wani haske sosai kasancewar babu wani security light a wurin kuma babu farin watan da zai hasko ta window,wayar ta fara dubawa tunawa da tayi a bakon wuri take yasata tashi zaune sosai, tunawa tayi yayi shimfida
a kasa yasa sauka a hankali daga gadan tana tafiya har tazo bakin kofa ta lalu min switch din dakin ta kunna Amma ganin babu nefa yasa cewa kila sun dauke, a haka tana lalube har ta lalubo kofar toilet din, Dan ma jiya da zatayi sallah nan tashiga shiyasa bata wani sha wahala ba,tayi abinda zatayi ta fito, lokacin har an idar da sallah a wani wuri, hasken da tagani ya tabbatar Mata da andawo da nepa, inda yake ta kalla yayi daidai Yana bacci da'alama kuma baccin ya masa dadi, parlourn ta fita ta dauko hijabinta da ta ajje jiya tana kallo, dadduma ta shimfida ta tada sallah sai da idar ganin beda alamar tashi yasata zuwa inda yake,ta fara bubbuga pillown da yake Kai,Amma ko motsi beyi ba,hannu tasa tafara,
cewa' Kai,Kai,Kai, Kai Ka tashi an idar da sallah,
Amma ko motsi beyi ba,haushi ne ya kamata Tama Rasa me zata masa ya yashi Kara buga pillown tayi amma a banza sai kara juyawa da yayi dayan barin ya juya Mata baya, wani takaici ne ya Kara kamata kawai takara sa hannu ,
tace' Ka tashi mun makara fa,kaga gari yafara wayewa Ka tashi,Kai Kai tashi, Ka tashi zaka makara fa Kai, Kai,
Ganin be tashi ba yasata nufar toilet ta debo ruwa a hannunta kafin ma tazo ya zube dankwalin kanta ta cire ta jiko da ruwa tana zuwa ta matsa masa Shi a fuska,
bawani firgita ba don tunda tafara cewa Kai Kai din nan ya tashi haushi ya ishe Shi wai kai,shine ma Kai,irin batasan sunansa ba,shiyasa yayi banza ya kyaleta yana jinta ta Shiga toilet yasan ruwa zata zuba masa shiyasa da yaji ruwan be firgita ba, Yana tashi kuwa ko kallan inda take beyi ba ya Shiga toilet.

Ita kuwa tabe Baki tayi ta cire hijabinta ta hau gado ta kwanta abinta,tana ji ya fito ya tada sallah daga nan kuma bacci ya dauke ta,
shima da ya idar da sallahr ko kallanta beyi ba koma zai kwanta yaga wurin ya Dan jike, kashe wutar dakin yayi yaje ya kwanta a bayanta ya juya Mata baya Yana kwanciya yayi bacci.
Chapter 34 · 0% Book details