← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 108

Sashe 93

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Binaif yace, ''mun san wannan word din sai a canza wata as usual sai dai Ka rame".

Turo Baki yayi ya fara gunguni Shi kadai, Yana Mita, har suka je gidan Daddy a bakin gate suka yi parking sannan suka shiga, cikin gidan.

Suna zaune su Duka hudun kowa da waya a hannun sa Banda Fati wacce
take karatu da sallama suka Shiga ko daga Kai Basu yi sun kalle su ba bare su amsa sallamar, saida suka Samu wuri kowa ya zauna.

Binaif yace "Baku ji anyi sallama ba ?

Ko kuma iya amsawa ne baku iya ba?"
Sai da ya fada sannan suka dago suka kalli su ganin su tare da Ummusalma wacce take Danna wayar ta bata dago ta kalle su ba suka kalli su Mus'ab da Mas'ud a tare suka ja wani wawan tsaki, sannan.

Saima tace, "ai munga anzo da karuwa ne shiyasa, taya za'a mu ansa sallamar karuwar da ko sallah batayi ita da arba babu banbanci Dan bazan ce Christans ba sai dai arna arnan ma kafirai cikin su".

Ameera tace, ''abin takaici wai karuwa ce ta dake mu fah ko?"
Aneesa tace, ''ai watan cin uwar su ne ya kama tsautsayi ne ya kawo ta cikin gidan nan shima Binaif din ba tsoran sa ake ji ba 'ya Tama na rashin kunya wallahi mu balla ta a gun nan".

Fati de bata ce komai ba, Dan iskancin ta tana da tsoro shiyasa ma ta tashi sum sum ta bar wurin.

Binaif kuwa jira kawai yake su gama duk Wanda yayi magana idan sa ne yake komawa kan sa har yazo wurin fati ya zaci zata yi magana sai yaga ta fita.

So calm ya tashi ya nufi remote ya dauko ya tsaya yana Yana kallo ganin channel din da suke kallo Boom tv ta waka kawai, yasa Shi yayi murmushi ya Kara volume ya karade gidan, remote din TV ya hango a tsakiyar Saima da Ameera a Kan hannun kujera hakan yasa ya nufi wurin Yana zuwa ya Basu aune ba Dan Basu yi tsammani ganin sa ba ya Gwara kan su, Aneesa da tana magana tasa earphone sai wani karkade kai take sai Jin saukar sani lafiyayyan Mari tayi.

Duk abinda ya faru befi a cikin seconds ba, gaba dayan su gigice sukayi sun ma Rasa me zasu yi gudu wa ko kuma a kasin haka, kasa ya jawo su ya rinka ball dasu idan yayi ball dasu sai sun ture kujera a cikin lokaci kankani sun har gutsa parlour dan dansa yayi masifar baci kana gani zaka sa dukan da ya jima yana Tarawa ne be shi ba ya bude fridge ya dauko kankarori ya jawo su saitin goshin su ya rinka fasa wa akai ihu suke amma ba'a ji bare asan me suke yi sai da ya Kai ihun ma basa iyawa bare suyi azamar gudu wa ganin sunyi lakwas yasa Ummusalma kallan Mas'ud dake kusa da ita.

Tace "kaje Ka taimake su mana".

Alama ya Mata na Bana ji da hannu ya cigaba da kallan sa Yana gyada Kai, haushi ne ya ishe ta tama Rasa me zata yi kawai ta dungure masa kyeya ya juya ta kalli mus'ab da yasa earphone a kunnan sa ya kwanta Yana Danna waya, tsaki tayi ta tashi taje wurin Shi, rasa me zatayi ta Hana Shi dukan su tayi Shi kansa ya hada zufa ba kadan ba, samun kanta tayi da rungume Shi ta baya tare da hannun sa ta daura kanta a bayan sa tana sauke numfashi.

Runtse Ido yayi ya tsaya da dukan nasu Yana nishi, sai da ya dan saitu sannan ya juyo da ita ya rungume ta sosai kamar zai balla ta, ita rungume Shi din tayi sosai kamar yarda ya Mata, kansa ya kwantar a kafadar ta Yana Jin kamshin turaren ta Wanda a kullum yake Kara sa shi nutsuwa.

Sai da ya daidaita sannan nemi remote yaja ta kujera suka zauna, rage volume din yayi sosai sannan ya canza channel,
ya kalle su yarda suke wani tankwashe wa tsabar radadin da azaba kukan ma ya dena zubowa.

Yace, ''inaga biyo Ku zanyi na janyo Ku".

Bashiri suka nemi tashi sai dai ko rabin daga wa ma Basu yi ba, haka ma rarrafe kin yi yayi, sai da tafiyar miciji suja isa wurin shi.

Dauke yayi
Yana kallan Ummusalma ya nuna musu ita.
yace ''kunga wannan, Mata ce".

Dagowa yayi ya kalle su yace ''kinsan abind yasa na deke Ku?''
Girgiza Kai sukayi alamar a'a.

"I think dukan be isheku ba kuna nema Kari".

Dasauri suka ce "a,a bamu Santa ba".

"Daga yau Anty,daga yau me?"
"Anty".

Suka fada a tare murya can kasa.

"Oohh daga murya zanke yi Kenan ko?"
"A'a".

"Daga yau babu reni a tsakanin Ku da ita babu a tsakanin Ku da Mas'ud Mus'ab babu wannan respect nake so na fara gani kunji ko baku ji ba".

"Munji".

Wannan Karan da karfi suka fada.

Daddy yana waje daga Baya Yana Jin disco na tashi yazo Dan musu magana ganin irin dukan da Binaif yake musu yasa Shi ya koma da baya sai yaji kidan ya Ragu sannan ya nufo cikin gidan, a gaban Binaif ya gansu ga parlour an har gutsa sai ya samu kujera ya zauna.
yace, ''Ku kuma duk rawar ce haka kome kunzo kunyi zube a kasa sai kace Wanda aka dake ku gashi kun bata mana parlour lafiya?"
Saima da ta Dan tashi tace, " bakomai Daddy laifi mukayi aka hukun ta mu".

Yace, "Ku tashi Ku gyara parlour nan".

Babu zan cen musu suka tashi suka fara gyara wa dakyar suke aikin Dan sun jigata ba karya.

Gaida Daddy suka yi ya amsa musu Yana tsokanar su, sun jima sosai a gidan tare da Daddy sune har aka Kira la'asar sannan suka tafi.

A mota Ummusalma tace, "ina San na zama ta farko da Zan fadawa Yaya auren sa da Ummu".

"Idan kin isa na make ni zan fada".

"Sai Ka fada mugani ai".

"Ni daman an hada harda ke an zabga Dana ji dadi".

Binaif yace, " idan Baka kiyaye ni ranka zai Baci".

Mus'ab yace, "Gwara tun wuri kayi shiru kafin kaima a Baka naka kasan, don Naga bb idan Yana Duka manta a'ina yake".

"Fav idan aka min wannan dukan ba tabbatar bazan tashi ba woo Kai kaga duka?

Daman bb haka kake bamu sani ba taaabb".

"Ai ni babu ruwa na yanzu da Shiga harkar bb".

"Nima de kuwa amma bazan ce wannan aljanar Anty ba a haife ta a gaba na nace Mata Anty ita ko Dan yayan nan bata ce min".

Banza tayi dasu ta kyalesu, Hiran suma suke da Binaif har suka isa asibiti suna zuwa.

Mas'ud ya fita haka ita ma suka bar su Mus'ab a Baya...

By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt
A BAKIN WAWA
_Akanji magana_
Har wani sauri yake yi yaga ta wuce ta, Yana gaba tana bayan sa har suka isa dakin a kusan tare suka shiga suna Shiga suka ga su Yusuf a dakin Shi kuma Yana kwance yana kallan su suna fa Hiran su Banda Ummu Dan ca tace baza ta zo ba.

Mas'ud murya kasa kasa yace,
"kun fada masa?"
Yaseer yace, "a'a Ummun ce tace Kar a fada".

Wuri ya samu ya zauna ita kuma Ummusalma fita tayi ta Kira ummu a waya Jin abin da suka ce, tana daga wa.
tace, "me yasa kika ce kar a fada masa?"
Ummu daga can tana kwance a daki haka nan taji yau duk jikin ta yayi sanyi ga wata irin kunyar Uncle da take ji ta Rasa dalili tasan su Baba da Abie ba fada masa zasu yi ba tunda Binaif ne ya ruki da a daura din sun zaci zai fada koma ya fada.

Tace, "yaya salama fa kunya nake ji shiyasa".

Murmushi tayi har hakora ya fito dimple din ta ya loma.
tace, "yanzu de
idan Anty zata barki to ki fito asibiti ki taho min da abinci da freshyo".

"To Allah yasa ta barni idan nazo zan kira ki sai ki shigo Dani".

Murmushi tayi tace, "to sai kinzo".

Juyo wa tayi da murmushi a fuskar ta sosai kana gani zaka san abin ya bata dariya amma maimakon tayi sai take yin wannan murmushin, kicibus suka yi dashi yana tsaye Yana kallan ta ba wayar ta ta yake ba kawai kallan ta yake ta yarda ta Kara masa kyau da fari na musamman.

Daga masa gira Daya tayi tace, "kallan fa?"
Murmushi yayi Yana sa hannun sa a dimple din ta yace, "I miss you".

Ya fada Yana wani lumshe ido,cire hannun sa tayi tace, "kaga asibiti fa muke zake tabani salan wasu su fara thinking otherwise".

"And so?"
"Hmmm let's go".

Hannun ta ya kama suka Shiga ciki ganin su sun tare a wuri daya suna ta hira yasa suka karasa wurin gadan ya zaunar ta shikuma yaje ya tashi Mas'ud ya dauki kujera daya ya koma kusa da Shi ya zauna.

Ummusalma tace, "kunzo kun wani tare kuna damun marar lafiya haka ake zuwa dubiyar su Chatty harda tafa hannu sannu tou".

"Ai daman ni kika Rena ga marenin wayon ki duk wurin nan ki rasa Wanda zaki Kira sunan sa sai ni, Bari de Nayi aure nan duk Wanda Baya respect dina bazai je gidan na ba".

Binaif yace, "wai gidan nan nawa ne da Kai ne?

Gidan har yanzu be kare bane ayi ta fada ayi ta fada abar Shi haka mana".

Turo Baki yayi yace, "daman ai Ka kwace min kujera kuma kake fadar haka dole ai wallahi bakomai zaku gani ai idan anyi auren".

"Chatty Allah ya shirya min kai".

"Ji 'yar renin hankali?

Sai kace ita ce babba hmmm".

Mus'ab yace, "dude rabu da su kawai let's continue".

Ummusalma ta kalli uncle taga wani annuri a kwance a fuskar sa Yana murmushi kawai Yana kallan su kana gani zaka san kawai yana cikin annash wa da murna.
Chapter 93 · 0% Book details