← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 108

Sashe 75

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zatasa skirt din taga zani,ta juyo kamar zatayi kuka shikuwa yi yayi kamar be ganta ba, ganin haka yasa ta fara kiciniyar daurawa sai ta daura sai ta kunce, Yana tsaye Yana kallanta Sam bata iya ba, sai dakyayta daura shima bewani yiba, yade fi na Baya, harda sauke ajiyar zuciya Kai kace wani aikin tayi, sannan ya bata hijabi tasaka harda nikaf ta kunshe fuska suka fito,
Mas'ud yace' da tafiya zamuyi fah,
Idan kasan inda za'a tafi ko?

Yace' to meye?

Nasan inda zamuje ai,
Binaif da yayi gaba yace' Ku tsaya jaraba Nayi tafiya ta,
Mas'ud ne ya bude gate suka fita, sai da ya Shiga mota yace' wai bb baza'a samu Mai gadi ba?

Tace' muna dakai meye wani Mai gadi,
Mus'ab yace' aikuwa de kayi Kala Kala daman dasu,
Naushi ya Kai masa ya goce yace' bakasan a kule nake da kuba?

Taam,
Tace' Chatty na, munce fah kayi hakuri Kar ma Ka kwana damu kuma Ka margaya,
Yace' kut kuji muguwa? so kike na mutu Kenan ko?

A,a ni na'isa?

Bankai ba,
Shiru yayi ya kyaleta yace' laaa ga gidan budur wata, a ajjeni, tana Ka biyo?

Ashe fah unguwar mu daya,
Binaif kuwa yayi parking yace' to fito,
Haba bb daga fada kuma?

Irin fa abin nanne Kar a Rena ni,
Girgiza Kai yayi,ta kalle Shi tace' Allah ya shirya ko?

Kallanta Binaif yayi yace' keko?

Murmushi kawai tayi, suna cigaba da tafiya,
mas'ud yace' Ku hirar nan ma ta masoya bakwa yi,kun wani yi shiru,
Mus'ab yace' to idan zasuyi suna gaba ki zakayi?

Yanzu kaji me suka ce?

Ina ruwanka?

Kafiye gulma da sa Ido,
Mas'ud yace ansa idan,Kai na Sawa?

Ehh?

Bana San shishigi fah, Ka kiyaye ni,karami da Kai sai Shiga lamarin manya,
Inyeee sannu tou?

Babban Yaya,
Dariya Ummusalma ta kwashe dashi ta juyo tace' Glip kasan dazu da Ummu tace masa yayanah har wani bada Fadi yayi harda gyara Zama wai ance masa yaya,
Mus'ab yace' Ashe kin gani,
Ahh nagani ni ai irin Abu banann Bana mantawa dashi ai,
Mas'ud yace' kunsan de Zan Rama ko?

Binaif yace' aikuwa zakayibta ramewa, nikuwa nace Ka Rama marinka?

God bless you BB ba Rama ba Amma very soon za Rama tacigaba da Shiga min hanci idan na tashi fato ta fitt zan
fatota, kici gaba,
Tace' bakyau de tuna abinda ya wuce,
Wanne Hadithn?

Zaki ce ba kyau?

Banza tayi da Shi, ganin inda suka zo yasa yace' laa gidan Abban Khalid,
Da bakinka kamar na loro,
Kwafa yayi yace' naji Tou,
Horn yayi Mai gadi ya bude masu suka Shiga, yayi parking suka fito su agaba sukuma a baya da sallama a bakin Shi ya Shiga, amsa masa akayi,
Matar gidan na zaune da yaranta mata mazan sun tafi masallaci,
tace' wanake gani haka?

Muna da manyan Baki gaskiya,
Karasowa
suka yi
tace' Ku zauna zauna, sai da suka zauna yaran suka gaida su suka tashi, sannan suna suka gaisa
tace' Baku da kirki Sam Binaif shikenan tun bayan rasuwar Ummi befi zuwanka nawa ba, shiru babu amo ba labari sai kawai mukaji wai kayi aure,
Sunkuyar da Kai yayi yasan be kyauta ba Kam, tace' shima a wurin Safiya naji, haka akeyi?

Takalli su Mas'ud tace' Ku mahaka da kuna Dan zuwa De amma daga Baya sai yayan Ku ya koya maku rashin kirkin Shi ko?

Shiru sukayi, Basu tanka ba, Binaif ne yace' ayi hakuri Hajjo Insha za'a gyara,
Tace' a'a yanzu ma idan ba sa'a Amarya ce,tace azo,
Murmushi Binaif yayi yace' Bari muyi sallah,
Tace' kuje to sai kun dawo,
Tace' Amarya ya sunanki?

Tunda ko gayyatar mu ba'ayi ba,
Murmushi tayi tace' Ummusalma,
Kice sunan manyane,Bama fada ba, to muje daki sai kiyi Sallah ko?

Tashi sukayi tana binta a baya har sukaje dakinta,
Tace' kiyi ko?

Sannan ta fita, toilet ta Shiga ta watsa wa fuskar ta ruwa Dan Kar ace batayi ba, ta rike Nikaf din a hannu, ta fito ta zauna, ta jima a zaune sannan aka shigo da abinci, sai ga Hajjon nan ta shigo itama,
Tace'sauko kici abinci,
Ummusalma tace' a'a na koshi,
Bazade kuci ba,daga ke har su ko?

Murmushi tayi tana,kanta a kasa,
Ummusalma tace' Anty ummi fah ?

Hajjo tayi murmushi tace' Ummi duk inda aka Kai mace Ummi ta Kai, Tunda aka auri Ummi bamu taba samun wani sabini ba,duk muna zuwa can Spain Amma ita bata zuwa nan,duk zuwan da zamuyi ko zaizo to zata bada tsaraba akawo min, haka zaiyi ta Mita Shi bayasan Kaya, Amma a haka take aiko min, ban dauke ta a matsayin kishiya ba, haka kawai na bata wani matsayi na kawa kuma 'yar uwa, ni kaina naji rasuwar ta,
Tace' kinsan tana da ciwon zuciya?

Bansani ba,sai da tazo nan da bata da lafiyar nan Amata aikin nan taki sai bayan ma ta rasu nake ji,
Tace' kayanta nacan fah?

Suna can ai,ba'a dauko ba, dayake har yanzu Yana zuwa jiya ma ya dawo daga can Spain din,
Tace' zoki gaisa da Alhajin,
Sannan ta taso suka Shiga parlourn sa, anan suka ganshi suna ta zuba shida su Mas'ud, Shigowar su yasa su yin shiru,
Gaisawa sukayi
dayake a kasa ta Zauna,
yace' Mai sunan Manya da kin zauna asama ni ban surika,
Hajjo tace' aikuwa de mu nan ba'a mana wannan kunyar kode,
Daga nan kuma aka fara hira duk Rabi na Anty ummi ne,
Sai wurin karfe goma sannan suka masu sallama suka tafi,
A mota suna tafiya tace' Zan sha ice cream,
Yace' wayace maki idan ana period ana Shan Abu Mai sanyi? .....

By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
Tace' sabida me?

Yace' Shan abun Mai sanyi sosai sanda ake period yana da zubar Shi a bangon manhaifa bayan wasu shekaru, zai jawo uterus cancer or
tumor,
Tace' ya akayi kasani?

Be kamata ba ko?

Ni nasani ke Baki sani bako?

Nidai bance ba,
Yace' cin cucumber ma Yana Toshe wasu abubuwan period a bangon mahaifa hakan na iya sa Miscarriage,
Shiru tayi bata kuma cewa komai ba,
Mas'ud yace' wai me kuke cewa sai wani kuskus kuke yi kudai, mu ba mutane bane baza'ayi da mu ba?

Mus'ab yace' menace maka?

Daman ai na fada maka dazu dazun nan,
Mas'ud yace' ai naji yanzu,kaga wannan Mai fuskar masallacin nan kaidai a barta kawai,
Tace' chatty Ka dameni,Zan sa a ajje Ka, kabani a hankali tam,
Yasan shima ba karamin aikin bb bane ya sauketa shiyasa ya canza maganar da cewa'' wai yaushe Ummancy zata dawo ne,
Mus'ab yace' Umma ita da garin nan sai bb ya haihu,
Sai bb ya haihu ko sai waccan aljanar ta haihu,
Sai kuwa ya dawo tsakiyar su,
yace' yaushe zaki haihu da?

Juyowa tayi tace' gobe,
Hhhhh gobe fah, kina wasa kyanta ace bayan sallan cin nama ki haihu, kuyi addu'ah yaran nan yayi kama Dani, zakuji dadin Ku,
Kaga Ka koma baya,kana cika min kunne da surutu kawani zo Ka zauna a tsakiya sai kace wani yaro,
Laaaaa gwara ni ai badaga Baya bakina ya bude ba, ato
Binaif yace' chatty Ka fita idona, na fada maka Baka ji ko?
bb why chatty instead of Ka hanata fada Amma shine kake fada?

Haba bb,
Mus'ab yace' kaima Ka hakura kayi shiru kaki,
Juyowa yayi yace' Kai bafa nasan reni, Ka kiyayeni kasan na wuce Ka ko?

Dame Ka wuceni?

Budurwa mana,
Atare su Duka ukun suka saki tsaki, Mus'ab yace' Amma lalle ma dako hiran Baka iya ba?

Kai nifa yanzu Zan iya hira da yarinya, sabida wurin aikin mu wayanci Matane, kagane?

Fada a Baka ba?

Suna yi har suka karaso gidan mus'ab ne yaje ya bude gate, yayi parking suka fito suka Shiga ciki, a parlour suka zauna ta jingina da jikin sa, gyara Mata yayi ya kwantar da ita a cinyarsa ya cire Mata Hijabi, ya fara shafa Mata Kai,
Yace' bacci?

Daga masa kai, tayi alamar eh,
Yana kallanta yace da su,
Ya aikin Ku,
Mas'ud yace' aiki ta fara wannan aljanar?

Dagowa yayi ya zabga masa harara,
Mas'ud yace' a,a fah Naga ita kake kallo to na dauka magana kuke,
Mus'ab yace' komai Yana tafiya Normal,
Mas'ud yace' ehh haka ne komai qalau qalau,
Mas'ud ya tashi ya Shiga kitchen ya hado cornflakes yazo Yana sha,
Mus'ab yace' Ina nawa?

Kace kana so ne?

Amma kasan idan nine da Kai Zan hado ko?

To ban hado ba,kowa yana da hannu,kafa,Ido,sai kaje Ka hado nadena yiwa Gauro bauta ato,
Mus'ab yace' na Shaka, time will tell,
Shima tashi yayi ya bude fridge ya dauko yaga fruit salad ya a cikin bowl kawai ya dauko, ya dauko spoon, ya fito,
Ya zauna yana sha,
Mas'ud yace' Kai, meye wannan kake sha?

Kuma ko Ka hado Dani ko?

Dan tsabar rowa, Bama hadowa kayi ba wannan dauka kayi, Dan banga Ka jima ba,
Dora kafa yayi Akan center table Yana shan Kayansa,sai da yasha spoon biyar ya dago,
yace' kasa Gauro Shi daya yake hada abincin sa, sai hakuri fah,
Binaif girgiza Kai yayi ya dauketa da ta Riga tayi bacci yayi dakin sa da ita, fitowa yayi ya gansu suna dramar su, ya wuce dakinta ya dauko mata kayan bacci, yazo zai wuce,
yace' idan kun Gama ga key nan ku dauki nan Ku rufe mana gida sai da safen Ku,
Sun jima suna dramar su sannan suka tafi daki, shima a dakin sai da aka sha rigima da suka kwanta kuma aka fara hira.

Sai da yayi shirin baccin sa tsab
yasa mata rigar baccinta
dukda yasan ta
tashi dama bawani dauketa yayi sosai ba, ya kashe wutar dakin, ya kwanta ya janyota, tana gaba shikuma Yana Baya, hannun sa na yawo a jikinta,
yace' nafa dauki shawarar Mas'ud,
Shiru tayi irin Mai baccin nan,
Yace' ohh baza kiyi magana ba ko?

Namma shiru, yace' to shikenan Bari Nayi abinda bakya so, tunda kinki kulani,
Da sauri tace' na'am me ma kace?

Murmushi yayi yace' ai kinji,
To wacce shawara ce wannan?

Ya Baka kuma?

Ya kamata ki haihu bayan layya, aikin Santa,
Tace' kaiko?

Danayi me?

Daman Nayi missing dayawa gobe ne ko?
Chapter 75 · 0% Book details