← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 108

Sashe 45

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta tafi bata taba zuwa gida ba duk mace macen da ake da biki bikin da ake bata taba zuwa ba, sai da zata rasu tazo anan ta rasi abinta, sannan shima Adam Bansani ba ko Yana zuwa, ko Baya zuwa inda ya Kara aure ya auri wata 'yar kano har ya haifi 'ya'ya goma Duka Mata,yayinda yanzu Usman Yana da yara hudu biyu Maza biyu Mata Matan kusan sa'anin
su Mus'ab ne mazan ne zakuyi kai daya dasu, ban Baki labarin suba nasan Umma tabaki watakil nikuma 'ya'ya biyu Allah ya bani alokacin da na fitar da rai ga samu,Nafisa da kuma Ummi mai sunan Ruqayya,
Numfasawa tayi tace' yanzu kinji komai ko?

Daga Mata Kai tayi sannan tace' Amma me ta rubuta ajikin papern data Bari?

Anty safiya tace' ca tace kar a nemeta kar kuma a fadawa danta Yana da uwa.

Ta tafi tayi nesa da gida Kar kuma akai danta wurin Yan uwanta a bawa babansa, sannan asawa Danta sunan Kakanta Abdulshakur Kenan,
Amma abinda yabawa kowa mamaki irin yarda Ruqayya ta Hana kowa Binaif ta riki Shi gam ta Hana to dayake sun shaku sai ake ganin kamar shakuwar ce tasa haka,
Ummusalma tace' kinsan unguwar su a Adamawa ?

Nasani sosai don muna yawan Kai masu ziyara ma,
To yayanta fa na nan kano?

Gaskiya shima tun lokacin nan befi da wata ba shima da mukaje akecewa ya koma London daga nan de zumunci yayi karanci shima kansa Adam din inaga beda numbern sa ma.

Amma
je gaskiya Amma Bansan Adam ba,
Ummusalma tace' A ina suke to a Adamawa?

Fada Mata inda suke tayi tace Amma Bansan ko sun tashi ba,
Shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa a ransa Anty safiya tace' kinga Bari naje bangaida kowa ba,
Ummusalma tace' Zan iya tafiya da wannan?

Tafada tana nuna hotan hannunta,
Daga Mata Kai kawai tayi ta fita, itama Ummusalma fitowa tayi daga dakin takoma dakin Nafisa, ta kwanta tana tunanin wannan lamari, Nafisa ce ta shigo tana kuka ita da Ummi sai Ahmad a bayansu, tashi tayi zaune,
tace' Nafisa lafiya kuwa?

Bata bata amsa ba tacigaba da kukanta, Ahmad kuma Yana rarrashin Ummi Yana bata chocolate wai tayi shiru, hannunsa ta janyo,
tace' me yafaru?

Yace' Hajja ce tasa su kuka, daman Kullum idan sukaje sai ta daki ummi wai tana Mata barna,
Wacce Hajja?

Kakar muce, bata San Mommy itama mommy kullum sai ta fada Mata magana idan kuma bataje gaisheta ba nanma ta ringa fada,kuma ita Anty Hauwa ba kullum take zuwa gaidata ba,
To meyasa take masu haka?

Nima bansani ba sai dai naji tana cewa mai kashin tsiya bata haifi yara ba lokacin da ake so sai yanzu, haka kullum take fada, Mami na ce kawai kawarta shine itama ta dena sonta,
Shiru yayi yace' Nima kuma Bana Santa idan na girma daman soja Zan Zama wallahi harbe hannunta zanyi kowa ma ya huta,
Meyasa zaka harbeta?

Kakar kace fa?

Ummi fa take Duka kullum kullum sai ta duke ta,
Abun ya bata mamaki Bama Maminshi da ba'a soba a'a don ana Duka Ummi, sunkuyo wa tayi daidai kunna sa,
tace' kana San ummi ne?

Ta fada da Dan murmushi a fuskarta,
Shima cikin rada,
yace' taya kika sani?

Murmushi tayi tace' Ganewa nayi,
Tace' yanzu tunda kana Santa mezai Hana muyi wani Abu,
Hannunta ya kama suka fito parlour ya jata ta karamar kofa
suka fita wurin kamar hutawa ne haka yayi kyau ya kawatu suka zauna a kujera,
yace' kinga anan Yaya Abdul yake hutawa shima saboda Hajja yadena zuwa,
Waye haka?

Ya Abdulshakur,
Shiru tayi bata Kara magana ba ganin haka yasa Shi
cewa' kika ce muyi wani Abu?

Me Kenan?

Tace' soja kake son Zama ko?

Daga Kai yayi tace' soja bashi da tsoro, ko kadan kasan me zakayi ?

Yace' a,a
Tace' to farko Ka fara zuwa Ka tambayi Hajja dalilin tsanat da takewa Momy idan ta fada maka ,sai kazo Ka fada min nikuma Zan fada maka abinda zaka fada Mata.

Yace' to shikenan yanzu?

Tace' a,a ahankali zamu bi abin ai,
Yaron ya birgeta bakadan,sosai ya Shiga ranta sai take ganin kamar Yusuf sanda Yana karami shima akwai wayo da bin kwakwafi, shafa kansa take yarda yake zuba Mata surutu tana murmushi tana shafa kansa kaunar yaron taji sosai ta Shiga ranta, har wani hadawa yake da hannu idan Yana Mata bayani.

Da daddare kasa kwanciya tayi tana juya labarin a ranta mekenan?

Gaba daya komai tana da Karin bayani Inama ace Anty Ummi tana da rai, da duk amsar tambayar nan tana dasu, bata kwanta ba sai da ta tabbatar ta Gama duk wani Abu da zatayi,
Washegari da tunda asuba bata koma ba dayake ta fadawa Anty safiya zataje ta fadawa kawayenta kafin a fara gyaran jiki, Kuma ta yarda ta amince ita da kawarta zasuje ta kirashi wai ta fada masa, shiyasa bata koma ba, tayi shirin ta tsab tasa kayanta kalla uku da Abubuwan bukata fitowa tayi ta fadawa Anty safiya cewan zasu tafi don su Gama da wuri su dawo,
Anty safiya tace'to Allah ya kiyaye Banda shirme de Ummusalma kinji ko?

Murmushi kawai tayi,kudi Anty safiya tabata
tace'
gashi inji mijinki,
Karba tayi tayi godiya ta fice,tana fita ta kira waya tace' kana kofar gida?

Daga can aka amsa da eh,
Tana fita daga babbam gida kuwa ta hango bakar mota,nufar wurinta tayi ta Shiga Baya,
Yace' ina muka nufa?

Tace'
ADAMAWA
Da sassafe yayi shiryansa tsab ya fice agidan beyiwa kowa sallama bare ya su San ya tafi, hanyar Jigawa ya dauka,bashi ya isa ba sai goma sabida irin tafiyar da yake yi address din da ya rubuta yake bi har ya karaso wurin, kana gana zakasan company ne karami don ko Rabin Wanda ya siya beyi ba,
Knocking yayi mai gadi ya fito,sai da suka gaisa,
yace' don Allah shugaban wannan company din nake nema,
Mai gadi yace' to kaga de yau lahadi bazaka Sami kowa ba,
Yace' to ko Zan iya samun sa a gida?

Ehh zaka iya, samunsa Baya zuwa ko ina idan na uzuri ne ya taso ba,
Yace' am ina ne gidan nasa?

G9 zaka je,
Ai Bansan G9 din ba,ni bako ne,
To kuma kaga bakowa anan kusa da sai nasa a raka Ka,amma Ka jira kadan wanda zai karbeni zaizo sai mu tafi in nuna maka,
To shikenan nagode badamuwa Bana jira din,
Basu wani jima ba dayawa wani yazo ya karbeshi, suka tafi,tafiya suke Yana nuna masa hanya har suka isa kofar gidan nan sa,sai da suka fita sannan mai gadi yace' to ga gidan nasa,ni na wuce,
Kudi ya Ciro ya bashi ya kuma yimasa godiya,
Karasawa kofar gidan yayi tare da knocking,Jin shiru yasa ya karayin wani namma de shiru karawa yayi sannan yaji ance waye?

Shi besa ba da wani waye ba,hasalima yasaba kawai door bell zai Danna yazo a bude,
Amma wani waye?

Shiru yayi don besan mezai ce ba,
Zuwa tayi ta bude masa, yace' mai gidan nan?

Eh Yana nan,
Kice yayi bako,
Ta koma bata jima ta dawo tace' ance Ka shigo,ita ke masa jagora har cikin parlourn sannan taje ta kawo masa drinks da snacks, duda da safe ne.

Wani mutum yane ya fito kamili babba dashi, wuri ya samu ya zauna suka gaisa sai kuma sukayi shiru,
mutumin yace' ban shaida kaba,
Binaif yace' ai baka sanni ba, amma wala'allah idan na Baka tambaya zaka iya tambaya hadina da komawa waye,
Mutumin yace' wannan wacce irin tambaya ce haka?

Murmushi kawai Binaif yayi,
yace' game da companyn ka, bayan Kai waye shugaban Ka?

Sosai mamaki ya bayyana a Saman fuskar mutumin nan, yace' Kai waye din Muhammad ne?

Fadada murmushin sa yayi yace' Sirikinsa ne, nasan daman tambayar Kenan,
Yace' siriki?

Kai yaro Muhammad daga har 'ya'yan sa guda biyu da matar sa sun rasu, da dansa kace min
ne ma Zan yarda,
Binaif kamar yarda na fada maka ni sirikin sane kuma Ka yarda dani, 'yar sa nake aure Ummusalma koba ita bace?

Sosai mamaki ya lullubi mutumin yace' 'yarsa?

Bata mutu ba?

Tana ina?

Ina take?

Yace' bata mutuba,Abu daya nake so da Kai shine Ka fadamin Kai waye din shine?

Aboki ?

Dan uwa?

Kode wani Abu haka?

Numfashi mutumin yace' sunana Munir Yakubu, Dan asalin garin Gumel mahaifiya ta rasu tun ina yaro Babana Shi ya rikeni dukda mitar yayi aure da ake masa Amma yayi biris da zancen kuwa, Shi yaciga da Kula Dani har na Kaiga nagama Nce dina,Amma babu aikinyi a lokacin Babana ya fara ciwo kafa dayake Nika yake yi sai naciga dayi sabida aikin da za'a masa
Gashi kuma injin bayayi kullum Yana cikin gyara wayanci shike cinye mana kudin,kawai na saidashi na tafi Lagos don samu kudi,sai dai kuma kasan cewata sabon Shiga aka sa cemun kudi ga babu wurin kwana ga yunwa da wahala zafi komai ya hade min,nasami gafen titi na zauna kwatsam wata mota tazo ta bigeni tayi gaba Allah ya rufa asiri ma banji ciwo ba sai dai naji jiki,jiki ya kama ciwo Bansan meke damuna ba, idan nace zanyi dako kafin na dauka har andauke anyi gaba,ga ciwon kafa Ashe nayi tagade ruwan da zan shama aiki ne, ina kwance a gefen titi awannan lokacin mutuwa kawai nake bawa kaina,sai ga Ya
Muhammad da Matar sa Sunzo sun taimaka min sun kaini asibiti bayan na warke suka tambayeni inda nake na fada masu na kuma Basu labari,shine ya biya kudin aikin sannan yace zai Samar min aiki a kusa da gida don nake zuwa ina Kula da mahaifina,banyi musu ba na yarda bayan anyiwa Babana aiki yazo da kanshi ya daukeni ya kawo ni nan garin ya nuna min komai da komai da shagunan sa da inda yake da Zama gidajen sa komai nashi wai gudun bacin Rana, koda na tambaya shi Baya tsoran na cuce Shi?
Chapter 45 · 0% Book details