← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 108

Sashe 78

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan Shi a rufe ya amsa da uhm,
Tace' Ka dagani,kaga kayi bako,
Shikansa tasa masa kasalar,ya dago da kansa yayi ya kalleta idanta a rufe take wannan maganar, a hankali ya tashi ya matso daf da kanta ya sunkuya daidai bakinta ya fara kissing nata, daga nan aka Lula..

Kullum sai tazo store din da suka hadu,kullum ne wannan babu fashi Amma bata ganin ko Mai kama da sune, haka zata karaci yawonta ta koma gida Sam Tama ji zaman garin ya isheta transfer zata sa a Mata tace aure zatayi tasan za'a mata, da wannan shawarar taje office dinsu dukda yau weekend Amma tasan za'a dace,
yakan je da weekend, aikuwa
Yana nan,
tana zuwa tayi knocking aka bata izinin Shiga ta shiga,
Ta zauna suka gaisa,
yace' Brr Amina yau kece haka?

Ince ba wani case bane ya kawoki,
Murmushi tayi kadan tace' komai lafiya, daman wata alfarma nake nema,
Yace' tame fah?

Tace' daman so nake amin transfer shine kawai,
Shiru yayi ya dawo gaban kujerar dakyau,
yace' barrister bawai naki ta taki ba, Amma kisani kina taimakawa dukda ba wani jimawa kikayi da fara aikin nan ba,Amma kin samu nasarori,cikin kankanin lokaci kinyi sunan a wannan wurin namu, mezai Hana kiyi hakuri kicigaba da zama anan din?

Tace' Barrister bazan iya cigaba da Zama a garin nan ba, idan transfern ya samu kawai amin, idan be samu ba kuma shikenan Zan ajje aikina ne gaba kidaya,
To meyasa?

Ko an maki barazana ne?

Karamar kwallar data zubo Mata ta share tace' ko Daya, is family issue,
Daga Kai yayi yace' nagane, to Zan taimaka maki, ganin kin samu din, ko munce aure zakiyi sai an bincika angani dagaske ne ko kuma akasin haka,
Wayar sa ce tayi Kara ya daga, yace' Ummu me kuma ya faru?

Daga can ummu tace' Abie kaga yusuf ko?

Wai bazai bane kudi naba, sai munje shopping din,
Yace' ni nace kar ya Baki, karki zubar,wancan Dana Baki ai zubuwar kikayi, sai kace Karamar yarinya, yanzu ko Abdullahi dayake karami bazai zubar da kudi ba Amma kemam Allah ya shirya mana ke,
Tace' to naji Mama tace' za'a je Dani dagaske ne?

Za'a Dani?

Ummu gaba kidayan ki ciwon kaice, ina ke ina zuwa?

Zaku fara exams din?

Tace' to shikenan yau zaka dawo ?

Kinsan ai idan na tafi kwana nake a waje, stupid ajje min waya,
Ajiyar zuciya ya sauke yace' Ummu Mita,
Amina dake jinsa, tace' 'yar kace?

Yace' eh babbar 'yata ce,Amma karamin gidan yafita yin abin masu hankali,
Murmushi kawai tayi tace' nagode sosai barrister,
Yace' bakomai fatan mu Allah yasa ayi nasara kisamu, Bama San Barin aikin Ku, muna bukatar ku,koda kuwa awani wajen ne,
Sosai ta Kara yi masa godiya daga nan kuma aka suka Dan taba hira a har Kar aikin su sannan tayi masa sallama ta wuce.

Basu suka tashi ba sai yamma, sosai sukaji su garau kamar babu wani Abu dake damunsu, wani irin farin ciki suka tsinci kansu, babu Wanda yayi wa Dan uwansa magana sai dai annurin dake fuskar su ya tabbatar wa da kowanne su beda damuwa, wanka sukayi sannan suka Rama sallahn su, daga nan suka dawo kitchen Mas'ud ya Shiga ya kwasu abincin ya dawo ya Koma ya kwasu musu plate da cup, ya bude fridge Dan ya dauko lemo ganin wani juice a jug yasa ya dauko shi ya kawo musu, ya zuba masu abinci, sun dauko zasu Sa a Baki sai suka hada Ido a tare suka saki wani malalacin murmushi suka furta
" Inni's favourite,
Sai kuma saka, Mus'ab yace' Ka tuna komai?

Ka tuna?

Mas'ud Yana murmushi yace' na tuna abinda ya kamata na tuna sanda ina wayo ba?

Mus'ab yace' na manta kamanin su, na manta,
Mas'ud yace' dude manta kawai,the best thing mun tuna mu suwaye, that's all, and gamu ga sistern, ga kuma bb, sannan ga Bros, wannan kadai ma sun ishe mu,
Mus'ab yace' inasan sanin inda suke,
Sai Ka daura damarar neman su,Amma nikam bazan iya ba, Allah ma yagani,bansan ta ina Zan fara ba,idan muna da raban haduwa ba yau ba ko shekara nawa ne zamu hadu koda kuwa su sun rasu ko kuma mu mun rasu, kaddara ce ta raba mu,kuma kaddara ce zata sake hada mu Insha Allahu,
Daga nan shiru sukayi suna cin abincin su, can mas'ud yace'wai suna ina?

Sun kyale mutane su kadai,
Mus'ab yace' Kai wai baza ka canza ba?

Tunda hali na Bashi da kyau ko?

Kaifa Ka renani,
Waye babba?

Naga nine babba ?

Karye ne,nine nan babba,
Naji na baka girman, nine Karami that's all?

Dade yafi, a to, mtsww,
Ka tuna ?

Mefah?

Manta kawai zaka tuna,
Damuwarka,
Damuwar Ka ce,
Aikuwa karya ne, damuwata daban damuwar Ka daban atoh,kuma ba damuwata bace,kamin shiru ina cin abinci ba'a San ana cin abinci ana surutu (
Banza yayi da shi sai da suka Gama, sannan suka kwashe kayan suka ajje akan dining, juice din da ta hada kuwa tas suka masa, sukayi wanke wanke,
Mus'ab yaje kunna kallo yaga game yace' Fav bro kaga game,
wacce iri ce?

Ps?

A,a wannan sega ce,
Jona mana, muyi, Amma football fah,kasanni na iya, kamar Renaldo haka nake,
Gaskiya Kam,a can cikin mafarkin tsuntsuye ba?

Wai Kai mekake nufi Dani ne?

Karya nake?

Yana cigaba da hadawa yace' ni na'isa?

Bankai matsayin ba,kaifa yaya ne Babban yayaaaaa,
Zama aka gyara aka Kara makewa ance masa yaya, Kai Mas'ud akwaita san girma.

Saida ya Gama Jona masu aka je gaban TV aka fara buga game.

Tun ba'aje ko ina ba, aka cinye chatty.

Da suka tashi wanka sukayi sukayi sallah, tace' Bakajin hayaniyar su?

Yace' kyalesu, idan mun fita ma ba abinda zamu musu,
Yace' yunwa fah nake ji,
Kaifa Kace Kar mu fita, kuma kayi wannan korafin?

Yanzu nace mu fita tou,
'yar harara ta zuba masa, zatayi magana ya Riga ta,
yace' karki damu Zan fashe yau din nan, da daddare ba sai gobe ba,
Ware ido tayi tace' kuma wannan dakayi fah?

Wannan ai na missing juna mukayi,kema kinyi,ko bakiyi ba?

Murguda Baki tayi tazaci Bai Ganta ba yace' nagani wannan,
Biyu Kenan, kicigab kece a ruwa Bani ba,
Tashi tayi ta saka hijabin Akan mini skirt din da ya dauko Mata Akan tasa Shi, ta fita tana gunguni, murmushi mugunta yayi yace' Zan fashe shiyasa Bana hanaki,kici gaba, aga waye mai riba sannan shima ya fito,
Taji mugun mamakin ganin su
suna dariyan nan suna game gefe kuma an ajje Apple ana yi ana ci, daskarewa tayi a wurin tana kallan ikon Allah har sun ware?

Binaif ne ya dafata tare da Mata side hug suna tafiya,
yace' muje muci abinci, ok?

Wucewa sukayi, sukaje zasu ci tace' Bari ayi warming tun safe fa Nayi abincin,
Zama yayi yace' yunwa nakeji, kafin kiyi na koshi,
Girgiza Kai tayi ta sannan tayi serving dinshi, tana cikin yi
yace'
Allah ya shirya ko?

Murmushi gefen baki tayi hakan yasa dimple dinta lomawa ta gefe Daya,
Irin Mata murmushi yayi hakan yasa
tace' me kake Shirya wa?

Jawo abincin sa yayi ya fara ci itama Zama tayi ta zuba kadan tana ci,
yace' me kika gani?

Naga kayi wannan murmushin gulman naka?

Ware ido yayi yace' ni ne gulman?

Tace' a,a nifa ba haka bane,kawai Nayi noticing ne idan kayi wannan murmushin naka to na..na...am...am,Ka gane ai,
Harara ya balla ya cika Baki da abinci, batayi magana ba Amma hararan ya mugun bata dariya, mazewa kawai tayi, sai da suka gama ta tattare kayan ta Kai kitchen ya dawo ta ganshi a wurin, Yana Shan ruwa,
tace' Yau muje mu siyo sauran abinda babu,
Wata hararan ya balla mata, dariya tayi tace' ashe Mr lizard ya iya harara haka ban Sani ba,
Tasowa yayi yace' waye Mr lizard ?

Zai kamata ta goce tasa gudu shikuma ya biyota, sai cikin parlour,
Tana gudu tana dariya tayi nan yayi nan zai kamata sai ta gudu, Mas'ud da Mus'ab tsayawa sukayi kallan ikon Allah yaushe ma da suka wuce Basu gansu ba,
Mas'ud be ankaraba yaji an taka masa kafa, ita kuma tayi tuntube da abinda suka ajje a tsakiyar su, kawai ta zauna a wurin tana dariya, Binaif Yana zuwa ya daga ta
Yace' wana kama?

Tana haki sosai tace' bakowa ba, a kasa ya ajje ta yayi sauri ya kwanta a cinyarta, suna sauke numfashi,
Mas'ud yace' idan na yarda na zama danda kwashi, azo a biyani a kafata,
Mus'ab yace' dadina da kai ragwanta kamar mace, harKa fi ma wata macen,
Yace' ehh naji sai dai kuma ni Bana tsoron kadangare bare cockroach aje ga su tsaka Ku ma, su oo da oo kwa ba'a magana,
Binaif yace' sai Ka Fadi Mai tsoron su ai,
Mas'ud yace' ga mutane dayawa, wata da tana karama tsoron fasifa kamar kamar me,
Tasan da ita shiyasa ta aika masa da sakon harara,
Yana gyara kafarsa yace' wallahi kinji min ciwo,Inga ma karaya ce,
Mus'ab yace' daman tun tana yarinya taje jima so sai kayi hakuri zo mu cigaba da game din mu,
Yace' kaidai Bari wannan yarinyar ai aljana ce na fada maku,
Babu Wanda ya Kula ya Kula Shi suka ci gaba da game, shikuma Binaif yajata da hira iya sune kadai suke Jin hirar su, sunayi suna kallan game dinsu, ganin ana cinye Mas'ud Binaif ya tashi,
yace' kawo nan babu abinda Ka iya sai shirme, kawo kaga yarda ake,
Bashi yayi yace' yawwa bb zo Ka cinye Shi,
Karba yayi Kai kace da gaske yake, Yana karba ana cinsa,
Mas'ud yace' bb ya haka?

Ita kuwa mezatayi ba dariya ba, ganin ana ta cinsu, ya sa ta tashi, taje ta zauna
tace' Ku kawo na maku,
Me kika iya ke kuma?

Ball ce fah na cin abinci ba,
Tace' chatty kadena Shiga harkata taam,
Kwace handle din tayi daga hannun Binaif,
Yace' bb ya zaka bata wai?
Chapter 78 · 0% Book details