← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 108

Sashe 77

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafe bakinta yayi da Ido, ta bude Baki zatayi magana Kenan taji nashi ya ciki, sun jima suna aikawa da juna sako, Vai din kanta ya jima da fita,sai kuma ya saketa ya rungume ta zuciyar Shi Yana bugawa da sauri sauri, sai da ya daidaita kanshi
yace' ya naji lema a kanki,be karasa bushewa ba,
Turo Baki tayi tace' to tunna jiya ne,
Yace' ohh haka ne fah, Amma Zan duba da kaina sai na tabbatar,
Saida ya sankan ce, tace'
Haka Yana da kyau Mr lizard,
Ta zari Vail dinta tayi waje da gudu, murmushi yayi tare da girgiza Kai ya Shiga toilet ashe ko ruwan ma bata hada ba, kafin ya fito ta gyara dakin ta fece.

Tana zaune a parlour ya fito yace' ke Daya ina suke?

Tace' ba key ban ganshi ba, kuma Basu zoba,
Daki ya koma ya dauko key din ya bude kofar,
yace' jeki kirasu,
Tashi tayi ta fita tayi knocking a bakin kofar su shiru,da karfi tayi daga can yaji,
Mas'ud yace' wai waye ne?

Sarai yasan itace, shiyasa ya fada haka,
Zuwa yayi ya bude yace' kinzo kin dameni, lafiya?

Banza tayi dashi tace' kalla agogo,
Tare da balla masa harara ta wuce tayi tafiyar ta,
Komawa yayi ya Kira Mus'ab suka taho tare a hanya suka tarar da ita,
Yace' ohh mutum na tafiya kamar Hawainiya, ko snail ande ji kunya,
Bata kula shiba ta bude kofar tashiga tana shiga Binaif yace' yunwa nake ji, akawo mana anan,
Turo Baki tayi, ta wuce Shi ta je ta dauko abincin a dining ta ajje ta kuma komawa ta dauko ta ajje, sai da tagama Shirya komai sannan tazo ta zauna ta zuba mash ita da Binaif ta tura masu gaba su,
Saukowa sukayi kasa Binaif ya matso daf da ita ya hade a plate daya ya fara bata a Baki,
Mas'ud sakar Baki yayi Yana kallan ikon Allah,can de ganin bazai iya daurewa ba, yace' bb bafa hannunta ke ciwo ba, kawai tsabar tabara ?

Wannan jibgegiyar katuwar uwar?

Mus'ab yace' wai Kai ina ruwan ka ne, kaga a irin haka tam,
Yana cin abincinsa yace' barni nagani na Tanka ato,
Cigaba da bata yayi,itama ganin haka yasa ta dauki fork ta bashi ya bata ta bashi, sai can,
tace' wani waye yace Baya cin cheaps da kwai?

Binaif yace' wani ne Mai kama Mas'ud,
Mas'ud yace' ni?

Yaushe?

A'ina?

Wacce Rana?

Tace' waida fah wani ne m yace hakan amma yanzu harda batar hanya,
Mintsinta Binaif yayi yace' dawa kike?

Ouch!

Da zafi fah,kamar cinnaka,
Mas'ud yace'
Kujita irin tasan cinnakan nan,
Mus'ab yace' da cinnakan ya manna maki gwara kunama ta Dana maki,
Tace' Amma a wurinka ba'a wurin salama ba, ato,
Binaif yace' Cinnaka da ya ciji Mas'ud ranar bamuyi bacci ba,tsabr ragwanta,
Mus'ab ya kwashe da dariya yace' bb ranar kuwa kunama na cijeni Nima,
Binaif Yana murmushi sosai yace' wai fa da kunama ta ciji Mus'ab da yayi kuka sai yace masa Twinny bafa nasan ragwanta 'yar kunama ce fah,amma zaka damemu, sai gashi a ranar shima cinnaka ya manna masa, kinga tsalle?

Kinga kuka?

Ummusalma tayi dariya tace' ande ji kunya,
Mus'ab yace' washeri da kuna ta harbeshi,mune har asibiti, akayi alura Umma tace ya sha kwai danye, yace zai sha ba,Dan mutumin ki cikin dare ya Bani bacci Sai ganin sa Nayi a kitchen ya sha kwai Bakwa,
Mas'ud yace' sharrin ya isa haka,kunga na maku shiru ko?

Binaif zaiyi magana wayar sa tayi Kara, Ummusalma tace' kaima kaji kunya,
Yace' bankai mijin ki ba, Shi a tsoro ma farar Kura
ta fishi jarumta,
Tashi yayi ya fita yace' ga shinan yazo,
Tashi sukayi suna tattare kayan, tace' kuma ku wanke mun,
Mas'ud yace' ni bacci zanyi a Parlour nan, zaiyi dadin bacci,
Tace' bayan an wanke mun kayana hakan zai faru, kuyi sauri mana,
Sai kace wata uwar mu wani muyi sauri anki ayi saurin,
Sannan yayi gaba,daman Mus'ab yana kitchen din ya fara, ita kuma wurin ta Dan gyara sannan ta koma daki,.

Shigowa da bakon yayi parlour ya zauna yace' Bari akawo ma ruwa,
Sannan yayi hanyar dakinta bema ji abinda yake cemasa ba, Hijabi tasa har kasa tafito suka gaisa Yana kallanta, ta wuce taje ta dauko masa ruwa da lemo ta ajje,
Binaif yace' Ina su Mas'ud kirasu, su gaisa,
To, tace,
Kitchen ta koma taga har sun Gama tace' Anya ba jika jika kukayi ba?

Turo Baki mas'ud yayi yace' Baki aiki sai sa mutane aiki,
Dalle masa Baki tayi tace' wa keyiwa haka?

Kutruuuu,Kan baban wani kangon gidan?

Ni ?

Ina yayannaki?

Hannu ya kawo ya Rama,ita ta Rama,zai Kara ramawa ta fito da gudu tana dariya Sam Tama manta da wani bako a gidan tana zuwa bayan Binaif tayi,
tace' wai sai ya rama,
Bakon kuwa tunda suka fito da gudu ya juyo tare da tashi tsaye Yana kallan su babu tantama wannan Mas'ud ne,ga kuma Mus'ab Daya gani a bayan su,
Mus'ab kuwa wani tunaninne yazo masa wannan abun ma ya taba faruwa,
Binaif yace' wai meye hakan,
Mas'ud yace' dukana fah tayi Duka fah?

Sai kace kanninta?

Ko ita yaya tace,
Jiyayi ance MAS'UD? da wata murya kamar ya Santa, sannan kuma aka yaji ance MUS'AB?
a hankali ya juyo ya sauke su fes a bayan Alhaji Munir da ya juya ya furta sunan Mus'ab,
Mus'ab nuna Shi ya farayi da hannu Amma yakasa furta ko kalma Daya ce, juyowar da yayi ce yasa Mas'ud shima fara furtawa Yana nuna Shi da hannu Amma sun kasa fadar sunansa........
~```Fahh fahhh & Waleeda this is for you
It's your lunch,```~
By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt
A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
```Iife is an adventure!

Live it while u can.

You can never have today again, tomorrow only comes once,and yesterday it's gone forever.

MAKE your choice wisely,then live the adventure you create...!

Such is life...
```
Ture Binaif tayi dake gabanta ganin Mas'ud zai fadi,ta taro Shi sai dai ita ma kusan faduwar sukayi da sauri Binaif ya taimaka Mata, mus'ab kuwa sulalewa yayi a wurin, sannan ya suma, wurin sa ta koma tana taba Shi ya tashi Amma shiru, gaba kidaya ta rude ta hada zufa tana kuka cikin kankanin lokaci,
Alhaji munir yace' Shiga da ita ciki, I will handle this,
Shiga yayi
da ita zai fito ta rugungume Shi tana kuka, sosai
tace' sun mutu ko?

Girgiza Mata Kai yayi ya cire Mata Hijabin yace' zasu ta Shi fah, kinji?

Karki damu,
Daga masa Kai kawai take Amma ta rikeshi gam kaikace abin tsoro tagani, dakyar da dabara sannan ya fita,
A kujera yaga ya kwantar dasu, ya matsa kusa dashi ganin yana tofah masu addu'a a cikin ruwa, Zama yayi a kusa da Mas'ud ya rike hannunsa Yana kallan yarda ya hada wani uban gumi, meko masa ruwan addu'ar yayi,
yace' shafa masa a fuskar Shi da kanshi, sannan Ka yayyafa masa a jikinsa,
Tasowa yayi ya ansa ya koma ya daura kansa a cinyarsa ya fara shafa masa a hankali kamar Yana tsoron Kar ya farka, yagama kuma ya yayyafa masa a jikinsa, wata wawar ni'imtacciyar ajiyar zuciya suka sauke a kusan tare.

Sunjima a haka Basu San lokaci ya tafi ba, suna zaune kowa da abinda yake sakawa ransa, can sukaji Mus'ab ya fara juya kansa da sauri da sauri Yana magana, Inni,Inni,Inni,Inni,Inni,Inni, inniiiiii sai ya tashi zaune Yana sauke ajiyar zuciya sai nishi yake, can kuma ya fara addu'a ya koma ya kwanta Yana kallan Sama, sai da ya natsu,
Sannan a hankali ya bude idansa da sukayi jaaa, ya sauke su a Kan Alhaji munir, Kara rufe idansa yayi ya bude a zuciyar Shi daman ba mafarki nake ba?

Kara rufewa de yayi ya bude, harda su murza ido ganin shine de yasa ya tashi zaune,
yace' Uncle Muniiiirr?

Sai hawaye kuma,a hankali a hankali komai ya fara dawo masa sosai yaji kansa na Sara masa kamar ana buga guduma zai tarwatse, kama Shi Alhaji munir yayi yace' koma Ka kwanta, beyi musu ba ya koma ya kwanta,
Alhaji munir yace' ya kamata muyi sallah Naga lokaci ya ja sosai,
A hankali ya ajje Shi Akan kujera,ya tashi ya nuna masa wata kofa,
Da alama toilet ne, alwala sukayi suka yi sallah,
Alhaji munir yace' ni bana wuce yanzu,
Binaif yace' Ka tsaya kaci ko abinci ne,ko ruwa Baka sha ba,
Yace' a,a Abdul wucewa zanyi idan Allah ya kaimu gobe Zan dawo so ba dutse Zan koma ba, ina da Dan wani aikinda zanyi anan din,
Binaif yace' to shikenan Allah ya kaimu goben,tare suka fita suka ya raka Shi har bakin motar sa ya bude masa gate Sai da yaga ya tafi sannan ya dawo, dakinta ya wuce ya Shiga ya ganta a Kan sallaya ta kudundune, karasawa yayi ya dauketa ya Dora Akan gado, Yana daukanta tana bude Ido daman ba bacci take ba,
tace' sun tashi ?

Girgiza Mata Kai yayi yace' bacci suke,
Ajiyar zuciya ta sauke ta Kara lafewa Akan gadan,
Rigar jikin Shi ya cire ya cire Mata Hijabi yace' wani idan aka min kwalliya sai a wani kawo mayafi a maka akai, a kawo hijabi asa haka akeyi?

Turo Baki tayi batayi magana ba, gadan ya hau ya rungume ta, ta yarda bata so, ya daura kan Shi a kirginta ya daura Mata kafa,gashi ya rungume ta sosai, kanshi ya fara shafa a hankali,
tace' kasan de bana San haka ko?

Yace' me?

June,
Dagani to,
Naga de kema haka kike min,to laifi ne dannayi Nima?

Meye aciki,
Ni bahaka nake maka ba,
To ya kikeyi?

Kada gani sai na fada,
Ehhhmm naji wannan,
Ajiyar zuciya ta sauke, ta rufe Ido,Sam bata San wannan kwanciyar da ya keyi ita kadai gasan me takeji, gashi Baya Zama wurin Daya da kansa yayi nan yayi nan, Kara Jan wata ajiyar zuciyar tayi, murya kasa kasa, cikin wata irin kasalar da ta dirar
mata tana
shafar kansa,
tace'
Baby!
Chapter 77 · 0% Book details