← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 108

Sashe 60

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Make kafada tayi tace' a,a anan zanci,
Girgiza Kai yayi ya hawo gadan yace' to jeki wanke bakinki,
Tura Baki tayi gaba itafa yunwa takeji, ganin bata da niyya yasa Shi ya daga ya kaita toilet da kansa ya wanke Mata ita sai layi fuskar da ya wanke Matane yasa ma baccin Dan sakinta,dawowa sukayi ya zaunar ta a kasa ya Shiga Baya kazar da Yogurt tana ci har ya koshi,bawani koshi can sosai ba bacci ne kawai fal idanta kuma yasan duk gajiya ce komawa tayi ta kwanta shima beci wani sosai ba ya tashi ya mayar ya dawo suka kwanta,sai anan bacci ya dauke Shi.

Da Asuba ta Riga Shi tashi,jinta a jikin mutum yasa ta kalli fuskar sa da kyau bata ganin sosai, kasancewar babu haske sosai,a hankali ta zare hannunsa Daya rungume ta dashi ta kunna bedside lamp ta juyo tana kallami zata sauka ta tuna da lifata ce fa ajikinta to waya cire Mata?

A hankali kuma ta tuna sanda yake bata abinci, juyowa tayi ta kalleshe dakyau sannan ta tashi ta shiga tayi alwala, ta fito kuma sai ta Rasa yarda zata tashe Shi,kusa dashi taje ta sunkuyo har ta sa hannu zata bubbuga pillown sa sai kuma ta tuno indai zai tasheta to iska yake hura Mata sanda suna gidan Umma, Amma ai ba barinta yake kallo ba gashi an kusa a Kira a Shiga sallah, kamar yasan me take nufi sai gashi ya juyo barinda take, daidai fuskar Shi taje sai kuma ta kasa tasa hannu ta fara shafa masa fuska har ya bude Ido ya saukesu akanta ,ita dai tasan tana shafa masa fuska Amma bata San tunanin da take ba harda su murmushinta mai tsada take aikawa dashi,
Shima murmushi ya mayar Mata ya rike hannun Yana tashi zaune,
yace' duk acikin shaukin ne?

Har an Shiga sallah bakiji ba?

Ai bashiri ta tashi tana sunne Kai,Shi dariya ma take bashi idan tayi wani abun, tashi yayi yaje yayi alwala ya dawo har lokacin batayi sallah ba tana neman Hijabi bata gani ba,shine ya dauko Mata sannan ya jasu sallahr sun jima suna Azkhar har gari ya fara wayewa sannan,ya tashi zai kwanta,
Tace' Ina kwana?

Saida ya kwanta, yace' zo,
Ba musu ta tashi taje kusa dashi ta zauna,jawota yayi,tare da cire Mata Hijabin, suka kwanta tare Yana shafa kanta,
yace' ina kwana kawai?

Ba mi amor ba komai?

Ina laifin ma kice dear shine ba laifi,Amma kice ina kwana kawai ai sai nazaci ma ba Dani kike ba,
Shiru tayi batayi magana ba,batasan korafi da Mita, tasan idan tayi magana to yanzu zasu fara shikuwa bazak gaji ba ita kuma tanasan tayi bacci, matseta yayi hakan yasa,
tace' to kayi hakuri, bazan karaba,
Yace' good girl,
Tace' Mai gida ina kwana?

Takaici ne ya isheshi kawai ya rufe Ido irin nayi baccin nan,
Murmushi tayi ganin be amsa ba,tasan maganin Shi idan ya takura Mata,itama rufe idan tayi sai bacci.

Karfe takwas ta tashi sabida tayi bacci ya isheta sabinin Shi da beyi na kirki ba,baccin sa yake hankali kwance, wanka tayi tazo gaban mirror ta shafa mai da kayan kamshi yau de an murza powder ansa kwalli sai lipgloss data sa, wardrobe ta bude donta sa Kaya mezata gani,tarin atampha, lace,shadda, material, English wears kawai aciki babu doguwar Riga koda kuwa ta atampa ce Kota wani abun,ta duba ta duba Amma babu tasan wanna duk Shirin Anty safiya ne, gashi duk Wanda take daukowa zanine,dakyar ta samu Wata atampa Mai kyau gashi taji dinki kuma skirt ne, hakan yasa ta sa ta, taje tayi daurinta daidai yarda zata iya, tayi kyau sosai abinta mayafi ta dauka ta ajje Akan gado sannan ta fita parlour, parlourn ba karamin kyau yayi Mata ba,Shi bacan Katan nan ba bakuma karami ba,kujeru set biyu ne a ciki Amma dayan daga can wurin dining yake, dining din kuma daga wurin kitchen yake idan Zama Shiga ma har da San step din da Zaka bi ta hau befi shida ba zuwa biyar, ba abinda zatace da Daddy sai Allah yasa Ka alkhairi ta kuma bishi da addu'a kitchen tashiga shima ba karamin kyau yamata ba,irin rustic kitchen din nan ne, ga table a tsakiya Mai kujeru hudu Dan karamin m dashi sai kofa data gani tasan store ne, sai wani glass data hango daga gaban kujerun zuwa tayi taga Ashe kofa ce ma, itama komai ya Mata kyau, cupboards din ta duba ta dauko tukunys ta dafa ruwan zafi kawai ta Nemo flask tasa ta Kai dining.

Dakin ta dawo ganin baya nan yasata gyara shimfadar ta kuma fita parlour, Ganin su Mas'ud yasata Kara sa ta zauna a kujera, ta kalli mas'ud,
tace' meye za'a fa zuwa wa mutene gida da safe?

Yace' lalle ma yarinya nan ba gaisuwa ba komai sai wani anzo maku gida?

Mus'ab yace' Anty mu ina kwana?

Murmushi tayi tace' lafiya qalau glip Ka tashi lafiya?

Yace' lafiya qalau,
Mas'ud takaicine ya ishe shi,ya kasa magana, sai can kuma,
yace' yarinyar Kanwar tawa Zan gaidar?

Yarinyar da aka haifeta agaba na?

God forbid,
Banza tayi da Shi bata tanka masa ba, yace' kurma yunwa nake ji fah,tun jiya rabona da abinci,
Zaiyi magana Binaif ya fito, gaisawa suka karayi duksa sun gaida Shi daya bude musu kofa, akusa da ita ya zauna,
yace' ina abincin da kuka kawo?

Mas'ud yace' bacin matarka tace bazata bamu ba?

Wai muma muje muyi auren haka tace,
Binaif yace' ohhh wato Zama dakai zaisa ta koyi rashin kunya ko?

Daure fuska yayi yace' waini waini menayi ne?

Daga nace Abu daga nayi magana sai ace Banda kunya narasa menayi, kuma wallahi ganewa ce bakwayi fav bro yafini rashin kunya nesa ba kusa ba, kawai de kawai de idan an tsani mutum an tsana, daman na gane ai, Sam ba'a so.....

Kallan data aika masa dashi na irinka dameni fah, shiru yayi Yana kumbara baki, Binaif kuwa kawai Kai ya girgiza Baya ganin akwai ranar da zai dena, da kanshi ya tashi ya je ya dauko kayan abincin ya dawo dasu parlour yaje ya dauko plate da cups ya dawo, Mas'ud ne ya hadawa kowa tea ya sannan ya zuba a plate daya ajajje a tsakiya kowa ya sauko suka fara ci sai dai daga ita har Mas'ud babu Wanda yacj Finkaso ne kuma basa ci,Shi idan yaci to make zaiyi itama haka amai take, shiyasa kawai suka sauko suke kallansu suna Shan tea dinsu,
Mas'ud yace' Meyasa bakya ci?

Kai meyasa Baka ci?

Ni ai Bana ci,
Kefa?

Cine bazanyi ba,
Ka nida na tambayeki ma, nifa na fara maki tambaya aka kika maido min kuma wai na Baki amsa, mtsww ni din nan ma de wallahi,
Binaif yace' bakya cine?

Daga masa Kai kurum tayi,
Yace' Meyasa?

Yatsine fuska tayi tace' idan naci Amai nake,
.

Mus'ab yace' shima twinny amai yake idan yaci,
Binaif yace' to yanzu mezaki ci?

Tace' bakomai kamshin sa kadai ma yagama cika min ciki ko me naci idan ba tea ba to amarya dashi zanyi,sai zuwa can anjima tukunna,
Mas'ud yace' keda bake bace
aka haifemu tare ba bakomai ba,amma bakya cin abinda Bana ci,
Mus'ab yace' aikuwa komai bakwa ci to dayan ma baya ci,
Mas'ud yace' ai a London nagani wai yarinyar bb a London munje zamu sai fruit memakon tace ba komai take sha ba tayi shiru ta kyale aka siya komai wai in fada maka sai da muka zo aka bata nata wai kasan kawai me take ci?

Girgiza Kai Binaif yayi alamar a,a, yace' hmmm kawai Apple da Pineapple sai orange da Mango kawai ta dauka, wai baga sha idan ba leman su akayi ba,Kai kaji takaici gashi Nima ba sha nake ba sai anyi lemon su, Kai kaji takaici
kuma wai ta dauka barma su a wurin imagine ta kyauta ?

Dariya Binaif yayi yace' to mene zaka damu bayan kasan halinta?

Yace' hmm bb bazaka gane ba yarinyar nan ko?

Ni dayane maganinta kuma ba mantawa nayi ba har yanzu ina binki bashin Marin da kika zabga mini,ban manta ba,
Daure fuska tayi, tace' har yau ma idan Baka dena abinda kake ba wallahi ina daf Dana Kara maka wani, Kai kasan haushin da kuke Bani?

Wai mace ta mareku kutsaya sai kace sandunan da aka daure, hmmm,
Mus'ab yace' lallene dan Baki tashi a yarda Muka taso bane, ba tun muna yaro fah,muke ganin sharrin Mata Kala Kala kwanne da irin tashi,mace kanta bala'i ce, daman ba mune a matsayin ki,
Murmushin takaici Mas'ud yayi yace' gwara mu sau dubu Akan ita, Gwara mu mun taso Bamu da gata kuma munsan hakan munsan matsayin da muka ajje kammu Amma ita fa,kasan cin amana kuwa?

Kasan rashin tarbiya abinda yake haifarwa?

Bazaka gane ba,inaga ko?

Murmushi tayi tace' worry not please!

Binaif yace' Meyasa tasaka a blacklist?

Yace' Nima bansan sani ba,kawai gani Nayi tasani,
Ummusalma tace' tun yaushe Kenan?

Yace' ehh ba'a jima ba, kusan kwana biyu Kenan, kuma yau nake so na tafi gobe zamuyi Baki daga Chicago,
Tace' ba ita tasa Kaba,ca akace tasaka, nasan da wannan, Ka Kara kiranta, Amma ba wa'azi zaka cikata dashi ba,kaji ai?

Turo baki yayi yace' kinsan de ba hira na iya ba ai,
Zaka koya ne ai,
Naji kace Baki wanne Baki zakuyi?

Mus'ab yace' muma za'ayi wannan bakin Amma
mu daga Ghana ne,
Tace' ok fada maku akayi?

Ehh sun fada,
Tace' nasan ba daku za'ayi ba,Amma dole ku San yarda kukayi kukejin duk wani meeting dinsu, daga nan sai ku fara dauke documents masu amfani kafin nan,duk abinda zakuyi fa sai kun tabbata Baku bar shaida ko guda daya bace ba, kunji?

Mus'ab yace' yafi ji da companyn Abuja nan
Mas'ud yace' Baya zuwa sai sati sati daga Friday sai Friday nikuma wannan Friday din na dawo gida, shima ji nayi a wurin ma'aikatan sai dai Mai Kula da Shi kawai,
Tace' Friday kuma?

To mezaije yayi Friday Bama yaje Monday ba?

Dole akwai wani Abu Ka Kara bincikawa,
Binaif yace' ku dawo next week zanyi bako,
Kallan juna sukayi irin really din nan?

Harara ya watsa masu yace' bafa nasan gulma,
Mas'ud yace ni ba wannan ba,a fada min me Zan fadawa
wancan loron?
Chapter 60 · 0% Book details