Sashe 81
A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kin manta abinda yafi labe na koma ba labe ba"
" To meya kawo Ka?
" Daman maganar Sameera ce, nace kawai tunda ga su Yusuf nan suma zasu abinda zata yi,ko fiye ma da yarda zatayi, shine nace kawai a bar zancen ta hakan zaifi"
Za tayi magana Binaif ya matse hannunta dake cikin nasa kallan Shi tayi ya girgiza Mata Kai, alamar tayi shiru.
Tace'' to shikenan hakan ma zai yi,Ka barshi kawai"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da fezar da iskar bakin sa, kallan sa kawai tayi ta girgiza kai,
Binaif yace'' sai me kuma,ina mus'ab"
" Gashi can Yana shiryawa wai zai tafi"
"Ina"
"Abuja"
Tace'' okay, sai yaushe kuma?
" Oho masa, idan yazo ki tambaye shi"
Binaif yace'' Kai kuma fah?
" Ni Spain nake so na koma,akwai aikin da zanyi Dana wa dana twinny idan na tafi Zan jima gaskiya"
" Yaushe zaka tafi?
" Nanda sati daya"
" Ka Gama aikin da aka saka?
" Wannan ai ya gamu, sai dai wani kuma"
Tashi zaune yayi yace'' inaga tare zamu tafi"
" Kaima zakaje, harda wannan abar za'aje?
Binaif yace'' eh harda Antyn ku zamu tafi"
Bata fuska yayi ya tashi yace'' har nafara Jin wani ama-mai wai Anty, sai anjima"
Ya karasa fita, tace'' kaima kace wata Anty?
Taab kasan me kace ai"
Komawa yayi ya kwanta yace'' zamuje zata inga mi amor dinta yayi rayuwa ko?
" Ehh to kusan haka"
" Maybe mubi ta paris"
" Allah sarki sahr idan munje Dan Allah zan je gidan su, ban taba Kiran ta ba, gaskiya Bani da kirki"
" Damma ke kika fada ba wani ba''
" Eh naji din, Kira mana umma mu gaisa Banda numbern ta"
Wayar ya dauko yace'' nasan sai ta Gama zagin baba Usman tukunna"
Dariya kawai Ummusalma tayi, a speaker yasa wayar tana daga wa kuwa tace'' Assalamu Alaikum, nace batan hanya kayi?
Ko kuma bashi ake bina aka kira ni a tuna min?
Dan uban ka Adamu ba magana nake maka ba?
Yace'' Umma ina wuni?
" Ehh yayi baya da gudu be dawo ba"
" Haba Umma daga gaisu wa kuma?
" Naga na amsa eh?
Kai kaji yaro Ka kiyaye ni, meye kuma aka kirani ?
" Daman nace yaushe zaki dawo nayi kewar ki sosai"
Washe Baki tayi tace'' kaji yaran arziki ai kwanan nan
zan dawo ina zuwa sitiret sai gidan audushakuru bawan Allah Mai nema na"
Bashiri ya ta Shi zaune yace'' wanne gidan kenan?
" Kaji dan zakaraw'a kuma kake nema na?
Baka so na dawo ko?
To wallahi daga nan sai gidan ka, kaji dakyau, nace kaji ai"
Bata rai yayi yace'' daman ban Kira ba"
" Ba mutuwa zanyi ba,kuma ba yaushi zanji ba, daman ba Kira kake ba, munafikar matar Ka ce zata ce Ka kirani"
" Haba ummu me Mata ta tayi maki kuma"
" Ai wannan matar taka tayi ta sinne Kai wai ita kunya, idan tana yi sai kace wata tsohuwar munafikan da tayi sata aka kama haka take Kai Saima zatayi dariya a wani noke Kai ana taba abin hannu iwa sai kuma a danyi murmushi ace Kiki hmm hmm, wai dariya ce hakan"
Kallanta yayi da take kunshe dariya yace" umma Zan fada Mata fah"
" Dan uwar Ka safiya ai ba tsoranta nake ji ba"
" Gaskiya Umma kina da matsala"
" Nice gidan haya,nace nice gidan haya a matsala dan zakaraw'a Kai"
Yace'' kinga sai anjima nadena kuma kiranki"
"Hehehe audushakuru Kenan, daman ba Kira kake ba, Ka gaida dunkun Kumar matar ka idan kaga dama"
" Banida dankun Kumar Mata"
" Taje can ta sani maka"
Kashe wayar yayi yana bata fuska, kallanta yayi yaga ma dauriya take, yace'' duk ke kiga bada wannan shawarar ai, gashi nan zata dawo gidan ai"
Tace'' to ni menayi?
Pillow ya dauka ya wurga mata, tashi tayi daga kusa dashi tare da yi masa gwalo ta fita a guje, ya biyota yana kumbura fuska, a parlour taja ta tsaya ganin Mas'ud da Mus'ab yasa ta tsaya tana saisai ta dariyan ta,
Tace'' lafiya?
Naga glip da jaka ina zuwa?
Mas'ud yace'' ciwon mantau ya kama ki"
Binaif da ya karaso ko kallan su beyi ba ya samu wuri ya zauna.
Mas'ud yace'' me kika masa?
"Nasani?
Daga yin waya da Umma shikenan ya koma haka"
Mus'ab yace'' idan na biye ku baza Ku kaini airport din nan ba, sai nayi missing flight"
Tashi mas'ud yayi yacei kaga tashi na kaika a bamu key"
Tace'' Yana can parlourn"
Zuwa yayi ya dauko yace'' to muje''
Sallama ya masu suka wuce.
Zuwa tayi ta zauna a kusa dashi tace'' Mai gidanaaaaa,
Ta fada tana jingina da hannun sa ta daura kanta a kafadar sa,
Tace'' zo muje muyi girki"
Yace" sabida?
" Kaga wataran idan Bana nan shikuma sai Ka Shiga Ka girka abinka"
" Kuma ni barin ki zanyi kije wani wurin?
" Sosai ma,sai dai idan abu bai taso ba"
"Naji wannan, tashi muje muyi girkin to"
Tare suka Shiga kitchen suka fara aikin su, sunayi suna hira suna dariya abin su.
Yau za'ayi shari'a Dan haka da wuri kowa ya hallara a kotu Inda za'ayi daga su sai su babu wasu mutane,
Sun zauna kowa a zaune har alkali inda ya Gama Jin wannan karar ta Abba.
Alkali ya dubi Binaif yace''
Abdulshakur shin anyi haka?
Binaif cikin nutsuwa yace" anyi haka ya Mai girma Mai shari'a...
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
49
Alkali yace'' kana da ja a cikin?"
Yace'' ya Mai shari'a tabbas nasai company a hannun sa, sai dai kuma ba baka mu kayi dashi ba''
Alkali yace'' to meyasa kace anyi haka?''
Yace'' Nima bansani ba,haka kawai naji na fada Amma shine ya sayar min da companyn a hannun sa"
" Ina shaidu?"
Yace'' ga shaidu nan, barrister Ibrahim da Barrister Aliyu, dayan kuma be samu daman zuwa ba"
Kallan su alkali yayi yace'' a gaban Ku akayi?
Jinjina masa Kai sukayi, sannan barrister Ibrahim ya Dan rissina yace'' Anyi haka, sannan kuma shine yace bezo da takardun ba,sai gobe zai bayar"
Barrister Aliyu yace'' kuma shine ya bamu original din takardun wannan company"
Barrister Ibrahim yace'' kuma yanzu yazo yace besan zance ba?
Bacin anyi haka ya bamu ya sallame mu?
Akwai alamar tambaya anan ya Mai shari'a''
Shiru Mai Shari'a yayi yana nazarin abinda suka fada, barristern Abba yace'' ya me Shari'a wannan abinda suka fada ba haka bane, tunda sunce haka kawai su bada shida su hakan zai sa a gane waye Mai gaskiya"
Jinjina Kai alkali yayi kafin yace'' masu Kara da Wanda aka kawo karar ko sun zo da shaida?
Barrister Ibrahim yace'' ehh munzo d ita"
Sannan ya Mika masa, karba yayi ya duba, Suma su Abba suka Mika masa ya ansa ya duba, ya sosai, ya dago yace'' wannan takardun duka photocopy ne, kuma Yana yi da tsarin rubutun ba iri daya bane, hatta sighing din ba iri daya bane, ko Zan iya ganin original copy din?
Zufa ce ta fara ketowa Abba,da suka zo ai Basu ce masa su lawyers bane,kawai gaisawa sukayi, da sunce su lauyoyi ne da duk haka bata faru ba, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, alkali yace'' ina Original din?
Ya tambayi Abba Wanda hankalin sa gaba Daya Baya jikin sa,
Dakyar,
yace'' ya Mai girma Mai shari'a an barsu ai wannan sune original din"
Alkali ya bubi Binaif yace'' Kai fah,kana tare da naka shaidar?
Binaif yace'' eh ina tare da Shi"
Jakar sa ya bude ya dauko original copy din takardun na company ya mikawa alkali,karba yayi ya duba dakyau,
yace'' Zan iya karban wannan a matsayin sune na gaskiya, badan komai ba sai dan wannan takardun babu su yanzu''
Barrister Ibrahim yace'' kuma bugu da Kari ma shine ya bamu Shi"
Barristern Abba yace'' ya Mai shari'a wannan ba haka bane"
PA din Abba yace'' ya Mai shari'a tabbas mune muka basu, wannan takardun, a lokacin bamu taho dasu ba, sai washegari na Kai masa,nine na Bashi da hannun na, ina wurin ma ya bayar aka masa copy din shi"
Wani raza nannen, rikitaccan kallo Abba ya shiga yiwa PA din Shi besan sanda bakinsa ya furta "Inuwa??"
Ko kallansa PA beyi ba, ya make ya cigaba da bayani Sai da ya gama, Abba zaiyi magana,
Barrister Aliyu yace'' ya Mai shari'a wannan bashine Karo na farko da wannan bawan Allahn ya Saba yiba, ya yiwa mutane da yawa hakan, duk wani Wanda ya siyi kadarar Shi haka yake masa, haka a shaguna da dama dake cikin saban gari, da kuma kwari, du haka yayi musu"
Barrister Ibrahim yace'' sai sun zuba ma kudan kudin su, sun fara kasuwancin su, sai kawai yazo ya kwace, Basu da kudin Kai Kara, duka sun sa Shi a cikin kasuwan ci, kamar yarda Abdulshakur yayi,shima sai da ya bashi kudin companyn sa sannan yaga ya fara bunkasa yayi wannan aika aikar,
a duba irin ta'asar da yakeyi da kuma cin zarafi,kazafi, karya, caca, Da yake yi a biwa mutane hakkin su, ya Mai shari'a"
PA yace'' ya Mai shari'a duk abinda suka fada, tare Dani ake aikata wa nine jagora"
Idan aka ce ga tashin hankalin da Abba yake ciki, bata lokaci ne, Dan wata irin bugawa kirgin sa
keyi,ya rasa taka mai Mai zuciyar ce ke bugawa ko kuma de kirjinne ke bugawa?
Bekara tsinkewa da lamarin ba, sai da yaji, Barrister Aliyu ya kuma cewa'' sannan kuma ya Mai shari'a takardun gaskiya yake Basu Bana karya ba"
Mai shari'a wannan Abu ya daure masa Kai, Dan ya tabbatar da maganar su,
yace'' mun daga karar nan zuwa gobe, gobe azo min da mutanen da wannan abu ya faru da su"
Sannan ya tashi ya tafi, kowa tashi yayi Yana fitowa Banda Abba da lawyern sa, sai daga karshe suka fito kuma babu kowa, Abba na Shiga mota ya dafe kirjin sa, babu Abinda yafi komai ciwo irin cin amanar za Inuwa ya masa tambayar anan shine haka cin Amana take???
Ikon Allah!