← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 108

Sashe 89

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mus'ab tuni ya gane,
yace''
ya fita, ina gani shine ma ya Kira Daddy"
Tace'' to Kira min Shi, yunwa nake ji"
Tashi yayi ya fita, yana fita ya ganshi shida Amina a zaune suna hira, da'alama kuma ita keyin Rabin maganar, tafiya yayi zaije wuri Shi yaga Mas'ud yazo ya wuce Shi da gudu ya isa, Yana zuwa,
yace'' bb matar ka yunwa take ji fah, kuma naji ma Daddy yace kazo Ka dauke ta Ka maida ta gida Shi zai tafi da su Inni gida tare da mu"
Mus'ab ya karaso yace'' sai kace Kai aka aika"
Girgiza kai ya tashi ya tafi, Amina tace'' ba magana ko?"
Sai nan suka lura da ita, Mas'ud yace'' kut, twinny wallahi na canza wannan ce twinny na,Kai daman kafi kama da aljana"
Taske keyarsa yayi yace'' with respect har yanzu baka samu matar Ka ba"
Zama Mas'ud yayi yace'' Allah ya bawa yaya Mus'ab hakuri"
Tafiya yayi ya barshi a wurin, ya Shiga ciki,
A kusan tare suka Shiga shida Binaif, kansa a sunkuye ya Shiga babu Wanda ya lura dashi sai Baffa, wurin ta yaje ya zaune,
yace'' me zaki ci"
Tace'' kaje dakin da aka kwantar da uncle dakin na goma na ajje fruit Ka dauko min..."
Sai kuka tayi shiru, tuna wani Abu da tayi, kallan drip dinta tayi taga ya saura kadan,
tace'' cire min"
Beyi musu ba, ya cire Mata, ta tashi zaune ta kalli mus'ab tace'' a Abuja wanne unguwa Ka zauna"
Yace'' gidan Daddy dake garki"
Murmushi tayi Mai kyau sannan tace" bb muje dakin yaya"
Kama ta yayi suka tashi, sannan suka fita, dakin suka je, Anna suka ga su ummu suna zaune Shi Baya nan, Zama tayi ummu ta kawo Mata Tasha ta dayawa sai da taji garau, tayi sallah sannan,
tace'' Ina mus'ab?

"
Yusuf yace'' bezo ba, iya bb ne kuma shima ya tafi,kina sallah"
Tashi tayi ta hango su, su hudu har Binaif Shi Yana tsaye Yana waya sukuma a zaune Amina da Mas'ud sai zuba ake shikuma Mus'ab Yana binsu da Ido, wuce tayi Basu lura da ita ba, ta wuce male ward har wurin gadan su Muja,
Muja na ganin ta, ta taso ta tarbe ta, suka karasa, sai da ta zauna,
tace'' kuma Baki tsaya ba"
Muja tace'' Ina Zan tsaya kuwa"
Murmushi kawai Tama ta tace'' to shikenan,daman nazo duba ki ne, numbern ki fah"
Muja tace'' Banda waya sai dai numbern Abba na"
" Kash,kinga ban taho da waya ta ba"
" To muje mana, sai na sa maki,wayar Abban ma ma charge bare nace ki saka min Zan Kira ki"
Hakan ya mata dadi, fita suka yi daman ya samu yayi bacci, har suka zo wurin zasu wuce Basu lura da ita ba, a saitin wurin ta tsaya,
tace'' Glip Dan ban Aran wayar Ka"
Dayake amfani yake da ita ya kawai ya miko Mata ta, juyar da Kan da zaiyi kusa sukayi four eyes da Muja, Dan murmushi tayi
tace'' Ina wuni?"
Mas'ud yace'' lafiya qalau"
Shidai be amsa ba,Amma Yana kallan ta, ita kuwa,
tace'' kamar na Sanka,Amma na manta a'ina?

"
Janye idan sa yayi, beyi Mata magana Dan besan me zai ce ba,
Ummusalma tace'' zaki iya sanin sa, Dan ya zauna a unguwar ku, a Abuja, haka yake magana bata dame Shi"
Murmushi tayi tace'' Kannan kine?"
Mas'ud ta kalla yarda ya wani wurgo mata harara a fakai ce, tasan da namiji ne yayi maganar sai ya maida masa da martani Amma sanin macece yasa yayi shiru sai boyayyiyar harara, murmushi tayi tace'' a'a yayu na ne, wannan ce kawai kauwata"
Ya fada tana nuna Amina,
Muja tace'' Allah sarki, sannu"
Amina tace'' ina
wuni,yi hakuri bamu gaisa ba"
"Bakomai"
Mika Mata tayi wayar tace'' Samin"
Amsa tayi tasa mata sannan tayi musu sallama ta wuce...

By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt
A BAKIN WAWA
_Akanji magana_
Daki suka koma ita da Binaif suna Shiga sai ga Anty safiya tazo Dan su tafi gaba Daya ganin dakin ya cika da bakin fuska yasa ta gaida kowa suka gaisa,
Daddy yace'' ya kamata a samu aje a tafi haka nan ga Shi ana neman ayi la'asar"
Baba yace''gaskiya Kam, ya kamata a tafi"
Inni da Baffa dakin su suka koma sannan Baffa yaje yaga likita daga nan aka Basu takardar sallama, Baffa ne ya Kira Amina a wayar ta, tazo ta tattare kayan su sannan suka fito, kowa ya fito inda sukayi parking,
Daddy ya kalli Binaif yace'' Ka kaisu gida daga nan sai ku wuce gida Ku kuma"
Hakan akayi suka shiga, Baffa yashiga gaba su kuma a Baya, Su yusuf daman ba tare suka zo ba, kuma Basu San abinda ya faru ba sunma wuce tun da Dade wa, kowa Shiga yayi ya tafi,
Baffa na nuna masa hanya har suka je, unguwar su da bacirawa can ciki ce, har kofar gidan su, suka je, dukan su suka Shiga bayan yayi Parkinson, gida ne Karami na Mai kyau parlour Daya da two bedroom sai kitchen a waje, da 'yar bishaya Mai a tsakar gidan, Shiga sukayi suka zauna, Baffa da Binaif sukuma daki suka Shiga dan Inni ta huta tana bukatar hutu dukda tana cikin farin ciki,
Binaif yace'' Baffa kayi hakuri da duk abinda nayi maka,bamma san da bakin da zan Baka hakuri ba, ina Mai Baka hakuri nasan bai Zama lalle Ka yafe min ba, kuma zaka dauke marar..."
Baffa ne ya katse Shi ta hanyar cewa'' Baka da laifi, tabbas nine Mai laifi, kasan ma dadi naji?

Kowanne uba yana so ya aurar da 'yar sa ga mijin da yake so, naji dadi sosai, wannan ya nuna kana son ta,ya nuna zaka iya kare ta, koda kuwa babu mu, daman babu mu din Ka aure ta kuma Ka zauna da ita,bansan me Zan maka ba, Yana suna Ka?"
Binaif yace'' Abdulshakur ko Binaif"
Murmushi Baffa yayi ya taso daga wurin sa, ya zauna a kujeran dake Binaif ya jingina, ya shafi kansa cikin kulawa, yace'' Kai ba siriki bane, kaji ko?

Kai yarona ne, baka da banbanci da su, bansan sirikin nan kaji ko?"
Binaif ji yayi wata nutsuwa na Shigar Shi, gashi yarda yake shafa masa Kai,irin rarrashi a hankali ya zame ya kwanta a cinyar Baffa,
Baffa yace'' tell me more about you,and my children, mamanka ta rasu ne"
Yace'' Taya akayi san haka?"
" I can see, kayi rashin Uwa, kana son uwa, Naga wannan acikin idan Ka"
Kwalla ce ta taru da idan sa yace'' Baffa bansan ta ba,bansan sunan ta ba,ban taba ganin ta ba, but she's gone, ta tafi, I don't know ko tafiya tayi, ko kuma mutuwa tayi, but she's gone forever"
Shiru sukayi babu Wanda yayi magana, Saida ya natsu sannan,
yace'' Mas'ud ya fiye tsoka, Mus'ab kuma ya fiye hakuri"
Murmushi Baffa yayi yace'' Mas'ud tun Yana yaro haka yake,ga Dan Karen tsoro, shiyasa kullum suna fada da Ummusalma basa jituwa sam ita tsokana shima tsokana ga San girma me hali Baya fasa wa"
Murmushi Binaif yayi yace'' har yanzu basa jituwa, ga rashin hakuri haka itama"
Jin ana Kiran sallah yasa su tashi Dan gabatar da sallah, a waje sukayi alwala sannan suka tafi.

A daki kuwa Ummusalma a gata ga Inni haka suka kwanta, tana kallan tana
tambayar ta wasu abubuwan na rayuwar ta, a haka bacci yayi gaba da Inni ita kuwa kasa baccin tayi dan yunwa take ji, ji take kamar tayi amai Dan tsabar yunwa amma sai taji bakin ta yayi nauyi tace tana Jin yunwa a bata abinci, gashi Amina tana so tayi mata magana bata, bata dama ba bare ta saurare ta, a hankali ta tashi ta fita alwala tayi tayi sallah a parlour ta idar da sallah kenan,
Amina tace'' Salma"
Banza tayi mata, sai ma jingina tayi da kujera ta rufe ido, tana cigaba da tasbihin ta,
Amina tace'' Haba salma maganar ne bazaki min ba?"
Ummusalma tace'' na'am Neena, shikenan?"
" Ya kamata ace at least ki fada min abinda na maki "
"Mtsww"
Tashi tayi ta kwanta Akan kujera, zuciyar ta ta cigaba da tashi, su Baffa ne suka dawo gani su tayi tare su Mus'ab,
Mas'ud Yana shigowa ya zauna a kusa da Ummusalma,
yace'' dalla can tashi, ki koma gidan Ku,kin wani zo kin zauna mana a gida kowa ya tafi gidan su idan ba tsoro ba"
Baffa yace'' ai itama gidan su ne,sai dai Kai Ka tafi gidan Ku"
Binaif da ya zauna a wurin Kan ta,kamshin turaren kawai taji tasan shine, bude Ido tayi, tace masa "yunwa nake ji"
Dayake kallan ta yake yasan me ta fada, haka ma Amina, tashi tayi ta fita, ta daura abinci sannan ta fice,
Mus'ab yace'' Yawwa Baffa fada masa nan gidan mune"
Baffa yace'' Mas'ud bazaka taba girma ba,Naga ranar da Zaka girma Kai kuwa"
Binaif yace'' Ai Baffa ya kusa girma fa, shida zai yi aure nan da wata biyar?

Baffa yace'' ikon Allah, amma naji dadin wannan maganar sosai Mus'ab fa"
Mas'ud sunne kai akayi irin kunyar nan, besan kunyar tasa dariya take bawa mutane ba, abinka da ba'a Saba ba,
Baffa yace'' mus'ab fa"
Mus'ab sosai kai, yayi ya kalli Ummusalma ko zata yi magana,ita kuwa dauke Kan ta tayi, irin ba ruwan ta Kenan, sosai keya yayi,
yace'' inaga tare za'a hada"
Mas'ud yace'' inji uban wa?
Chapter 89 · 0% Book details