← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 108

Sashe 90

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Baza'a hada biki nada Yara ba, Kai da budurwa ma Baka da ita,da kama iya zancen ?"
Baffa yace'' Mas'ud!"
Ai tuni ya tashi ya nufi kofa har Yana neman bigewa, ya fice,
Girgiza Kai kawai Baffa yayi, mus'ab yace'' to Baffa kadan Ka gani Indai wannan yaran ne"
Amina ce ta shigo tace'' Ya Mas'ud ya na ganka anan, azaune"
Yace'' kedai bari,leka min kika Baffa Yana nan?"
Shiga tayi taga Baya nan, hakan yasa ta juyo ta girgiza masa Kai, taso wa yayi ya shiga ya gan su suna hiran su Banda Ummusalma da idan ta yake a rufe tsab zaka ce bacci take, zuwa yayi ya zauna, Yana wani daure fuska,
Amina ajje coolern da ta shigo dashi tayi a gaban Ummusalma tace'' ki tashi kici, awara na siyo maki"
Bata tanka Mata ba, ta tashi ta sauko kasa, tare da cire Hijabin ta, ta zauna ta baje kafa tasa coolern a tsakani kafar ta, ta fara ci, gawani yaji Mai dadin gaske, data kawo Mata, gashi awaran da zafin fa Tasha kayan Hadi, ta fara ci tana zirawa,
Mas'ud yace'' Lalle ma Neena mu ina namu"
Dago Kai tayi ta kalli Binaif tace'' mi amor zaka ci?"
Murmushi yayi ya girgiza Mata Kai, yace'' kici ki koshi"
" Ke Neena wai ba Kiran ki nake ba"
Daga waje yaji tace'' Ina zuwa"
Mus'ab yace'' Lalle samun wuri, wai ni nayi kauwa"
" Oho de ba kauwar wani bace, twinny Dinna ce, Daman Ku Kala kuke da aljanu"
Ita de cin kayan ta take sai da ci tayi nak, ta cinye tas saura Daya jal, ta rufe Coolern ta Mika masa,
tace''
kaina bawa ba kowa ba"
Karba yayi Yana wani dar waje baki,
yace'' sai na tuna sanda kika bawa Fav..."
Maganar ce ta makale ganin guda Daya jal a ciki, ya dago yace'' wannan ai rashin mutun ci ne meya hakan?"
Batayi magana ba, ta tashi taje ta wanke hannun ta, tazo ta zauna, tayi refilling,kome za'ayi ayi.

Babu kowa a gidan suna zaune a daki suna tattauna magana iya su uku ne kawai,
Cikin wata irin fusata,
tace'' Wannan zancen banza ne, wanne irin Abu ne hakan?

Ace ta gudu, ta balle kofa?

Kai bazai faru ba inaaaa"
Tashi tsaye Anty tayi tana zagaye tace'" shekara talatin bata taba guduwa ba sai yanzu?

Me take shirya wa kenan?"
Dayar matar tace'' Dana tambaya ance min batayi ne suka shigo unguwar suka dirar wa gidan"
" Barayin su mahaukata ne da zasu Shiga wannan ribabban gidan?"
Shiru sukayi babu abinda suke sai zagaye a dakin, kowa da abinda yake tunanin can,
Anty tace'' nikam nagaji da zaman jiran haushe Alhaji zai mutu na kwashi dukiya nayi ta kaina, ina so fa na ganni cikin daular da tafi wannan, insan naganni ina juyawa ina fanjama cikin manyan mutanen Mata, Amma Shi Naga besan wannan ba, ina dalili kawai mutun yayi ta zaune a gida kamar jakin jahili?

Nagaji daman can ba San Shi nake ba"
Matar tace'' Hajiya bamu taba boyewa juna sirrin mu ba, ya kamata ace ki fada min yau dalilin ki na yin haka"
Zama Hajiya tayi tace''
Ban taba tunanin Alhaji zai so wata Mata ba Sama Dani, sai gashi yaso wannan 'yar fulanin, be fada min ba, amma ni nagane hakan, Yana San ta fiye da tunanin ki, tun daga nan na fara azabtar ta, sai na samu Allah ya zuba mata zurfin cikin mala'i tayi ciki har sau Uku ina barar Shi, wani zuwa da Zuwaira tayi Anty Kenan, kawai ta Bani shawarar na barta ta haihu da kanta zafa gudu tabar min gidan, daga nan sai kika bada shawarar a kashe dan kawai tunda shine zai Bani ciwon kai, sai kuma Zuwaira ta bada shawarar da wata shawarar sanini zata amfani yasa na bi Tata shawarar shine kuma data gudu aka kama ta aka Kai ta wannan ribabban gidan aka sa ta, kinji yarda akayi shine kike zuwa duk wata kike kai mata dan abinci naso ace wahala ta kashe ta da yunwa amma har yanzu bata mutu ba"
" Kuma bakwa tunanin wani yasan wannan zancen naku?"
" Sam Bama yi, tunda babu Wanda yasani sai ke"
Anty tace'' lokaci yayi da zamu kama gaba mu, tun kafin ma asirin mu ya tuno tunda ta gudu waya San inda zata tafi"
Hajiya tace'' shiyasa yanzu Nima nake so dukiyar sa"
" Idan kuka jira sai ya mutu to har asirin Ku zai tuno Amma Idan kuka kashe Shi fah"
Anty tace'' tabbas haka ne kisa ce ta kama ce Shi"
" Idan ya mutu kuma dansa bashi ba gadan sa, haka uwar sa ma"
Zama Anty tayi ta kalli Hajiya a tare suka furta" A kashe Shi kawai..."
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt
*A BAKIN WAWA
_Akanji magana_
```When life gives you a hundred reasons to break down and cry,show life that u have a million reasons to smile and laugh.

Stay strong.```
54
Wani makirin murmushi,Ya jima da sanin hadin da hadin bakin su, ya jima ya zargin su, Shifa ya auri Zuwaira ne dan ya kunta tawa Hajiya, Yana gani ai kawar tace zata ji zafin abun,ashe bakin su a hade yake wai yau Shi za'a kashe, murmushi yayi Mai sauti, yana tuna shawarar Yayan sa, dan wayar da yayi dashi ne yasa yaji komai ya tafi, ga kuma abin farin ciki da ya samu su Mas'ud, bezai bata komai ba,dukda ya tuno masa babban ciwon abun kaunar sa,
a hankali ya wani runtse Ido ya bude Yana tuno duk wani moment nasu, yau ya hadu da yayan ta, bema san
yarda akayi ya yarda zumunci haka ba,dole gobe yaje ya Kai gaisuwa.

Tashi yayi ya fita yarda babu Wanda yaji shigowar sa haka ya fita babu Wanda yasani sai dai yanzu Shi kadai ne, ya ansa key a wurin driver sannan ya yace yaje gida yau,
Wayar Binaif yake kira, a lokacin Binaif suna zaune suna cin abinci yaga Kiran Daddy, daga can,
Daddy yace ''Binaif Umma tana gidan Ka ko gidan ta ne?"
Binaif yace ''tana gidan na"
Daddy yace ''kai kana ina?''
"Ina gidan Baffa"
"To shikenan"
Kashe wayar yayi ya dauki hanyar gidan Binaif, koda yaje a zaune ya ganta tana cin abinci tana kallo, da'alama kawo mata akayi Dan yaga cooler a gaban ta,
Da sallama ya shiga, ta amsa ta ciga da abinda take yi,
A kasa ya zauna,
yace ''Umma ina wuni"
" Lafiya, ina ce kaman ta hanyar gidan dan naka"
" Umma ya za'ayi na manta kuma"
" Yoo naga tunda nazo ba'azo an gaida ni ba shiyasa ai"
" Umma jiya fa kika zo"
"Ai yanzu naga rana ta fito"
Shiru yayi ganin yau a Sama take, sai da ta Gama cin abincin ta,
tace'' Yanzu ma ba zuwan Allah da Annabi bane, kafin ka zo Dan uwan Ka ya sanar min komai da komai, kuma abinda ya yanke yayi daidai kaji ai"
Sunkuyar da Kai yayi bece komai ba sai
yace "amma Umma zaki koma gidan ki ko?"
" Bazan koma ba"
"Umma ya kamata ki koma, namma fa gidan jikane ba gidan danki ba"
" Ohh!

Bukulu zaka min, idan Baka sani ba, kasani gidan nan wani abincin suke ci Mai dadi yauma wata Kala Kala aka mana,irin 'yan can Mai dadi, shayi ma kadai dadi ne dashi bare abincin su, aitun tana can take mana abin dadi"
"Umma kinga be kama ta ace ni Ida zan gaida ke ba,kullum sai nazo Haba Umma Dan Allah kuma kinsan shima yaya Baya zuwa gidan 'ya'yan sa yanzu idan yazo shima nan zai zo?"
"Da wannan naji zan koma, dan kace baban su amma da Kai ne bazan koma ba"
"Nagode"
"Gode wa Allah"
Be wani jima ba ya tafi suna gama hira ya wuce.
Chapter 90 · 0% Book details