Sashe 32
A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda ya dawo gida bai shiga wurinta ba,wanka kawai yayi yasa kaya marasa nauyi ya kwanta yunwa yake ji beci komai ba tunda safe gashi yanzu ana nema ayi la'asar,shafa kansa yayi Mai cike da suma sannan ya shafo cikinsa, ya lumshe ido yana tuno Anty ummi bata taba barinsa da yunwa bare kuma tabarshi da damuwa, a fili ya furta" Allah ya jikanki Antynah.
Jawo jakar da ya fita yayi,don yayi wani abu ganin ya fara tunani dukda kansa dake ciwo amma haka ya daure ya fito da takardun cikin jakar tashi yayi zaune dakyau takardun company din da ta bashi yasa shi dauka, dubawa yayi yaga yama fi na company daya ta dauko masa, sannan kamar harda ma takardun fili da gidaje, dubawa yakeyi daya bayan daya sai dai kuma kowanne yana ganin signing din Ummu da yake rubutawa a jiki,amma idan ba lura kayi ba bazaka taba gani ba, sosai ya nutsu yana kara nazarin takardun,Yana cikin dubawa wata karamar paper ta fado a ninke take sai dai kamar harda wani dan jajaja a jikinta, warwarewa yayi ya bude, ganinta da yayi tana da tsawo papern ashe nadinne aka yi karami sannan kuma rubutune a jikinta dayawa sai dai rubutun bawai a tsare akayi shiba, nadeta yayi yarda take ya mayarta inda ya gani.
Jin sosai yunwa yake ji yasa shi tattarawa ya ajje a gefe guda ya fito, fridge ya buda ya ciro malt ya fito don nemawa kansa abinci, ta wurin dakinta ya zo wuce sai kuma ya dawo da baya azuciyar Shi yace"' kome take yi yanzu?,
Samun kansa yayi da bude windown ta kadan, tana kan katifa tana faman taje kanta, gashinta yana da cika dayawa don yama fi karfinta saidai yana da tsayi amma bawani can tsayi na'azo a gani ba, sai dai ace Masha Allah, tana sanye da t shirt sai zani da ta daura sai da yagama mata kallon tsab sannan kuma ya kawar da kansa,a zuciyar Shi yace'" haka kawai nayi ta kallanta ba muharrama taba ba komai ba" har yayi gaba yadawo yakuma lekata a fili yace' ashe fa kedin halali nace, yafada yana yar karamar dariya,ganin bakinta na motsi yasa shi kara gyara tsayuwa ya zuba mata na mujiya Yana kallo,
Ita kuwa sai fama take da kanta tana mita ita fa a duniya shiyasa ta tsana zubawa kanta ruwa,kwata kwata bataso shiyasa idan ta kulle shi bama ta Kara kulashi sai wani lokacin kuma,ta tsani tajar Kai itakam,mitar ta take zubawa ba kakkautawa ita kadai,bakinta ne kawai yake motsi, haka ta bar kan badan ya taju ba sai don ta gaji, ribbon tasa ta daure kan shima dakyar sai kuma ta kama tufkar tayi mata kitso, kwanciya tayi ta lumshe ido tare da sauke a jiyar zuciya saidai kuma data kwanta sai taga kamar inuwar mutum a windown ta, kara bude ido tayi ganin bakowa yasata rufe idan ta, knocking din da taji a kofar dakinta yasa ta bude idanta ta zubawa kofar ido,ita fa tagaji wannan kwanciyar ta mata dadi bakadan ba,ji tayi ansake knocking tare da cewa "'ko in shigo ne?
Ai batasan sanda tayi saurin janyo hijabi ba ta bude kofar ta kalleshi sai kuma ta rasa me zatace,ta sunkuyar da kanta kasa kawai hannunta daya ta rike kofa dashi dayan kuma tana wasa dashi, murmushi yayi,
yace' Azo aban abinci yunwa nake ji tun safe banci komai ba, amma baki damu dani ba,
Kumbura baki tayi,amma batayi magana ba don batasan me zatace ba,sai dai kuma azuciyar ta maganar take,ita kadai tasan metake fada,kamar ya San metake fada
yace' aww zagina kike ?
Allah ya sauwake ki zubo min ko?
Kuma yazo ya dameki kina hutawa har da min Allah ya isa ko?
Zaro ido tayi Jin wannan lamari, batayi kuma magana ba kawai ido ta zuba masa,dafe Kai yayi
yace' kuma tsorata ni dazakiyi da wannan idan naki Masha Allah dashi, don kinga ni bani da su ko?
Shikenan bakomai nasan inda zani, shikenan wata rana zaki karasani shikenan ni daman babu mai dona babu mai kulada ni bari na tafi bakomai idan na mutu ki daure kyace Allah yaji kanshi ko sau daya kinji,
Yafada yana neman juyawa,
Itakam tasan idan tana tare dashi to komai nata kuncewa yakeyi,ganin ya juya zai tafi har ya sauka daga Kan barandar zai sha kwana yasa,
tace' Ka tsaya,
Wani irin dadi yaji dabata tsaidashi ba dabai san sai yaushe zaici abinci,dukda yaji dadi kuma har kasan zuciyar shi yakeji,amma a zahira sai yayi kalan tausayi ya juyo, koda ya juyo ma bata nan hakan yasa shi dan yin tsalle ya dawo ya dauko kujera ya zauna, harda suyin tagumi ji yayi an Kira sallah, lokacin ta fito da abinci a plate tare da lemo sai anan ma ya tuna Ashe fa ya fito da malt a hannunsa ko ina take oho, mika masa tayi abinci yaki karba,kallansa tayi,
tace' idan baka so na mayar,
Kar yayi biyun babu ukun zero yasa shi saurin karba ta mikasa lemun hannunta ya amsa,bata jira cewar sa ba ta wuce daki ta rufe sannan ta jingina da kofar tana sauke ajiyar zuciya saida ta dawo normal sannan ta tashi tayi alwala Jin za'a shiga sallah.
Shikuma Allah ya gani ba duka lemo yake sha ba don shi wannan ma basan shi yake ba,tashi yayi wai da zummar yaje ya dauko malt dinsa sai dai kuma ganin gwangwaninta yasa shi tsayawa irin yaushe na shanye, zuciyar shi ta bashi amsa da kana kallanta, shafa kanshi yayi ya koma ya fara zira abinci lemon ya bude ya fara sha sai kuma yaji lemon da dadi haka ya cinye tas ya mayar da plate din,sai dai kuma yana shiga kitchen yaga Hajiya ko kallanta baiyi ba ya ajiye plate din ya fito hana jinta tana tambayar wanda ya debo masa abinci a dining ko kallanta baiyi ba bare ya bata amsa,itama haka ta gama masifarta ta fita......
By: '''Hijjart Abdoul'''
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
Tana kwance a dakinta ta fara jiyo hayaniya tun daga waje,bata yi yunkunrin tashi ba tana nan akwance har ta ji an shigo parlourn, ta window ta tashi ta leka,wata tshohuwa tagani da Daddy sai kuma Binaif Yana binta abaya, ji tayi tshohuwar nacewa
" Naji labarin akwai kurma a gidan nan, kuma ai aiki take Akan me zaku marta kurma fa akace to wallahi yau zata bar gidan nan yau yau din nan bazan laminta ba kurma a gidan nan,inaaa gidan 'da na?
Kurma?
Binaif ji yayi gababsa ya Fadi lalle ma matar wai batasan yanzu matar sa bace kome?
Zaiyi magana ta katseshi dacewa
" Yimin shiru yau zan korata kowa ma ya huta, kurma fa,
Ummusalma hantar cikinta ce ta kada Jin abinda take fada,daman yau tun da ta tashi takejin gabanta na faduwa Ashe wannan matar ce zata koreta, tunanin fara hada kayanta tayi,hakan yasa cikin sauri tafara shirya kayanta tasaka muhimman abubuwanta akasan bakkonta, tana shirya,
Hajiya da tuntuni tana parlour jin wannan batu na Umma yasata Jin wani dadi daman ko bata koreta ba tana da niyyar koranta don ta lura wannan yarinyar akwai sa ido baya ga haka kuma bata jin zata iya barinta saboda gudun tuna mata asiri, shiyasa take yawan koren yan aikinta cikin sauki abinta, wannan ma kuwa sao gashi Umma zata koreta, murmushi ne ya kubce mata,tayi Maza ta mayar Shi gudun magana,
Anty ce ta fito da sauran yaran Jin hayaniya,
Anty tace' Umma ina wuni,
Harda tsugunnawa irin biyayyar nan,
Umma da har yanzu bata zauna ba tana dagare da sandar ta ga glashinta,ta kalleta ta tabe Baki,
tace' hmmm ai wuni ya ruga da gudu, tunda yanzu magariba zamu shiga, ai nazaci gaisuwar ma kun manta yarda akeyi tunda ba'a San hanyar gidana ba,
Ganin Saima da tayi yasata rabka uban salati,
tace' yanzu daman wannan yarinyar batayi aure ba ??
Wannan ai banbanci na da ita kadan ne, kawai ita ras take tafiya nikuma ina dogara kafata kuma bana gani da kyau,Amma babu wani banbanci taab lalle akwai kallo, idan ban manta ba kinkai shekara dai dai dai har ashirin da takwas
haka ne ko ba haka ba?
Hajiya
tace'.
Umma ashirin da bakwai ne ai,
" Kwana nawa ne za'a ce mana da takwas ji shashanci banza,daman kina nan kika barni a parlourn ko tayin Zama ba'a min ba??
Saima tace' naji kina zancen korar mana mai aiki,gaskiya bazamu lamunta ato ke zakiyi mana aiki ne ko me?
Daddy ne ya daka Mata wata tsawa yace' mahaifiyar tawa kike fadawa haka,
Ya tafi gadan gadan zai buge Umma,
tace' a,a saurara bashi ya kawo ni nan ba, yanzu abin da za'ayi shine Zan Kori mai aiki idan na koreta kuma kune zaku keyin komai da komai idan kuma kai,ta kalli Daddy, Baka da 'ya'yanka sunayi ba to kana nufin kace minne bana da martaba mana da kima Bana da daraja a wurinka,Zan kuma sa ake bincika min,Naga karshen rashin kunya,kuma kuna Kara fadar magana Zan bullo wani Abu,ko na dawo Zama a gidan nan fakat,
Dame magana?
Shiru kake ji anyi babu Wanda yake
ko tari,sai yaran da suke kumbura Baki suna Mita iya ka zuciyar su, Binaif ta kalla,
tace' Kai kuma muje Ka nuna min dakin wancan kurmar na Gama aikina na fice,
Ja yayi ya tsaya ko kallanta beyi ba,
Tace' laa shikenan shima ya koyi kurmanci wuce nace ko sai na maka maka wannan sandar ne,
Ganin tana Shirin maka masa yasa Shi yin gaba yana gunguni, itama tana digisa kafa da
dogara sandarta ta bishi a baya, sai dai kafin tayi Rabin parlourn Shi yaje kitchen, aikuwa ta tsaya,
tace'.
Kai,Kai audushakuru, badakai nake ba?